Showing 18001 words to 21000 words out of 94796 words

Chapter 7 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

3842

hankali don samun abinda zata tsira.
Kamar injin haka yake rubutun zu..zu..zuu kafin tayi layi hudu har ya juya , haushi ya turnuketa
bai jira ta gama? Wannan wace irin mugunta ce?
Nan da Nan ta zuciya kawai sai ta ci gaba da rubuta shirme.
Gara naci zero da in yi naka ....ta fada cikin zuciya.
Kafin kace kwabo har ya gama ya janyo wata sabuwar takardar, ya canza biro black ya ci gaba
da rubutu, sakamakon ta farkon da ya Fara da blue biro.
Tana kallon sa ta wutsiyar ido ko ya Turo mata wacce ya Gama da ita ta rubuta sai ma ya
sanyata kasan tashi , idanun ta har ruwa ruwa sukeyi saboda fushi .
Wallahi Ni da Anwar har abada au Ni zai ma rashin mutunci?
Duk inda ka waiga kowa sai mazurai yakeyi an kasa rubuta abin kirki.
Tana kallon sa ya gama kawai yasa hannu biyu a kirji.
Kamar tayi ta tsunkulinsa takeji don takaici.
*stop writing*, ya Fara karbar wadanda ke gaba layi layi........ai kamar jira akeyi ajin yau dauki
gungunai.
Jin haka kawai taga ya dauro mata takarda bisa tata.
Sunanta, number, course code.....da komai da komai.
Ta zaro ido Wai Daman biyu yayi tawa da tasa?
Tayi saurin kallon sa, ki soke wannan shirmen da kikayi kisa mistake. Ta kalli takardar ita ce ya
Fara solving da blue biro.
Suleiman ya Fara kunno Kai zai Fara kwafa , malamin har ya zo wurin su, duk suka Mika.
Shiru Suleiman din yayi yama rasa meye zaiyi don takaici, Tabbas yasan don Shi Anwar yayi
haka.
Ta kalli Suleiman din cike da damuwa ka gama kuwa?
Wallahi banyi komai ba ya fada Yana kakaro murmushi,
Innalillahi..... Ta juya zata ma Anwar magana Ashe har ya bar class din.

Ta waiga ta Kara waigawa Amma Ina tuni yabar shiyyar class din ma.
Kayi hakuri , ta juya tana ma Suleiman magana.
Nima wallahi har na sadakas, ashe rubuta mun yayi. Kai Anwar karshe ne wallahi.
Murmushi kawai yayi.
Ai kaga da ya barni na kwafa har kaima kayi.....kayi hakuri Suleiman.
Haba ba komai wallahi. Ya fada Yana Yar dariya.
Haka suka fito duk jikinta wani iri.
Kai Anwar case ne. Watan Shi dole inba wulakanci yayi ba baya taba Jin dadi.
A bakin kofa sadeeq ya karaso Bilkisu ya test din....yawwa sadeeq zo kaji Dan Allah. Ta yi gaba
Yana binta.
Sun danyi nisa kadan inda ba mutane sosai ta tsaya.
Ka ringa yi ma Anwar fada Dan Allah Shi me ya dauki rayuwa?
Me yayi ba dai tashi yayi ba ya bada ba tare da ya baku ba?
Hmmm , kusan haka.
Kaga yasan tare nake da Suleiman na Kuma fada mishi Amma sai ya hana in copying Yana ta
sauri sauri Ashe so yakeyi yaci lokaci yayi nawa yayi nashi Kuma don mugunta bai bani ba har
sai da za'ayi submitting saboda Allah ya kyauta?
Tun tsirewa yayi da dariya, Dan iska, abinda yayi kenan?
Wallahi kuwa, kaga ai Babu dadi.
Gaskiya ba dadi.
Kiyi hakuri Dan Allah Yana Ina yanzu?
Kasan halinsa ai, har ya gudu ya tafi.
Kiyi hakuri Zan mishi magana.
Ka kyaleshi Daman idan ka lura bai niyyar Zama Dani ba yau tun safe yake ta wani Shan
kunu..... Baki tunanin ko kin Masa laifi? ...Laifin meye?
Jiya ne mukayi Zan kirashi a waya na manta inaga kilan shine ......shine ma kawai.
Mtseww.....to kyaleshi .
Anwar na Bilkisu.... Bilkisu ta Anwar ai in ba keba Shi.
Kai ai kyaleshi zanyi don ban iya hakurin wannan mugun halin nasa.
Dariya sadeeq keyi sosai.
Ta wuce fuuuu.
Waya ta dauka, ta kirashi.
Yana tsaye zai siyi *Pepsi* yaga Kira.
True caller ta bayyana sunanta a screen din wayar sa *Balky gada*
Kawai sai yaji gabansa ya Fadi ras!
Ya danyi murmushi....... Hello
Kana Ina?, Ta fada?
Cikin dakewa kamar bai San wake magana ba yace Ina Ina?
Eh kana Ina?
Wake magana ne?
Bilkisu.....kana Ina Wai?
Wace Bilkisu ? Ya Kara bukata.... Dariya ta kusa kubuce mishi Jin har ta Fara hasala.
Bilkisu Gada ....... Oh ya fada tare da yin shiru.

