Showing 1 words to 3000 words out of 84763 words

Chapter 1 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt

[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writter Asso*☀️



*shafi na ɗaya*


Wani irin kuka take mai tsuma zuciya kai dagajin kukan kasan irin kukan nan ne wanda yake tasowa daga karkashin zuciya, ba kowa ke gane mai kakeji ba sai wanda yataɓa irin kukan"Yah Mus'af mai nake gani da gaske ne?dan Allah kagayamin ba gaskiyya bane wannan katin dana gani bana gaske bane kace karya ne" gaba ɗaya yayun nata dasuka zagayeta ba wanda yai magana wanda ta kira da Mus'af kasa yayi da kansa yana kwafa, kallo ɗaya zaka masa kasan ran maza yaɓaci saboda tsananin ɓacin rai yama kasa magana, Mami da batasan abin dake faruwa ba futowarta kenan daga ɗakinta da shirinta natafiya wajan aiki da sauri ta karaso wajan su inda taga yaran nata gaba ɗaya a tsugunne sun saka Aimanah a tsakiya "Mansur maiya farune kuka zagaye Aimanah lafiya?" da sauri wanda aka kira da Mansur yaɗago batareda yayi magana ba ya nunawa Mami katin hannunsa yamaida kallonsa kan Aimanah dake kuka har sannan kamar ranta zai fita, Mami da sauri ta lalubi kujera mafi kusa ta zauna saboda wani jirine yaɗebe tai luuu zata faɗi kaɗan yarage taje kass tasoma ambaton "Innalillahi wa'inna ilaiheer raji'un ban gargaɗeku akan maganar nan ba Muneer bakuji abinda nafaɗa ba"

Adakile Mas'ud yafara magana ransa ɓace "Mahh mufa bamu muka gaya mata ba da abinta ta shigo gidan nan"

"Ku bani waje, ke Aimanah zonan"

"Mah yanzu dan Allah shi..."Kamun shuru Mus'af" mami tafaɗa a tsawace ranta ɓace, fuuu Mus'af yafice daga falon kamar yana shirin tashi sama Mansur Yakalli Manneer yace "Bi yaron nan ban yarda dashiba kasan halinsa" da sauri Muneer yafita Mas'ud yakalli agogo yai tsaki yafice.
Ma'aruf yakama hannun kanwar tasa yamikar da ita tsaye yakaita wajan Mami, kanta taɗora saman cinyar Mami tana cigaba da kukanta
"Yi shuru Aimanah daina kukan muyi magana, nasani nasan abinda kikeji please daina dan Allah"
"Mahh nayi shuru kike cewa fa?"Katin ɗaurin auran Al'Mustapha nagani, yanzu Murja tabani shi a kofar gida har tana gayamin maganganu marassa daɗi"
"Naji daina manta dashi"

"Mahh daman daina zuwan da Mustapha yayi fasa aurena yayi shine kukaƙi gayamin gaskiyya kuke faɗamin yakoma jordan ashe yana kasar nan Mah mainayiwa Mustapha ya yaudare ni har haka?"

"Baki masa komaiba Aimanah lamarine ya canza" Ammi ke faɗin haka wacce tashugo falon yanzu fuskarta cunkushe da damuwa, a kasa ta zauna tareda wurgar da makullin motarta da handbag ɗinta, hawaye yafara zuba a idanunta tana kuka sosai
"Anty yaya zanyi ina zansa rayuta yanzu ya zanyi afasa auran nan Amarya ta cuceni wallahi nasan ba haka tabar Mustapha ba harni Mai sunan manya zai kalla yace min nayi duk abinda zanyi amma baizai fasa auran Sumayya ba" rushewa takuma yi da kuka tareda haɗa kanta da jikin kujera

"Saudat yakike so nayi ina kuke so nasaka raina, kuka yana maganin matsala ne?"Baya maganin komai ke kuka Aimanah kuka dame kukeso naji kubarni naji da kaina dan Allah"

"Kuka bashi zaiyi magani ba gaba ɗaya ku manta da komai kuyi addu'a ke Aimanah bar wannan kuka kona ɓallaki haba duk kinbi kin tasar mana hankali saboda Mustapha yafasa aurenaki Mustaphan shine autan maza" afusace Aimana tamike fuuu tawuce ɗakinta gado tafaɗa taci gaba da kukanta son rai anan barci yayi awon gaba da ita mai cikeda mafarkan Mustapha.

