Showing 69001 words to 72000 words out of 184071 words
Chapter 24 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt
mishi wasu takardun makarantarshi,
saboda go slow basu iso kaduna ba sai to 5,
A daidai gonin gora Musaddiq ya tsaya ya daukoshi cike da farin cikin sake haduwarsu bayan watanni,
hira sosai sukeyi a motar kamar wadanda suka shekara goma basu hadu ba,
ko wanne a cikinsu yayi kyau sosai,
musamman Hilal da ya fara practicing karatun da yayi ta hanyar yin zanen da ya doke na dubban mutane a cyprus,
Ba kananan kudi yake rikewa ba,
shiko Musaddiq bautar kasa yakeyi,
shima yana samun kudi sosai tunda yana taya Daddy wasu yan ayyukan, saboda tsabar kaguwar da Hilal yayi ya sanyata a ido shi ya sanya shi ganin kamar Musaddiq baya gudu, tsayar dashi yayi hade da karbar tukin ya taka motar a 140....
Tsayawa yayi da ya sauke Anty Raly a kofar gidan,
ganin da tayi bai tafi ba yasa ta dawo tana murmushi tace
"ko in kira maka ita ne?,
Murmushi ya sakar mata mai kyau wanda ya bata amsar manufarshi,
shigewa ciki tayi tana adduar Allah yasa Daddy baya gida,
dan tasan a gidan basa zance sai sun gama secondary school,
ita kuma bazata iya hana Taheer ba domin nauyinshi take ji sosai...
A parlor ta samesu zaune suna kallo,
saboda akwai Badar a parlon shi ya sanya Nadeeyah zama daga lungun Husnah tana gyara kumbarta da tasha jan lallen da ya rinu sosai ya koma maroon,
zama tayi ta kalli Nadeeyah da take ta mata murmushi,
"ina wuni Anty, ta fadi hade da mikewa ta dauki Fadeel,
hannunta ta kama tace "wow waye ya muku lalle,
Nuno mata hannu Husna tayi tace "Sadiya,
jiya tayi mana,
shafawa Anty Raly tayi tace "kaii gaskiya yayi kyau,
kwa kirata tamin in Abban Fadeel zai dawo,
kallon Badar tayi tace "Rasa kunya ina wuni,
bata kalli inda take ba ta mike tana fadin lfy lau ta wuce daki,
girgiza kai tayi tace "Allah ya shirya,
Nadeeyah jeki waje ki karbo min sako pls,
ajiye Fadeel tayi ta dauko dark purple hijab din islamiyya har kasa tasa ta yi hanyar waje,
tsayar da ita Anty Raly tayi ta taso tazo inda take,
gyara mata Hijab din tayi dan ya karbeta sosai bata ga dalilin sata ta canza ba,
"karki bani kunya kadai ta fadi hade da tura ta waje,
Tafiya ta fara yi tana maimaita "karki bani kunya a cikin zuciyarta,
sharewa tayi kawai ta fita dan ganin sakon da zata amso mata,
Tana fita idanuwansu suka sarkafu cikin na juna,
tsayawa tayi a bakin gate din ta kasa karasawa gurin da yake,
Tunanin juyawa tayi sai ta tuno kalaman Anty Raly,
Kamar zatayi kuka ta makale a jikin gate din gidan,
karasowa yayi yana murmushi,
yanayin tsoronta na matukar burgeshi,
gab da ita ya tsaya yana kallon yadda take wasa da yatsun hannunta,
Hankalinshi kacokan ya tattaro ya maida kan yatsun hannunta da kafa,
ya ilahi ya fadi a cikin ranshi,
"Son yarinyar nan dada narkar da zuciyarshi take,
Saida suka dauki minti uku babu wanda yayi magana,
ganin shurun yayi yawa yasa ta dago kai ta kalleshi,
saida ta gwammaci da bata dago ba saboda wani irin mayataccen kallon da yake mata,
maida kanta tayi da sauri murya na rawa tace
"ina wuni, wai ka bani sako inji Anty!
Dariya yayi hade da sauke ajiyar zuciya,
"sakon zuciyata zan baki,
ki taimakeni ki amsheta hannu biyu,
kinsan ita zuciya sakarya ce akan abin da take so,
Kallon ki kaɗai kan sanya in samu kuzari,
duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe.
Jin daɗi da walwala ba za su taɓa samuwa a tattare da ni ba matuƙar babu soyayyarki a cikin zuciyata.
