Showing 18001 words to 21000 words out of 184071 words

Chapter 7 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

ce, lokacin yinta a gareki baiyi ba Nadeeyah,

Tafiya suka fara yi Nadeeyah na binsu tana kuka tana fadin karku tafi ku barni,
tun tana hangensu har haske ya kara kewaye gurin,
tsayawa tayi hade da runtse ido tana kiran sunayensu hade da shashshekar kuka...

Hannun da taji kan kuncinta mai sanyin kamshi ne ya soma farkar da ita,
a hankali ta bude idonta ta saukesu kan Hinad da itama kukan takeyi..

"Sorry Nadeeyah,
kiyita karanta innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
i know it hurts but bamu da yadda zamuyi,
addu'a itace tafi dacewa dasu a wannan lokacin,
Allahn da ya halicce su ya fimu sansu.. 

kawar da kai Nadeeyah tayi tana tunano hirarsu ta cikin mafarkinta,

"kunyi tafiya mai nisa Mamma,
tafiya mai dadi a gareku in shaa Allah,
sannan mai radadi a garemu,
hawayen idonta bai bar ambaliya ba ta cigaba da maganar zucin da takeyi, yanzu yaya rayuwarmu zata kasance,
shikenan bamu da wani sauran gata...

"Gatan kowa Allah ne Kanwata,
babu wani gata mai daraja, dadi, da dadadawa irin na ubangiji,
in Allah ya baiwa bawa gata, to babu wanda ya isa ya tauye ko ya kwace mishi,
mika lamarinki gurin ubangiji, kuma kiyi tawakkali kisan shi ne kadai maiyi...

saida ya kai aya Nadeeyah ta dago ta kalli gefen da yake,
tabbas zancen da takeyi a zuci ne ya fito har ya iske kunnuwanshi,
shi din ma tsaye yake idon nan nashi yayi jawur kamar gauta,
wani hawayen ya share sannan ya karaso jikin gadon da take,
zama yayi gefenta yace "ya jikin naki, runtse ido tayi ta amsa da sauki,
Allah ya baki lafiya da hakuri hade da juriya,
"Ameen yaya Musaddiq,  Hinad fadi tana share mata sauran hawayen dake gefen kunnenta..

Ina Zainab take yaya Musaddiq?
Kafin Musaddiq yayi magana sukaji an murda kofar,
Hafeezu ne ya fara shigowa sai su Anty Reemah,
Hilal ne karshen shigowa shi da zainab, hannunta rike da ledojin kayan kwalama,
fuskar nan tata tayi jawur,
tana ganin Nadeeyah ta saki ledar ta karasa ta fada jikinta tana kuka,

mikewa Nadeeyah tayi a hankali sannan ta janye daga kusa da  musaddiq, ta dago kan zainab tace "menene, me aka miki?
Anti Nadeeyah mamma ma ta mutu, ta tafi gurin baba,
sun dauketa sun fita da ita,
shikenan bazamu sake ganinta ba,
dariya Nadeeyah tayi tace "inji wa yace miki,
mamma bata mutu ba,
kinsan tace miki zata je Agadaz rannan ko?
Eh zainab tace tana me kallon Nadeeyah,
to can ta tafi, kina gani sun shiryata ta hau jirgi tana jin dadinta ke kuma kina nan kina kuka,
oya share hawayenki ki ji abin da mamma tace in fada miki dazu kafin ta tafi,
da sauri ta share hawayenta ta matso da kunnenta kusa da bakin Nadeeyah, rada tayi mata a kunne wanda Allah kadai yasan me tace mata, sai ko Zainab ta kyalkyace da dariya hade da rungume Nadeeyah, tace "dagaske kikeyi Anti? 
Gyada kai Nadeeya tayi tace "eh,
hawayen da ta boye ne ya fara bin idanuwanta, ta kankame zainab tana zubar dasu ba tare da ta bari ta gansu ba, wayyo mutuwa.....!

@
Mrs Tijjani Shattima....!