*Anty Amarya Home*
"Murjana ku kula da abubuwan nan sosai banaso asami matsala kisaka su a karkashin gadon idan kun gama jera komai, ki kula sosai kada su Hajiya Luba sugani kinsan dai wahalar damuka sha kafin a juyo da hankalin Al Mustapha kan Sumayya"

"Nasani Mama nafasan komai kuma zan kula da komai ba abinda zai faru, haba nabari akaga wannan layun ai bancika jininki ba Mama"

"Yawwa guda liyata Nasani nakuma yarda dake shiyasa nasako ki acikin wannan tafiyar banda ma auranku ya haramta da Mustapha ai daman da bashida mata saike"Sumayya ta haɗe rai tana hararar Amarya

"Kai Amarya nimafa zan iya"dariya kawai mama Amarya tayi tamike ta futa can falon ta inda yan uwanta suke shirin tafiya gidan Mustapha yiwa Sumayya jere, sai da suka fito tsakar gida da gayya Amarya tasaki guɗa tafara rawa tana wake wakenta, Ammi mahaifiyar Al Mustapha dake ɗakinta tana jiyo guɗar Amarya ranta yakuma ɓaci zuciyarta tai wani irin kunci hawaye suka zuraro daga idaniyarta kamar ta share amma zuciya taɗebeta ta fito afusace tana gafda fita daga ɗakinta Ahmad ɗanta na biyun dake tsaye a falon yana zagaye yace "Ammi dan Allah karki kulata kibarta da halinta neman abokin yi take kuyi atafi dake abaki ana faɗar bakida kirki wasuma suce bakin ciki kikeyi da auran ɗanki"
"Ahmad nabari fa kace in tsaya ina kallo anamin cin kashi akan ɗana, ɗan dana tsugunna na haifeshi amma arinkamin gadara afaɗa mana daman ai ba farin ciki nake da wannan auran ba yaje ya yaudari yar yayata sannan nayi farin ciki da nasa zaɓin Mustapha zai gani in..."
"Kidaure karki yiwa Yaya baki Ammi kimanta da komai kiyi addu'a, nagama maki shirin barin gidan nan kutafi saudiyya kuyi umara keda Aimanah ku ruki Allah akan wannan al'amarin na tabbata wannan aikin asiri ne kigafa irin soyayya dake tsakanin Aimanah da Mustapha amma yanzu ko maganar ta bayaso ayi masa"

"Ahamad saima kaga Aimanah yau tabani tausayi sai yau taji labarin auran nan bakaga yanda hankalinta yatashi ba, harna baro gida tana barci"

"Nasan za'ayi haka shiyasa Alhaji Mansur yace kar asanar mata naji daɗima daya kasance yana gari hakan ta faru yace abuja zai wuce da ita" Ammi bata tanka ba ta koma ciki duk da har sannan tana jiyo maganganun Amarya tanata sakin habaici

Alhaji Kamal tsaye a ɗakinsa yakasa zaune yakasa tsaye kallon kanin nasa kawai yake yanda yaketa zuba alawa biskit da goro cikin babban kwali afusace Alhaji Kamal yake magana

"Sadik nizaku tozarta? nace ba hannuna a ɗaurin auran nan amma kashige gaba kunason jonyo matsala tsakanina da amini na? da wacce fuskar zan kalli prop wanda muka gama tsaida ranar auran Mustapha da Aimanah dashi?"

"Da fuskar da kaje kanema masa auran Mustapha shiya zo yace maka yanason Aimanah yanzu kuma yadawo yace yanason Sumayya to mene aciki za'ayi masa auran dole ne namiji ne fa shi kabawa Alhaji Faruok hakuri kawai yarinya tanemi wani Allah baisa Mustapha mijinta bane" Alhaji Sadik yana gama faɗar haka yafuce da goransa da alawa a kwali batare daya kalli inda Alhaji Kamal yake ba.

Aimanah ko bayan data tashi daga barci alwala tayi ta gabatar da sallar la'asar da akayita tana barci addu'o'i tayi sosai sannan ta fito babban falon gidan, shuru ba kowa sai fanka da T b dake kunne suna faman aiki shuru tayi tazurawa tibin idanu tana kallo azahiri zakace kalon take amma a baɗini tunani take irin soyayyar dasukai da Al Mustapha