Ki taimaki wannan zuciyar da bata taba furta so ba sai akanki
*Umm Nadeeyah*.
Kalamanshi sunyi mata nauyi matuka,
sun sanya ta rikirkicewa ta kasa tsayuwa,
sun sanya dukkan jikinta mutuwa,
ta rasa ainihin abin da take ji a cikin jinin jikinta,
"Dan Allah zan shiga gida kafin wani yazo ya ganni a waje,
yanayin yadda tayi maganar ya sanya duk wata kasala sauka a jikinshi,
yarintarta mai cike da nutsuwa ita tafi komai tafiya da imaninshi,
Rankwafowa yayi ta kasan fuskarta yana kokarin hada ido da nata,
gigitaccen Hon din da sukaji ne yasanyata dagowa da sauri har tana gogar kwantaccen sajen Taheer.........
Mrs Tijjani Shattima......@
[24/03 9:36 PM] Ummu Abdul 2: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣1⃣
By *Aysha Ya'u kurah*
Hannu Musaddiq yasa ya toshe kunnuwanshi saboda karar horn din ,
da yaga Hilal baida niyyar cire hannunshi a kan horn din yayi saurin janye hannun yana fadin "Haba Malam,
sai kace tashin hankali,
nasan yaji horn din da kayi zai bude,
ko kallon inda Musaddiq yake baiyi ba bare yasan me yake fadi,
nan da nan fararen idanuwanshi suka rine zuwa jajaye,
da ace wani zai rabi saitin kirjinshi da yaji mugun bugun da yakeyi kamar ana lugude,
ido ya zubawa Taheer dake tsaye jikin kofar gate din har lokacin bai matsa ba shima kallon motar yakeyi,
kokarin bude gate din Nadeeyah tayi taga yafi karfinta ta shiga kwala kiran mai gadin,
jin bai amsa ba ya bata tabbacin baya kusa,
hannu tasa da niyar sake gwadawa ko zata iya taji hannun Taheer akan nata,
da sauri ta zame hannunta taja baya,
murmushi yayi ya bude gate din yana jiran mai motar ya shigo ya rufe,
shuru har minti biyu ba'a motsa motar ba,
"Muje Mana, an bude gate kuma ka barmu a zaune,
har lokacin bai kalli Musaddiq ba, ganin da Taheer yayi motar ba shigowa zatayi ba yasashi kokarin rufe gate din,
da sauri ta tare gate din tace "shigowa zaiyi,
inaga motar ta samu matsala ne, bari in tambayeshi,
samm bata kawo Hilal na cikin motar ba,
karasowa gefen drivern tayi ta buga windon hade da fadin "Yaya Musaddiq zaka shigo ne?
Bude kofar taji anyi da karfi... na take ta maida Murmushin fuskarta tayi da sauri saboda ganin yanayinshi, wani mugun kallo yake mata wanda ya sanya hantar cikinta kadawa, cikin dacin rai yace "wanene wancan? Un-un-cle din mu ne na school, kamar ta watsa mishi wuta yaji, uncle? Karatu yake koya miki anan? "Um um ta fadi tana girgiza kanta, tare da Anty Raly suka zo,
Ehen sai ke kuma kika fito kina mishi me, "in ina ta fara yi wanda ya tabbatar mishi da zarginshi, dakyar ya iya controlling yaja tsaki hade wucewa gurin Taheer,
Zagayawo Musaddiq yayi yana tsokanarta ya shiga gefen driver ya shige cikin gida,
Bayan motar tabi tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki,
bata kalli inda su Hilal suke ba ta wuce da niyyar shigewa cikin gidan,
kallo Taheer ya bita dashi har ta kurewa ganinshi,
maido da kallonshi yayi gurin Hilal da ya tsareshi da tambayoyi,
Amsar wasu ya bashi ciki harda fada mishi dalilin zuwanshi,
tambayar karshe da yayi mishi ita yake ta juyawa cikin kwakwalwarshi,
" *Shin soyayya kuke koyarwa a makarantar*?
