Showing 36001 words to 39000 words out of 94796 words
Chapter 13 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf
Tace sai da safe.......ya bita da kallo Jin bai amsa ba ta Dan waigo....ya tsareta da ido ta dalla
mishi harara.....wallahi ka fiye kallo da yawa. Ya matso da sauri me?
Ta kwasa da gudu ta fada gida tana fadin Wai yau meke damunka ni Bilkisu??????
Ya Kama dariya kawai ya juya ya haye mashin. Tana jinsa ya tada ya tafi sannan ta shige
daki.
Ta cire kayan ta mayar Dana barcin da ta cire ta kwanta.......akwai tambayoyin da nake son
yiwa Anwar amma inajin nauyi.
Ta lumshe ido.....yau dole ta kwana karatu kada gobe taci kaniyarta, abubuwan da suka faru
suna dawo Mata a hankali.
Ya Allah kasa Anwar mijina ne....ta fada a hankali.
Tayi tagumi, nasan Yana Sona.....Amma Ina son ji daga bakin sa, ya Allah yasa da gaske
abinda nake gani a idanun sa har cikin zuciya ne ya bashi ikon *FURTAWA*........ Ta lumshe
ido........
Sha biyu saura ya shiga daki.
Dakin a cike ana jiransa.
Ganin hada Yan 100level yasa bai saki fuska ba kada su Anas su kawo mishi wasa( .....Kai
Anwar case ne ).
Kowa jinin sa akan akaifa don karamin aikin sa ne ya fatattaki kowa yace barci zaiyi.
A hankali yake kallon kowa daman duk dudumar za'ayi dakin Babu Mai hawan gadon sa,
Ya zauna bakin gado yace to bisimillah....... Duk suka zaburo.
Bai Sami kansa ba sai uku saura.
Tuni su Anas sunyi barci.
Ya kwanta daga Shi da best Daman akwai wuta ya janyo laptop dinsa yayi connecting da wayar
Bilkisu ta nuna mishi option ya shiga *transfer file*...
Gallery din ya shiga, a screen din system din yake kallon pictures din......ba karamin tashin
hankali ya shiga ba ganin hotunan ta da yayi ba Wanda ta dauka babu hijab.
Duk duniya ba abinda yake son gani a kullum irin ya kalleta ba tare da hijabi ba.
Tsikar jikinsa sai tashi takeyi yayi ma wani hotonta kuri da ido Yana kallon
kirjinta........hazbunallah ya fada.
Ya zaro ido ganin wani hoton Shi Kuma ba kallabi gashin ya zubo Mata a kafada ya zarce kirjin
ta...... Attachment ne ko nata? Ya fada Yana rike Baki......
Wannan yarinyar anya Bata fi karfina ba?
Zumbur yayi ganin ta cikin kanan Kaya riga da wando tana rungume jikin daddyn ta, gefe
mommy ce da kannen ta biyu maza. daganin pic din kasan ba Nigeria bane......yayi Mata kuri
da ido Yana kallon kugunta..... Ya fadada murmushi *this is Dubai*....... Nawaoooo.
A hankali yake ingiza hotunan a system din sa. yarinyar nan gaskiya ta gama
haduwa.......kutt!!! Ya Kara rike Baki.
Duk wani hotonta dake cikin wayar sai da yasa a system dinsa.
Ya shiga videos, mafi yawa Indian music ne.
Ya shiga text nan yayi karo da text din Suleiman Yana kyarma ya Buda.
```Aslm, Dan Allah lecture din yau karfe nawa ne ?```
Ansa: ```Four```
Na biyun
```Bilkisu ya murar? Allah ya Kara lafiya?```
Ansa:
```Amin thank```
Ya buga tsoki...... Dan iska uban chusu..... I hate this idiot.
Ya bincika ba wani sauran text daga na kawayenta Mata sai nasu Daddy da mommy.
Ya tafi dialing calls, mafi yawan Kiran Suleiman shine yake Kira kusan idanun sa Kira biyu ya
gani tayi mishi.
Ya Kara doka tsoki.
Ya Kara komawa message baiga text din da ta mishi na birthday ba.
Ya doka tsoki watan ni ta goge ni ko?
Ya Fara dialing number sa Nan da nan sunansa ya bayyana ```ANWAR```
Ya saki ajiyar zuciya ya Danna sunan ya bi ta message sai kawai yaga text din ya fito, Nan da
nan ya gane ta saka Shi secret conversation ne.