[07/03 6:31 AM] fareedah: ●ZUMUNCINMU A YAU● 1⃣9⃣
By Aysha Ya'u Kurah




Had'a kayayyakinsu cikin jaka Nadeeyah keyi, idanuwan nan nata sai ambaliyar ruwa suke,

Hafeez ke tayata had'a kayan yana labarta mata abubuwan da suka gifta tsakaninshi da iyayensu a yan watannin da suka shude,
jan numfashi yayi kamar karamin yaro,
daga zuciya har idaniyar shi zubar ruwan hawaye sukeyi,

"yan kudaden da suka fara shigowa hannuna su suka ruda ni,
na canza abokai,
kullum bani wancan club bani wancan,
ban tsaya nan ba har sai da na koma harkar mata,
tun ina boyewa, su Baba basu sani ba har takai ga mata har gida suke biyoni,
bazan taba manta daren da zan bar gida ba,
Baba ya fito zai tafi Sallar asuba ya jiyo muryata da SAILUBA yar gidan Hinde mai tuwo,
ranar a daki na ta kwana, Koda Baba ya bude kofar, Sailuba na kwance a jikina,
duk yadda na kai ga tureta in suturta jikina ta kafe ta danneni, na kasa tabuka komai,
saida Baba ya juya, nayi karfin halin turata na mike nasa jallabiya nabi bayanshi,
Kuka na tarar dashi yana yi a tsakar gida,
a tare muka iso inda yake ni da Mamma,
ajiye butar hannunta tayi ta fara tambayarshi dalilin zubar hawayenshi,
bai kai ga yin magana ba Sailuba ta fito da daurin kirji da kayanta a hannu tana sawa tana fadin
"Zo ka sallameni Hafeezu in tafi kar a nemeni a gida,
wani irin juwa Mamma ta ji a tsakiyar kanta, bakinta da kyar yake iya furta innalillahi wa inna ilaihir rajiun, daki Baba ya jata ba tare da ya dubi inda na ke ba,
koda na biyosu ciki da sauri Baba ya dakatar dani yace
"fitar min a daki da kazantar dake jikinka,
tafi kaje ka sallameta,
ka wadata ta da duk wani nau'i na jin dadi tunda kaima ta jiyar da kai dadin,
ubangiji Allah ya shiryar dakai Ameen,
Har na iso kofar dakina ina jiyo sautin kukan mamma, Baba yana ta bata hakuri..

Da kudin da ni kaina bansan yawansu ba na sallami Sailuba,
sai na wuce nayi wanka nayi sallah,
shaidan ya dinga raya min in bar gidanmu in tafi can inda babu wanda yasanni, tunda ina da kudina inje in ci karena babu babbaka,
a haka nabi umurnin zuciyata na shirya kayana tsaff na sasu a mota,

Zainab na gani a kofar shagon Tasi, na bata dubu biyar ta kaiwa Mamma, nace ta fada musu nayi tafiya,
tun kafin ta shiga gidan na shige mota nayi gaba,
a tunanina duniyata zatayi kyau tunda babu mai samin ido,
ashe tafiyar da zata kashemin zuciya ta barni da dana sani har karshen rayuwata nayi... ya karashe maganar cikin matsanancin kuka...


Takalman Zainab Nadeeyah ta tura cikin ledar dake hannunta, wacce tun fara bata labarin ta budeta da niyyar zuba takalman,
ledar ta jike sharkaff saboda hawayen da ke sauka a kanta,

kallon Hafeez tayi tace "Yaya Allah yayi mana jarabawa mai zafin gaske,
rayuwa ce yanzu zamu fara ta wacce bamu san inda zata kaimu ba,
ka godewa Allah da yasa suka yafe maka, sannan kaji tsoron Allah,
ka nisanci duk wani aikin alfasha, kasani duk abinda zakayi yanzu za'a tada su Mamma ace su tashi suga dansu, shin irin wannan tarbiyar suka baka,
kasani yanzu babu wani wanda zai fada maka gaskiya,
rayuwa ce zakayi ta ta rashin mafadi,
kai da kanka zaka zama mafad'in kanka,
ni da zainab kuma duk inda zamuje na tabbatar bazamu rasa mai kwaba mana ba, kaga mummy yanzu ta canza,
matsalata daya itace "Bad----- shigowar Hinad cikin dakin ya katseta, ta kallesu tace "Nadeeyah Mummy tace kuyi sauri,
hawaye ta share ta dauki karamar jakar, Hafeez ya dauki babbar suka fito sukayi waje,
loda kayan sukayi a motar Hafeez, sannan kowa ya shiga mota,
Hinad da Nadeeyah motar Hafeez suka shiga,
makota suka kewaye su Nadeeya anata musu fatan alkhairi,

Tasi ya leko ta windon motar, ya miko mata ledar lolli pop idonshi cike da kwalla yace "ki ajiyewa Zainab, Allah ya hadaku da alkhairi Nadeeyah,

Wani kukan ta fashe dashi na tuno memories dinsu na lokacin da dukkan iyayenta suna da rai,
da irin kara kainin da sukayi tsakanin gida da shagon Tasi,
Tasi ya bada gudunmuwa mai karfi a rayuwarsu, bai taba kazawa gurin tallafa musu da bashi da kuma kyauta ba,
kallonshi tayi yana share hawaye tace "mun gode Tasi Allah ya saka maka da gidan aljanna....




