Showing 150001 words to 153000 words out of 184071 words

Chapter 51 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

Advertisement

sata haďe da furta mata wasu rikitattun kalmomin da baisan ranar da ya iya su ba,

Shidai yasan ya horu matuka da rashin jin muryar dake kwantar mishi da hankali,
sannan idanuwanshi sunyi matukar kewarta,
tayi matukar sabar mishi da kaunarta mai sanyin dadi,
a halin da yake ciki yanzu baya jin zai iya koda yini ne ba tare da ganinta ba,

"Ikon Allah kenan,
shi yakan sanya so a lokacin da yaso,

Ko a cikin mafarkinshi bai taba tunanin zai iya samarwa wata mace gurbi a zuciyarshi ba, bayan wacce ya kira da mamallakiyar Qalbinshi,
*Zuciyar gaba daya*..

Sai gashi cikin kankanin lokaci soyayyar Maleekah na neman shafe babin dake adane da boyayyar soyayyar da tun yarinta yake dakonta,


Wasu lokutan in ya zauna yana tunani sai ya alakanta abun da cewar saboda ita din jinin Nadeeyah ce,
sai yanzu ne da ta hora shi na ďan kwanaki ya tabbatar wa kanshi irin kaunar da yake mata...


"Fushin masoya hutu,
cikin kankanin lokaci Maleekah ta manta komai ta saki jiki suka sha soyayyarsu wacce armashinta yafi na baya saboda amintar dukkan zuciyoyin biyu..

Sai da dare ya tsala sosai sannan Hilal ya rakata har cikin parlo ya juya ya tafi cike da kewarta....

Maleekah is very nice,
halayyarta da kyakykyawar zuciya irin ta Mahaifinta shi ya kara mata matsayi a zuciyar Hilal...


Har ya kai gida bai bar tunaninta ba,
koda yayi parking mota saida ya dan jima cikin motar sannan ya fito fuskar nan cike da annashuwa,
ta steps yabi zuwa sama,
duk inda yazo wucewa sai an mishi congrat harda masu bashi gift din aure,

"Al'adar larabawa da yan Nigerian dake cikin estate din kenan,
musulmi da arne in abun farin ciki ko bakin ciki ya sameka to fa tare za'a raba jajen da farin cikin,
wayewarsu tasa suka dauki juna tamkar jini ďaya...



Yana karasawa kofar flat dinsu ya soma jiyo hira da shewa cikin parlon kasa,
hakan ne ya bashi tabbacin yan uwa sunzo,
farin cikin da yake ciki ya mantar dashi miskilin halinshi,
nan ya murda kofar da sauri yagansu cike da parlon yan kangiwa da su Mummy,


Cike da farin ciki ya karaso ya dauki Fadeel ya jefa shi sama,

Sannunku da zuwa,
kun sha hanya,
gefen da Goggo ke zaune tana karkaďa kafa ya kalla yace "Harda su Goggo,
Lallai yau muna da manyan baki,
bata kalli inda yake ba ta cigaba da kaďa kafa tana sakucen hakori,

"Tunda ta shigo gidan taga hoton Maleekah shikenan farin cikin da ta guntso ya tafi,
da fari ta fara masifa akan duk matan duniya ya rasa wacce zai auro sai mai zubin karuwai,
saida Mummy tayi tsaye akanta sannan ta maida hankalinta ta zauna a gefe tana cika tana batsewa..


"Ina Anty Rally, ya tambaya yana duban mahaifiyarshi,

"Suna sama da su Raudha,
wani aiki suke ma Hinad,
Musaddiq na ďaki tun dazu yake jiranka,

Hanyar saman ya nufa da sauri cike da farin ciki,
yasan zaman su Mummy a parlon ne ya hanashi zama ayi hira dashi...




"Hey Mr Soft,
kana ina ne? 

Kafin Musaddiq ya bashi amsa ya karaso balcony din inda Musaddiq ke tsaye yana duban sararin samaniya,

Jingina yayi jikin karfen yanda zasu fuskanci juna,

"how r u Kyari?
Gyaďa kai Musaddiq yayi fuskarshi dauke da Murmushin da yafi kama da na ciwo,
ganin Hilal ne ya sanya zuciyarshi karyewa har murmushin ya fito,

A ko da yaushe in ya kasance shi kaďai yana jin sam rayuwarshi bata da amfani,

Ya kasa daukar hakurin mantawa da ita,
ita din mace ce da take da wuyar mantawa,
rayuwa yinta kawai saboda mahaifinshi da kuma Hilal,
amma yasan tabbas zuciyarshi na gab da bugawa dan ya kasa yin rayuwa mai dadi babu ita...


