Showing 21001 words to 24000 words out of 94796 words
Chapter 8 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf
please...
Tayi murmushi yace yau bazai shigo school ba.
Aji ya dau surutu suka ce ko hostel ne yau sai sun bishi.
Kamar yanda sukayi alkawari da zainab sai ga cake...... Cake abinda ka cake sky blue yayi
kyau karshe an nado Shi a leda cikin kwali. Sai kamshi ke tashi. Flowers din sunyi kyau Mai
Rose ne da wasu design cake din ya tsaru.
Tana kwance daki ya kirata.
Yana jiranta bakin hanya.
Ta ce toh, sanye yake da round neck shirt orange Mai ratsin fari a jikinta an rubuta *You are
mine only* a gaban rigar. Dark blue jeans ne wandon da facing cap Fara anyi rubutu orange
*Mine for ever* daga sama.
Kunnensa like da ear piece. Kanta a kasa tana tafiya a hankali.
Ya saki ajiyar zuciya kadan idonsa na kanta har ta karaso.....
Murmushi ta sakar mishi kafin tace happy birthday once again.
Godiya! Ya fada Yana latsa waya Shi adole ba kallonta yake ba.
Ta harareshi dai dai ya Dan dago.
Yayi murmushi ko amsar Bata Miki ba?
Yayi kyau karshe....ta fada a zuci a zahiri Kuma tayi shiru kawai.
Muje.......tace tare da yin gaba kadan.
Ki jira muyi hoto Mana..... Da wa? Tabb
Ya Dan Sha mur, dake ko bazakiyi ba?
Eh, tace tana Kara ci gaba da tafiya.
Yaji haushi sosai.
Are you serious? Ya biyota.
Ta Dan waigo *did I look like a joker?*
Dan Allah kizo muyi pic Bilkisu........ Ta zaro ido Wai da gaske kakeyi?
Sai ta danyi dariya kawai ta sunne Kai....
Ya ja tsoki, don ya karanci kunya takeji.
Suna Isa shagon ta ce me kake so?
Ya Sha mur Yana fushi duk abinda ya Miki.
Tayi kamar Bata lura ba ta amso meat pie da soya milk drink na cikin kwalba Mai tsadar guda
goma.
Ta fito, gashi sai me?
Ya karba da hannu daya dayan Kuma Yana latsa waya. Yace shikenan thanks.
Duk taji ba dadi kamar tace suje to suyi hoton Amma gaskiya Bata iyawa.
Suka jera zuwa bakin hanya sai fushi yakeyi.
Zaka koma hostel ne?
Akwai abinda Zan Miki ne idan na tsaya?
Zan baka sako ne muje da mashin din a bakin gidan mu ka karba....... Ki je ki kawon Ina Nan.
Har lokacin fuskarsa ba fara'a.
Ta langabe Kai Wai Anwar fushin na menene?
Mtsew kawai yaja guntun tsoki.
Kaji?
Oh my God , me kike so Yanzu Wai?
Muje ka karbi sakon.
Jeki gani Nan zuwa.
Har zata Kara magana sai Kuma ta fasa ta wuce don itama ta Fara kulewa.
Tana niyyar shiga gida taji tsayuwar mashin, da sauri ta waiga sai kawai tayi murmushi ganin
shine ya Dan harareta.
Tayi ciki tana dariya.
Kwalin lemun ta Fara fitowa dashi tasa agaban mashin din sannan tace Ina zuwa ku jira.
Ta dawo da cake din ta Mika mishi ga cake kaci sosai........ Da sauri ya kalleta.
Tayi murmushi.
Kamar zaiyi magana sai Kuma ya fasa yace da Dan mashin din muje.........
Kamar tace dawo muyi hoton Amma bakinta yayi nauyi.
Haka ta shiga gida sukuku............
A hostel party sosai akayi yaji dadi abinda tayi mishi Yana son Allah ya kawo ranar da Shima zai
Bata mamaki. Amma rashin yin hoton nan ya Bata Masa rai matuka, ya Fara gajiya da halin
ko'inkula da ta keyi mishi, yanda Yan Mata ke rokonsa akan suyi hoton dashi Amma shi yau
yabroki mace suyi taki amincewa *dame Bilkisu ke takama?* Wajen Sha biyu ya tura Mata text *Thanks for the cake* sai da safe ta gani.
Bata Sami halin reply ba.
