Showing 51001 words to 54000 words out of 184071 words

Chapter 18 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

Advertisement

ma dai meyasa nake fada maka,
and karka damu tana bani tausayi as well, in shaa Allahu bazan bari tayi lacking komai ba, kuma zansa ido akanta,

"yayyy dats my Good Boy, shiyasa nake sonka kanina, kuma kasan sosai fa nake sonka,Hilal ya fadi yana dariyar tsokana.
"And i hate u ni kuma Musaddiq ya fadi murya a kausashe,
dariya sosai Hilal yayi yace "chill kanina zamu shiga jirgi, take care plss,
bai jira amsarshi ba ya kashe wayar ya isa gurin jirgin cike da annashuwa.....




Satittika sun zo sun wuce,
zaman gidan mummy a gurin Nadeeyah ya zama babu yabo babu fallasa,
kula sosai Musaddiq yake bata duk da bata cika sakin jiki dashi ba,
ita ma Husnah duk da tana shakkar Badar takan zauna suyi hira jefi jefi da Nadeeyah,
kyawun Nadeeyar da yanayin jikinta ke matukar burge Husna, ita haka Allah yayita tanason ganin farar mace,
uwa uba farin ya hada duk ingredients na dangin kyau,

Matsalarta Nadeeyah 'Badar ce kadai, shima sai sunzo bacci,
ta dinga zaginta kenan tana fadin saidai ta kwana a kasa,
wani lokaci in Husna tasa baki fadan ya dawo kanta,
haka dai Nadeeya ta maida gurin kwananta kasa kan bargo dan dai hankalin kowa ya kwanta,
saboda mugunta irinta Badar sai ta kure a.c. ta kuma dukunkune a cikin bargo,
in sanyin yayi yawa cikin dare sai Husna ta tashi ta rage ko ta kashe gaba daya ba tare da Badar ta sani ba, saidai in safiya tayi kaji hayagagar ta tana masifar dalilin da zaisa a dinga kashe mata a.c.,

kullum haka sukeyi har Husna ta gaji da kashewa,
in taga sanyin yayi yawa sai ta tashi Nadeeyah ta matsa mata su kwanta,
da yake tana rigasu tashi shiyasa Badar bata ganewa....




Zaune suke a tsakarsu gidan ta can baya,
Badar na gyara kumbar ta,
ita kuma Husna na tsifa, dayake kalaba ne shiyasa take tsefewa da hannu,
kallon Nadeeyah tayi wacce take zaune tana taya mai aikunsu gyaran cabbage,
"Nadeeyah yaushe zaki koma school? Barin yankan Nadeeyah tayi tace "15th,
bude baki Husna tayi tace "jiya kenan, gyada kai Nadeeyah tayi tace eh amma zan iya komawa next week,
"tabe baki Husna tayi tace "kuma kinajin dadin boarding?
Kai ni ai bazan iya rayuwar wani guri, in ba gida ba,
dariya Nadeeyah tayi tace "kuma akwai dadi, mutum na koyan abubuwa da dama na daga halin mutane,
mabanbantan mutane kake haduwa dasu masu halaye kala kala,
comb Husna ta dauka tace "ni fa koma meye bazan iya ba,
kema da zaki yi ma Mummy magana a canza miki makaranta ki dawo day da yafi miki,,
sai a sannan Badar tasa musu baki,
"miss I too knw,
madam over sabi, ai sai ki canza mata,
tsaki taja da karfi ta mike hade da cewa "wallahi shegen iyayinki ya fiki karfinki,
ita tasan public school ne daidai ita,
in kuma kina da kudin canza mata sai ki bada himma tasa kai ta shige kitchen tana hararar Nadeeyah,
tsaki Husnah tayi tace "gama muje ki rakani saloon ayi min kitso, kema sai ayi miki kiji dadin kanki, gurin famfon tsakar gidan Nadeeyah ta kai cabbage din ta kunna ta wanke shi tass ta tsane,
tace ma Husna "na gama! muyi sallah sai mu wuce,
da to Husna ta amsata suka wuce ciki,
abubuwan Badariyya sam basu dameta ba tunda tana samun sassauci a gurin Husna...




