Showing 57001 words to 60000 words out of 94796 words

Chapter 20 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

3843

sumke dariya.
Suna saukowa yace hau Bilkisu...... Tayi karfin halin maka mishi harara sannan ta dafa Aisha
suka wuce..... Ya biyota Baki lafiya amma Baki daina gardama ba ko?
Dashi aka shiga wurin doctor.
Ka ce ya fita , ta fada tana kallon doctor din cikin fushi..,.. yadanyi dariya to kaji yallabai an
koreka.
Wallahi ba inda zanje ka Mata test kayi scanning..... Ya Fara Mata tambayoyi.
Ta yi shiru.. akayi Justin duniya tayi magana taki.
Dole Anwar ya fita. Yana fita sadeeq na isowa....Aisha na zaune tayi zugummm tana kallon ikon
Allah.
Doctor menstrual pain ke damuna Amma bana son ya sani. Ina Shan wannan maganin amma
baya mun idan akwai Wanda ya fishi pls help me...... Ya danyi murmushi I expect it.
Ya karbi maganin ta runtse ido tare da dafe cikin lokacin da ya katsa.....
Sorry ya fada tare da mikewa..... Ya dauko wata allura yace Amma fa zata Sanya ki barci sosai,
sannan ya rubuta wani magani ya ce gaskiya babu Shi anan sai Kano ko katsina Yana da tsada
kwarai.... Ba komai rubuta... Burummm ya banko kofa daidai ya Gama allurar tana murzawa. Ta
dalla mishi harara..... Doctor meye tace Yana damunta?
Yayi dariya it's normal an Mata allura ga magani nan na rubuta Yana da tsada da kudi sosai.......
Ya karbe takardar Yana karanta sunan maganin.
Ya fiddo waya..... Hello musbah ga magani Nan Zan turo maka asiyo mun carton dinsa a Aiko
Yanzu Yanzu ko ka tado wani ya kawo sannan kace a fada maka maganin menene da Kuma
yanda ake shansa.
Kaje wurin nagari pharmacy kace ni na Aiko kaga hamisu a wurin.......

Ya Mika mishi hannu thank you doctor.
Tashi muje.... Idan kin hada Baki da doctor wannan maganin zaisa na San komai.
Idanunta suka Fara nauyi alamar allurar ya Fara aiki.
Allaurar zata sanyata barci sosai fa.....okay.
Ya ce Yana Shirin Kai hannu ya taba ta, ta mike da sauri tare da maka mishi harara...... Yayi
dariya Kai yau Ina Shan harara ni Hamza.
Ta fito ya biyota ga oat din ki zauna Kisha Aisha Bata... Ka barshi Zan Sha a daki.. muje please.
Ya kalli Aisha allura akayi Mata Mai Sanya barci shine ke dibarta ga idanunta nan sun Fara
canzawa da kunje kada ki yarda ta kwanta bata ci komai ba...... Ko na ajiyeta.... Ya banka mishi
wani kallo. Wancen Mai napep din da na tsayar Kuma fa?
Ta kalleshi ka bi sadeeq ku tafi mu sai muje a napep din na gode.
Kamar zaiyi gardama yayi shiru....sai Kuma ya kada Kai okay.
Idan kin tashi barcin ki mun flashing please.
Ta ce toh.
Ya zaro dubu biyu ya Mika ma driver yace mayar dasu inda ka dauko mu.
Ya Dan leka Allah ya bada lafiya Zan kawo Miki maganin kinji ko?
Ta ce toh, tana ta faman lumshe ido..... Jinsa take har cikin ranta. Bata so ya tafi.....ashe shima
hakan yakeji.......Sadeeq ya kalleshi abokin Bilkisu..... Ya Kai mishi duka. Shi Kuma ya tuntsure
da dariya.....