Yana zaune ta shiga class din Koda suka hada ido tayi murmushi Shi Kuma ya daure fuska ya
kawar da Kai.
Gabanta ya fadi, ranta ya Fara baci menene abin Jin haushi daga tace bazatayi hoto dashi ba?
Ya taba ganin tayi hoto da wani ko wata?
Ta ajiye books dinta ta Isa wurin sa.
Ina kwana?
Ya dago Kai tare da cire ear piece. Ya kalleta Yaya? Fuskar sa ba yabo ba fallasa,
Zamuyi macro after this lecture please if you are free........ It's alright. Ya fada a takaice.
Ta juya ranta ba dadi.
Yan aji sai zolayar sukeyi jiya yaji tsoro baizo class ba kada a mishi wanka yana ta dariya da
yazo zasu hada ido sai ya kawar.
Duk taji babu dadi.
Ana Gama lecture wasu suka shigo alamar venue din su ne.
Fitowa sukayi, ajin dake hade dashi ba mutane sosai Yana tsaye bakin taga tace Anwar muje
Nan naga ba kowa......... Anwar let's snap please Helen ta karaso tare da dafa kafadarsa.......
Wani dadi ya ziyarce Shi yace anzo wurin.
Ya kalli Bilkisu okay jirani Ina zuwa.
Kawai suka Fara hotuna. Kamar jira akeyi sai ko wace ta taso wasu ma wucewa zasuyi ga
Anwar da farin jini
Nan da Nan hankalin Bilkisu ya tashi ta kasa daurewa ganin yanda suke faman rikeshi wasu na
kwanciya kafadar sa.
Ta shiga ajin idanun ta duk sunyi ja.....
Yafi mintuna talatin tana zaune ta ma kasa tashi suk tana hangensu ta taga.
Sadeeq ya karaso maigadon ya naga kinyi zaune baku Fara ba?
Eh, hotuna yakeyi yabar Ni Nan kamar sakarai, ta fada a wahale kamar zata kurma ihu.
Malami ya shigo yace ku fita zamuyi darasi......
Haka suka fito tare da jingina jikin icce ita da sadeeq har lokacin hotuna sukeyi ko kallon inda
take baiyi ba.
Sadeeq ko zamu je ka nuna mun Dan Allah? Ta fada Rai bace........ A 'a ki jira ya Gama kinsan
halin mutumin....wallahi yau Kam bana so ko da kuwa yazo.
Tohhhh..... sadeeq yace kafin ya Kara magana sai ga Anwar din.
Bilkisu muje.
Ta kalleshi kallon da ya gwammace bugu dashi sannan tace bana so kaje kawai.......
Duk akayo musu ratai da ido.
Nan da Nan ya hasala don yasan a rina iyakar rainin wayo yarinyar nan ta daukeshi sakarai,
Saboda me Baki so? Ya bukata a hasale....
Ina ce hoto ne a gabanka, ko? Ina jiranka mintuna kusan talatin.....Kai ma abokina meye haka.
Zanci ubanka sadeeq...ya daka mishi tsawa.
Kada Allah yasa taso waya rasa?
Don kinga Ina lallabaki naje nayi hoton me ya hana kizo ayi dake?
Ko Zaki hanani ne?
Sadeeq zai Kara magana ya nuna Shi da yatsa a hostel zamu hadu zanga ubanda ya tsaya
maka kaima......duk suka zaro ido lallai fa da gaske yake. Sannan ya kalleta kada Allah yasa
kiso ke Kika rasa........ Ya wuce fuuuuu ya fada wani class ya zauna Rai bace kamar zaiyi hauka
idanun sa sunyi jawur. Bilkisu ta rasa inda zata Sanya kanta, kuka zatayi ihu zatayi, itama nata idanun sukayi ja tare da
kawo ruwa kamar zatayi kuka abin yazo kaina?
Hakan take ta nanatawa cikin zuciya.
Sadeeq ya kalleta hankali tashi, wallahi fada zamuyi dashi tunda Kika ji ya rantse....... Ta zaro
ido fada?
Hmmmmm Baki San halin Anwar ba..... Sai akwai tabar Shi nan ta wuce class din da taga ya
shiga....
Yana zaune ya hade Kai da table. Ta zauna kujerar gabansa, ta Kira sunan sa,
Anwar!..
Ya dago da sauri sai da gabanta ya Fadi ganin yanayinsa.