Gyara tsayuwa Hilal yayi cike da damuwar yanayin da yake mishi ciwo a duk lokacin da suka haďu da Musaddiq,
kafaďunshi ya dafa can cikin zuciyarshi yace

"Nasan yadda kake ji,
naji makamancin hakan,
saidai nawa mai sauki ne dan nesa nesa nayi da ita,
shakuwar mu bata kai ta ma'auratan da sukayi wa juna dandani haukaci ba...

Amma a fili zancen Maleekah yayi mishi dan ya mantar dashi damuwa,
labarinta ya dinga bashi ya kuma bashi labarin irin karamcin mahaifinta,


"Inaa kayan mu,
zamu kafa tarihi,
dan nasan sai munyi faďa da Maleekah akan kayan da zan sa,
dazu take faďa min tayi ordern kayan da zamu sa,
muje inga yanayin dinki...

Dakin suka koma Musaddiq na yaba tsarin dinkin da akayi musu,

  Hilal yayi matukar farin cikin ganin kayan dan daga shaddar har dinki sunci kudinsu,
ga wasu huluna masu matukar kyau kalar aikin kayan,
baje kayan sukayi suka cigaba da hira cike da debewa juna kewa.....





A katafaren masallacin gidan sheik aka daura auren,
farin cikin da wannan zuri'a take ciki a wannan ranar ba mai misaltuwa bane,
musamman Papa da Anty Reemah wacce saida tayi kukan farin ciki,
'yayanta Allah ya aurar mata dasu rana ďaya kuma cikin irin wannan zuri'a,
ita kuwa me zata cema Allah banda godiya,
yanzu Zainab ce kaďai a gabanta wacce take da burin faranta mata ta jiyar da ita dadin duniya....




Biki ne akayi shi mai kayatarwa dan an ci an sha kamar baza'a mutu ba,
sai kusan uku suka shirya tafiya reception,
yadda Hilal yayi zaton Maleekah sai ta bashi mamaki dan itama wani lace tasa wanda Anty Reemah tasa aka dinko mata,
riga da skirt ne Ash yasha duwatsu,
sunyi matukar kyau,
hakan da sukayi yazo da sabon salo, hotunansu suka dinga yawo a kafafen sadarwa na kasa da duniya baki ďaya,
wanda ma basu taba tunani ba yaga hoton,
domin babu inda hotunansu bai zaga ba,
Balarabiya da bahaushe cikin shiga ta hausawa,



A wannan daren boyayyen ruhi na nesa yayi kukan farin ciki da kuma na kewar makusanta,

hoton zamewa yayi tamkar wani kwai domin ya sanya ma'abocin kallonshi cikin shaukin son kasancewa da yan uwa..........






*6 years later*



*Cambridge Montessori Elementary School.*



The final round is here, *Expression words*
we have only three players left,

1 *Naurah Josephine*
2 *Mukhtar Hilal M Kyari*
3 *Victoria vertran*


Nan fa filin ya sake barkewa da ihu,
kowa na kiran sunan dan uwanshi....


Naurah ce farko,
tayi matukar kokarinta sai a wasu guraren ta kakare,


Sai Mukhtar,
kafin ya fara saida ya kalli inda wani mai irin kayanshi yake, kyakyawan mutum wanda hutu ya ratsa shi sosai,

Nuni yayi mishi da addu'a da hannu sannan ya sumbaci hannun ya hura mishi iska,

Lumshe ido Junior yayi ya rungume hannunshi haďe da jero adduoin da ya iya wanda ake koyar dashi a gida duk dare,
*Suratul nasr*
ya karanta karshe dan ya riga ya saba duk in zai zauna a aji sai ya karanta ta,


Bayan gaisuwar da ya gabatar cikin kwarewa sannan ya rufe da godiya haďe da kambama makarantarsu,
sannan ya rufe da wata siga ta marasa jin magana haďe da buga kwallon da ta gangaro gurin kafarshi,
bayan ya gama ya rufe da wata godiyar ya jero sunayenshi kamar haka..


Yours most lovely one
*HABIBI MUKHTAR HILAL MUSADDIQ KYARI*
A.K.A
*MHK TAHEER*.....

ya karashe yana juya rigarshi baya dan kowa ga sunan karshe,

Da sauri Taheer ya iso inda yake ya dagashi sama,
duk wanda ya gansu yasan uba da ďa ne saboda ba kaya ba hatta glass din su irin daya ne.......
tafin hannu da ihu kadai ke tashi a gurin.....