Bai iya amsata ba dan yana mishi kallon kuruciya karara,
hannu ya sake mika mishi a karo na biyu yace "zan tafi mutumina, dan Allah ka dan turo min ita akwai sakon da zan bata,
wani irin mugun kallo ya watsa mishi yace
"kaga malam yarinyar nan marainiya ce,
soyayya ba tata bace yanzu,
ilimi shine kadai zai zama gatanta,
in ta gama school den she decide abun yi next,
nd ko ta gama karatu ma tana da mijin aure,
Musaddiq ya nuna mishi wanda bai ma san sunayi ba,
wakarshi yake ji a earpiece yana kada kai yace "kaga wancan he is her cousin nd husband to be,
so plss spare her,
ka barta tayi concentrating pls,
wani irin dumi Taheer yaji a cikin jininshi,
kallon Musaddiq din yayi sannan ya dawo da dubanshi gurin Hilal da ya fara tafiya yace
"Hey....
tsayawa Hilal yayi ba tare da ya waigo ba,
gurin da yake Taheer ya karasa yace
"as far as batayi aure ba, ta zama allura cikin ruwa,
in rabona ce ko an sa mata rana da shi, sai na aureta,
nd da kake cewa Marainiya ce, dama Marainiyar nake nema, wacce zamu zama gatan juna,
karatu kuwa *Umm Nadeeyah* zata yi shi daga matakin farko har karshe,
ina yi ma kaina fatan nasara domin ina kallon future dinmu tare...
have a nyc day.. ya karashe fadi hade da taba kafadunshi,..
*umm Nadeeyah*
Hilal ya maimata zuciyarshi na dabdalar bugawa,
wato ma ta fada mishi yadda take son ya dinga kiranta,
kasa dagawa yayi a gurin da yake, kalaman Taheer sun zame mishi kamar dagger a cikin zuciyarshi,
Yana tsaye a gurin ya jiyo muryar Musaddiq yana tambayar *Idi* meye a hannunshi,
"sako ne akace in kai ciki,
"kawo nan Hilal ya fadi cikin dacin rai,
gurin da yake tsaya ya karaso ya rankwafo ya miko mishi,
kamshi ne ya daki hancinshi da ya karbi ledar, wasu cards ne a ciki wadanda suke bayyana irin tsantsar son da akeyiwa wanda aka mallakawa su,
sai sabuwar waya mai masifar kyau da tsada,
Yana gama dubasu ya kwala kiran Idi yana fadin ina mutumin da ya baka wannan ledar
"ya wuce yallabai, Idi ya fadi cike da girmamawa,
a hasale ya wuce hanyar parlon, bugun kofar yayi da karfi wanda hakan ya firgita Anty Raly da Nadeeyah da suke tsaye Anty Raly na jero mata tambayoyi,
wurgi yayi da kayan a kasan carpet yana yi musu wani irin kallo,
murmushi Anty Raly tayi tace
"a,a My son, yaushe ka shigo garin?
Bai amsata ba ya isa gaban Nadeeyah dake tsaye a tsorace,
"Aure kike so ko Umm Nadeeyah?yadda ya kira sunan kamar me ciwon baki saboda tsananin kishin dake cinshi..
Dago ido tayi a firgice tana girgiza kai,
sunan da ya kirata dashi ya firgita ta saboda ba hakan ya saba kiranta ba,
rai a bace yace "to me kike so?
at ur early age kinsan ki dinga kawo samari gida har ki fita zance, kina gab dashi kamar zaki shiga cikinshi,
bazaki ko iya hakurin ki gama secondary school ba,
ko tausayin kanki bakya ji,
in aure kike so ayi miki,
sai ki fada a sashi ya turo kije can ki bata rayuwarki tunda karatun ne bakya so,
shi kanshi baisan yana zubo wasu maganganun ba saboda tsananin bacin rai,
kukan da takeyi shi ya sanya Musaddiq dafa shi yace
"calm down mana, haba, zunubi tayi ne?
Meye laifi dan ta tsaya da saurayi?
karbewa Anty Raly tayi tace "kuma Taheer ma bashi da matsala sam,
kusa da gidana suke,
shin ba gara tayi aurenta ba ma ta huta,
"sai ki aurar da ita,
ya fadi cikin ficewar hayyaci, gaba daya idanuwanshi sun rufe, saboda bacin rai da tsananin kishi ko kukan da takeyi bai kula dashi ba,
ya nuna ta da yatsa yace
"na rantse da Allah in na sake jin kin tsaya da wani ko kin bashi dama har ya iya zuwa ki tsaya kuna taďi dashi sai na masifar ci miki mutunci tunda naga alamar baki san ciwon kanki ba,
Anty Raly da ranta ya gama baci tace
"yau naga ikon Allah,
kai zaka aureta da zaka hanata kula samari,
cike da rashin kunyar da ko yana ma wasu ita baya mata yace "Bazan aureta, domin ba sa'ar aurena bace, she is too young for my liking..