Ta kalli Aisha kinji yayi waya maganin da aka rubuta a kawo carton dinsa daga Kano.....ta zaro
ido carton?
Wallahi....
Bilkisu Anwar ya Fara bani tsoro...Nima Aisha. Anwar Yana bani tsoro. Da na motsa sai yace
mun friend.... Ke ya mayar friend wannan abun nasa ya Fara wuce shari'a...Ni saboda ma duk
na rikice can daki na bar wayar.
Aisha tayi dariya nima. Wai Kinga yanda ya wani fado kamar an jefo Shi????
Tayi tagumi tawa ta sameni Aisha......
Ta kyalkyace da dariya ai sai ma ya *FURTA* saboda tabbas Anwar gabbb yake da furta Miki
Yana sonki alamomi dai sun gama bayyana..... Gabanta ya Fadi ta dafe kirji..... Na shiga
uku.....ta galla Mata harara *Baki sonsa?*..........✍ *Zainab wowo*�

mowa
� Unex
Alaweez
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: *WA ZAI FURTA?*
2⃣0⃣
*Gargadi* Bana son ana rubuta mun komai a page din dana tura. Naga 1⃣9⃣ wat t rubuta *Anzo
wurin* bana so. Duk wacce ta Kara taba mun page daga ranar *Wallahi wazai furta ya Kare*
Labarin Nan saboda soyayyar makarantar ne nake rubuta tashi na fada don ku nakeyi to a
daure a karbi iya abinda aka gani.
Sannan masu cewa na Sanya sunan su a page ku sani cewa wallahi idan dambu yayi yawa
bayajin Mai. Duk yanda kuke Sona wallahi nafiku. Akan KU nakan hana kaina abubuwa da

yawa don kada na Bata muku. Dan Allah a bani uzuri. Ina kaunar duk Wanda ke Sona ko
wanene wallahi bana Raina masoya.���

Tsoron Corona yasa har yau na kasa lekawa RIGASA KADUNA



*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya
shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

�� *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this
always*.

****************

*Federal University dutsinma*

........Ta rude ta kidime Ni kake Kora..... Ya bude mota da karfi ya fita ya zagayo ya bude kofar
bayan....get out I said are you dumb?
Kwalla suka zubo Mata sharrrr...... Ta sauko a hankali. Suleiman na gefe yaga ta fito.
Ya koma gefe ya tsaya, tana fita ya maida kofar da karfi gammmm. Ta kalleshi da sauri, ya
banka mata harara am I safe now??? Idanun sa sunyi jawur duk sun kawo ruwan masifa.
Ta kawar da Kai ta nufi wurin driver ya finciko ta da karfi kada ki shigar mun mota...... Zan
dauki plate ne ta fada kwallah naci gaba da shatatowa.....ya ingijeta ya kwaso plates din watso
kasa....ya kalleta Yana zare ido you can go now!!!!!!........ Anwar duk akan Suleiman....... Ya
doka tsoki ya juya zai fada mota, wata zuciya ta debeta Bata San lokacin da ta fizgo rigarsa ba
ya dawo da karfi...... Kai har ka iya kamun irin wannan wulakancin in kyaleka??........ Ya zaro
ido. Suleiman dake kallon su shima fiddo nashi....... Ya daskare ya sankame tare da tsareta da
jajayen idanun sa.....Wai me yasa yarinyar nan bata tsoro na.????
......... Kwallah kwance cikin idanun ta, ta turashi da karfi bayanta ya daki murfin mota tayi kansa
kamar zata matseshi duk ta fita hayyacinta......... Na rokeka kazo Nan????
Ya yunkura zai dawo ta mayar dashi da karfi wasu zasu wuce suka Dan tsaya kamar zasu
fahimci wani Abu, hakan yasa Shi kasa biye Mata kada su Tara jama'a........ Na ce kiranka nayi
kazo??????
Matsa Bilkisu in wuce..... Ta galla mishi harara sannan ta juya kadan ta kalli inda ya watsar
plates din ta ce ```dauko su day hanmunka``` ...... Ya kalleta da sauri..... Wallahi tallahi ka dauko
su ka Miko mun da hannunka ko Kuma nida Kai har abada mun rabu daga Nan...... Gabansa ya
Fadi... Ya Kara kallonta.