Islamiyyar su Zainab suka biya dan daukota,
motar Mahmoud suka tarar a kofar makarantar,
kafin suyi parking suka hango Musaddiq rike da hannunta sun fito daga ciki,
baya ya bude mata suka shige, Mahmoud yaja motar suka wuce,

Bayansu Hafeez yabi, zuciyarshi ta dan rage zafi da fargaba saboda yasan in shaa Allahu Musaddiq da mahaifinshi bazasu bar kannenshi cikin garari ba.....





A katafaran gidan "Alhaji Mukhtar Kyari dukka motocin sukayi parking,

Ta window Badariyya take lekensu daya bayan daya,
Husna da dawowarta daga saloon kenan ta fito daga bayi tana kallon Badariyya a jikin Window tana leke,
murmushi tayi ta zira Hijab dinta ta fito tsakar gidan tana ma mummy barka da dawowa, dan ita ba gidan rasuwar take kwana ba,
gidan Anty Raudha take bin ta su kwana,
yau ne kadai bata je gidan rasuwar ba taje saloon dan wanke kanta,

Anty Radiya da Anty Raudha suka kalleta cike da shakiyanci suka ce "Amarsu ta ango,
cikin rashin fahimta ta waiga bayanta taga babu kowa tace
"wacece haka? Dariya suka kwashe da ita suka ce ke mana!
Zatayi Magana Anty Reemah tace "wani irin sakarci ne wannan, ku dan matsa daga can mu wuce sai ku cigaba da shakiyancin tunda sa'arku ce Husnan,
darewa sukayi ta wuce ita da Anty Raliya, harara Raudha tabi Raliya dashi tayi tsaki tana kunkuni a ranta,
"su in an barsu mutanen kirki, Radiya tace "manta dasu dallah, taja Husna sukayi ciki,
mummy tayi kamar bata jinsu tace ma Nadeeyah su kamo kayan su shigo,

A d'arare ta dauki jakar ta fara tafiya, kama gefen jakar Hinad tayi suka karasa cikin parlon,

wani irin faduwar gaba Nadeeyah taji,
idanuwanta suka ciko da kwalla,
tuno abubuwa mabanbanta da suka faru da mahaifiyarta na rashin dadi ta dingayi,
wani lungu ta zauna inda suka saba zama da mahaifiyarta in sunzo gidan.....


Labulen windon Badariyya ta saki kirjinta kamar zai fado saboda bakin ciki,
bata hango Nadeeyah ba, amma ganin Zainab a gurin Musaddiq suna magana yana dariya ya tabbatar mata da lallai su Nadeeyah sun dawo gidansu da zama,
bata karasa tunaninta ba taji an shigo dakin ana dariya,

Cikin kaguwa Husnah tace
"Anty Raudha tell me, waye amaryar plss,
Radiya ta ajiye yaronta Fadeel a kan gadon tayi hanyar bayi tace
"ke mana, kece amaryar Hafeez,
wata dariyar suka sake kecewa da ita sannan Radiya ta shige bayi,

Husnah ta turnube fuska tace "wani Hafeez din,
Anty Raudha tace "Hafeez din mama Suwaiba mana,
kaff ta kwashe labarin abinda ya faru ta fadawa Husna suka karashe da dariya dukkaninsu,

Badariyya tayi tsaki mai karfi tace "da an hadasu din, da zaifi mana alkhairi walhy,
domin zuwansu nan din gaskiya akwai matsala,
bama mai yiwuwa bane zamansu anan!! ta karasa fadi a gadarance,

"Saboda kece mai gidan ko,
Raliya da shigowarta kenan ta fadi tana harararta,

Raudha tayi tsaki tace "nima zamansu anan din walhy bana sanshi,
ni fa Allah ya sani na tsani talaka,
ko sunan talauci banasan ji,
Radiya daga bayi ta dago murya tace "ai talauci masifa ne, ni na rasa laifin me talaka yayiwa Allah,

subhanallahi!!! Raliya tayi saurin cewa, ya salam, ku kuwa kuji tsoron Allah,
talaucin nan fa wadanda suke cikinsa basu suka sawa kansu ba,
kuma basu isa su cireshi ba sai Allah yaso,
haka zalika arzikin da kuke ciki baku kuka bawa kanku ba,
babu banbanci tsakaninmu, tunda duk abinda da talaka zaiyi mai kudi ma zaiyi,
wadatar zuci tafi komai a rayuwa,
suma Allah bai mance dasu ba,
kuyi fatan kar Allah ya jarbceku da dandana rayuwar talauc-----

