Showing 21001 words to 24000 words out of 184071 words

Chapter 8 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

nata juya kalamansu,
lallai ya yarjewa kanshi duk zumuncin da ake samun tsaiko ko rashin jituwa a cikinshi daga tushe abin ke farawa,
duniya ina zaki damu, wannan shi ake kira da Zumuncin zamani,
tun ranar farko da ya fara ziyartar gidan da niyyar neman aure yasan akwai matsala a cikin zuri'ar,

ko gurin bashi auren yasan cewa suwaiba bata da galihu,
da tana da galihu da----- bismillah zauna mana Alhaji, "Goggo ta katse mishi zancen zucin da ya tafi na tunanin abubuwan da suka faru shekaru da dama,
zama yayi fuskar nan babu yabo ba fallasa,
a lokacin duk sauran yan yaran suka karaso,

Dakin ya musu kadan, amma haka suka rab'a suka zazzauna,
hankalinsu suka mayar gurin Baffa dan jin abin da yasa ya tarasu,


Da bismilla ya fara,
kowa ya shiga nutsuwarshi dan duk tunaninsu maganar da zai fada ta dattaku ce,
sai da ya fara jajantawa su Nadeeyah akan zazzafar rashin da sukayi,
sannan ya cigaba da cewa wannan mutuwar duk ta shafemu kuma ta taba mu fiye da tunanin me tunani,

Abun da yasa na taraku anan ba komai bane sai dan in fada muku na yanke shawarar yadda zamuyi da Nadeeyah da Zainab,

Kallon gefen da Hafeezu yake yayi yace "kai Hafeezu, kana da yarinyar da kake so?
Girgiza kai Hafeez yayi cikin rashin fahimta,
Baffa ya cigaba da cewa "to na baka nan da wata daya ka nemo yarinyar da zaka aura domin ta zo ta rike maka kannenka,

wani irin kallo mummy ta yi ma Baffa,
a lokacin in ranta yayi dubu to duk sun baci saboda a tunaninta Baffa ne zai rikesu Nadeeyah saboda sune suka fi cancanta da rikesu din,
maganar da Baffa ya cigaba dayi ne ta katse ta,
"abinda yasa nace haka, saboda kaga rabaku zai iya zama matsala,
duk inda kuka je bazaku ji dadin zama ba saboda kun saba da junanku, ku kadai kun isa ku debewa kanku kewar rashin iyayenku,

Goggo ta amshe da cewa kwarai kuwa, kuma kai Hafeezu hankalinka zai fi kwanciya in kasan kannenka na gurin ka,
fatanmu dai Allah yasa a samu mace ta gari,

Duk cikar gurin babu wanda maganarsu tayi mishi dadi,
har shi Baffa din bayan gama maganar saida yayi ajiyar zuciya sannan ya cigaba da zubda hawayen zuciya,

Anty Reemah ta bude baki zatayi magana Daddy ya rigata,
"kwarai kuwa Goggo shawararki tayi kuma na gamsu da ita dari bisa dari,

Musaddiq da Hilal na jin furucin Daddy wanda ya zama shine na karshe da ya rage suji me zaice, zuciyoyinsu suka tsinke a tare,
nan take kwalla ta taru a idon musaddiq da ya kalli gefen Nadeeyah da Hafeez yaga dukkaninsu kukan rashin gata sukeyi,

kallon bakin Daddy yayi da ya cigaba da cewa
"ba sai Hafeezu ya fita neman aure ba, ni nan zan bashi mata wacce nasan bazata cutar da kannenshi ba, Ya kalli Baffa da yayi kasake yana sauraronshi yace "ina son hada auren HAFEEZU da HUSNA.....


Kamar saukar aradu haka Goggo taji zancen, zaro ido tayi cike da firgici tace wace Husnan,
" *Husnah Mukhtar Kyari*,
Daddy ya fadi da gadara saboda yasan shi kadai keda iko da ita,,

Nawa Husnan take muntari, Goggo ta fadi tana share gumin daya fara tsatsasafowa a goshinta,

Daddy yace "Ita da Nadeeyah shekarunsu daya,
in har zamu iya barin Nadeeya ta rike kanta da zainab me zai hana mu hada auren da Husna sai su zauna su rike kansu gaba daya, jinin ai daya ne, babu wani bare ko Baffa,

wani irin murmushi Hilal yayi da karfi yace "You are the best grandpa..