Yana gama nunawa plumber gurin dake zubar ruwa daga sama ya biyo ta kitchen dan duba ko akwai inda ke toshe a makwarar,
tsaff yagama saurarar maganganunsu,
maganar Badariyya ta tsaya mishi a rai,
"wai yarinyar nan me ta dauki kanta ne,
danne bacin ranshi yayi yakoma ya shiga ta parlonshi,
a gurin dining ya samu Mummy tana hada plates din da suka ci abinci shi da bakinshi,
gyaran murya yayi yace
"Zainab wani class Nadeeyah take?
Tunani Mummy ta farayi tace "mate din su Husna ce nasan class dinsu daya,
zama yayi akan kujera yace "ki fada mata gobe su shirya tare da su Husna zan kaita makarantarsu ta karasa acan,
duk da taji ba dadin yadda yakeson hada Nadeeya da ya'yanta baisa ta nuna mishi ba saboda yadda take taka tsantsan da zamansu,
amsa mishi tayi da "to Allah ya saka da alkhairi, bai amsa mata ba ya cigaba da kallon tv....




Shiryawa tayi cikin wata koriyar atamfa mai ratsin ja,
dinkin zamani riga da straight skirt mai tsagu,
rigar kuma matsatstsa mai budadden hannu,
tayi kyau sosai,
Husnah ce ta bata a cikin kayanta da suka dan kamata dan tafi Nadeeya fadi kadan,
dankwali ta daura ta kunshe kanta ta dauko hijab zata sa,
fisgewa Husna tayi tace "u are a joker,
wa zaki bi da wannan hijab din,
gyale ta miko mata tace "dankwalin ma cireshi zakiyi,
kallon Husna tayi tace "da wannan matsatsun kayan zan fita babu hijab?
gyada mata kai tayi tace "hango kanki har kin fita ma,
zatayi magana Husnah ta kwacee dan dankwali ta turasu cikin drawer ta rufe,
shiryawa tayi tana waka tana rawa tana ma Nadeeyah gwalo,
ita abin dariya ma ya bata ta sake kallon kanta a jikin madubi,
babu ta inda kayan nan basu bayyana surorin ta ba,
marairecewa tayi tace "kiyi hakuri Husna ko dankwali ne in daura,
bata saurereta ba ta fara shafa mata powder tana fadin "ki cigaba da butulcewa Allah,
dan dai So ba samu bane,
wallahi da nice tsirara ne kadai bazanyi yawo ba,
lallausan gashinta ta taje mata tayi mata parking da katon ribon,
light janbaki ja ta bata tace "ki dan sa kadan kiga yadda zakiyi, amsa tayi tadan goga a bakinta, gurin madubin Husna ta jata tace "dan Allah kalla, kamar a bakinki aka halicceshi,
mtsww taja tsaki hade da cije lips tana hango inama akai Nadeeyah school dinsu tayi ma gayu iskanci, ta nunawa *SABRINAH BILAL* ba ita kadai aka halitto da kyau da sura ba,
gyale ta daura ma Nadeeyah a kanta irin yadda tayi tace "muje ko,
a kunyace Nadeeyah ta bi bayanta tana tunanin yadda zata fita da kayan nan ba hijab,

Fitowarsu tayi daidai da mikewar Badariyya, hade da fitowar mummy daga parlon Daddy,
fassara yadda idon Badar ke nuna tsantsan tsana da kishin Nadeeyah mai wuyar fadi ne a alkalami,
bata ankara ba taji Mummy ta sake furto maganar da taji ta kamar saukar Aradu,
"yawwa Nadeeyah gobe ki shirya da wuri zaku je makaranta tare dasu Husnah,
wani irin tsalle Husna tayi tace "so quick Ya Allah, lallai luck is on her side today,

kallon Badariyya Mummy tayi tace "ke bazaki kitson bane? dauke kanta tayi tace "umm bazanje school ba gobe,
tana kaiwa nan tayi hanyar daki, dakatar da ita Mummy tayi tace "saboda me?
Kafin ta bata amsa Musaddiq ya shigo parlon yana hamma, tsayawa yayi daga nesa yana kallon Nadeeyah daga sama har kasa..