Au shine kayi shiru mtseww.....ta katse waya.
Yabi fuskar wayar da kallo Yana kyalkyatar dariya ohh ni Hamza tawa ta sameni.
Wai yarinyar nan idan Sona takeyi haka zata shigar da kanta da tsiya ba da ARZIKI ba?
Ni wallahi na Fara tsarguwa da tambayoyin da nake faman amasawa kullum akanta .
Ya kirawo ta......kamar bazata dauka ba har ta fito cikin makarantar sun rabu da Suleiman tun a
bakin gate.
Ai naji kana ta wani rainan wayo saboda nice na kiraka ba credit Dinka ba. .......Allah ya bada
hakuri. Kina Ina ne?
Ni na Fara maka wannan tambayar baka bani amsa ba don haka........ohhhhh na ma hangoki.
Kawai ya kashe wayar.
Ta Fara waige waige....
**************
*KADUNA RIGASA*

Kutumar bala'i .....Kai Wai me aka daukeni gidan nan?
To bafa Zan Dauka ba.
Daman some somen hauka zubda miyau, Ni fa ko lallashin da akeyi ma Amarya ban samu ba,
bani da wata kima sai ta bisa gado ya iya lallaba da lallashi bisa gado....yau za ayi ta takare.
Ta tashi Yana kwance rubda ciki, ta banka kofar da karfi har ya Dan razana....kace nan ba gidan
mu bane daman na ce Nan din gidan mu ne?
Ya dago Kai da sauri ....kada ki kawo man hauka....an kawo ma hauka kayi maganina Mana
mijin tace?
Nine mijin tace?
Kaine......kana da wani sunan da yafi wannan shanyayye?
To Bari kaji in fada maka idan an shanye ka ni ba'a shanye Ni ba, ba malam ba boka amma
dole ka maidani gidan ubana bani wannan wahalallen auren naka marar fa'ida..... Ke ba a Isa a
Gaya miki gaskiya ba ko? Duk lokacin da kikayi kuskure aka nemi a Miki gyara......haka ake
gyara a wulakance da cin fuska? Ai Daman kallon ka nakeyi tun kafin in zo gidannan kake nuna mun bani da wani matsayi sai
matarka..... Shut up.....ya daka mata tsawa......bazanyi Shurin ba......ita ma ta daka mishi
tsawa....ka sake Ni a yau Mana idan kana ganin Kai ke iko da kanka ba wat ke juya ka ba. Idan
Kuma baka iyawa .....ta bude kofa kazo ka wuce ka tambayo ta idan ta amince yau ka bani
takarda ta ita wacce ke auren naka.
Kai Bari kaji in fada ma Bashir.....wallahi wallahi baka cikin tsarin mazan da nake so in aura
saboda Ni duk Mai mata baya gabana musamman Wanda bai da gabata irinka sai abinda aka
gindaya mishi.....Ummi Ashe Baki da kunya?.... Yau ne kasan haka?
Kai baka iya maganin rashin kunya ba?
Ka je ka tambayo ta ya ake maganin marar kunya sai kazo kayi hakan Dani mijin tace....fuuuuu
ya tashi yabar dakin ta bishi tana balbala bala'i ta inda take shiga Bata Nan take fita ba....idan
hankalinsa tayi dubu yau a tashi yake, yayi hanyar dakin Amirar....ta daga murya....Arrrrrr Ni
nasan baka da idea din kanka sai wacce aka saka maka.......nesa nesa yake Jin maganar. Da karfi yake buga mata kofa.....a rude tazo cikin tsoro take magana...wanene?
....ke bude nine....da sauri ta bude....lafiya baban Ahmed?

