Showing 60001 words to 63000 words out of 94796 words
Chapter 21 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf
...ya kamata ko don tsohuwar nan ka daina wannan abun, nasan wallahi duk
wannan damuwar Bilkisu ce... Ta kirani dazun ta fada mun duk abinda ya faru hada kukanta, ta
ce wallahi Babu abinda ke tsakanin ta da Suleiman, Anwar hakuri akeyi..... Please sadeeq ka
kyaleni..... Bazan kyaleka ba tunda kaima baka kyale kanka ba . Ta ce na baka hakuri....bazanyi ba tace na Kyaleta hakurin me zata bani?..... Har wannan
maganar ta fada mun ta ce kuskure ne bacin Rai yasa ta Fadi hakan..... Karya takeyi. Tana son
bani haushi ne don na Mari Suleiman...... Wannan zafin kishin naka bazai taba sany.... Kishin
ubanwa zanyi? Ya Mike ....ya kamoshi da karfi ya mayar.... Dan Allah kayi hakuri Anwar tunda
wallahi Koda mukayi ways kuka takeyi..... Kaine zata Kira taba hakuri ba ni ba? Tunda Kaine
tayi wa laifi ko?
Ikon Allah.... Tana tsoron kada ku Kara wani fadan ko kaki dauka ....... Ni zaka zo ka tsara
sadeeq???
Tsari??? Wallahi da gaske nake ita ce ta kirani....ya fiddo waya aljihu...duba ka gani ni na Kira
ko ita? Minti nawa ka gani?
Sai kawai yayi murmushi ko kadan bai San yayi ba.....ya zaro ido are you smiling?????
Ya Kai mishi duka ya goce..... Munafuki ni na dade da sanin wannan cutar taka Bilkisu ce....
Dan Allah fada mun tayi maganar cikin damuwa?
Wallahi kuka takeyi lokacin da muna maganar alamar abun ya dameta...... Mtseww ita ce ke
Sanya mu damuwa ai..... Iye? Sadeeq ya fada , ya banka mishi harara Yanzu dai kirata kace ta
kirani da kanta ta bani hakuri..... Message ya shiga wayar Anwar din karammm..... Ya dauko da
sauri jin alamar shigowar message din ta ne, ```I'm sorry very sorry please and I don't mean to hurt you```..... Sai kawai ya washe fuska....
Sadeeq Bilkisu ce....
Dan Allah Kira mun ita.... Suna Kira wayar a kashe. Abu kamar wasa kusan kwana uku duk
lokacin da aka Kira a kashe..... Shi kansa ya nema Amma bai Samu ba.... Hajiya dai taga
Anwar lokaci guda an warware har Yana fita tawon *Bike* da suke zuwa da marece Shi da
yaran governor. Ta warware amma duk ta Dan rame kadan..... Kullum tunanin Anwar.
Ta kasa bude wayar ta saboda tana Jin kunyar idan ya Kira me zata fada mishi bayan ita ce ta
bayar da hakuri?
Ta Kama lahadi suna gida duka har daddy, tana sanye da Riga da skirt na atamfa super
Holland Mai flower yellow dinkin ya bi jikinta, dogon hannu ne na *net* yellow duk atamfar
yayyabe flowers din suke da stones masu sheki kamar diamond.
Kanta ba kallabi ta maida gashinta baya ta kulle jelar kwance bisa bayanta..... Motsin get suka
jiyo. Daddy ya Mike da sauri ya daga labule....jibga jibgan motoci ne bakake suke shigowa.... Ya
ce innalillahi.. waye zai bamu surprise visit Haka?.. aka Fara fitowa yaga securities ko wane da
abin magana a kunnensa ya saki labule da sauri, ya kallesu inajin foreign affairs minister ne .....
Yayi ciki da sauri..
Suka tashi duk suka fada daki. Bilkisu ma ta shige nata.