Alhaji Umar Farouk mai naira hafaffan garin kano ne a karamar hukumar Ɗanbatta wani karamin kauye dake karkashin ɗanbatta local govement mahaifin Alhaji Farouk ba fulatanine yanada arzikin shanu kaji zabbi akuyoyi da tumaki Farouk shine ɗansa guda ɗaya tak daya haifa hakan yasa bakaramin so yakewa Farouk ba, birni yakawo sa anan yayi karatun sceoundry bayan ya kammala yatafi A b u zariya acan yayi digiri yai masters ɗinsa, yadawo cikin garin kano da zama kasuwanci yafara kafin daga baya yafara koyarwa a jami'ar bayaro dake cikin garin kano, yahaɗu da matarsa Hajiya Aisha anan garin kano sukai aure shekera guda ta haifo ɗanta namiji ranar suna aka saka masa Mansur Aisha irin matan nan ne masu haihuwa duk shekara hakan yasa kafin shekaru shida auransu ta haifo yaranta maza biyar Cif Mansur ne babba Muneer Mas'ud sai Mus'af da Ma'ruf daga nan ta saida haihuwa ta koma karatu tazama cikakkiyar likitar mata tana aiki asibitin nasarawa, Bayan wani lokaci tahaifo kyakkyawar yarta budurwa yarinyar datasha gata wajan yayunta maza ba kamarma Mus'af wanda yaɗau son duniya yaɗorawa babyn da tun randa aka haifeta Ya Mansur dake ajin karshe a makarantar scoundry yasa mata suna Ummu Aimanah suke kiranta da Aimanah, Alhaji Farouk yanada babban aboki Kamal wanda sukai A b u zariya tare babban abokinsa ne kuma amini tare akai bikinsu da Farouk ya auri Asiya haihuwarta biyu duka mata anan gidan Farouk Alhaji kamal yaga kanwar Aisha Saudat ba ɓata lokaci akai auransu ta tare gidansa inda yake zaune da matarsa, Asiya da Saudat zama suke na amana bakajin kansu wata tara Saudat ta haifo santalelan ɗanta namiji aka saka masa Mustapha bayan wani lokaci Alhaji kamal na zaune da matansa da yaransa guda shida Asiya da Saudat zama suke na amana ba'ajin kansu atsakaninsu baka banbance wancan ne ɗan wancan gaba ɗaya yaran nasu ɗaya suka ɗaukesu suna kiran Asiya da Momy Saudat kuma Ammi, wata rana Alhaji Kamal sunje taro Katsina shida Alhaji Farouk anan yaga Naja bayan wasu satittika aka ɗaura auransa da ita yakawota cikin gidan sa yahaɗeta da matansa daga farko zaman nasu abin sha'awa sai daga baya Naja tafito da wasu halaye na rashin mitumci bata ragawa kowa a cikinsu hakan yasa suka tattara ta suka ajjeta gefe suka rungumi yaransu, Mustapha yana kammala scoundry ɗinsa kanin babansa Alhaji Sadik yatafi dashi jordan inda yake aiki, acan yayi karatunsa na gaba da scoundry harya fara aikin banki har sannan bai dawo nageriya ba yana can saidai waya, sosai suke zumunci da yaran gidan Alhaji Farouk waɗanda suka dungule suka zama zuri'a guda Mas'ud da Mustapha sa'anine abokai kuma komai nasu tare, scoundry ɗaya sukayi koda Mustapha yakoma jordan abotarsu bata rabuba kullum suna tare a waya,
Aimanah ta taso cikin yayunta masa masu matukar kaunarta kowa burinsa ya kyautata mata gata suke bata ta ko'ina saidai gatan dasuke nuna mata baisa sun bari ta sangarce ba daga tayi ba dai daiba zasu sata a gaba suyita mata faɗa da nasiha har zuwa sanda ta girma ta zama yammata saiya zamana komai suka samu na Aimanah ne ba kamar ma Yaya Mansur daya zama babban mutum yafara aiki a wani gidan talvision dake nan garin kano, Albashinsa na farko Aimanah yakashewa su saida Alhaji Farouk dasuke kira da Daddy yayi masa faɗa tareda nuna masa ya tattala kuɗinsa yasamu yasai fili yafara gini kafin ya fara neman aure, ko ina Aimanah zataje ya Mus'af ke kaita kasancewar duk yayun nata sunada motocin hawa, yau Aimanah tun safe take ɗoki zataje gidan yaya Mansur da'akayi bikinsa watanni uku dasuka wuce bata taɓa zuwa gidanba matar yayan Mansur tana yawan kiranta yaushe zatazo takawo masu ziyara in tace zataje sai Mus'af yace bazataje ba Yaya Muneer ne yau yamata alkawarin ta shirya zai kaita, ɗoki take sosai tana dawowa daga school tayi wanka ta shirya sai dai har la'asar yayan baidawo daga kasuwa ba duk tabi ta damu tasami Mah aɗakinta bayan ta gaidata tace