Ta daure ta Kura mishi ido zuciyarta kamar zata fito amma ta daure kada tayi sanadin raba
abokai . Ta Fara magana a hankali.....
Ba ruwan sadeeq cikin maganar nan, kada laifina ya shafeshi duk abinda zakayi mishi kayi mun
Amma kada ka Sanya Shi ciki kayi hakuri ka kyaleshi .......bazanyi hakurin ba. Ya fada kamar
zai mareta.
Duk ajin akayi shiru ana kallonsu,
Ya daga murya, ke har Zaki ce na Bata lokaci Baki so na koya miki? Ni idan naje wurin malamai
su koya mun korata sukeyi wani lokacin sai na kwashe fiye da awa daya sannan suce in tafi in
Basu wuri, bana zuciya gobe sai na koma sai ke daga Yan mintoci Zaki nemi kiyi mun wulakanci
cikin jama'a?...... Naji kayi hakuri,...... Bazanyi ba nace ki tashi ki bani wuri.....gabanta ya Fadi.
Ta daure ta hadiye kwallan dake son taruwa a idonta tace sadeeq nake nufi kayi....... Bazanyi
hakurin ba ya Mike, idan ke bazaki tashi ba ni na tafi.....kawai yabarta wurin.
Na shiga uku ni Bilkisu ta fada.
Tashi tayi tabar class din don kwallar sun kasa tsaiduwa.
Ni Anwar zaiyi ma wannan wulakancin? Ni Anwar zai dizga?
Ni Anwar zaiyi ma gorin karatu?
Me yasa tun farko na bashi fuska?
Idan sai Anwar ya koya mun karatu zanci jarabawa billahil azim na hakura da degree har
abada. Biji biji take ganin hanya....ba abinda kanta keyi sai sarawa, kaicho na ni Bilkisu na kyale
Anwar har abada tallahi ko kallonsa bazan karayi ba.....ta bude daki ta fada bisa katifa sai
kuka......... Hankalin sa yafi nata tashi, kamar mahaukaci ya Isa daki Anas ne kwance ya fada bisa katifa
Anas na shiga uku nayiwa Bilkisu wulakanci.
Ya zaro ido me ya faru.?
Yarinyar nan kureni tayi yau, na rasa ta inda Zan bullo mata.....naji me ya faru.
Ya Mike kamar mahaukaci.......laifinta ne nasan gobe zata Kara bani hakuri. Zamu shirya .....ya
fice dakin.
Duk duniya Yanzu Babu Wanda takejin tsanar say ranta irin Anwar ko sunan sa Bata so a fada
ta fita batunsa Amma kullum cikin kuka take.
Kwananta biyu daki kwance ta kasa zuwa lecture saboda Bata kaunar Kara ganin sa.
Shi Kuma jira kawai yakeyi tazo ta Kara bashi hakuri su dai dai gashi Yana ganin ya zubda ma
kanshi class matukar ya kirata a waya, abinda bai sani ba har ta goge no. Sa cikin wayarta.
Abu kamar wasa kusan sati Bata zo school ba, sai dai kullum tabi dakuna ta karbi note tayi.
Ranar laraba ta Kama kwananta tara rabonta da school Shima tazo ne dole saboda za'ayi C.A
Kuma course din da tafi tsoro.
Dadi ya kamashi yasan dole yau ta nemeshi.
Yana zaune Yana koya masu Helen ta shigo gabansa ya Fadi ganin irin ramar da tayi though
Shima ya Dan fada.
Layin da yake Bata kalla ba ta Isa can baya, Damian please help me here ta fada a hankali.....
Ashe bai iya uwar komai ba nan da Nan hankalin Anwar ya tashi ganin ana koya Mata wrong.
Helen ta zungureshi ga fa Bilkisu..... Eh na ganta, tana fushi dani ne Kinga taje Damian na koya
Mata hauka. Mtsew ya buga tsoki.
Ya kasa ci gaba da koya ma Helen din.
Damian na gamawa tabar class din sai lokacin test ta dawo.
Tana shigowa ta hango sadeeq ta Isa wurin Shi....... Alhamdulillah dama Ina ta addu'ar kada a
riga ni.
Yayi murmushi kawai, tare suka zauna ya Bata ta kwashe hankalin Anwar na kansu kamar zai
haukace.