Ya fito Yana gyara hula, falon kamshi kawai ke tashi na freshner ta ko Ina .... Ga A.C ta
gauraye ko'ina.... Ring bell ya Fara kadawa a hankali... Da daddy da kansa ya bude..... Ya bude
ido sosai cike da mamaki compound din gidan makil da securities suna tsaye ya Sha fararr
gizna dinkin falmara ce yasha aiki kansa cikin kube murjin kanawa...... *Waye in ba Anwar
ba*....... Anwar??? Daddy ya fada ....sukayi saurin zubewa shida Sadeeq daddy Barka da
yammaci...... Ku tashi .... ku tashi.... Ya kamo Anwar.... Ya riko hannun sa suka shigo ya
kwadawa mommy Kira ta fito da sauri.... Tayi turus ganin Anwar tare da washe Baki *Anwar a
gidan mu*? Sai sumke Kai yakeyi.... Daddy ya zauna suka gaisa sosai ya kasa hada ido dashi sai sadeeq
ne ke faman amsawa .
Tuni mommy tayi ciki tasa Rahina Mai aiki ta fara kawo musu abin Sha....
Daddy ya Mike ya haye sama.
Mommy ta shigo suka Kara gaisawa ta koma ciki.... ya kalli sadeeq Dan ubanka ka tamabaya
kace Ina Bilkisu?????...... Ya zaro ido ya Kai mishi duka......
Tana kwance ta kunna t.v din ta tana kallon wani Korea series *Innocent man*
Mommy ta shigo, ke kullum idan anyi Baki sai ance kizo ki gaishesu??? Tayi zumbur Ina da
niyya mommy ayi hakuri..... Ta galla Mata harara.... Tabbas kowa yasan surprise visit ya Bata
don me zata fada Mata.... Gara ta fita idanunta su gane Mata.
Ta dauki dan mitsilin gyale ta Yana a fuska bai ko rufe rufe rabin gashinta dake kwance a baya
ba..... Ta raba momyn ta wuce ..
Assalamu alai........ Ya dago da sauri sukayi tozali.... Sai kawai ta dafe kirji tayi baya da sauri
kamar wacce taji tsoro , mommy na tsaye bakin kofar dakinta Bata fita ba.... Ta ruga ta
makalkaleta..... Mommy da gaske Anwar ne?.........✍
*Zainab wowo*
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: *WA ZAI FURTA?*
1⃣9⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya
shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*RUKAYYA DAN BATTA I love you so much, remember this always*.
***************
*Federal University dutsinma*
........ Bani da wani feelings akan Anwar he always telling me we are just friends....just friends,
so Ina tunanin all this is because he likes me as that shine kawai....... Kada ki yaudari zuciyar ki
wallahi....... Kada ki rantse Anwar bashi da alkibla.
Idan Yana Sona let him say it idan Kuma bai *FURTA* ba I cannot waste my time and wait for
unknown..... Anwar din ne unknown...yes to me he is.
Abinda na tabbatar wa kaina shine ko naji Ina sonsa bazan taba yarda ya gane ba bare har
nace Zan fada mishi..nooo! Bana iya hakan.
Dai dai sunzo kofar gida, suka sauka Aisha ta biyota da sauri ganin ta yi saurin shigewa.......
Amma saboda Allah bakya jin kin Fara son sa?
Tayi murmushi.
Um?
Aisha forget about this.... Dan Allah ki amsa ni. Ko kadan bakya jin kina sonsa?...
So!, So!.... Ta maimaita.
Suka bude daki ta fada bisa katifa..... To Wai ya zanji idan na Fara sonsa?
Yawan tunanin sa, son ganinsa ko Jin muryar sa, komeye zai yi zakiga baya Baki haushi....
Koda kin fusata zakiji azuciya Baki Jin haushinsa, kishin sa...... Tayi Yar dariya.... Please Aisha
fita Kija mun daki barcin nan ya dameni.
Anya Bilkisu????
Anya meye?
To nidai Kisha oat din kada ki haddasa mun fitina anjima don Anwar sai ke wallahi.... Abeg go.!!
Zan fita but please Kisha.... Zan Sha Yanzu.
..........ya dafa kafadar sadeeq, kaji menstrual pain ke damun Bilkisu.... Ka dubi girman Allah
kada ka nuna Mata kasan haka zaka Bata kunya Anwar.
Ya tuntsure da dariya, to me yasa Bata boyewa Dr ba sai .....
Sai ubanwa? Shi ba Dr bane? Idan bata fada mishi rashin lafiyar ta ba zai San wane magani
zai bata ne?.... Ikon Allah, sadeeq akan Bilkisu wata Rana kilan ka dakan ko?