Waccen yarinyar Bata da tarbiyya Amira wallahi wallahi ban tunanin Zan iya Zama da ita.....Nan
da Nan tamu ta mata ta motsa ( kishi )....to Yanzu me kake nufi?
Zan kwanta anan ne saboda........saboda ita tafi karfin ka?
To ba anan ba wallahi.
Ta barshi tsaye ta shige dakinta kawai tasa key........
Ya zaro ido

Nima na zaro nawa........✍

Ayi hakuri da kadan.......✍ *ZAINAB WOWO*
*Maman Abdallah*�
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: *WA ZAI FURTA?*
0⃣9⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya
shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*Wallahi tallahi inajin dadin masu kirana da mun text WhatsApp musamman don jinjinawa Aunty
Rabi dayi Mata addu'a da masu yiwa mahaifina addu'a na gode Allah yabar kauna my fans my
pride ana mugun tare irin sosai dinnan*�.
*Arziki irin na Aunty Rabi kowa ke fata Wanda zaka ba kowa ba arziki irin nasu o'e ba daga mu
sai 'ya'yanmu Wanda ya tsargu dashi nake*‍♀

_Wayata na bani matsala wallahi Shi yasa bana update da wuri_


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Ke ta tabance UMMI MAMAN KHAIRAT DA ZARAH, makwabciyar Alawiyya Ina godiya*

*Unex*�( Babu kamar ki ).

*Alawiyya Ina Kara godiya fa Allah yabar tare Allah yabarki da malam ya tsone idon
munafukai*

*AUREN FARI FANS*����one love well.

*INA CIGIYAR MZ*

***************
*KADUNA RIGASA*
Tabbas Ummi Taji uwar bari,

Ta zabga uban tagumi, competition zanyi da Amira wallahi dole in ajiye wannan jahilcin in
kwatar ma kaina yanci. Mutane dake cewar duk namijin da yayi sabuwar Amarya uwargida ta
Zama banza yau na karyata hakan, naga inda year gida ke fin Amarya daraja da kima.
Tun kafin inzo gidan Nan yakeyi man gargadi akan matarsa, ban Kara tabbatar da hakan ba
sai da nazo, Bata laifi, bata gundurar sa. Ya Zama wajibi Nima nabi hanyar da tabi don
mallakarsa.
Ranar ya koma aiki, tunda ya tafi tana bangaren Amira suna fira, abin ya bata mamaki ganin ba
wani alamun sauyi daga fuskarta, ta sakar Mata jiki suna ta fira Mai dadi ( ba abinda yafi Zama
lafiya dadi, abinda mutane suka kasa ganewa kenan ).
Ta Dan muskuta Aunty wata alfarma nake nema wurin ki.
Ta kalleta cikin natsuwa sosai kafin tace Ina jinki ummi.
Wallahi Aunty na rasa gane Kan Abban Ahmad ko wane lokaci duk abinda nayi Ni Kam ban iya
ba.
Kinga ko abinci na dafa mishi idan na kawo mafi yawa fushi yakeyi yabarshi a wurin Koda kuwa
nayi abinda yake so. Idan Kuma na sameshi daki...........ohhhhh na fahimci zancen ki. Ta
katseta tana Yar dariya.
Baya Miki korafin Baki da kula?
Wallahi yanayi Aunty.
Yawwa, kin gane, Shi mutum ne Mai son kula gaskiya.
Misali: wurin abincin da kike korafi, Shi yafi so idan Kika kawo mishi abinci ko ki zauna kuci tare,
ko Kuma ki zauna kusa dashi yanaci Koda kuwa kin koshi, ya tsani ki bashi abinci kibar
wurin.....ke abinda ma yafi so Bari in fada Miki shine ki na bashi da kansa.
Ya tsani lokacin da yake zaune dake ki maida hankali akan waya ko kallo ko wani abu saboda
Shi mutum ne Mai tsananin son kula.
Ko a kwanciya ya tsani mace tayi mishi tabababaaa Nan da Nan sai ya harzuka.......gabanta ya
Fadi...tohhh wannan dalilin ke sawa kullum sai sunyi rigima?
Ikon Allah.
Ta yi shiru dai, taji Amira ta shiga ranta sosai ganin ba bakin ciki ba Jin zafi ta zauna tana Mata
irin wannan bayani Mai tsada Wanda ta tabbatar idan ita ce bazatayi hakan ba.
Kunya ta kamata sai kawai ta sauko bisa kujera.....Dan Allah Aunty Amira kiyi hakuri abubuwan
da nayi a baya wallahi hada zuga irin ta mutane Amma Yanzu na gane........Dan Allah tashi ki
zauna ba komai. Shawarar da Zan baki shine ki kuji fitar da sirrin auren ki ga ko wanene wasu
ba shawarar kwarai zasu Baki ba, ko meye kiyi keda mijinki ba Wanda yaji ya gani ko wace Kika
gani gidan aurenta wallahi hakuri takeyi. Shi Aure 90% hakuri ke raya Shi sauran 10%din ne
ilimi da soyayya. Saboda haka Dan Allah ki zauna mu fahimci juna tunda kaddara ta hada mu
ba kanmu aka Fara ba iyayenmu da kakanni duk haka muka gansu Kuma zamansu lafiya ba
don Babu kishi ba sai don hakuri da hangen nesa.
In shaa Allah Aunty Zan kiyaye Allah yayi Mana jagora..........
Tirkashi, competition zai tashi muje zuwa muga cikin Amarya da uwar gida wacece zata amshi
first position????????
**************
*Federal University dutsinma*