"Mah Yaya Muneer har yanzu baidawo ba yayimin alkawarin zai kaini gidan Yah Mansur najisa shuru ki aramin wayarki na kirasa" Mah batace komai ba tazaro dubu ɗaya sabuwa cikin jakarta tabawa Aimanah "gashi nan shiyace nabaki bazai dawo da wuri ba an kawo kaya yana store ana saukewa idan yatawo zai kira Anty Ummin saiki futo titi ku haɗu" da ɗokinta ta amshi kuɗin tana tsallan murna ta fita tana faɗin "Mah saina dawo" Mah murmushi tayi tareda faɗin "Allah yakiyaye hanya"

Aimanah tajima bakin titi tana jiran abin hawa amma bata samuba saboda walahar abin hawa da'ake fama dashi a wannan lokacin, harta fara shirin komawa gida tana kokarin tsallaka titi mota ta faka a gabanta murmushi tayi da sauri takarasa wajan motan ta buɗe murfin motan ɓangaran mai zaman banza murfin motar tarufe tajuyo tana murna
"Ya Mas'ud ina zaka na jima anan ina jiran..." wanda tagani zaune wajan mai tuki yasa tai saurin katse maganar datake tana zaro idanu😳cikeda tashin hankali tasoma magana "Afuwan malam nashugo maka mota kai tsaye nayi zaton motar yaya Mas'ud ce" ɗaure fuska wanda ke zaune a wajan tukin yayi yana cigaba da tukinsa cikin kwanciyar hankali da kwarewa "Malam magana fa nake ka ajjeni"
"Na ajje ki wayace kishugo motata kin shugo kenan daman ina neman kan mutane kungiyarmu sun bukaci kan mace daga nan wajan yanka zan kaiki abani kan na wurgar da gangar jikin ko nabawa karena ya cinye"
"Innalillahi wa'inna ilaiheer raji'un kataimaka ka ajjeni su Yaya Muneer zasuyi kuka suna sona sosai" wayansa ce tayi kara yaɗaga kiran yana dariya bataji abinda akace ba a wayar amma abinda yace ne yasata buɗe baki "E ina hanya gani nan na ɗakkota nan zan kawota wajan yanka a gyara wukaken nan"........✍🏻


07039793439
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Associations*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na biyu*

A tsorace tasoma kokarin buɗe murfin motar amma motar taki buɗuwa hannayanta ta haɗa waje ɗaya alamar roko "Dan Allah bawan Allah kabuɗemin na fita wallahi na tuba bazan sake shiga motar kowa ba kataimaka kaji tausayi na in koma gida inna koma bazan sake futowa ba ko makarantama na daina zuwa" Lumshe ido yayi tareda buɗesu tarwai akan fuskarta azahiri fuskarsa turɓune take ba alamar fara'a amma a baɗini dariya ce fal cikinsa ganin yanda gaba ɗaya hankalinta yatashi alamun tsoro karara sun bayyana a gareta,
"In sauke ki? In saukekifa kika ce na rantse bazan sauke kiba sai munje inda muka nufa" Kuka tasaki tareda ɗora hannunta aka tana karanto Innalillahi wa'inna ilahir raji'un tsabar kiɗimewa da tsoratan datayi har batasan an karaso gidan Yaya Mansur ba, ganin anbuɗe murfin motar yasa ta fita da sauri tana waige waige, motar yaya Mansur ta hanga a harabar gidan ita ta tabbatar mata da tabbas gidan Yayane da gudu ta kwasa zuwa ciki kamar zata tashi sama ta faɗa falon gidan bako sallama,

"Innalillahi Anty Ummi ɓoyeni a ina zan ɓuya ɗan yankan kai ne ya satoni" Anty Ummi dariya take sosai ganin yanda duk tafita a hayyacinta ta firgice
"Zo nan Auta bafa ɗan yankan kai bane Mustapha ne fa ɗan Ammi baki gane saba?" wata ajjiyar zuciya ta sauke tai saurin zama saman kujera taci gaba da ajjiyar zuciya har sanda Yaya Mansur suka shigo tareda Mustapha, Aimanah ta ɗaga kai tana kalon Mustapha da Anty tace mata ɗan Ammi ne inbata mantaba ai tasan Al mustapha babban yaron Ammi wani dogo fari marar jiki yaza'ayi ace wannan shine, wannan kakkauran mai murɗaɗɗan jiki shine Mustapha kai sam hakan bazata yuwuba, ita dai bata yarda ba jefi jefi tana yawan kallon Mustaphan wanda shima itan yake yawan kallo insun haɗa idanu yasakar mata murmushi itako ta harareshi ta ɗauke idanunta har zuwa sanda Yah Muneer yazo ɗaukarta su koma gida.