Tabbas, saboda ka takura Mata da yawa fa...... Meye abin takura anan.
Na dai fada ma, wallahi kada ka nuna kasan me ke damunta zata ji babu dadi... Kai nafi so ta
Saba da Hali na tun Yanz.... Maganar ta makale da alama yayi *Subul da baka*.
Hahahahahahahaha, finally..... Ya galla mishi harara finally what?
Nothing forget...ya fada Yana dariya.
*Sixtus* ya shigo kunji anyi closing school till further notice?????
Sadeeq ya kalleshi saboda me?
Corona virus...... Anwar yace hazbunallah are you serious?
Of course. Ya fada.
Anwar yayi saurin daukar waya ya Kira academic secretary.... Ya tabbatar mishi....
Ya kalleshi sadeeq is true.
Ya zaro ido Nawaoooo..... ya zanyi da yarinyar nan sadeeq??
Kamar ya?
Sai yayi shiru..... Ya kura mishi ido huh?
Mtsew ya buga tsoki ya fita waje.... Ya bishi da ido Yana murmushi, saboda ya gano inda
zancen sa ya dosa.
Abinda ya tayar mishi da hankali ganin student nata parking ana buga ma wadanda Basu
dawo ba akan su yi zamansu.....
Ya Kira number Bilkisu gashi tana ringing Amma Bata dauka ba, saboda barci ta sanyata silent
mode da alama ta sami yin barci.
Aisha ta Kyaleta har kusan karfe shidda ta wuni zungur tana barci... Ko da ta tashi wata
azababbiyar yunwa ce ta tashe ta, ga mamakin ta taga Yar cooler kusa da katifar, tana budawa
taga kuskus da miyar Dankalin turawa, tayi murmushi Allah sarki Aisha.
Sai da taci nayi nat! Sannan ta shiga wanka ..... Tana cikin saka riga Aisha ta shigo, kin tashi?
Ta fada tana murmushi, ta mayar mata da murmushin ta nuna Mata cooler da Baki tace Kinga
alama can..... Sai duk sukayi dariya.
Yunwa ta tasheni, wallahi kin taimaka..... Ai kin shaa barci, Ni kuwa nasan haka na farka naga
23 missed calls..... Tabbb.
Kin kirasu ko?
Mommy kadai na Kira sauran sa nemeni idan ya damesuuu......wayar ta Fara kugi duk suka kalli
juna.
Ta nufi wayar, ta Dan kalli Aisha *Anwar* ne.... Tayi Yar dariya Ina zuwa , ta juya tabar dakin....
Assalamu alaikum,
Kin tashi kenann....
Amsa sallama wajibi ne malam..... Wa'alaiki assalam. Sai me Kuma? Tayi Yar dariya, Ina wuni?
Ya kike ya jiki?
Alhamdulillah.
Cikin ya daina ciwo ko kina ji har Yanzu?
Bana ji da sauki sosai.
Zan kawo Miki maganin anjima kinji ko?
Ka bada akawo mun Mana ..... Saboda bakya son ganina?
Ba haka bane.
Haka ne Mana . Ba maganin kadai Zan kawo ba ai Ina son duba jikin ki ne...
Shikenan sai kazo.
Zaki iya dafan indomie din????
Innalillahi kaii Anwar fitina ne wallahi.... Nine fitina Bilkisu.????
Ta zaro ido kayi hakuri wallahi maganar zuci ce ta fito....... Da kyau Ashe a fili kike nunan ba
wani abu kina can kina zagina cikin Rai ko?
A'a wallahi....eh Mana. Gashi kin kirani da fitina....Dan Allah kayi hakuri.
Bazanyi ba.... Ya Fara fada kamar da gaske Yana son yaga how much she care about him ...
Kina da fuska biyu kenan Bilkisu? Watau a fuska kike nuna mun .....Anwar kayi hakuri....
Bazanyi ba nace.
Ba zakayi hakurin ba?
Gabansa ya Fadi ya tuna fadan su na baya..... Yayi saurin cewa zanyi amma ba Yanzu ba .
Sai yaushe?
Sai nazo anjima kin kalleni kin bani hakurin da gaske..... Tayi Yar dariya wannan na karya ne?