Karasowa yayi ya kewayeta yana kallon fuskarta da ta sunkuyar kasa,
murmushi yayi yace "tsarki ya tabbata ga ubangijin da halicci kyawawan mata a cikin gidan mu,
ina zaku je da irin wannan kwalliyar,
Kusa dashi Husna ta matso tace "saloon, ko zaka kaimu ne?
bata fuska yayi yace "na kwaso rana,
bacci nakeji amma bazan iya refusing daukar kyawawan kannena a mota ba,
kallonshi Mummy tayi tace "kyalesu su tafi Diku,
jeka ka huta abinka,
girgiza kanshi yayi yace "bari in kaisu Mummy, zanyi aski nima,

jin haka ya sa Badariyya sakin ranta tace "Mummy su jirani nima zanje kitson,
bata rai Husna tayi tace "wallahi Mummy Badar bata mana lokaci zatayi,
harara mummy ta sakar mata tace "in ma zata kai la'asar sai kun jirata,
turo baki Husnah tayi suka dawo parlon suka zauna,


Wayarshi kirar iPhone x max ya ciro a aljihu ya kalli Husnah yace "meye zai bata ran autarmu,
tashi muje waje inyi miki hoto da portrait camera,
sanin halinta nasan hoto yasa shi fadin haka dan ya kwantar mata da hankali,
da sauri ta bi bayanshi tana kiran Nadeeyah da tazo suyi tare,
kin fitowa Nadeeya tayi saboda yadda mummy ta kafa mata ido,
kyawunta da ta gani na yau da yafi na ko yaushe shi ya daga hankalinta,
bata so samm Musaddiq ya fada tarkon kyawun nan,
taci buri akan nema mishi 'yayan abokan Daddy ministoci dan samun karin girma a idon kawayenta,
dole ta san abin yi akan irin wannan kwalliyar da Nadeeya ta fara yi,
dawowa Husna tayi taja hannunta suka fita dan yin hoton..



Hotuna sukayi masu matukar kyau kamar an wankesu,
wanda sukayi su biyu shi yafi komai yi mishi kyau,
suna gama hotunan ya gyarasu ya daurasu akan status dinshi da instagram,
bai rage ko daya cikin goman da suka dauka ba,
yana gama daurasu ya sauka dan ganin fitowar Badariyya,
gaba Badariyya ta bude da sauri ta shiga ta zauna,
kallonta yayi ya kasa cewa komai yashiga ya waigo ya kalli su Husna a baya,
tada motar yayi suka wuce,
ta gefen ido Badar ke satar kallonshi, shi kuwa hankalinshi na kan titi yana tambayar inda zasu, cikin doki Husnah tace *MEENA'S TOUCH* Sabon saloon din da Anty Amina ta bude,
ta madubi ya harereta yace "inada Allahn misirun sanin shagon kenan,
kafin Husnah ta bashi amsa Badar tayi saurin cewa " *Kura plaza* bai sake magana ba ya dauki hanyar Yakubu gawon way..


Yana saukesu ya bawa Husna dubu shidda yace "bani da enough ku kara,
kinsan nima sammin akeyi babu aikin yi,
dariya tayi tace aiki kam zaka samu yaya, kaima kasani, lokaci ne, dariya yayi ya wuce yana dagawa Nadeeyah hannu...




Wayarshi ya dauko a inda ya ajiyeta, yana bude ta kiran *Haidar Galadanci* ya shigo..

Dauka yayi yana dariya yace "Head Boy how far, ya kake,
daga daya bangaren Haidar yace "fine kyari, kana ina ne?
Taka birki yayi da karfi saboda mai mashin din da shigo mishi, tsakii yaja yace "ina gurin Leventis zanje waff road any probs?
Kwantar da murya yayi yace "Kyari naga bebs din story dinka, plss farar fa,
kanwarka ce?,
nasan Husna, ban dai gane farar bane,
dariya sosai Musaddiq yayi yace "kanwata ce Galadanci,
kafin ya karashe maganar yaji kiran Hilal ya shigo wayarshi a karo na uku,
hakuri ya bashi ya katse wayar dan ya dauki ta Hilal, kafin ya dauka ma ta katse,
duba missed calls yayi sunfi hamsin,
Hilal kadai talatin da uku yayi mishi,
sai sauran daga abokanshi,
kafin ya kira Hilal wayarshi ta shigo,
bai jira jin kalmar Hello ba saboda baya cikin nutsuwa da hankalinshi yace "dis is madness Kyari,
in banda rashin hankali ya zaka sanya hoton yarinyar nan a ig,
a story is understandable, but ig is very bad, duk inda ka zaga su arewa cuties nd co hotonta ne ke trending,
ya zakayi exposing dinta haka, wat is the need of all dis,
kuma baka ma duba kayan jikinta ba kawai ka tashi ka sata a social media,
idon mazan duniya su gama ganeta,
am very angry with u wallahi,
tunda ya fara masifar musaddiq yayi parking, saida ya gama zazzaga masifar yace "ka gama?