Ta matsa nesa dashi ta tsaya tare da rungume hannuwa..... Kaka kara Kaka...ya yi
shiruuuu..... Ban tilasta maka ba, kana iya shiga mota ka tafi, wacce ka koreni cikinta kana
ikirarin *motar ka*........ Ya runtse ido, taci gaba da cewa Amma ka sani na fita motarka salin alin
wallahi Alan plates din nan Zan rabu dakai rabuwa ta har abada........ Ya Kara runtse ido tamau. In ba rainin wayo ba, Kai har yau baka ganin kowa da mutunci kana iya cin mutuncin kowa
baka shakkar......kawai taga ya dauko plates din ya Miko mata. Fuskar sa murtuk....... Ta karba
ta juya...... Kizo ki dauki maganin...... Bana so *jikan karuna*..... Ka hada da maganin da motar
ka cinye nafi karfin dukiyarka da wulakancin ka Anwar...... Ya fizgota da karfi, Ni kike gayawa
magana????........ Ta fincike an fada maka ta nuna Shi da yatsa wallahi Ka Kuma taba ni Zan
sharara maka Mari....... Ya zaro ido what?????
Ta kalleshi shekeke....kafi karfin hakan ne? To idan kana musu ka jaraba... mtsewww ta buga
tsoki ta juya.....ya tari gabanta da sauri....
Wai ke da me kike takama ne? Ya fada da karfi..... Lokacin ne Suleiman ya karaso.
...... Anwar meke faruwa ne...... Ji kakeyi tasssssssss ya ramtse Shi da Mari..... Ya kidime ya
gigice..... Bilkisu ta ja baya da sauri tare da daura hannu aka...... Yana dagowa ya daga hannu
zai Rama ya Kara wanka mishi biyu double one after another.....sai jini ta hanci......... Bilkisu ta
kwada ihu zata ruga ya janyota da karfi ta dawo kanta ya daki kirjinta........ Gashi na taba ki ,
Kuma na Mari wannan Dan iskan sai ki Rama mishi Kuma ki hukuntani da wani Marin Wanda
Kika mun...... Ta zukunna kasa ta fashe da kuka .... Ya kalli Suleiman ko bar nan ko na halaka
ka....... Suleiman Dan Allah tafi..... Dan girman Allah Suleiman tafi..... Sai nanatawa takeyi tana
kuka, yasa habar rigarsa ya toshe hancin ya wuce kawai Yana huci,... ya fizgi Wayarta ya Kira
Aisha..... Anwar ne fito ina waje......
Cikin hanzari ta fito, ganin Bilkisu duke tana kuka yasa ta rikice wata kila ya Mata halin nasa..
Ya fiddo kwalin maganin ungo kije Mata dashi ciki, ko soke soken wuka mukayi hakan bazai
shafi neman lafiyarta ba........ Bana so Ina ruwanka da lafiyata??? Aisha bar mishi tsiyarsa bana
so, ta rushe da kuka........ Kin dai ga halin kawarki ko? Kiyi Mata fada........ Haihuwata tayi da
zata mun fada? Wai me ya faru Bilkisu??? Aisha ta bukata cikin damuwa....... Wai daga Suleiman ya kirani a
waya fa, Ina abinda ya dameshi da wayata Ashe Yana son yace mun yazo ne ...... Uban me
yazo yi?........ Kai me ya kawo ka? Ta daka mishi tsawa..... Ta kalli Aisha Kinga Marin da yayi
mishi ya fasa mishi hanci........ Innalillahi yaushe? Aisha ta fada a rude. Yanzu Mana, Ya buga tsoki, idan Baki ja mishi kunne yayi nesa da ke ba wallahi Zaki janyo mishi nasifa da
bala'in....... Kai a wa? Ta Mike tare da rike kugu..... Ya kalli Aisha Kinga irin action dinta da mood
ko? To a duk lokacin da wancen Dan iskan..... Ka daina zagin sa wallahi..... na ce mishi Dan
iska ko Zaki Rama mishi?........ Don darajar Allah kuyi hakuri......... Bilkisu ta buga tsoki ta juya
kawai ya fincikota da karfi........ Ta kuwa Kama hannunsa ta gantsara mishi cizo da karfi.....ya
saketa da sauri Yana fadin Kai Kai Kai Kai, ta kwashi kasa ta watsa mishi a jiki sannan ta kwasa
da gudu tayi ciki........ Tana shiga daki ta Sanya sakata ta ciki....... Ya biyota a guje, kafin ya
karaso ta garkame........Aisha ta rude ta rikice gidan ya harmutse Jin irin hargagin da yakeyi
akan ta bude..... Wallahi zan karya kofar nan ki bude kizo ki fada mun dalilin watsan kasa......
Ban budewa.......har daya yayi ma kofar ta fada ciki tayi tsalle ta Haye katifa ganin zata
bigeta........ Aisha ta Fara rokonsa yayi hakuri ita Kuma ta makure ta Fara ihu tana kuka........ Ni
Zaki watsa ma kasa saboda wancen Dan iskan........ Wallahi ba saboda Shi ba....... Ya