Nan dayan yaron yazo ya gabatar da nashi shima,
bayan sun gama aka basu kyaututtuka sosai dukkansu su ukun,
kowa cikinsu cikin farin ciki yake domin anyi making day dinsu......
yara na san irin ranar nan musamman a makaranta......





*****

*Queens University, Faculty of Law Ontario*


Yan mata ne biyu a tsaye cikin shiga mafi kyau da tsari wacce sai mai tsananin kamun kai ke yinta cikin university din..


Farar ciki sosai sanye take da koriyar riga wacce takai mata har kasa,
kasan rigar ta baya a tsage yake saboda ta dan tsuke,
jan sandals din kafarta mai tsini sosai ya kara mata tsayi wanda ya sake kayata dirin jikinta da hutu ya ratsa ko ina,
daga sama kuma ta yane kanta da jan mayafi ďan karami wanda ya fitar da kwantaccen gashinta har gadon baya,
gucci glass din dake makale a kan fuskarta shi ya sake fitar da natural kyan fuskarta wanda sam babu kwalliya a kanta,
gyara rigar Barristers din dake hannunta tayi ta duba bakin agogon hannunta,

Budurwar dake tsaye a gefenta wacce itama irin shigarta ce saidai colour da ya banbanta sannan ita babu rigar a hannunta tace

"It's late,
Aman is useless wallahi,
batayi magana ba sai juyar da kanta gefe da tayi domin hango M.I Saleem da tayi,

Muje Amal, mu koma office,
dariya Amal tayi tace
"Kinsan dai ko office din VC kika je sai ya biki,
gara kawai ki tsaya,
tsaki taja haďe da sake kiran Aman a karo na babu adadi,
jin wayar ta shiga ya sata murna ta fara tafiyarta mai daukar hankali,

"Haba Uncle Aman,
ya zakayi mana haka?

Mik'a yayi haďe da hamma cikin muryar bacci yace

"Anty Mamma wallahi bacci nakeyi ma,
banajin dadi,

Uncle T ya tafi dauko Junior yace in bari zai biyo ya daukeku..

"Subhallah,
sorry Uncle,
kasha magani?

"Eh shiyasa ma na samu na kwanta, ya faďi yana mikewa..

"Allah ya baka lafiya, ta mayar mishi cikin tausawa

"Ameen sai kun dawo!!!..




Assalam Nadeeyah..

"Wa alaika salam M.I ya kake?

Gyara tsayuwa yayi cike da jin dadi yace
"Lafiya kalau,
yanzu nabar office din director, vector yace min kina waje,

Fisabilillah kin kyauta kenan, wayarki sam bata shiga,
gashi bansan inda kuke ba,

jiya na dawo daga Nigeria,


"Ayya sorry Muhammad Ishaq, wayar ta ce ta lalece,
ya ka baro Nigeria?
Amal ta tambayeshi tana karasowa gurin...

Lfy kalau Amal,
amma da sai ta kirani,
kin san yadda na damu kuwa, dakyar na iya kaiwa wannan lokacin,
na kusa mutuwa fa,


"Thank Goodness baka mutu ba,
Nadeeyah ta faďi tana dariya,
kuma gashi har wata yar kiba kayi
Barr.. M.I,

"kasan na-------  

karar wusir din da ta ji ne ya katseta,
da sauri ta waigo ta kai idonta gurin,
tsaye ta hangoshi ta saman motar kanshi dauke da hular sport,
farin glashin da ya mayarda tamkar dashi aka haifeshi yana makale a idonshi,

Shekarunshi bakwai da doriya amma saboda girman jiki zaka rantse ya shekara tara zuwa goma,
bakar chocolate fatarshi da a kullum in ana mishi wanka yake magiyar a wanke mishi ita saboda dukkan wadanda yake kewaye dasu farare ne tass sai kyalli takeyi saboda ranar da suka kwaso,

Motar na tsayawa dab dasu ya kara sautin wusir din,

*Anty Mammaa*

*Your MHK will always win, we won Mamma*,

Da sauri ta fara sakkowa daga matakalar dake kofar faculty din ta nufi inda suke,
kafin ta karaso ya bude motar haďe da dakko wani cup da aka bashi a school ya nufeta da gudu ya dane jikinta,
baya tayi zasu faďi saboda tsabar nauyin da yayi mata,

rikeshi tayi da karfi dan kar su faďi tare tace

"Kasan fa ka fini nauyi,
kana son ka kai Mamma kasa ne?