Yana son buga tsalle ya kasa , kanshi ya kumbura jinshi yake Babu kamar sa, ya gyara kwalar
rigarsa sannan ya kalleta sama da kasa I warned you several times but u refused to listen to
me, idan takamar ki *Hauka* ki sani Nan school din akwai *iyayenki*.........Shima yasa Kai yabi
bayan Bilkisu. Wuri ya dauki ihu.......mufeeda tayi tsaye ta kasa motsi tana sonyin kuka Amma
ta daure kada ta Kara zubda ma kanta abin magana......
Yasan wata sabuwar rigimar ce, tana niyyar Zama Aisha tace me Kuma ya faru naji ana ihu?
Ni da waccen sakaran fa, ta tareni jiya suna mun wani kuri na banza akan Anwar shine na kaita
gabansa nayi Mata nawa gargadin ta gane cewa ni ba tashi nake ba........wa?
Aisha ta bukata tana zaro ido.....dai dai lokacin da ya karaso tayi kamar Bata ganshi ba tace
*Anwar* Mana.
Me nayi? Ya bukata tare da tsareta da ido,
Wai ke me yasa bakya Sona da kwanciyar hankali?
Ta kalli Aisha tana Yar dariya kinji fa?
Sannan ta kalleshi, Da sunyi mun tsinannen duka jiya ai Ni Dana shiga tashin hankali ko? Ya
zaro ido, duka?
Ta balla mishi harara wallahi tallahi duk ranar da ka janyo mun duka wajen ajabon Yan matanka
a school dinnan har Kai sai sunja maka bala'i don security office zanje nayi reporting......ya
kyalkyace da dariya Yan matan nawa ne ajebo?
Ke meye naki da zasu dake ki?
Ban sani ba kaje su baka amsa........ya Kara dariya matsa in zauna.....da sauri ta matsa ganin
Yana kokarin Haye Mata kafa.......kana da hankali Anwar?
Wani lokacin Ina taba hauka,, ya fada Yana dariya.
Aisha Mike Kai wallahi bazan biye muku ba Bari in koma baya inyi karatu.
Ita da yunkura zata tashi yayi saurin rike habar hijab dinta ya mayar da ita ta zauna....... Ba inda
zakije wallahi.
Wai ke me yasa kin rainani?
Idan kina son abu gardama banayi sai nine Zaki ..........zaniyi me?
Mutane fa na kallon mu ya sunan abinda kayi?
Aisha ta girgiza Kai ta wuce tana murmushi.
Tasha mur, karatu zanyi ko ka tashi ko Kuma Ni na tashi.......babu daya ciki. Kiyi abinki bazan
dameki ba.
Gobe ne birthday dina me Zaki bani gift?
Tayi murmushi kai dai ka cika roko wlhi. Zan siyi ledojin pure water na ba Yan class suyi maka
wanka,
Tabbb, ai bazan zo class ba gobe saboda hakan.
Wasa kakeyi ......
Allah kuwa.
To shikenan ka huta.
To meye Zaki bani?
Ta kalleshi cike da kosawa to meye Zan baka ne?
Gift!, Yace Yana Yar dariya.
Ta Sha mur, ka Fadi abinda kakeso Zan baka.
Zakiyi mun special girki, sannan ki kaini shopping.......... Ta kyalkyace da dariya.