Anty Reemah da ta harbo jirgin mahaifinta tayi saurin amsheshi da fadin "hakan shine daidai Daddy,
kaga basai ma an shigo da bare ba, kuma Husna ma ai ba yarinya bace, muma muna kamarta aka daura mana aure,
Allah ubangiji ya inganta wannan hadin...

sai dai ya inganta uwarki Goggo ta fadi ba tare da tasan ta danno ashar ba,
Kowa a gurin ya gimtse dariyarshi saboda sunsan yadda Goggo ke son Husna da Badariyya,
barin Husna ma son ta na musamman ne a ranta,
kullum hango Husna take cikin villar rahamaniya,
bazai yiwu ta bari rayuwar Husna ta kare a gurin wadannan masu kashin mindirikin ba,

Haukar gangan ta fara yi musu harda kuka wai Daddy yayi mata Gadara da diyarshi,
cikin sanyin murya Daddy yace "Goggo ba gadara bane, ai naga duk jikokin ne, tsatso daya suka fito, basu da wani banbanci,
cikin ficewar hayyaci tace "Allah ya kyauta wadannan masu kashin tsiyan su fito a tsatson---- da sauri mummy ta mike ta rufe mata baki tayi mata ihun da bata san ta mata shi ba,
itama a nata bangaren ko sama da kasa zasu hade bazata bar autarta ta auri Hafeez ba,
dan ta kawo karshen rigimar tayi kasa da murya mai alamar kuka tana matso hawaye tace "Rike su Nadeeyah bazai taba zame min matsala ba, basu da kowa sai ni, nice uwa kuma ubansu,
dangin mahaifinsu suna nesa damu "Aagadaz" ba nan kusa bane bare muce zamu tura wani nashi yazo,
durkusawa tayi gaban Daddy tace "dan Allah in bazaka damu ba zan rike yaran nan a gidanka,
ajiyar zuciya Daddy yayi cike da farin ciki yace "Babu wani matsala ai d'a duk na kowa ne, bare kuma yaran nan jininki ne,
Baffa farin ciki cike fal a zuciyarshi yace "Nagode nagode Alhaji Allah ya saka da alkhairi,
"babu komai Daddy ya fadi yana kallon Goggo dake zabga mishi harara,
zuciyarta cike take famm saboda bata san jinin suwaiba ya rabi kowa nata, bata ankara ba taji muryar Anty Reemah na cewa
"Mummy dan Allah ku bani daya daga cikinsu in tafi da ita, nima in samu ladan rikon maraya,,
Goggo ta kara hassala ta figi hijabinta a kan gado tace "ki je cikin kabari ki fito da Suwaiba da *ATIKA* ki hada duk ki tafi dasu.....

Banda Mummy da Baffa da suka san wacece Atika, babu wanda a cikinsu yasan wacece Atika??
Sunan Atika ya shiga yawo a kunnuwan dukkan yaran dake gurin.......WACECE ATIKA???? Shine tambayar da zuciyoyin mazauna gurin ke yi.......!


Mrs Tijjani Shattima......
[07/03 6:31 AM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣2⃣
By *Aysha Ya'u Kurah*



Share zufa Goggo tayi cike da tashin hankali tace "To Allah ya kaimu, sai kunzo,
Ajiyar zuciya Mummy tayi tace "to Goggo, amma bakya ganin fadin sirrin zai iya kawo karshen zama na da Muntari,

"Ko kusa, Goggo ta fadi cike da dakiya tace "in ya rabu dake ina zai kai yaran da kika haifa mishi, ai zancen rabuwa babu shi, domin kuwa yanzu girma ya kamaku, ki kwantar da hankalinki ni nasan abun da zanyi.....



Ajiye wayar Goggo tayi ta shiga safa da marwa a cikin dakinta,
Gumin dake tsatstsafowa a fuskarta bai tsaya ba duk ko da irin sanyin fankar dake kad'awa a dakin,
jiki na rawa ta haye can saman gadonta mai rumfa dakyar tana numfarfashi, ta mika hannu tayi ta dauko wani akushi,
bude cikin shi tayi ta zuraa mishi idonuwanta duk jikinta a sanyaye kamar wacce aka tsinkewa lakka,
nan take tunaninta ya tafi can shekaru da dama da suka wuce...