zan dai zame mata garkuwar da zata rike kanta a ko wani ta samu kanta,
kalmar "sa'ar aurena bace ta bata ran Musaddiq da Anty Raly matuka,
kallonshi Musaddiq yayi rai a bace yace "hey bata bukatar garkuwarka,
live ur life nd let her live hers,
Hannunta ya kama ya cigaba da cewa
"ba sa'arka bace, kamar yadda kace, so ka barta tayi abun da takeso,
ka nemi sa'oinka ka zame musu garkuwa,
yana kaiwa nan yaja ta zuwa dakinsu,
Hilal kamar zai mutu saboda takaicin zuciyarshi da furucinshi,
To ya zaiyi,
shi kanshi baisan ya fadi wasu abubuwan ba saboda tsananin kishin da ya nemi zautashi,
Kalaman Taheer sun matukar hassala shi,
ledar da yayi wurgi da ita ya dauka ya mikawa Anty Raly yace
"ki mayar mishi da abunshi,
babu wanda a gidannan waya ta gagareshi,
wallahi in kika ce baza ki mayar ba yanzu zan kira Daddy in fada mishi yadda kike son lalata rayuwar marainyar Allah,
Yana kaiwa nan ya fara tafiya zuwa dakin Musaddiq,
"In ka fasa Hilal,
in ka fasa ka fada ka raina kanka,
bazan mayar da wayar ba dan Allah in kana iyawa kazo ka zaneni,
mara kunyan banza da wofi,
Bayan Hilal Husna tabi tana fadin "sorry my PP,
rabu da Anty gobe zan mayar mishi da wayar school,
wani irin miyau ya hadiye mai daci a hankali yace
" laifi ne dan inason gyara rayuwarta,
girgiza kai tayi tace
"a'a ya Hilal,
in akwai irinka cikin rayuwarmu bazamu taba tagayyara ba,
amma pls ka dinga danne zuciyarka,
in kayi fushi kai kanka tsoron kanka kakeji, bana son ganin fushin..
gyada mata kai yayi ya murda dakin ya shiga hade cewa ta tafi ta barshi shi kadai....
A can daki kuwa Musaddiq keta rarrashin Nadeeyah wacce keta kuka sosai harda shashsheka tana fadin "walhi ban taba mishi magana ba,
kuma ni bance ina sonshi ba, nima buri na inyi karatu mai zurfi,
dan Allah Ya Musaddiq ka bashi hakuri,
wallahi bazan kara ba..
Zaunar da ita yayi a gefen gadonsu, ya tsuguna a gabanta ya sa hannu yana share mata hawaye yace
"karki damu,
ranshi ne ya baci,
duk tausayinki ne yaja hakan,
Yasha fada min in dinga sa ido a kanki saboda maraicinki,
Hilal na matukar son kiyi karatun da zai sa ki dogara da kanki,
A iya sanina ban taba ganin abun da Hilal ya damu dashi ba bayan iyayenshi, sai ni,
sai ke yanzu da kike son kwace min mishi,
nidai bazan yarda ba,
kawai kinsa ya daina damuwa dani,
ko waya mukeyi ya dinga tambayata ke kenan,
Dariya tayi sosai, yadda yayi maganar a shagwabe ya sanya ta manta duk wani kuncin da ya tokare zuciyarta,
Murmushi yayi shima ya mike yaja kumatunta yace "haka nake so kanwata,
karki kara zubda hawaye kinji?
kai ta gyada mishi ya kashe mata ido daya ya juya zai fita a dakin,
Ganin Badariyya yayi tsaye a bayanshi tana huci,
wani irin kallo yayi mata hade da cewa "lafiya?
