Showing 45001 words to 48000 words out of 184071 words

Chapter 16 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

Advertisement

ta fidda rai,

lokacin Zainab Mummy ta haifi yarta Raudha,
dakatar da haihuwar tayi ta hanyar allura saboda ita a ganinta in dai zata cigaba da haihuwa tofa tabbas mata zata haifa,
wannan jinin zuri'ar mahaifinta ne kamar yadda suka canfa,

a lokacin da aka haifi Hafeez ba karamin girgiza mummy tayi ba, ta dinga tambayar suwaiba yadda akayi ta samu namiji a haihuwar farko wanda saidai tajishi a gari ba'a zuri'arsu ba,

ko da ta tambayeta saidai tayi murmushi tace "daga Allah ne,
tun daga haihuwar Hafeez abubuwa suka fara dan ja baya saboda mai gidan da Adamu ke gadi ya bar garin,
jikin gidanshi ya manna shagonshi da babu isassun kaya a ciki,
dama da albashin shi yake cika shagon yayi hidimar gida,
babu wanda a cikin yan uwanta yake taimaka musu, a ganinta basai ta fito ta fada ba sun san bata dashi...


Shekarar Reemah 15 ta tafi karatun gaba da secondary sokoto,
hazakar ta tasa aka dinga promoting dinta har Allah ya kaita jami'a, anan ne ta hadu da Gaddafi dan 400l,

sanadiyar haduwarsu saboda ya kasance hazikin da ake ji dashi a engineering department,
ko wani irin science course ya iya, kuma yana koya musu dan su biyashi ya samu na siyan hand out,

zuwan Reemah ne yasa suka shaku,
itace siyan hand out da komai nashi,
shiyasa baya kasa a gwiwa gurin kowa mata karatu,
ko da ya gama makaranta ya fito da first class babu wanda ya lura dashi bare yayi yunkurin bashi aiki,
ajiye takardunshi yayi ya dawo cikin school yana hada tutorial dan a dinga biyanshi,
tausayinshi yasa Reemah tayi ma Daddy magana har ya amshi takardunshi ya samar mishi babban aiki a lagos,
tun daga lokacin kauna mai karfi ta kullu a tsakaninsu har ta kaisu ga aure...



A shekarar Farko Allah ya azurta ta da ciki,,
lokacin Mummy ta fidda rai da haihuwa saboda dadewar da tayi, bata san akwai dan makale a tare da ita ba,

Tsirar Haihuwar su kwana tara ne,
domin Reemah ta haihu da kwana tara Mummy ma ta haihu, wannan abun ga mutanen "Da", bawani abun kunya bane,

murnar Samun Musaddiq ba a gurin mummy bane kadai,
har da kakanninshi da babanshi da ya dauki dukkan so ya daura mishi, gata babu irin wacce (Mukhtar) Hilal da Musaddiq basu gani ba, babu tafiyar da Daddy zaiyi ba tare dasu ba..



Kamar yan biyu haka suka taso, kansu daya, kayansu iri daya, kamanni ne kadai suka banbanta shi Hilal fari ne musaddiq kuma Baki ne irin bakin barebari,
gasu da jikin girma Masha Allah, komawar su Reema Cypros ne ya raba su, amma kafin nan koda yaushe suna yare.....




Bangaren Halima kuwa tunda tayi karyar makaranta sun tura ta china karatu shikenan su Goggo suka hau suka zauna ba tare da bincike ba,

yawon barikinta ta tafi yi da kuma neman kudi,
saida ta zama hamshakiyar kanta sannan ta waiwayi gida bayan shudaddun shekaru,

ko da ta dawo saida ta gyara gidansu dan acewarta bazata iya zama a irin gidan ba,


Sana'arta ta business ta cigaba dayi tunda dai yanzu ta gama rikewa tasan babu wanda zaizo yace zai aureta,
abu daya gareta wanda za'a yabeta dashi
shine duk irin duniyancin ta bata yarda da karunwanci ba saboda shegen kyankyami gareta,

shekaru da dama bayan dawowarta ta hadu da wani mayaudarin yaro mai tsantsar *SIHRUL KALAM*
a take ya baibayeta ta fada tarkon kaunarshi,
bata tsaya dogon bincike ba ta yarda ya aureta, hatta sadaki ita ta biya mishi saboda shaukin samun wanda ya furta mata kalmar so...