Tsaki Hilal yayi yace "ban gama ba, ka hau kaga banzayen comments din da akeyi maka,
na rokeka ka hau ka cire hotunan nan, cikin fada musaddiq yace "Bazan cire ba,
nace bazan cire ba,
hoton ta ita kadai nasaka,
au su sauran matan da suke saka hotonsu ba mata bane,
a fusace Hilal yace "ba irin su bace kyari,
ka kasa fahimtar ba irin matan da za'a dinga exposing bace,
yawo kalmar ta dingayi cikin kwakwalwar musaddiq yace
"wat do u mean, kana nufin bata kai matsayin da zata hau instagram ba,
ko kuwa tana da makusar da--- katse shi Hilal yayi yana share zufar da ta addabashi tun ganin hotunan da comments din abokan musaddiq yace "bazaka gane ba Kyari,
taushi yayi da muryarshi ya cigaba da cewa "rayuwarta zaka duba, marainiya ce, a yanzu gatanta shine ilimi,
wannan gayun ba nata bane, ilimin shine zai zamo gatanta gaba da baya,
yanzu wannan hoton baka san abubuwan da zai janyo mata ba,
samari zasu fara kawo mata hari, daga nan shikenan zasu zo su--- runtse idonshi yayi kafin ya furta kalman *aureta*, at end of the day kuma rayuwarta zata kare a bauta,
wasu kuma will come su yaudareta, wasu su lalata ta,
plss Musaddiq ka cire hoton nan,

cike da gamsuwa Musaddiq yace "very true, kamar kasan yanzu *Galadanci* ya kirani akanta and lots more, gara da ka fahimtar dani,
bari inyi maza in cire...



Safa da marwah ya dinga yi a cikin dakinshi,
pencil din da yake zane dashi yayi dagaga a bakinshi saboda tauna,
hoton ya sake kallo kashi na ba adadi yace "ya Allah ka cire idon duk wani namiji akan hoton nan,
yana cikin haka yaji karar notification din story a ig, *Husnah_kyari is live on instagram* da sauri ya hau,
yana budewa ya zauna dabass, *what is dis, ya ilahi!!
Ya fadi yana rike kanshi,
video Husna tayi musu da kai a bude,
gashin Nadeeyah ya sakko har baya,
a juye take tana parking din kanta, bata san Husna na mata video ba,
tsaki yaja sannan ya lalubi number wayarta, a zuciyarshi yace "kasheshi suke so suyi,


"My Personal person ta fadi da karfi,
bai amsa ba yace "tarbiyyar musulmi ne daura video babu dankwali,
come on je ki cire shi,
dariya tayi tace "done my PP, yanzu zan cire,
ajiyar zuciya yayi yace "hope kuna nan lafiya,
amsawa tayi da cewa lafiya kalau kowa yake,
"Good yace hade da cewa ku kula sosai fa,
kunsan samarin yanzu basu da kirki,
is hardly su soku tsakani da Allah, ku kama kanku ku daina kwalliya kuyi focusing akan karatunku kinji,
gyada kai tayi tace "in shaa Allah my pp,
murmushin jindadi yayi yace "bani Nadeeyah,
saida yaji kunya da ya fada,
cire wayar yayi a kunnenshi ya kalleta hade da jin haushin kanshi,
to me zaice mata?
, sansanyar muryata yaji tana fadin "Assalamu alaikum,
"kara wayar yayi a kunnenshi yace "Alaiki salam, ya kk
, lafiya lau ina wuni ta fadi darare,
lafiya lau,
kinada abubuwa a gabanki kike kwalliya harda wani possing ayi hoto ko?,
murya na rawa tace "a'a yau ne kawai,
kuma munje saloon ne,
dadi yaji har cikin ranshi yace "to ya zama na karshe,
karatunki yanzu shi kadai zaki sa a gaba,
ko powder ki daina shafawa,
u are very ok a haka,
ki daure kiyi karatu sosai ki zama independent woman kinji ko?
Gyada kanta tayi kamar tana gabanshi tace "in shaa Allah zan kiyaye,
"yauwa kanwata take care ya fadi hade da kashe wayar ba tare da ya barta ta bashi amsa ba.......