Yayi tsammmmm! To me take nufi da hakan?
Bana son Mata yawan tambayoyi ko don munyi fada tayi hiding?...
Ya kada Kai kawai.....hmm.
Ya hada xender ya tura Mata GB WhatsApp ya Mata installing.....
Ya rubuta Mata a wall status din ta *You can hide what is on your mind not eyes...*
Profile picture din Kuma ya saka Mata hoton Mommy da daddy Wanda suka dauka tare cikin
jirgi......
Kiran sallah yaji an Fara ..... Ya zaro ido....yau akwai chakwakiya fa.....ya rufe da sauri, ya
kashe wayar ta sannan ya dauko littafi saboda 8 suke da exam.
Rutsum , itama bata runtsa ba, Rabi karatu Rabi tunani.
Shi ya tayar dasu sadeeq sallah.
Daga masallaci Basu Kara ganin sa ba ashe school ya gudu ya boye Yana karatu.
Babu abinda idanun ta keyi sai zafi. Tana zaune can baya ana shirya su har an Fara raba
question paper babu Anwar.
Hankalinta a tashe ga sadeeq ya Mata nisa bare ta tambayeshi.
Tana Shirin mikewa ta dauki excuse ta ari waya ta kirashi ya shigo, Yana ta mazurai Yana Bata
rai...... Malamin ya bashi question dinsa da booklet ya ce biyoni..... Sukayi baya.
Yana zuwa dai dai inda take zaune ya sa biro ya zunguri hancin ta malama kalli paper karki sa
in Fadi.....ta rasa inda zata sa kanta saboda kunya saboda hatta malaman kowa yaga abinda
yayi Kuma Harga Allah ita ba Shi take kallo ba. Tayi sauri ta sunkuyar da Kai bisa table.
Kowa addu'a yakeyi Allah yasa akawo Shi kusa dashi amma malamin nan ya kaishi can karshe
last.
Jarabawar tayi zafi, matuka.
Tunda yaga questions din Shima hankalin sa ya tashi yasan sunyi wahala though Shi ba wacce
bazai amsa ba.
Bilkisu kawai yake tunani saboda jiya yayi obstructing karatunta.
Yana rubutu Yana dago Kai. Sai ya hango ta tayi zugummm.
Addu'a kawai yakeyi Mata Allah yasa ta Sami mafita...... Da kyar ta iya amsa tambaya daya *b*
part din ma da kame kame ta karasa...... Na shiga uku ta fada.
Na kusa da ita kowa yayi zugummm.
Wadanda ke gaban Anwar suka Fara juyawa Nan ya Fara fada musu kwatsam..... invigilator ya
hango su.....hey.....hey....yayo baya.
Come....come.....come....ya nuna Anwar taso daga Nan zonan....
Ya tashi a hasale Yana jiyawa na kusa da Bilkisu na Mata magana ko ta gane question 2? Ya
hangoshi yace Shima ya taso.......saura kadan Anwar ya taka rawa yace Alhamdulillah a
hankali.....suka hada ido da sadeeq ya daga mishi gira sadeeq din ya mishi dakuwa kasa
kasa......ya danyi dariya. Ya fiddo wurin yace ma Bilkisu matsa ciki ya ce Kai Kuma zauna. Yana juyawa Anwar din kafin ya zauna ya ajiye Mata booklet dinsa Shi Kuma ya dauki nata
sannan ya zauna kawai ya Buda .
Ya Fara karanta shirmen da ta rubuta kawai ya soke ya bude sabon shafi.....
Tsoro gareta....jikinta ya Fara karkarwa, ta bude tana karantawa.... Ya cika booklet din
tabbb...kaiii Anwar *guru* ne wallahi. Ta fada cikin zuciya.
Ya iya bada amsa ga turanci Shi yasa kullum cikin photocopy din C.A din sa akeyi Yan aji.
Tunani kawai takeyi ta Yaya zai karbi tashi ya Bata nata?. Tayi sukutiiiii........ Chinyere ta hango
zata you submitting...... Ya daga kai, idan kin gaji go and submit..... Bata San ta mishi wata uwar
harara ba......shin nashin zata bayar amatsayin tata?
Dukewa yayi Yana Yar dariya yaci gaba da rubutu.
Sit biyu ne tsakanin ta da Suleiman tana son daga mishi na Anwar Amma sunyi nisa.