Sai bayan auren ne ta gane yaudararta yayi,
yazo ne kawai dan ya kwashi dukiyarta yayi gaba,
ko da ta fahimci haka bata dauki zafi ba dan ita mai bashi dukiyarta ne,
abin da ya tsiro dashi na shigowa da mata gidane yafi tunzurata har ta kai ga aikata kisa a gareshi cikin rashin sani,


A kotu ne aka fahimci cewar tana dauke da cikinshi na wata hudu, koda ta fahimci hakan saida taci kukan dana sanin zuciyarta marar kyau,
Kotu bata yanke mata hukunci ba har sai ta haifi dan dake cikin ta ta yaye,

haka kuwa akayi har cikinta ya isa watan haihuwa,
kamar hadin baki dukka ukun ya'yan Baffa cikin garesu,

Husna aka fara haifa, washe gari Nadiya ta biyo baya,
haihuwar Badariyya tayi gardama saida aka yanka Leemah,
ba karamar wuya Badariyya ta ba mahaifiyarta ba,
bayan awanni da yi mata aikin aka fahimci jikin nata babu dadi,

cike da kwarewa doctors ke aikinsu amma ina abin yaci tura, aikin mala'ika da na mutun ba daya bane,
Ashe leemah ajalinta ta auro har ta haifo mishi 'ya,
ba karamin tashin hankali duk suka shiga ba na rashin yar uwarsu, musamman Goggo da tayi karamar hauka...
mummy ce ta dauki Badariyya ta hada da Husna ta shayar dasu cike da kulawa...



Tun a karancin shekarun 'yayan suwaiba suka fahimci zumuncin zuri'arsu sai in kana da kumbar susa, marasa wulakantasu aciki kadan ne....


Rayuwa Badariyya tun tana karama ta tashi a sangarce, bata ganin mutunci ko jin kunyar kowa,
Hilal shine wanda tun fil'azal basa shiri, a gurinshi tasan ba mummy bace ta haifeta,
ranar yaci dukan tsiya a gurin mummy,
Tana gama dukanshi ya fita dan ko a jikinshi dama so yakeyi ya nuna mata ita fa ba yar gidansu bace ta daina kusu fi'ili......


Da wannan labarin zumunci ya faro,
sila itace mace,
uwa,
wacce take da daraja,
wacce Allah swt ya bata ragamar tafiyar da zuri'a,
lallai Macce ta gari itace ginshikin alumma,
domin gyara rayuwae ya mace kamar gyara alumma ne,
mu dage tun yanzu gurin yi ma 'yayanmu maza adduar mace ta gari domin wayau ko dabara bazai basu ba,
sukuma yayanmu matan ka sanya su zamto Mar'atus saliha ga mazansu.....


Mrs Tijjani Shattimah....



[08/03 12:28 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣1⃣
By *Aysha Ya'u kurah*



_HAKKI, HAKKI BABBAN ABU NE YAN UWA, KOMIN KANKANTARSHI MU GUJI DAUKARSHI DAN KANANAN ZUNUBBAI SUNFI MANYA ILLAH, DAN ALLAH MU KIYAYE HAKKIN JUNA_


*Cigaban Labari*



Jiki a sanyaye ta dauko sarkar dake cikin akushin tayita juya ta a hannunta,
tasan Baffa ya dade da mantawa da zaman sarkar shiyasa tayi mata muguwar ajiya,
ko da wasa bata taba yunkurin sata ba,
tun da taje ta tambayi kudin sarkar taji kudi ne masu tarin yawa ya sanyata kara yi mata kyakykyawan ajiye,
ajiye sarkar tayi hade da tagumi. ya zame mata dole ta nuna musu gaskiyarta, shiyasa ta fito da sarkar dan bawa su Nadeeyah gadonsu,
tasan wannan ita ce kadai mafita a gareta da diyarta,
tasan in tayi hakan Muntari bazai yi mata zargin muguwar uwa ba,
zaiyi mata kallon mai amanar da ta iya rike abu mai daraja saboda soyayyar uwarsu,
wannan hanyar ita kadai ce abin da zai samar mata mafita...


Rufe akushin tayi bayan ta dauko wasu magunguna a ciki,
inda ta daukoshi nan ta maidashi ta fito parlor ta dauko leda mai kyau ta zuba sarkar a ciki, sannan ta shiga yin amfanin da magungunan domin rufewa su Daddy da sauran baki....