Da alama. Ya fada.
Shikenan sai kazo. Ya kake son indomie din?
Ki barshi kawai bana ci.
Dan Allah kayi hakuri..... Na ce ban hakura ba?
To ka fada mun yanda kake son indomie din kasan kowa da yanda yake son dahuwar
indomie.....kiyi mun yarda ki ke dafawa idan zakici... Karfe nawa zaka zo?
Eight, ya fada Yana Yar dariya ko nayi latti?
Ta Dan harari wayar kamar Yana kallonta kawai tayi shiru..
Kinyi shiru kina ta Duran zagi a zuciya ko?..... Kaiii Anwar.
Eh Mana.
A'a wallahi.
To fadan da kikayi shiru me zuciyarki ta saka Miki?
Ta kyalkyace da dariya kaiii nikam na bani ..... Yayi murmushi.
Ke Kam kin bani zuciyar ta saka Miki?
Ta zaro ido... A'a.
To fadan me ta ayyano Miki.?
Cewa tayi eight din is okay..... Yayi Yar dariya are you sure???
Yes. Ta fada tana ci gaba da murmushi.
Shikenan sai nazo. Kin hada kayanki ko?
Sai anjima.
Ya zaro ido kinji labarin Coronan ne?
Eh, mommy ta fada mun da mukayi waya.
Yaushe Zaki tafi?
To gani dai.... Ban gane gaki dai ba.
Ka bari idan kazo anjima zamuyi magana.... Shikenan sai nazo.
Ashe yayi waya yace a kawo mishi mota da maganin. Ko da aka kawo sai driver ya juya gata
haya yabar musu motar.
Katuwar mota kirar Jeep Amma Honda baka, Kai da kaga motar kasan lallai Mai ita *Don* ne.
Ta Sami Aisha daki, sai na jiki shiru.
Eh, wallahi Ina parking ne.
To Wai strike din ne ko Corona?
Duka fa, Anwar ya fada Miki?
Mommy, Ina tashi naga ta kira nabi Kiran,shine take fada mun, kema gobe Zaki wuce?
In shaa Allah, sai gida....Kare yasha taba. Duk suka bushe da dariya.
Ke sai jibi ko goben zaku wuce?...... Har na ma driver waya gobe in shaa Allah na fada mishi
ana gama sallar asubah zamu bar garin nan six da izinin Allah..... Anwar din fa, ba dashi zaku
tafi this Time ba????
Noooo, bama zai sani ba..... Gaskiya bazai ji dadi ba....kada Allah yasa yaji so what?
Ta kura Mata ido, wannan Jan ajin naki fa ya Fara yawa ki zauna idan zaren ya tsinke zakiyi wa
kanki.
Tayi murmushi, sai dai ya tsinke Amma ko Zan rasa Anwar bazan taba binsa kamar rakumi da
akala...... Yanzu me Zaki fada mishi? Ko kunyi maganar?
Bamuyi ba, sai anjima ya ce zaizo kawai Zan nuna mishi banyi deciding ba.... Bilkisu....
Aisha please mubar maganar Nan.
Dan Allah idan ya kawo Miki maganin ki dibar mun saboda Hafsa ( kanwarta ) ita ma the same
problem with you.
In shaa Allah.....ohhh Wai carton, komai Shi sai yayi hauka..... Ba hauka bane kulawa ce.
Gasu mufeeda can time dinsa kawai suke so Amma sun kasa samu..... Haka ne .
Ai shu'umi ne wallahi. Nake ga kamar duk abun Nan Yana Axergurating ne don ya Sami sauki
Yan mata.... Yanayi bil hakki da gaskiya.
Ko?
Allah kuwa.
Ta ce hmmm. Kawai.
Suleiman ya kirata, da sauri ta daga hello, Suleiman Ina wuni.
Bilkisu ya karfin jiki?
Na zo dazun har Kun fita da Anwar halan asibiti kuka je.
Eh wallahi. Jikin ma Alhamdulillah.
Mashaa Allah, sai Kika ji Kuma hutu ko?
Bari Kai dai.
Wallahi naji haushi da na Kara jinkirtawa Kinga da ban wahala a banza ba.
Ai kuwa. Ta fada.