Sauka yayi da sauri yana dariya, "kinga award cup dina,
sauran gifts dina cikin motar Daddy,

Sai a lokacin ta kalli motar,
haďa ido sukayi tayi saurin saukar da idonta kasa,
sport wear ne a jikinshi shima irin na jikin Junior,
babu wanda zai musa cewa ba mahaifinshi bane,
saboda komai nasu iri daya ne, glass din idon ma kadai ya isa baka shedar duk tare suke ciwon, in ba su da suka sani ba kowa ya dauka medicated ke idon junior, basu san tsabar fitinar sai yayi abin da Taheer yayi bane,

sai kuma  kamanni da ya banbanta su,
duk wanda yasan Musaddiq in yaga Junior yasan ďanshi ne domin babu abinda ya rabasu,
zuciyarsu ce kaďai ta banbanta,

Junior Allah yayi mishi zafi sabanin Musaddiq da yafi ruwa sanyi...


"Nadeeyah zan wuce anata kirana,
bani phone number din zamuyi waya,

Ba Nadeeyah kaďai ba har Amal dake tsaye rike da cup din Junior saida hantar cikinta ta kaďa,
a tare suka kalli gurin da Taheer ke tsaye yana kaďa mukullin mota,


Cikin sauri Amal tace "M.I bata da waya,
bari in baka tawa in ta s------

"Amal...
Taheer ya katseta cikin kausassar murya,
haďiye miyan da ya taru a bakinta tayi ta nufo inda yake, lokacin Nadeeyah har tayi ma kanta mazauni a baya,

"9100619"

wayar Mamma na bata lalace ba, Anty Amal wasa take maka,
Junior ya faďi da karfi yana kallon M.i dake tsaye galala,

Turashi cikin motar Amal tayi ta zagaya baya ta zauna kusa da Nadeeyah....


Karasawa gurin da M.i ke tsaye Taheer yayi,
duk cikinsu babu wanda yaji abinda yace mishi,
har Junior dake ta kokarin buďe kofa suna hanashi,
ga mamakinsu sai hango Taheer da Muhammad sukayi suna dariya haďe da tafawa,
sunfi minti biyar a tsaye sannan sukayi sallama.....




Daddy kaga Mamma ta dukeni a kai na ko?,
cikin harcen hausa ya faďi wacce bai iyata sosai ba,
tada motar Taheer yayi yace "Sorry big boy,
Mamma tayi sabon aboki,
yanzu batayi damu,
karka damu kaji kai ma zan nema maka new Mamma,
wacce bazata dukar min kai ba...

Mikewa Junior yayi ya hau kan kujerar ya tura kanshi baya,

Gwalo yayi ma Nadeeyah yace "New Mamma is coming,
ba ruwan mu dake,

Daddy harda Anty Amal ko? Itama ta ja min hannu,

"Rabu da ita sweetheart munafuka ce,
ita Aman ne zaiyi mana maganinta,

"Allah uncle ba ruwana, ta faďi a shagwabe tana turo baki,

"Laa Daddy ta turo maka baki,

"Rama min Juju!

Ya faďi yana gimtse dariyarshi, yanayin da ya hango fuskar Nadeeyah yasan tabbas hankalinta a tashe yake,

wani irin shauki yake ciki tunda yaji kalaman M.i akanta,
yasan tabbas bata da lokacin kula wasu dan da tana yi bazata fito da sakamako mai kyau a makaranta ba,



"Aaaaaaaaaaaa....


Burki ya taka da karfi saboda ihun da junior ya saki,
"Subhanallah lafy?,


Amal da ta rufe idonta tana baccin karya ya nuna da yatsunshi...


"Ya salam,
Amaaaal...


"Na'am Uncle ta faďi tana mutstsika ido,
"har mun kawo gida ne?


Dariya mara shiri Taheer ya saki yace
"Wallahi zan bata miki rai,
zaki sauka ki karasa gida a kafa dan jakarki ma kwace ta zanyi,


"Kawai kace in muku bankwana dan ko nan da pizza hut bazan iya zuwa a kafa ba,
saidai gawa ta,


Tsaki yayi ya tada motar haďe da nutsar da junior a gaba ta hanya siya mishi candy ice cream..,
babu wanda ya sake magana a motar sai zuciyoyi dake ta zance isu isu.......





Ayi hakuri baifi 5 pages suka rage ba in shaa Allah......


Masu faďin maganganu san ransu karku damu, in shaa Allah  tafiyarmu ta kusa karewa,
dan Allah kuyi hakuri maganganunku na sanya gwiwata karyewa,
suna sanya typing fita a raina,
ku kara hakuri...
in sauri kuke so bazan yi shi yadda nakeso ba thou wasu guraren takaita su nayi, Nagode sosai.....



Mrs Tijjani Shattima........
[10/06 9:33 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣6⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





*A square Turkey constructing company*....