*1:51pm*

Motaci uku ne suka shigo cikin harabar gidan Baffa,
Motar Anty Reemah ce ta fara shigowa, sannan sauran kannenta suka rufa mata baya,

Raliya ce zaune a gaban motar Anty Reemah, sai Zainab (kanwar Nadeeyah) da Hinad,

a motar Radiya aka tara taron marasa mutunci,
Raudha da Badar,
Cikin kunci Badar take saboda Nadeeyah da Husnah sun shiga motar Hilal,
duk yadda taso taja Husna suzo a mota daya taki saboda farin cikin tayin da Hilal yayi mata na shiga motarshi,
ko kallon motarsu batayi ba ta wuce cikin gidan tana huci,
a zaune ta samu Goggo hannu rike da carbi tana ja,
Allah kadai yasan abin da take furtawa domin janshi kawai takeyi,
babban tashin hankalinta bai wuce kar Baffa ya fada musu komai na labarin Atika ba,
burinta su sameta ita kadai ta hada musu kirkirarren labari ta fada musu saboda tseratar da auren yarta,
jikin ta Badar ta fada ta fara zuba mata shagwaba,
gyaran murya Goggo tayi ta mata nuni da carbi alamar ja takeyi,
sauka tayi ta daura kanta a kan cinyarta,
damuwar da Goggo take ciki ta hana ta fahimtar damuwar dake kan fuskar yar lelenta...

Sallamar su Anty Reema ne ya sanya Goggo sakin Murmushi hade da tattara hannu guri daya tana musu gaisuwa dan su gane carbin take ja bata son a katseta,

neman guri sukayi suka zauna suka bude flow din hirarsu ta kasuwanci,

shigowar su Nadeeya ne ya katse musu hirar saboda yadda Goggo ta yafito su da hannu ita da Zainab,
a darare Nadeeyah ta sauke zainab suka matsa kusa da ita suka durkusa zasu gaisar da ita tayi saurin durowa daga kan kujerar ta hadesu ta rungumesu hade da kuka mai karfi,
"Allah sarki Suwaiba,
ganin jininki ya tuno min ke,
inama ni mutuwa ta dauke ta barki cikin 'yayanki,
inama zan juyo da hannun agogo baya da na nuna miki irin muhimmacin da kike dashi a cikin rayuwata,

cike da mamaki daukacin mutanen parlon ke kallon Goggo,

Ciki kuwa harda Baffa da ya sanyo kanshi cikin parlon ya tarar da abun da idanuwanshi basu taba tozali dashi ba,
yaran da ko cikin parlon basa samun albarkacin shiga bare har su samu darajar runguma,

wani dadi ne ya ziyarci zuciyarshi yayi tunanin mutuwar Suwaibar ce ta kadata haka,
da sallama ya katse shurun mamakin yace "yau gidan nawa cike yake da matana kenan,
sai wacce na zaba,
Murmushi dukkansu sukayi suka gaida shi hade da cewa ai dukkan mu zaka hada,

Badariyya ya kalla da ta rike kanta saboda bugeta da Goggo tayi gurin sakkowa daga kujera,
"a'a Amaryata me akayi miki naga kin rike kai?
sakin kan tayi ta turo baki tace "ba Goggo bace ta bigeni, kallonta Goggo tayi tace "yi hakuri Badariyya ban kula bane, hankalina nakan marayun Allah, babu uwa babu uba, kai wannan rayuwa abar tsoro ce,

Anty Reemah da abun ya bar bata mamaki tace "dama haka ne Goggo,
Allah baya barin wani dan wani yaji dadi,
ta yiwu mutuwar ita kadai Allah ya ga zata zamto hutu a garesu, shiyasa yayi gaggawar daukesu, Allah sarki Mama Suwaiba,,

wani kukan Goggo ta kuma kecewa dashi tana dada kankame zainab,
kallon tsoro zainab din take mata shiyasa ta saki kuka ta fisge kanta ta koma jikin Nadeeya,

share ma juna hawaye sukeyi gunin tausayi,
shigowar su Mummy dakin ne yasa duk suka mike domin bawa Daddy gurin zama,
bayan yan gaishe gaishe Baffa yace " yau gida yayi albarka, dariya Daddy yayi ya tsuguna ya gaishesu,
bayan yan hirarraki Daddy ya gabatarwa da Baffa dalilin zuwansu, ya kuma kara da cewa "kayi hakuri Baffa nayi maka shishigi a cikin alamarin gidanka,
inason sanin dalilin kiyayyar ne saboda yana neman zama min matsala a cikin Zuri'ata...