Tana gamawa taje tayi submitting tayi tafiyarta daki Koda Anwar din ya fito bai ganta ba ya Kara
hasala....... Sadeeq na fitowa ya Fara surma mishi Zaki har Yana yunkurin dukansa Wai ya
zauna tare da Bilkisu test.......橙提橙提橙提橙提橙提橙提 Tirkashi.
Ayi hakuri da kadan...潤蕉. Zainab wowo ce踫
Juma@ mubarak don't forget to receive suratul kahfi踫潤蕉
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: 橙 *WA ZAI FURTA?*橙
07
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya
shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*Ina alfahari daku kawayen yarinta:*
*Rakiya Amadu m/bread da badiyya Amadu m/bread*
***************
*Federal University dutsinma*
Aisha, sumayya da khausar sune kawayen Bilkisu na kut da kut!, Tare suka zo makarantar
secondary school daya sukayi watan federal Bakori dake shiyyar funtua ta jihar katsina.
Aisha da sumayya political science sukeyi, khausar na micro biology sai ita Bilkisu dake
Economics.
Su ukun dakin su daya, Bilkisu kadai ke nata dakin.
Mafi yawa su ne suka fi zuwa dakinta ko a secondary ana tare Amma ita komai nata daban ne.
Tana yawan yin girki baka raba ta da ko miya ce Shi yasa Mafi yawa sune ke zuwa wurinta
neman abincin musamman irin lokacin da semester ta raba tsakiya komai yayi zafi.
Khausar na bala'in son Anwar Amma tun lokacin da ya dizga ta daga magana taji ya fita ranta.
Aisha ce ta shigo dakin tana ta kokarin yanka carrot da zata Sanya cikin farar hinkafar Daman
tun safe kafin ta fita tayi miyar kifinta.
Ke yunwa fa nakeji har bana gani.
Tayi murmushi to gashi Bata karasa tsanewa ba ko zakiyi tsame yau ma?
Mtsew tayi guntun tsoki, tare da kwanciya bisa lumtsetsiyar katifarta, wannan uwar shinkafar
Kuma fa ko yau kin tabbatar zamu zo kwaraka ne?
Ta dan tabe baki Anwar ne Mana da rigimar sa nace zanyi girki Wai zaici na tafin mishi dashi
class 4 idan zamuyi tutorial.
Hmmm, kawai tace.
Ta Dan waigo Fadi kada ta kasheki.
Ta kyalkyace da dariya keji Kama Kai ai bandai *furta* ba ko?
Murmushi tayi kawai,
Daga Nan Bata kara mata magana ba.
Yar madaidaiciyar cooler ta samu ta zuba mishi miyar Kuma tayi amfani da Yar roba Mai
marfi.
Saboda kurewar lokaci a daki tayi sallah tun kafin ta sallame yayi mata missed call biyu.
A gurguje ta shirya ta fito.
A bakin gate ta kirawo shi, bugu daya ya dauka.
Malama kinfa shanyani,
Ya hankuri gani na shigo school kana Ina?
Lecture room 2, ya fada.
Okay I'm coming......ta kashe wayar.
Sanye take da doguwar riga ta lace coffee brown, hijqbinta kalar flowers lace din maroon.
Tana saka kafa wayar ta na Kara *Daddy ne ke mata video call* ta karasa da sauri tana
murmushi.
Ya hangota Amma sai yayi kaman bai ganta ba har ta zauna kusa dashi dai dai kuma lokacin da
ta ajiye mishi ledar abincin sannan ta latsa wayar.....Hello daddy. Ta fada tare da fadada
murmushinta zuwa Yar dariya.
Yabi fuskar ta ta da kallo Yana masifar son tayi dariya Shi kadai yake ganin abinda yake gani.
Bilkisu ya kike?
Kina class ne?
Eh daddy kaga nazo karatu ne wurin Anwar ta kanga fuskar wayar saitin Anwar din.
Yayi saurin sunkuyar da Kai...... yarinyar nan nada hankali kuwa?
Anwar?.......ya dago ido da sauri....barka da wuni Daddy ya fada da sauri tare da rusunawa
Yana Dan murmushi.
Dariya yayi ......Kaine Anwar? Yau ba'ayi fadan ba kenan?
Ya zaro ido kadan kunya ta baibayeshi yayi saurin kallon Bilkisu atuhumce.
Ta janye wayar.....mun shirya daddy yaban hakuri ta fada tana dariya.