Tun dare Daddy ya kira principal din makarantar,
da yake suna ganin girmanshi shiyasa basuyi rejecting ba suka ce gobe a zo da ita a mata interview,
godiya yayi mishi sukayi sallama, a waya ya kira Musaddiq yace gobe ya shirya ya kaisu school yayi mata registration,
amsawa yayi yace "Allah ya kaimu Daddy...




Kallo ne ya koma kan su Husna lokacin da suka fito a cikin motar, jar jallabiya Husna ta zabowa Nadeeya tace ta saka, saboda tayi bagu a makaranta,
ai kuwa sun kawo kallo,
har a registrar office duk staff din da ya shigo sai ya kalli Nadeeyah,
bayan an gama mata komai suka mata interview,
dakyar ta wuce saboda karatunsu yayi mata tsauri,
Ss3 Art 1 suka kaita saboda Art take a makarantar da ta baro..

Sallama Musaddiq yayi musu ya wuce yana jaddada musu muhimmacin karatu,
commerce class Husna take,
saida taja ta suka je class dinsu kafin teacher ya shigo,

zagayesu akayi ana tambayar Husna sunan sistern ta,
murmushi tayi kanta yayi girma tace "She is my cousin,
Nadeeyah Adam,
wow nice name suka hada baki suka fadi, *Jameelah Aja* ce tace "a sit dina zata zauna,
nan fa class din ya kaure kowa na a gurinshi zata zauna harda mazan class din,
Dariya sosai Husna tayi tace "to a Art take,
tsaki sukayi sukace 1 or 2, one ofcourse Salmah Habeeb ta fadi hade da cewa "wai halan uncle Kamal zabar kyawawa yakeyi ya kaisu art da kanshi badan suna so ba,
dariya duka class din suka kece dashi suka ce very true,
duk taron kyawawa ne a art,
halan gani yayi duk sunfi dacewa da art gidan da babu Maths,

Hango Economics teachernsu sukayi kowa ya nemi gurin zama ya nutsu,
hannunta Husna taja suka hau sama inda class dinsu yake, daukar excuse tayi gurin Uncle Tahir literature teacher tace
"new comer ce sir,
uncle Kamal yace a kawota nan class din, kuma yace a bata special treatment,
hararta yayi cikin slangs turancin shi yace go to your class,
da sauri ta fita tana dariya,

kallon Nadeeyah yayi yace "welcome, what is your Name?
Gyara baki tayi cike da kunyar kallon da yan ajin suke mata tace "Nadeeyah Adam from Fgc malali, "Good ya fadi yana kare mata kallo,
seat din Sabrinah ya kalla yaga ita kadaice bata barin kowa ya zauna,
nuni yayi mata da sit din yace "go and sit down der,
bata rai Sabrinah tayi fuska da alamar shagwaba tace "sir,
Hararta yayi ya cigaba da abin da yakeyi,
tana zama tace "sannu,
ko kallonta Sabrinah bata yi ba tace ciwo nakeyi?
Nadeeyah bata sake kulata ba ta maida hankalinta kan allo...





*Gombe state university*

9:34am
Monday 17th july,




Assalamu alaikum..

Waigowa gungun samarin sukayi suka amsa da "wa alaikum salam hade da mika mashi hannu suka gaisa,
dan Allah ina ne Acadamic planning? Hafeez ya tambaya yana gyara jakarshi,
kwatance suka mishi yayi musu godiya ya koma motarshi,
hanyar da suka nuna mishi yabi, yana zuwa gurin yaga sunan a manne,
fitowa yayi da takardunshi ya karasa kofar shiga,
layin students ya gani suna turereniya suna mika takardu, wani ya samu a gurin yace "dan Allah ina ne office din Director academic planing,
nuna mishi office din yayi ya juya ya kutsa cikin layin,

Da sallama ya shiga ya tarar da secertary dinshi,
bayan sun gaisa ya tambayeshi ko lafiya,
takardu ya mika mishi yace "nazo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login