"" eeeeeeh eeeh wait hang it, Radiya tayi saurin katseta,
" har abada bazamu taba dandanawa ba "idiotic being, saboda muna sharhi kan talauci shine zaki rabashi jikinmu,
to we reject it walhy, sakarai kawai,,

uhmmm kawai Raliya tace ta fita tana mamakinsu,
har ta kure dakin bata daina jiyo muryoyinsu ba....


Har karfe biyar na yamma Nadeeyah na zaune a inda take, da himilin kayansu,
anan taci abincin da me aikinsu ta zubo mata,
tana kallon dukkan ahalin mummy a cikin parlon ana hira,
Anty Reemah ce kawai bata cikinsu, dan ita tun zuwansu suka wuce can gidansu ita dasu Hinad,
ba yadda Hinad batayi tazo su tafi ba taki,
kwanciyar hankalinta daya zainab ta bisu shiyasa ma zaman bai gundureta ba,
gyangyadi ta farayi a zaune ta jiyo muryar Badariyya tana zuba rashin kunya tana fadin "wallahi mummy indai yarinyar can zata zauna a gidan nan ni bazan zauna ba,
saidai ku zabi daya,

janyota mummy tayi jikinta tace "haba baby,
kiyi hakuri mana, dalili ne yasa zata zauna, kiyi hakuri pls na lokaci ne, kuma kinga makaranta zata koma,
ba ganinta zaki dinga yi kullum ba,

Keyn mota Raliya ta dauka a kan center table, ta dauki danta tace "Mummy sai anjimanku,
tayi hanyar waje ba tare da ta jira amsarsu ba,
badan a karkashin wani take ba, wallhy babu abinda zai hanata tafiya da Nadeeyah,

mutuwa mai tonan asiri, duk talaucinsu basa zuwa gurinsu maula,
rikon na Nadeeyah nawa yake?
abinci ne fa kadai sai gurin kwanciya, sai dan kyautatawar yau da kullum,
share kwallar idonta tayi ta shiga motar tana fadin, "ya Allah ka raya mu cikin ya'yanmu....



Dakyar mummy ta shawo kan Badar ta yarda, da sharadin a dakin mai aikinsu Nadeeyah zata zauna,
dan ita sam bazata iya hada daki da Nadeeyah ba,
dan a samu kwanciyar hankali mummy ta yarda amma can cikin ranta badan taso ba,
Husna ma abin ya mata zafi sosai,
Raudha da Radiya kuwa tsaff suka goyi bayan Badar...


Dakin mai aikin nasu ma da d'an kyanshi,
kayanta kawai ta shigar ciki ta fada bayi,

sai da tayi kuka mai isarta sannan tayi wanka ta daura alwala ta fito...

A inda ta idar da sallar ishaa bacci yayi gaba da ita,
sai ajiyar zuciya take cikin baccinta,
mai aikin nasu yar dattijuwa ce, taji tausayinta matuka, ta kuma yi tirr da hali irin nasu mummy, masu yin watsi da jininsu saboda talauci, tashinta tayi ta maida ita kan gado taja mata abun rufa......






Mrs Tijjani Shattima........!
[07/03 6:31 AM] fareedah: ●ZUMUNCINMU A YAU● 1⃣8⃣
By Aysha Ya'u Kurah




Tsakurar abincin dake gabanta takeyi tana juya cokalin,
ta rasa menene asalin abinda take ji cikin ranta,
farin cikin sanin halin da Nadeeyah ke ciki na rashin iyayenta takeyi ko kuwa bakin cikin tarewar da kowa yayi a gidansu Nadeeyan,

Mutuwar mamma na iskarta tayi murmushin farin ciki,
tasan Nadeeyah na can cikin radadin da ta sanya ta,
saidai takaicinta daya musaddiq sam baya yarda su hadu, duk wata kafa da zata sadasu ya tosheta, dan sam baya son jin ko muryarta,
wani irin tsanarta yakeji a zuciyarshi na rashin imaninta,
babu wanda bai ziyarci gidan mutuwar ba sai ita,
kullum tana zaune a gida daga kallo sai cin abinci sai game,
babu yadda mummy batayi ba akan tazo gidan mutuwar tun farkon yin ta, amma sam taki zuwa,
gashi wata mutuwar ta sake bullo kai...
Tura abincin gefe tayi ta mike ta wuce daki dan ta watsa ruwa, ita kadai ta kwana a gidan, sai daddy da taji tashin motarshi da asuba tasan shima a gidan ya kwana,
ko gezau bata ji ba a zuciyarta bare ta karaya ta shirya zuwa gidan su Nadeeyan,
ita sam bata san zafin mutuwa ba, a ganinta kuncin da Nadeeyah ta sanyata yafi zafi akan radadin mutuwa, tsaki taja hade da wurgi da kayan jikinta ta fada bayi......