Kuka Goggo ta saki tace "Babu kiyayya cikin zuri'ata da na gina ta shekara da shekaru,
kasan zumunci yanzu ya zama na yan zamani,
amma ni a gurina kowa daya yake,
bana banbanta su,,
gyara zama Daddy yayi yace "nasan bakya banbanta su, domin dukkansu 'yayanki ne babu bare a ciki, amma ya kamata ku tsawatar akan yadda akayi ma zumunci rikon sakainar kashi,
bana san yadda abubuwa suka kasance a nan gidan su kasance a cikin 'ya'yana,
bazan dauka ba,
inason 'yayana su fahimci muhimmancin mai shi da marar shi,
banason dattin duniya ya zamana sillar yankewar zumuncin 'ya'yana,
shiyasa nazo a warware min komai kuma ayi ma tufkar hanci,

Gyaran Murya Baffa yayi zai fara Magana Anty Reemah tayi saurin cewa "yi hakuri Baffa zan katseka, dan Allah so nakeyi ka fada mana wacece *ATIKA*
a duburce Goggo ta waigo ta harareta ba tare da sun hada ido ba,
a zuciyarta tace "kaji shegiyar yarinya, ana neman kai magana karshe ba tare da an bullo da maganar Atika ba ta sako zancen ciki,
kara gyara zaman carbinta tayi tana kallon Baffa dake shirin basu labarin Atika....




Kuka sosai Nadeeyah da Hafeez sukayi najin ba Goggo bace ta haifi mahaifiyarsu,
ashe dalilin kiyayyar kenan,
sun sani tabbas in har uwa daya suke dasu Mummy bazasu taba wulakanta mahaifiyarsu ba ko da kuwa mijinta yafi *KAMAYE* talauci


Shi kuwa Daddy banda daurewar kai zuciyarshi ce ta tafi tunanin lokutan da ta dinga mishi magiya akan ya janye maganar aurenta,

kalaman Abbakar ya shiga dawo mishi " *Kyari, yarinyar nan tana cikin matsala, anya kuwa mutanen gidannan su suka haifeta? "Ko a makaranta bata hutawa saboda hidimar yar uwarta, yadda kasan baiwa haka suka maida ta, ina tunanin yar riko ce, ka bita a hankali ka lallabata zaka fahimci daga inda matsalar take, walhi ta bani tausayi matuka saboda yadda naji tana kuka kamar ana yankan naman jikinta*
dana sani marar amfani ne yayi mishi dirar mikiya cikin zuciyarshi,

muryar Goggo ce ta katse tunaninshi,
cikin kuka ta fito da sarkar da ta zame mata mafitar karshe da zaisa ta fita a zargi ta damkawa Hafeez a hannu, tace "wannan sarkar Kakarku ce da mahaifiyarku ta gada,
nayi nayi suwaiba ta karba taki, yanzu gashi bata raye dole in sauke nauyin magada a kaina,

kallon sarkar Baffa yayi ya share hawayenshi yace "Samun mace mai rikon Amana irinki sai an tona Ma'u,
nagode da rike min Amana da kikayi,

Anty Reemah dai kallonsu kawai takeyi hawaye yaki tsaya mata,
tuno irin ukubar da mama Suwaiba tasha takeyi,
babu abinda bata sani ba na daga halayyar da kakarsu kewa mama suwaiba da ahalinta,
wannan shine dalilin da sanyata take matukar kauna da tausayinsu...

Labarin halin kirkin Suwaiba Goggo ta dinga fadi saboda dai ta wanke kanta a idon Daddy,
shi kuwa ya gama fahimtar komai tun da yaji cewar ba ita ta haifeta ba,
sai Gab da la'asar suka fara shirin tafiya,

kallon Aljihun Hafeez Goggo ke tayi tana tsine mishi a ranta,
wato ma bazai ce mata ta ajiye musu sarkar ba,
taso hada baki da Mummy su karbe sarkar taga mummy ta kanta takeyi,
burinta kar Daddy ya canza mata...
ko da ta fito waje ya riga ya shiga mota har ya tada ta yana kokarin tafiya, da sauri ta karasa ta shiga ciki tana mishi kallon tsoro da mamaki....