Yabi kumatun ta da kallo Yana son dimple dinta ainun.
Shikenan Zan maka what next?
Karfe nawa zanzo?
Da safe kafin na tafi class kaga gobe har 6 Ina school.....no is too early. Bayan magrib dai.........
Bana fitar dare sai dai kazo 2 kafin muyi lecture 4........ Hmmm shikenan ya fada ba don ransa
yaso ba sai don gudun kada tace duka ta fasa.
Tare suka shiga test din ka kujerarta ga tashi. Ta kanga mishi fuskar computer din Yana tashi
yanayin nata.
Sai gashi suna gamawa taci 20/20 Shi Kuma Yana da 18/20.
Tayi ta tsalle tana Murna.
Sun jero sai dariya takeyi tana Jin dadi, ta kalleshi yau wace rana naci CBT 20 last session
wallahi naci da yawa 11 ko 12.
Murmushi kawai yayi.
Ta hango su Aisha shikenan bye bye wanna go thank you till tomorrow.
Ya juyo zai magana tuni ta tsallaka tana sauri so takeyi kawai ta Basu labari.
Ya danyi tsoki kawai ya wuce.
Nawa kuka samu?
Aisha ta yatsine fuska 13, khausar tayi tsoki Ni 10....... Wallahi saura kadan na shiga cikin
department dinku Kinga ruwan Yan 7,8 da 9?
Ta zaro ido wallahi Anwar yayi mun duka na cinye........duk suka zaburo 20?.
Cike da Murna tace wallahi kuwa.
Ohhh Allah ya kashe ya Baki inji Aisha.
Ai yau nayi sa'a Kuma wallahi ba layi daya muka hau ba.
Yana tsaye shagon Abdul ya hangosu.
Kamar ya kwada musu Kira kwatsam sai ga Dr Dan Musa ya tari gabansu.
Bilkisu see me by 2 in ma office........okay sir. Ta ce kawai suka wuce.
Wahalalle naga ubanda zai gani.
Baki zuwa? Inji khausar,
Eh, kullum aikin kenan kuma ba wat maganar arziki ba kame kame.
Anwar ya bishi da harara lokacin da yazo zai gitta.
Bayan sallar la'asar ta tafi dakin su Jennifer sukayi mata kwatancen gidan zainab wowo wacce
keyi wa Yan makarantar cake. Ta iya cake sosai na biki da birthday ga sauki.
Aisha ta rakata. Mata Mai fara'a ta amshe su hannu biyu biyu.
Sannan suka ce cake sukeso na birthday Amma na maza.
Tace ba matsala.
Ko na nawa kike so Zaki samu. Kuma karfe nawa? Akwai Wanda Zaki ba yakai man goben
wajen 1:30 haka?
In shaa Allah bani number da za a nemeki da ita.
Sukayi musayar number ta biya kudin babban cake na gani na fada.
Bayan sun fito ta kalli Aisha Zan surprising din sa ne.
Suka biya super market ta siyo manya manyan lemuka carton daya *na grapes*
Hmm kawai Aisha ta ce tana murmushi.
Ta harareta, Fadi ta cikinki Mana, *there's nothing ooo just wanna surprise him and show my

gratitude on what he has done for me Sha*
I knew, inji Aisha tana Yar dariya.
Karfe shidda na safe ta tura mishi text ```Happy birthday Anwar wishing you more dollars in
your account, you are an amazing person stay blessed```
KO minti daya ba'ayi ba yayi reply
``` Thank you my personal person```
Murmushi kawai tayi.
Shi kuwa ya karanta text din yafi sau dari.
Ko wa ka gani a class da ledar pure water saboda Shima haka yakeyi wa mutane Amma ba
Anwar ba alamar sa, ko su sadeeq Basu San cewar baya zuwa class ba.
Bilkisu kadai tasan haka.
Sadeeq ya karaso kusa da ita hajia Kira Mana Anwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login