sungumeta a kafada yayo waje Aisha da sauran mutane suka biyo su....... Ya juya duk shegiyar
data fito sai na karya ta. Aisha zo muje........ Ko wace tayi dakinta tana surutai......... Kafin kace
kwabo magana har kunnen mufeeda.
Ya direta jikin mota ya kalli Aisha tambaye mun ita dalilin watsan kasa.......Dan Allah kayi hakuri
Anwar.
Kika kawai Bilkisu keyi......
Ya kalleta ke kina da gadara da taurin Kai ko? Kina tunanin duk wannan abun ba shine Kika
janyo wa fitina ba?...... Dan Allah kayi hakuri Anwar. Aisha ta Kara fada.
Aisha na fadawa Yarinyar Nan bana son yaron can me yasa bazata kyaleshi ba?.......Akan wane
dalili Zan kyaleshi Kai meye naka aciki da zaka hanani mu'a mala da wani?.....saboda..... Sai
Kuma yayi shiru.
Saboda me?
To baka Isa ba, Yanzu na Fara kula Suleiman...... Kinji ko Aysha? Kinji abinda take fada ko?
Dan Allah kayi hakuri Anwar zata daina kulashi........ Yaudarar ka zatayi, ba Wanda ya Isa ya
rabani da Suleiman Kuma ka sani daga yau bani bakai, bana son abotar kaje ka nemi wata idan
na Kara ganin ka anan ko kamun waya Kai ko tunani na kayi a zuciya ban yafe.......... Ya buge
Mata Baki. Ke kin Isa ki yanka mun doka?
Ta rike bakin tare da runtse ido...... Ya kalli Aisha kina Jin halin kawarki ko? Duk garin nan akwai
yarinyar dake mun haka?
Ta girgiza Kai da sauri Babu kayi hakuri.....
Idan kin lura ta na nemana da rigima sosai......
Kayi zuciya ka kyaleni daga yau a fita harkar Bilkisu..... It's alright take care, Kawai ya fada
mota yaja ya tafi .... Gabanta yayi mummunan faduwa, ta yi shiruuuuu kafin Ta figi hannun
Aisha zo muje.
Suna zuwa daki ta fada katifa ta saki kuka.... Ai kinyi kuskure me yasa zakiyi mishi irin wannan
wulakancin Bilkisu...... Ta dago fuska jage jage da hawaye.... Aisha na rasa gane inda Anwar ya
dosa, masifar nan tashi ta isheni gara ya kyaleni na huta.... Wallahi bazaki huta ba. Ta Kara
kallon ta da sauri, yes bazaki taba hutawa ba saboda kina matukar kaunarsa.... Bilkisu nasanki
nasan wacece ke, gwargwado nasan waye Anwar shima wallahi tallahi matukar baku fito Kun
fadawa junanku surrin da ke zukatanku ba tabbas zaku kashe kanku a banza...... Ni na taba
ganin jarababbiyar soyayya irin taku?
Ko wane idan kishin Dan uwansa ya motsa sai ya Kare kansa?...... Ta kife Kai a filo ...ta Kara
sakin kuka a hankali.......
Idan kin gama ki tashi kiyi parking, ga maganin nan na dauki kwaki goma .... Ta fice jikinta duk
ya mutu tana mamakin irin wannan soyayya wacce ko a littafi Bata taba karanta irin ta ba.
Gaban sadeeq ya Fadi....... Anwar lafiya na ganka a firgice haka ko jikin....... Tashi ka shirya
mu tafi Kano.
What?
Ya mishi wani kallo gaban Sadeeq ya Fadi ya tsorata Anwar lafiya?
Zaka je ko na tafi?
Ya kamo Shi ......ya fizge sadeeq Dan Allah ka kyaleni *I hate this world*........ Ya ci gaba da
harhada Kaya...... Dole sadeeq ya Mike shima ya Fara hada jaka..... Amma wallahi bazaka tuka