Bata iya bashi amsa ba sai hawaye ya ga suna sauka a idanuwanta,
mtswwwww....
dogon tsaki yaja ya bi ta gefenta ya bude kofar dakin ya fita,
wani kololon bakin ciki ne ya turnuke Badariyya tayi ma Nadeeyah wani irin kallo hawaye na cigaba da ambaliya a idonta,
Mikewa Nadeeyah zata wuce Badar ta janyo ta ta hankada ta baya,
"uban me kukeyi a dakin nan ta fadi murya kausashe,
Husnah da shigowarta dakin kenan tace "me ko sukeyi, *Soyayya*
mana,
baki san suna soyayya ba dama?
ta fadi hakan ne dan ta tunzura ta, dan ta gane take takenta da dadewa....
aiko ta tunzuru,
dan hauka ta fara yi, ta cakumi wuyan Nadeeyah iya karfinta tana fadin
"wallahi saina kasheki,
shakar da tayi mata ita ta hana ta ihu mai karfi,
sai hawayen azaba da take fitarwa,
Da Husnah taga ta kasa kwace Nadeeyah a hannunta kuma tana ganin take taken zata iya kashetan da gaske tace
"na shiga uku,
wallahi karya nakeyi,
ki saketa Badar,
inaa kesashshiyar zuciyar Badariyya bata ji bata gani wen it comes to Musaddiq,
Da sauri Husnah ta fita tana ihu tana fadin
"Zata kasheta,
wayyo Allah Anty Raly kizo zata kashe ta,
Wa za'a kashe?
Daddy da ya shigo a lokacin ya tambaya a gigice,
Husnah da kuka ya kufce mata ta nuna dakinsu tace Badariyya zata kashe Nadee----
kafin ta karasa fadi Hilal ya murda kofar da karfi har yana cire handle din kofar,
lokacin da ya shiga kiriss ya rage Nadeeyah ta suma,
dan idonta da ya jike da hawaye ya fara lumshewa,
ita kanta Badar din kukan takeyi, amma zuciyarta ta ki bari ta saketa,
dama wannan damar take jira,
tsanar da tayi ma Nadeeyah mara misaltuwa ce,
gara ta kasheta kowa ya huta,
tasan hukuncinta kadan ne tunda bata kai 18yrs ba "a karancin iliminta na addini",
Iya karfinshi ya sa ya janye Badar, yayi wurgi da ita jikin drawer dakin har saida mudubin drawer ya fashe,
da gudu Musaddiq yayi kan Nadeeyah da ta durkushe tana tari dakyar,
rungumota yayi jikinshi yana jijjigata,
yana kiran sunanta da karfi saboda firgici......
Mrs Tijjani Shattimah......
[24/03 9:36 PM] Ummu Abdul 2: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣2⃣
By *Aysha Ya'u kurah*
Ganin yadda take lumshe ido ya sa Daddy cewa
"kawo ruwa da sauri Husnah,
rige rigen dauko ruwa sukayi ita da Anty Raly,
A kidime Musaddiq ya bude bakinta yana hura mata iskar bakinshi saboda yadda jikinta ya fara saki,
babu wanda a cikinsu ya ji, ko ya saurari irin dukan da Hilal yakewa Badariyya kamar Allah ya aikoshi,
Tun tana ihu anaji har muryarta ta dashe,
da gudu ta rarrafa ta rike kafar Daddy tace
"dan Allah Daddy kace yayi hakuri bazan kara ba wallahi,
finciko Hilal yayi yace "kin san Allah dama,
belt din hannunshi har ya tattare saboda azabar duka,
Badan tausayi ba,
sai dan saboda muryarta ta ishi Daddy yasashi cewa
"kyaleta Muktar!
Badan yaso ba ya kyaleta yana yi mata kallon ban gama dake ba,
a guje ta bar dakin tana ihun azabar haurin da yayi mata a baya,
a kofar shigowa palon taci karo da Su Mummy,
rungumarta tayi a tsorace tace "ke lafiya,
meya faru?
Kankameta Badar tayi tace
"zasu kasheni Mummy,
wayyo Allah bayana,
kallon su Mami da Anni tayi tace "ku shigo ciki ku zauna,
shigowa sukayi suka zauna,
Mummy taja hannun Badar suka shiga dakin,
Tsaye ta samesu dukkansu akan Nadeeyah da ta bude idonta tana maida numfashi,
Belt din hannun Hilal ta kalla rai a bace tace
"uban me tayi maka kayi mata dukan ficewar hayyaci,
abin da ya kawoka gidan nan kenan,
ya ilahi kayi min maganin yaron nan da duk in yazo gidana sai ya tayar min da husuma,
wannan wace irin mas----
dakata min!!
Daddy ya katseta fuskarshi a murtuke babu alamun wasa,
Naji alamar zuwan baki,
muje in samesu,
da kaina zanyi maganin matsalar gidana,
naji duk abin da ke faruwa tun zuwan Nadeeyah gidannan har kawo yau da idona ya gane min,
"Nadeeyah,
Mummy ta fadi a