Wasa wasa saiga zazzafar soyayya tashiga tsakanin Mustapha da Aimanah wata iriyar soyayya mai zafi ko yaushe suna tare a gidan Mahh harta kai ga manya sun shuga ciki kowa yayi murna da wannan haɗin, Aimana tana gama scoundry Mustapha yabiya mata tayi jam, jam ɗinta tayi kyau sosai hakan yasa tasami gurbin karatu a jami'ar B u k tamaida hankalinta sosai kan karatu musamman daya kasance Mustapha alokacin yakoma Jordan sunyi nisa da juna amma ko yaushe suna tare a waya suna kashe juna da kalamai masu daɗi da sanya shauƙi ko yaushe suna bege da mararin ganin juna dasan kasancewa tare a karkashin inuwar aure, Mustapha gaba ɗaya zaman Jordan ya ishesa hakan yasa yatattaro yadawo kano gaba ɗaya da aikinsa, kusancin dasuka samu yasa soyayyar su takara karfi hakan yasa iyaye suka tsaida lokacin aure, kwatsam cikin hakan Mustapha gaba ɗaya ya ɗauke wuta daga zuwa wajan Aimana hakan bakaramin tasar hankalinta yayi ba tadamu sosai ko wayarsa ta daina shiga ta tambayi Mahh ina Mustpha tace mata yakoma Jordan aikin gaggawa yasa aka kirasa shine yasa tafiyar ba shiri...Aimanah tayi nisa sosai a tunani har bataji maganar da Mah ke mata ba, Mah cikeda damuwa ta zauna kusada Aimanah "Aimanah dan Allah ki daina damuwar nan kisa aranki daman Mustapha ba mijinki bane kimaida hankalinki kan karatunki kinga kina fenal year namiji kudan zumane kimanta da damuwar sa ki dubi gobenki kimanta da jiyanki"
"Mahh shikenan shikenan narabu da Mustapha bazan aure shiba"...
"Ke dayallah kimana shuru wai akanki aka fara hakane zaki tsaya kina yima mutane kuka" Mus'af ke faɗar hakan a hasale kamar yakai mata duka
"Kuma kizama cikin shiri gobe zakubi jirgi karfe goma keda Ammi zuwa saudiyya"

Mama Amarya shagalin biki tasha sosai a gidan daga ita sai kawayanta da ƴan uwanta dasuka zo daga katsina, ango sai nan nan yake da amarya Sumayya wacce yakeji nan duniya bayada sama da ita, gaba ɗaya gidan ba wani shaƙiƙi na Mustapha kowa yakama gabansa cewarsu bazasu tsaya suga kayan takaici ba, Yayunsa mata na gidan aure kuwa fatan alkhairi sukayi tareda cewar bazasu zo ba, Ahmad da Shaheed ƙannansa ba wanda yaje wajan ɗaurin aure gaba ɗaya kowa haushin Mustapha yakeji, Mama kaɗai ke tausaya masa kusan itace kan komai nasa na bikin, da daddare karfe takwas aka kai amarya gidanta dake nan jikin gidansu Mustapha Alhaji Kamal ne yabasa gidan tun lokacin daya dawo Kano da zama.

Aimanah maida hankali tayi sosai wajan addu'a da rokon Allah yacire mata son Al Mustapha ya mata zaɓin alkhairi, sosai takejin haushin Musty yanda ya yaudareta yaje ya sami wata ya aura, ta kullacesa sosai a zuciyarta sosai takejin haushin maza da tsanarsu a zuciyarta aganinta duk halinsu ɗaya, satinsu biyu a saudiyya suka dawo nageria a Abuja jirgi ya saukesu Yaya Mansur dake zaune acan da iyalansa shiyaje ya ɗakko su daga filin jirgi, washe gari Ammi tabi jirgi zuwa kano Aimanah Yaya Mansur yahanata komawa ganinsa inta zauna anan ɗin zata kara samun nutsuwa, tanajin daɗin zama da Anty Ummi dayaranta maza guda biyu, kullum tana cikin ɗaki bata wani sakewa a gidan nusamman yanda su Anty Ummi keshan soyayyar su gaban kowa, har yanzu bata koma nomal ba wani iri takeji sam jiki da zuciyarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login