mu cikin wannan mood din ba ... Bai rufe Baki ba ya wurga mishi keys din a kirji ya figi jakar sa
yayi waje..... sadeeq ya bishi da gudu tare da rufe dakin....Sha biyu da Rabi na dare suka bar
dutsinma yana kwance a sit ya Dora kafa daya a dash board ya kwantar da sit yayi filo da
hannayen sa idanun sa rufe..... Kadan kadan sadeeq na lura dashi sai faman tsoki yakeyi. Batayi tunanin abin zai dameta ba sai da ta koma gida, kwana daya , biyu...sati. Anwar bai
nemeta ba.
Suleiman kuwa yayi Kiran duniya ta kasa dauka kamar tana son Jin haushin sa ganin shine
jigon wannan fitina.
Gaba daya gidan an ga canjinta, bata walwala, kullum tana daki kwance.
Ranar da tayi sati biyu da dawowa mommy ta sameta daki, ta zauna bakin gado, Bilkisu mi ke
damunki? Na lura tunda Kika dawo Baki da walwala, meke damunki? Saboda har dadyn ki ya
Kai ga yin magana...... Ko maganin da Kika ce Anwar ya siya Miki ne kike ganin yayi
yawa?....sai kawai taga kwallah na zubo Mata.... Hankalin momy ya tashi ko dai daukar magana
Yar tata taje......subhanallah. tayi saurin kawar da tunanin. Ta janyota fada mun menene?
Ta goge hawayen mommy bana Jin dadin abinda Anwar keyi mun...... Ta Bata labarin duk
abinda ya faru..... Sai kawai taga mommy na dariya.
To Bilkisu Anwar ai kishi ne ke damunsa tunda baya son ki kula Suleiman din sai ki kyaleshi....
Ina wayar ki?
Ta Mika Mata kawai..... A'a Anwar din Zaki Kira kice yayi hakuri tunda ke kin damu bai Kira
ba..... Tabbb wallahi bazan kirashi ba mommy..... To ya Zama dole ki fitar dashi a Ranki domin
Shi da alama ya manta da ke kamar yanda Kika mishi gargadi...... Kirjinta ya buga da karfi
kwallah suka Kara cika idonta ...mommy ta mike wannan shine sai ki zabi daya cikin biyu,
Amma bazan dauki wannan dararewar ba da kikeyi cikin gidan Nan... Tana Gama fada ta fice
tare da Jan kofa gammmm.

Tayi zugummm, dabara ta fado Mata kawai Bari ta Kira Sadeeq......
Anwar kuwa yafi Bilkisu shiga tashin hankali, ya koma kurman karfi da yaji, hankalin Hajiya
yayi mummunan tashi tana zargin ASIRI ne ke son kamashi.
Ita kadai ke shiga dakin sa sai kuwa sadeeq, kullum sai ta lallasheshi yake cin abinci....
Abun har ya Fara affecting kasuwar sa, kowa shakkar kiransa yakeyi a waya saboda masifa da
bala'i.
Tana zaune ta tsareshi ya shanye tea din ta Sha mur alamar ba wasa kamar kullum, ya Sha
mur, ya tsuke fuska rabonsa da dariya tun ranar da ya rabu da Bilkisu Yana cusa kwai a Baki
jinsa yakeyi kamar madaci.
....... Sadeeq ne ya turo kofa Assalamu alaikum.
Hajiya yau kina ciki?
Eh sadeeq maraba, Wa'alaikumus Salam.
Kamar zatayi kuka ta kalli sadeeq na rasa ainahin meke damun Anwar, shin ko ta sanar dakai
......ya wurga mishi harara Yana horonsa da ido kamar kullum akan kada yace wani Abu......
Hajiya ina ga malaria ce, kin San fa dutsinma akwai sauro sosai Daman ya Saba duk hutu sai
ya kwanta ..... Ba irin wannan kwanciyar ba. Yaro ya takure ya makure sammm Anwar ko
murmushi ya daina yi...... Zai dawo normal hajia aci gaba da addu'a.
Ta Mike , kaima ai bakin ku daya, ko ma menene bazan yarda da wasa da abinci ba... Ta fita.

Ya kalleshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login