Shikenan Allah ya say ya zamo alkhairi garemu duka ya kawo Mana karshen wannan fitina.
Amin ya Allah.
Sai nazo Allah ya Kara lafuya.....ta ce Ai.... Amma tuni ya latse Kiran Sam bai ji cewar zatayi
wata magana ba.
Ta kalli Aisha naji Yana sai yazo kada yazo gobe na tafi ko in Kuma kiransa Kinga babu dadi.
Kyaleshi goben sai ki Kira. Yanzu kada ya zargi wani abu kin San maza..... Eh Kuma fa. Ta
fada.
Ta dafa mishi indomie da kifin gwangwani, ta Sanya tarugu da albasa Mai lawashi sai kuwa
spices dinta.
Tayi masifar dadi sai kamshi ke tashi..... Kafin ta sauke ya kirata.
Ta dauka hello...
Ina waje. Yana fadin haka ya kashe.
Gabanta ya Fadi,jikinta ya Dan dauki rawa, ( Wai me yasa Yanzu ko waya sukeyi takejin
wannan yanayin? ).
Doguwar Riga ce jikinta blue, tana da duwatsu yayyabe jikinta.
Ta dauko hijab maroon har kasa ta saka, ko kwalliya batayi ba turaren da ya siyo Mata ne ta
fesa kawai ta juye indomie a plate ta rufe ta dauki robar ruwa da maltina ta fita.
Yana hangota da Kaya ya fito daga motar..... Gabanta ya Fadi. Anwar a irin motar uncle? ( Wani
kanin mommy ne Mai masifar kudi ) wurin Shi suka Fara ganin motar Shi bama Nigeria yake
zaune ba Soja ne a America.
....... Ya karbi plate din Yana Yar dariya, kawo na taimaka Miki.
Ya shiga motar ya zauna wurin Mai tuki ita Kuma tana tsaye ta rike murfin kofar tana son ya
karbi ruwan da maltina.
Ya Dan kalleta zagayo Mana ki zauna....um um Nan ma ya Isa.
Ya Kara kafa Mata ido , sai Kuma yaki cewa komai ya Mika hannu ya karbi ruwan.
Zaman kujera yayi ya sako kafafunsa waje duka biyun Yan facing dinta. Ta Dan ja baya ,yayi
kamar bai lura ba .
Riga round neck navy blue ya saka da jeans dark blue. Kansa yau ba hula, ya kwantar da
gashin sa inda ya bada kusurwa kusurwa ( waves ).
Yayi kyau matuka.
Ya bude plate din sama, kamshi ya daki hancin sa ya Dan lumshe ido waww.... Daga ji zatayi
dadi fa.
Tayi murmushi kawai.
Ina folk din ko hannu Zan saka????
Ta Dan bude idanu innalillahi...Bari na dauko na manta..... Ta juya da sauri.
Kinga dawo ga wani Nan ...
Ya fada .
Ta dawo ya gyara fuska alamar seriousness yace duba aljihun kujera a baya akwai spoons
dauko mun ciki.
Ba gardama ta ce toh.... Ta bude ta shiga lalube takeyi sosai tun kafar ta na waje har ta shiga
motar ciki tana tura hannu kawai taji kofa ta rufe wani Abu yayi Kara Nan da Nan ta gane
locking yayi.
Ta dago Kai da sauri sai taga Yana ta cin indomie din a hankali..... Au dama da spoon dinka a
aljihu kana son na shigo motar ne...... Kina baya Ina gaba hakan ai ba matsala bane unless
Zaki takura na dawo bayan..... Karka dawo ta fada da sauri.
Motar ta dau sanyi da wani da dadden kamshi..... Kamshin ya Mata dadi Amma hankalin ta duk
ba a kwance yake ba.
........ Amma indomie din nan tamun dadi kin ci?
Eh, ta fada da sauri.
Kice wallahi na ci.... Ba sai na rantse ba.
To idan ma bakici ba nidai na cinye tas!
Ta ce hmm.
Ya bude maltinar ya kafa Kai.... Yana shanyewa ya kalleta kina da fridge ne?
A'a.
Yanaji da sanyi ko siyo mun kikayi?
Ina ruwanka Kai dai kasha maltina.
Ya kyalkyace da dariya. Wallahi ke Bilkisun nan kin iya gwasale