To yayi kyau. Allah ya taimaka a kula dai kada amanta Allah Yana tare da kowa a zahiri ko
badini.
Na sani daddy.
Ta zaro ido Wai daddy kana sokoto ne???
Eh mun zo nida mommy bikin saifullahi ko?
Ta zumburo Baki daddy......ke sai anjima kuyi karatu kada lokaci ya shige......
Daddy zakuzo din ko?
Eh in shaa Allah zamu shigo jibi......yeeeeeee ta fasa Kara yayi saurin latse wayar Yana dariya.
Ta kalli Anwar su daddy zasu zo jibi......ya dalla mata harara. Ya akayi yasan muna fada?
Ta danyi guntun tsoki.... Ai sun Sanka Ina Basu labarinka sosai.....kina cewa me?
Tayi murmushi.
Kinji?
Hmmm kawai tace.
Magana zakiyi meye kike fada ne?
Ka gane sun San wajen ka nake daukar karatu to ya kirane yace yau bamuje karatu ba nace
munyi fada dakai shine........yaushe mukayi fada?
Me yasa zakiyi karya? Sai kice fushi nakeyi dashi ba kice muna fada ba.......naji sorry oya muje
ta bude littafin.
Ko sai kaci abincin zamuyi?
No, Zan tafi dashi hostel ne.
Okay.
Lafiya lau sukeyi tana ganewa sosai, yana magana tana satar kallonsa idan taga ya maida
hankali ga littafin sai ta daddage kuwa ta Kura mishi ido.
Yana da kyau, natsuwa da Kuma kamala problem dinsa kawai miskilanci.....da yazo zai kalleta
sai tayi saurin kawar da ido....haka..haka....sunyi nisa sosai sai taji an kwada mishi Kira
```ANWAR```.....
Dukkansu suka kalli wajen... Mufeeda ce.
Gaban Bilkisu yayi mummunan faduwa.
Saboda, mufeeda ana raderadin budurwar Anwar ce physics department take yarinyar ta hadu
karshe saboda iya daukar wanka, Bata fi Bilkisu kyau ba Amma saboda iya gayun ta yasa idan
tana wajen baza'a taba ganin kyan Bilkisu ba da kullum cikin hijabi.
Sanye take da wani material dinkin Riga da skirt, tayi kyau matuka fuskarta sanye da
kwamemen glass ya mata kyau sosai.
......... Ta tsaya daga jikin taga alamar ganinsa take sonyi.
Kawayen ta Kuma na gefe suna jiranta.
Ya kalli Bilkisu please Ina zuwa, ya mike.
Wani abu ya taso mata ya tokare a makogoro tunda ta yi kasa da Kai bata dago ba.
Tana ta latsa waya ta ma kasa gane inane take shiga tana fita.
Agogo kawai take dubawa.
Mufeeda nada daukar hankali, kafin kace me.....Anwar ya fara shafa'a.
Ai nayi tunanin bazaka taso ba tunda ance tsoron ta kake ji.
Yayi murmushi sai kuma na taso Kika gane hakan ba gaskiya bane ko?
Wai meye tsakanin ka da yarinyar can da kullum baka tashi koya mata sai da marece Kuma ku
biyu kawai?.
Yanzu dai gani. Ya fada Yana murmushi.....
Ta dalla mishi harara minti nawa ta baka ne?
Ni kamar baka cikin natsuwa ma wallahi. Baka daukar waya baka amsa gayyata idan ma an
iske ka..... Ikon Allah mufeeda ki Bari zamuyi waya anjima Kinga Babu dadi......babu dadi ka
barota kazo wurina?
Bai San lokacin da ya kyalkyace da dariya ba ......dai dai lokacin da Bilkisu ta dago Kai, kutumar
bala'i....
Yana mamakin yanda yanmata ke tuhumar Shi akan Bilkisu.
Mikewa tayi ta hada litattafan sannan ta dauki ledar abincin kawai ta fito......
Ba karamin razana yayi ba don yasan kwanan zancen..... *Bilkisu*.......... *Bilkisu*....
*Bilkisu*!!!....... Amma Ina! Ko waige....
Duka yaushe ya samu suka daidaita, mtseww.
Please zamuyi waya ya fada tare da Dan rugawa *Bilkisu*.......
Sauri takeyi sosai, ya cimmata da kyar...Dan Allah kiyi hakuri.
KO kallonsa batayi ba.
Wallahi ban manta dake ba Ina cikin