***********
Bayan doguwar addu'ar da aka gabatar a kofar gidan malam Adamu na sadakar ukun mamma Suwaiba,
sadakar abinci akayi sosai,
duk wanda yake gurin saida ya wadatu da abinci saboda yawanshi, cikin kankanin lokaci jama'a suka watse ya rage saura makusanta kawai,

Baffa da shock din mutuwar bai sakeshi ba har lokacin ya mike kamar ba laka a jikinshi ya shige cikin gidan,
Saida ya zauna yana maida numfashi sannan ya dubi gurin da mummy da Goggo ke magana,
fada mummy keyi akan rashin zuwan Badariyya,
ita kuwa goggo goyon bayan Badariyya take hade da fadin "kinsan yarinya ce kuma bata san hayaniya, duk mu da muka zauna a gidan har kwana uku bamu wakilceta ba,
Baffa dai kallonsu yakeyi zuciyarshi na tafasa amma bakinshi yayi nauyi ya gaza furta koda kalma daya ce,

Hinad dake zaune can gefe kusa da Nadeeyah ya yafito da hannu alamar tazo,
da sauri ta karaso gabanshi tace gani Baffa, cikin murya mai rauni yace, taje ta kira Hafeezu da Daddy a waje,
sai a sannan mummy tasan da shigowarshi, karasowa tayi ta zauna kusa dashi tace
"Baffa yaushe ka shigo, murmushin yake yayi yace "yanzun nan,
tafi ki kirawo min dukkan ya'yanki akwai maganar da nake so muyi daku, kai ta gyada tace "to Baffa, ta mike ta fita tsakar gidan,

Zama Goggo tayi tana matsa mishi hannu hade da cewa duk kwana ukun nan baka da wani kuzari,
mutuwar nan fa ba a kanta aka fara yi maka ba,
ka rasa uwa, uba, mata, da ya'ya,
saidai wannan mutuwar na lura tafi razana ka,
wanda ni bansan dalili ba,
mutuwa daya ce, in mutum yayi ta baya dawowa, inda ana dawowa sai ince ka cigaba da damuwar, watakil damuwar taka na iya dawo da ita,
ya kamata ka sanya wa kanka nutsuwa kayi tawakkali,

Hawayen da ya zubo a gefen idonshi ya share zuciyarshi na rawa yace "Asama'u! duk mutuwar da akemin ta Suwaiba tafi tsaya min,
kinfi kowa sanin hal---- da sauri ya dauke idonshi cikin nata, ya kauda kanshi ya canza maganar da cewa "ina matukar tausayin halin da yaran nan zasu shiga ne, waye zai rike su? Ina zasu je?

Goggo tayi saurin cewa "ai Nadeeya ta mallaki hankalin kanta,
sannan ga Hafeezu shi zai fito da mata yayi aure sai ya hada ya rikesu gaba daya,
in suka zauna anan shine hankalinsu zaifi kwanciya, d'an abun da baza'a rasa ba ma dinga taimaka musu,
ai su yan gata ne, tunda akwai Hafeezu, kuma su uku ne zasu dinga ganin junansu,
kama kwantar da hankalinka akan maganarsu babu abinda zai samesu,
ake mutuwa abar jariri ma bare su da suka mallaki hankalin kansu,

Daddy dake tsaye cike da al'ajabin kalaman Goggo ya kasa motsawa bare yayi magana,
jiran ta bakin Baffa kadai yake in hukuncin da zai yanke mai yiwuwa ne,
A d'arare Baffa yace "eh kuma haka ne kema kin kawo shawara,
rabasu din baida amfani gara Hafeezu yayi aure ya rike kannanshi tunda yanzu da dan jari a hannunshi,
yanzu bari Hafizun yazo sai mu ce mishi ya fito da matar da zai aura cikin gaggawa, kuma ya gyara gidannan ya zauna da matarshi ta rike mishi kannenshi...


Sallama Daddy yayi ya karaso gurinsu cikin kunan rai,
zuciyarshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login