A hankali aka Fara submitting...... invigilator din nan yazo yayi tsayi tagar kusa da su.
Anwar na gamawa kawai ya Mike yaje yayi submitting yayi signing out ya fice.....
Kaiii Anwar karshe ne.
Ta kasa tashi. Har sai da akace time out....stop writing, aka bi ana karba...... Ta saki ajiyar
zuciya a hankali sannan ta mike taje tayi signing out.
Yana can zaune bisa taga..... Ya kura ma kofar fitowar ido. Tare suka jero da Suleiman....
Bilkisu yau Nasha wahala Allah dai ya kyauta..... Bilkisu kinyi duka ko? Naga Anwar aka maido
miki.....Helen ta dafa kafadarta.
Tayi murmushi eh.
Suleiman yayi karaf, da kyar na amsa question one *b* da question three *a*.
Sai na tafi question 4 na buga mishi kame kame ya Allah kasa ko *e* mu Samu na gaji da carry
over wallahi....ai Bata da dadi ta fada tana Mai jajanta mishi.
Wallahi Suleiman *Anwar* dan rigima ne Wai kasan Shi yamun jarabawa yayi submitting Ni
kuwa yaban tashi na bayar?
Ya zaro ido ban gane ba.
Ta bashi labari...yayi dariya yace *Hmmm* kawai.
Yana ta kallonsu...ji yakeyi kamar ya je ya Shakure Shi.
Na Miki Barka wallahi Allah ne ya duba Miki.
Wallahi kuwa Alhamdulillah ai jiya na kwana du'a'i wallahi saboda daman na tabbatar Ina
ruwa....... Karaf suka hada ido dashi.
Ya bata rai,....Ina zuwa Bari na karbo wayata wurin Anwar....... Okay sai gobe Nima zanje waje
wani ke jirana.
Ya wuce, saboda yasan ba dawowa zatayi ba dan Yanzu.
Kun gama? Idan baku gama ba kije gashi can zai tafi.....Anya ba kishin Suleiman Anwar keyi
ba?
Ta fada a zuciya. Shiru kawai tayi.
Baki da lokaci na?
Ta kalleshi, wallahi duk ka sauya Mani, Yanzu Abu kadan sai ka Fara fada kana sako Suleiman,
Yana fada mun yanda yasha wahalar exam ne shine fa ka ganmu....... Bana sonji.
Kina son fada mun cewa kowa baisan Shi din saurayinki bane.?
Zatayi magana ya Mika Mata wayarta, ungo idan daddy ya tambayeki kice wayar ba chargy ta
kwana saboda na kasheta b4 ya Kira don't know what to tell him.
Fishi kayi?, Ta ce ba tare da ta karbi wayar ba.
Akan meye zanyi fushi, Ina abinda ya dameni, na Isa in rabaki da Suleiman ne while Nima
albarkacin sa nakeci na........ *Anwar*..... Ta Kira sunan sa.
Ya kalleta,
Wallahi ka canza, bana Jin dadin abubuwan nan har ga Allah.
Magana takeyi kamar me Shirin yin kuka.
Yayi shiru kawai,
Amma kayi hakuri idan na bata maka Rai shikenan ko?
Naji karbi wayar ......
Ta danyi murmushi ta Kai hannu.
Kina Sanya attachment?
Da sauri ta kalleshi, ya kura Mata ido....
Ta sunkuyar da Kai Allah ya sawake ban taba ba...... Gashin ki ne haka?
Haka me?.... Daman ka karbi wayar ne don ka man kwakkwafi kazo ka addabeni da tambaya?
Ya bushe da dariya...... Me yasa anan bakya sa ko gyale bare ki kwatanta saka wando mu
gani........ Juyawa tayi ta Fara tafiya, ya dirko da sauri ya bita....Ina zakije?
Yasha gabanta.... Dan Allah kiyi hakuri na daina.
Hmmm, ta ce.
Na ce na daina ko?
Shikenan, bani wayar.
Tafiya zakiyi?
Eh, tace,
Suka jera suna tafiya,
gobe ne last paper kuma morning ana fitowa Zan gudu......... Nima gobe Zan tafi. Ta fada mishi.
Haba, Abuja ko sokoto.
Tayi Yar dariya Abuja..... Shikenan na Sami lift har gida ke zanbi ko? Ance Kano kike kawa jirgi
Yar gayu ......... Tayi Yar dariya.....inji wane magulmacin.?