Shekarun da Allah subhanahu wa ta'ala ya arawa Goggo su,
Shekaru masu cike da abubuwan al'ajabi wadanda aka shafe tunaninsu a doron kasa...

"sau tari Allah na arawa mutane lokaci ko zasu samu su gyara abubuwan da sukeyi marasa kyau,
amma ita Goggo a gareta gani takeyi cancantarta ne yasa har yanzu Allah bai mata komai ba, saboda yasan irin gwagwarmayar da tasha ....




*********TARABA 1969*********


Kauyen *GEMBU* dake Karkashin karamar hukumar *SARDAUNA* a cikin jahar TARABA,
Babban kauye ne wanda yake cike da fulani arna da kuma tsirarun musulmai,

Irin arnan da babu abinda sukeyi a rayuwarsu sai kiwo da noma,
mazan su da matansu,
Hatta abin da zasu ci ma su suke noma shi da kansu,

Kauye ne inda babu wanda ya damu da addini bare har sukai ga assasa shi, "walau Addinin kirista ko na musulunci"

kowa harkar gabanshi yakeyi, da yawansu saboda rashin addini basu dauki kowacce irin mugunta a bakin komai ba, komai suke aikatawa a garin su a ganinsu dai dai ne......



Ihun shanaye ne kawai ke fitowa daga cikin wagegen bukkar gidan JAURO,

Samarin dake zaune a kofar gidan kowa ya fara gyara zaman jarkarshi dan sun san yanzu za'a fara kiran layi..

Cike da gadara ya ajiye jarkarshi a gaban ta kowa, ya koma jikin gidan yana sakuce hakorinshi..

Shuru sauran mutanen sukayi saboda tsoronshi da sukeji,

Cike da damuwa saurayin da ke zaune tun safe a gaba ya daga jarkarshi a kasa,
ya kuma ga in yayi shuru to fa za'a cuce shi,

Mikewa yayi cikin sanyi ya fara magana da gurbatacciyar hausarshi ta kabilun fulani

"Tun asuba nake nan,
kayi hakuri can tsauni zan kai madara kaga da nisa banasan dare yayi mana,
bude idoo saurayin yayi cike da gatsali yace "amma kai bako ne anan ko?
gyada kai saurayin yayi yace "eh a can tsaunin Mambila nake,
nazo siyan madara ne akwai bakin da suka zo daga Cameroon zasu tafi anjima da maraice kuma suna son madara irin ta gidan jauro, shine nazo siya, kayi hakuri a bamu, tare muke da yar su gata can a zaune duk ta gaji,

Dago kai saurayin me suna SHAHO yayi ya kalli gurin bishiyar da saurayin ya nuna mishi,
kyakyawar budurwa ya hango zaune a gefen bishiyar fuskarta da alamun gajiya,
da ganinta kasan ba yar nigeria bace,
jikinta rufe yake ruff da bakar riga har kanta,

sandar dake hannunshi ya ajiye yace "a zuba maka in ma jarkar da ka kawo sun kai goma,
kanshi ya fara kakkabewa ya fara nufar inda budurwar take,

Da sauri saurayin ya taro shi yace "ina zaka je?
Yarinyar nan bata jin hausa haka fulatanci, larabci kadai take ji, kayi hakuri muyi abinda ya kawo mu, mu tafi mu bar muku garinku,

wani irin kallo Shaho yayi mishi, baice dashi kala ba ya bi ta gefenshi ya karasa kusa da yarinyar,
gyara rigarshi yayi zai zauna saurayin ya tureshi ya tare gurin zaman,
"Na fada maka, yarinyar nan bakuwa ce,
alama yayi mata da hannu yace ",ga motar da muka zo can je ki shiga ki jirani,
gurin kwarababbiyar motar shanun ta nufa ta haye tana ta kalle kalle jikinta duk a mace,

wani irin ihu Shaho yayi har saida matan dake gefen bukkar suka tsaya da tatsar madara saboda firgici,
saurayin dai bai girgiza ba sai ma kara komawa jikin motar da yayi ya tsaya,
sauran mutanen gurin suna kallonshi cike da mamaki suna tsoron irin hukuncin da Shaho zaima saurayin,
tunkarar motar shaho yayi gadan gadan,
cikin harshen larabci saurayin yayi wa budurwar magana,
a firgice tabi umarnin shi ta kwanta kan kujerar hade da runtse idonta,
yana isowa gurin ya dunkule hannu ya kai wa saurayin naushi, gocewa yayi ya daki karfen motar har saida ta girgiza,
kafin ya kai mishi wani naushin saurayin ya kai mishi a baya,
nan fa suka fara kokawa sosai,