Ya rasulullah...
dattijon ya faďi haďe da dafe kanshi,
coffee din dake gabanshi ya ture gefe yana mai sake duba cikin system dinsa,
ya dade bai duba ayyukan gidajen shi ba saboda yadda ya yarda da ingancin masu yi mishi aiki musamman mai mishi zane da engineern dake tsaye gurin ganin an tsara ginin yadda ya kamata,

"kusan watanni shida kenan da gama aikin wasu gini amma har yanzu mutane biyar kaďai suka siya wasu bangare daga gidan,
tun yana Egypt yake damuwa da outcome din business dinshi dake turkey,
yau dai ya shirya zuwa dan ganin dalilin da ya sanya companynshi ya fara zama koma baya wurin ciniki a kasar instanbul,
ganin yanayin tsarin ginin da ya kashe makudai kudi yayi su ya sanya hankalinshi tashi matuka,
sam zubin tsarin baiyi ba,
komai anyi shi a gaggauce,
kama daga zanen har ginin,
sam bai iya bacin rai ba domin shi mutum ne wanda ya yarda da kaddara mai kyau da marar kyau,
asarar da yayi bata kananan kudade bace,
haka ya bar gurin yana istigfari haďe da adduar Allah ya sanya asarar da yake shirin yi ta zame mishi alkhairi....



Yana komawa office ya bukaci sanin a inda matsalar take, engineern ya fara kira,
nan ya gabatar mishi da zanen da aka bashi domin yin aikin sannan ya ďora da cewa

"kanin manager ne yayi zanen,
wanda ya saba yin zanen ya bar aiki damu kamar yadda manager ya faďa min..

Sheik na ganin zanen ya gane a inda matsalar take,
bai bukaci jin wani karin bayani ba yayi zaune hankali duk a tashe yana hango dakushewar kasuwancinshi kwana kusa,


Rufe system din yayi ya mike ya danna wata kararrawa dan yin taro na gaggawa da ma'aikatanshi,
nan fa suka shiga tururuwar shigowa cike da ladabi suka tsaytsaya a muhallinsu.....



Bayan ya gama musu bayanai na abun da ya tarasu sannan ya dora da irin barazanar da companynshi yake fuskanta ya kuma yi umurni da kar a sake baiwa wanda yayi zanen gidajen da sukayi musu bandaro aiki,

Bayan nan ya bukaci duk wani wanda yasan mai zane wanda ya kware a zane ya je ya kawo shi ya kuma sashi ya taho da aikin da yayi,
rabin yan gurin wadanda suka san Hilal suka fara ihun sunan

*M H K*...

wasunsu kuma suka fita domin kiran makusantansu suzo ga aiki ya samu,

Cikin awanni uku aka haďa masu zane kusan su 15,
nan duk suka gabatar da ayyukansu wanda ko rabin na Hilal basu kamo ba,
cike da kosawa ya kalli zanen na karshen haďe da mikawa engineern,

"Call for another meeting plss,
ina son sanin dalilin da yasa Hilal ya bar aiki anan gurin..
cike da girmamawa engineern ya amsa shi ya fita da sauri ya sake kiran wani meeting din..




"Da harcen turancin dattijon da bai wuce shekaru hamsin da doriya ba yake magana,

"Nasan akwai masu zanen gidaje da yawa,
amma companyn nan kowa yasan "Hilal Kangiwa" ne yake zanen gidajen da muke ginawa masu daukar hankalin jama'a,
duk wadannan masu zanen da kuka tara min dan Allah ku basu hakuri,
a je a nemo min Hilal muyi eye to eye dashi inji nawa yake son a kara mishi,

Cikin girmamawa manajan kamfanin yace

"Ba kudin bane sukayi mishi kadan,
matsala suka samu da IRFAN,
shine yace ya bar aiki,

Ya salam...
dattijon ya fadi yana mai dafe kanshi,
wato Irfan sai ya kori duk wani wanda suke kasuwanci tare,

a kausashe yace
"bani number wayarshi zan kirashi yanzu yazo office ya sameni...



******

"Duk tashoshin cartoon din yau basu yi zee,
kin gani? ta tsaida kan Mbc 1,
tana yunkurin canzawa wayarta ta dau kara,
mikewa tayi da sauri ta zare wayar a charge,
daki ta wuce tana waya da Jamal cike da so da qauna,


Lamoo Zainab tayi cikin lallausar kujerar parlon tana kallo haďe da lumshe ido alamun bacci nason yin gaba da ita, 
bata dauke idonta a kan tvn ba dan tasan in suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login