Ke fada mun Zaki tafi dani na shirya ko..... Shatar mota zanyi fa ba zuwa akeyi daukana ba.......
Shatar mota?
Eh,
To kawai ki Bari mubi motar gidan su sadeeq idan anzo......Kai nifa bana son rabe rabe..... Ba
damuwa nida sadeeq daya ne kada ki damu we are now family.
Shikenan Zan fadawa mommy yanda tace ....... Ya watsa hannu fine.
Ta harareshi Kai wallahi Anwar din Nan ka fiye yanga kamar mace......
Ya tuntsure da dariya a'a kin manta nine Bilkisu.
Barci kawai kowannen su keji. Koda suka suka rabu gado kowa yabi lafiya..........
Shako wuyansa yayi suka yi bayan daki.....Kai lafiya ....Wai Anwar kana da hankali
kuwa?????
Warning Zan maka wallahi tallahi idan kayi kuskure *you are dead* ya mishi nuni da yanda a
wuya.
Da Bilkisu zamu tafi gobe na fada Mata Kai zamubi idan ka saki ka nuna Mata inada alaka da
tafiyar you are sorry Dan ubanka.
Zan ma Umar waya in mishi bayanin komai...... Kaji ko?
Naji banza....sakarni toh.
Yayi murmushi. Good and fine.
Wace karyar ka shirga Mata?
Ya tabe baki wallahi bance Mata komai ba Kuma nasan bazata tambayeni ba.....
To kaja ma Umar kunne wallahi......bai da matsala. Kuma wannan karon Shi kadai zaizo ba
wani security saboda Kai zaka zauna gaba nida Bilkisu a baya ...... Dan ubanka ni oga Kuma a
gaba? Eh, Kai zakayi arranging hakan.......mtsew naji.
Cikin kwanciyar hankali tayi wa mommy bayani. Tayi Mata nasiha da addu'a , ganin Bata boye
Mata hakan ba, (munafunci ga yaro Shi keda ciwo).
Umar yasan dakin su, can ya biya aka Sanya musu kayansu kafin ya karaso cikin makarantar.
Suna fitowa ya tareta Yaya?
Ta ce ta shirya.
Haka suka biya ta dauki jakar ta suka wuce.
Sadeeq ne oga ya kame a gaba.
Shida ita baya..... Ya kalleta. Kinga WhatsApp???? Tayi murmushi eh,
Zamu ringa chatting kinji?
Toh,
Ko Baki da time?
Me zai hana......
Good, ya fada.
Kinyi break?
....tambayo. Ta fada a zuci. A zahiri tace Nasha tea.
Tea?
Umar akwai abinci motar nan?
Eh, yalla....... Yayi saurin datse maganar ya canza da cewa, Yana daga Nan baya.....
Sadeeq ya juyo Kai bana son hauka abincin nawa zaka cinye?
Bilkisu zata ci ko zaka Mata rowa ne......Ni na koshi ma ta fada tana Yar dariya....... Au Bilkisu
waa nakeyi I tot koshine keson ci.
Ya yunkura ya dauko cooler sadeeq ya Miko mishi spoons biyu, yabude.....kamshi ya buge
motar... Gasassun kaji ne da soyayyen dankali da kwai.
Ya kalleta kici ....
Tayi murmushi.....na gode.
Wani kallo yayi Mata....bakici?
Ta tabe baki Alhamdulillah.
Ya daga kafada, kufa wadannan an Saba haduwa ko? Wurin mu ne sabbin zuwa ya waxgi kaza
ya Fara ci.
A hankali a hankali yaci ya koshi tana kallonsa ........Kai namiji baida kunya ita Ina zata iya Shan
ko ruwa a nan?.
Ya Mika ma sadeeq ungo...... Miko mun maltina Mai sanyi gaban ban......Ashe Yar cooler ce ta
ruwan sanyi dankare da lemuka .......
Ya kalleta me zai Miko Miki?
Ta girgiza Kai na koshi...... Ke kuwa Dan Allah hajiya Kisha ko Mai sanyin ne.......Kyaleta umar
tana tsoron kada mu saka Mata baliyan....... Ta zaro ido....yasha mur...... sadeeq bani maltinar
Nima...... Ungo wannan Kisha Ni ta isheni. .....ya Miko mata tasa.
Kurba biyu tayi da kyar, ya tsareta da ido.....ko kadan baijin kunya ko nauyin kallonta, taci gaba
da rikon ta.........tana jujjuyawa.