*GOMBE*

Uncle Abdallah..
Kawu Abdallah...
Sweet Papy Abdallah


Ajiye takardun hannunshi yayi yace "Ruwaidah problem,
ta dawo makaranta yanzu fa babu wanda zai huta,

kafin ya ankara yaji ta fado jikinshi,
nishi yayi da karfi yace "Ruwaida ai sai ki karya ni,
baki san yanzu kinfi *OBENIZA* girma ba,
dagashi tayi hade da bude baki tace "Papy Obe what?
Hancinta ya ja da karfi yace "OBENIZA,
bata rai tayi ta fara daga hannun rigarta tace "yanzu Papy har girmana ya kai na Obeniza ben?
Wallahi sai na hadaka da *Anni* !
nan ta bar jakar islamiyyarta ta ruga cikin gida da gudunta tana kiran Mamy nd Anni da iya karfinta,

Jamal ne ya fito daga daki hannunshi rike da Game yace "problem child is back again,
tana zuwa zata gifta dakinshi tace "Yaya Jay,
wai dagaske nakai girman obeniza ben?
Kallonta yayi sama da kasa yace "to ai an cuci obeniza ma da ake hadaku,
kinfi shi girma sau goma, hannunta ya kamo hade da rike kunnenta yace" warning na fito in miki,
yau sunday,
wallahi in kika kuskura kika dameni a gidan nan sai na kusa maida ke jaka dan duka,
salin alin kije kiyi baccin rana kafin a kira la'asar,
da fatan kinjini da kyau?

Wani irin karaaa ta saki mai karfi tana bubbuga kafarta a kasa,
Da gudu Mamy ta fito daga dakin Anni tace "waye? lafiya,
motsin kofar Jamal ta gani ya tabbatar mata da shine ya taba ta, "bude kofar nan Jay,
ta window ya leko yace "Mamy babu abin da na mata fa,
kawai dan nace mata Anni bata da lafiya yau karta damu mutane shine fa ta fara kuka,
daukarta mamy tayi tace "Sorry my love, Anni will get well soon in shaa Allah kinji,
muje ki ganta,

gefen Anni ta zauna tana fadin Anni wanene ya saki ciwo,
hannunta Anni ta rike tace "bana ciwo takwara,
lafiyata kalau,
tashi kije kici abinci kizo kiyi min fira kinji,
mikewa tayi tabi bayan mamy hade da cewa "to Anni na ni kadai banda Wicked yaya Jay...

Suna fita Alh Abdallah ya shigo dakin ya zauna a kusa da ita,
Anni likita yace "idan baki daina tunani ba zamu iya rasaki,
zuciyarki ta kusa shiga matakin Karshe,
me kike so wanda Allah bai miki ba,
duk irin tsanar da akayi miki a gida saboda ni yanzu bai zame miki alkhairi ba,
babu abinda na rasa Anni, dukiya, mace, 'yaya, ga kuma ke da kika zamo jigo a rayuwata,
kece mafarin komai Anni, hawayen da ya zubo a idonta ta share tace "Uba" Abdallah,
ka rasa uba,
tun kana ciki ake min kallon fasika,
har fitowarka duniya ban huta ba saboda kiranka shege da akeyi,
nasani kayi min kawaici na rashin ganin laifina akan rashin sanin inda ubanka yake,
A yau ma abun da na saba fada maka shi zan fada maka,
wallahi tallahi Abdallah kai dan Aure ne,
sunnar manzon Allah ita ta samar dakai,
amma babban abin takaicin shine har yanzu bazan ce ga inda mahaifinka yake ba.... ta karashe da kuka mai hade da tari......

(Twist) karku rude ku biyoni da muje komai zai warware....




Daddy nayi magana da papa akan ina so a bani daya daga cikin yaran mama suwaiba mu rike,
yardarshi tasa nace bari in tambayeka ko za'a bani,
ajiye cup din hannunshi yayi yace "banajin ki Reemah,
na yarje miki ki dauki zainab domin itace karama,
ita take bukatar uwa irinki,
ita kuwa Nadeeya yanzu ta girma gara ta zauna anan ta cigaba da makarantarta,
Allah yayi miki albarka, ya kara miki soyayyar yan uwanki a cikin zuciyarki,
Ameen Anty Reemah tace hade da janyo abin cire farce ta cire mishi wata kumba da ta dago a kafarshi..
yaushe zaku koma ne? Daddy ya tambayeta yana taba gurin da ta cire farce,,
jibi in shaa Allahu Daddy,
to Allah ya kaimu....
ta amsa da Ameen sannan suka cigaba da hirar ya da mahaifi...



Mrs Tijjani shattima
[09/03 6:50 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login