......... Kina tunanin Suleiman ne?...
Wohohoho Kai kuwa a Rana sau nawa kake ambaton Suleiman a rayuwar ka Wai meye ya
tsare maka?.
Inba tunanin sa kikeyi ba Kisha.....na koshi ne kaima ka kasa shanyewa bare Ni?
Kuna da Yan uwa a Kano?
Um, um.... Ni ban ma taba zuwa Kano ba sai ta dalilin karatun nan.
Da gaske?
Allah kuwa.....
Kai Dan asalain Kano ne?
Yayi murmushi ciki da bai kuwa.....ya bangan ka da tsagen kanawa ba?
Yayi Yar dariya, daga kaina aka daina gidan mu kinsan nine auta gidan mu muna da yawa.....
Ya sunan anguwar ku?.
Keda Baki San Kano ba Ina ruwan ki da sunan anguwar mu kuma?.
Eh, Ina son sani.
Yayi Yar dariya ni ba cikin garin Kano nake ba kauyen Kano karkashin karamar hukumar *Rano*
kin San wani gari *Dagama*?
Nope, ta fada.
Yayi Yar dariya.
Suna shiga Kano ya ce a tsaya ya sauka.
Ya Dan fita can gefen hanya.....ya Kira Alhaji Mubarak a airport.
Hello an Gama komai?
Ya rusuna, angama Allah Shi taimakeka.
Yawwah.
Ya shigo motar da sauri, Umar airport muje Airport da sauri please....... Ta kalleshi
zakewa????? Shi Dan karo sai instruction yake badawa tun dazun.
Tun daga bakin gate ake Basu girma. Ko kadan Bata kawo wani Abu a ranta ba.
Ya tokare bakin kofa zan koma mota, sadeeq sune Yan gari zasu raka ki har ciki......
Toh, na gode sai munyi. Sai Yan waige waige kamar marar gaskiya......zamuyi chat kinji?
Tayi murmushi ba damuwa....... Manyan mutane biyu ta gani sun zube gabansa Allah Shi
taimakeka Barka da sauka.........
Ya zaro ido ita Kuma tabi fuskar sa da kallo........✍
Alawiyya ma na gefe...
*ZAINAB WOWO*
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: *WA ZAI FURTA?*
1⃣3⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya
shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*For Gaje Abu*
Alaweez Ana mugun tare.
*Ya Allah ka Kara Mana katangar karfe da masu bakinciki damu* *Hassada ga Mai rabo taki ce
duk Wanda Allah ya tarfa ma garinsa nono wallahi ko ana mazuru ana shaho sai yasha*
masoyana ga taku
***************
*KADUNA RIGASA*
Tayi zaune falon suna labari da hajiya bayan ta sako doguwar hijab.
Ta kawo Mata lemu da naman kaji......gidan Alhaji shamsu naje shine na biyo ni in ganku tunda
Shi ya kwammace yayi ta kullenku da ya barku zumunci.
Murmushi tayi kawai.
Ya kuke ba wata damuwa dai ko?
Babu damuwa, ta mike tsaye bari na Kira ummin ku gaisa.
Da gasken gaske hankalinsa ya tashi sha"'awar Amira ta addabeshi.
Da farko yaji haushin kwalelen da ta mishi amma da ya tuna haramcin yin haka saboda ya
shiga hakkin Ummi, sai ya bata uxuri.
Ya shiga toilet dinta yasa ruwan zafi ya warwatsa a jiki saboda ya Sami sauki, sannan ya fito.
Zaune suka tarar dashi suna labari da hajiar, ya kasa dauke idonsa daga Amirar duk inda tayi
idanun sa na kanta har Ummi ta Shaka.
Koda suka raka hajiyar Sashen Amirar ya koma.
Ya riko kugunta wallahi gobe sai kin gane kurenki......
Wai Ina Kika saki Kaya haka bayan nasan ke ba ma'abociyar su ba ce?
Inji waye? Ina ra'ayi Kaine naga kamar basa birgeka.......wallahi Ina so. Da kin tsaya dazun
tabbas da ba kiss kadai zanyi ba........... Maganar ta makale ganin Ummi ta banko kofa kamar
an biyo ta....
**************
*Federal University dutsinma*
......Malam ba Wanda kake tunani bane get lost.... Ya bude baki zai Kara magana ya fiddo
mishi idanu I said get lost ya fada cikin tsawa.......... Wai Kai baka