ganin da shaho yayi saurayin yafi karfinshi yasa shi zaro wata sharbebiyar wuka ya zabtari naman gefen kanshi,
Nan fa jini yayi tsalle ya fallatsa har fuskar budurwar,
wani irin ihu ta saki tana fadin "Ya subhanallah, Ya Hayyu ya kayyum bhi rahmatika astagithu"
cikin zafin nama saurayin ya sake yin kan shaho,
kafin ya karaso kusa dashi ya sake luma mishi wukar a ciki,
ihu mutanen gurin suka shiga yi, wasu na tausayin saurayin wasu na kuranta shaho,

kaca kaca shaho yayi wa saurayin da wuka sannan yayi wani ihun murnar ganin ya samu galaba akan saurayin,
bakin motar yayi yana maida numfashi,
"wayam"
ya gani babu kowa a ciki, dube dube ya fara yi yana fadin ina ta shiga, ina yarinyar nan ta shiga, babu wanda ya lura da sanda yarinyar ta bacewa gurin, nan Shaho ya hargitsa gurin da nemanta...


Da sassarfa ya isa gida ya turo kofar gidan gam harda kara sanya wani karfe,

"Ma'u, Ma'u am,
da sauri ta fito daga sakarkari hannunta rike da yar jinjira,
lafiya dai irin wannan kiran me muka samu ne,
sauke budurwar yayi a bayanshi ya kwantar da ita akan wata tabarma,
ajiye jinjirar ma'u tayi cikin daki kusa da wata yar yarinya da bata wuce shekara 8 ba,
da sauri ta fito tana mai zumudin sanin inda mijinta ya samo yar MAKKA, dan su duk wani balarabe a gurinsu dan Makka ne,

" kawo di yam ma'u, ya fadi yana mata firfita hade da share jinin fuskarta,
ruwa ta debo cike da koko ta mika mishi ta zauna a kusa dashi,
a hankali ya fara shafa mata ruwan a fuskarta da hannunta,

Ajiyar zuciya tayi mai karfi hade da fashewa da kuka tana kiran sunan "HABEEB"
toshe mata baki yayi da sauri saboda jiyo ihun su shaho a bayan gidanshi,
cikin harshen filatanci yacewa ma'u tayi saurin shigewa daki da ita,
kama hannunta tayi suka shige can kuryar daki ta turata cikin wani yayi ta daura mata kaya a kanta,
kafin su kai ga taba kofar bukkar mai gidan ya fito daga gidan yana mika, tsayawa su shaho sukayi yace "Kai Baffan Bingel da Boddo kaga wata yarinya Makka da bakin kaya,
hamma ya kakaro yace a ina zan ganta ni da na tashi daga bacci yanzu,
wucewa sukayi suna ta maganganu cikin fushin rashin ganinta, muryar shaho ya jiyo daga can yana fadin "babu abinda zai hanashi kasheta in ya ganta,
da yaso ya sameta yayi yadda yake so da ita amma yanzu kasheta zaiyi dan in ya barta zata iya zama barazana ga rayuwarshi, jin haka yasa Baffa cikin tashin hankali yayi saurin komawa cikin gidan,

A kofar sakarkari ya samu ma'u zaune tana damun fura da nono, ganin da tayi ya shigo a firgice yasa ta mikewa ta nufo shi, "lafiya?, ta tambaya tana kallon yadda jikinshi yake rawa, daki ya jata yace "ina bakuwar balarabiyar nan,
maza fito da ita mu nemi wani gurin mu korata dan walhy rayuwarmu tana cikin hatsari, ya kwashe duk abin da yaji shaho ya fadi ya gaya mata,
cikin dakiya irin tata da jarumta tace babu inda zaka kaita in ba iyayenta ne suka zo neman ta ba, ya zama dole a samu me tsawatarwa shaho,
abubuwan da yakeyi a cikin garin nan ya isa haka,

kallonta yayi galala yace "wa kike ganin zai tsawatar mishi?,
ki fada min wake da wannan zarrar?
kwaryar damunta ta dauko tace "nidai na fada maka babu inda zata,
ta wuce daki tana tsuma tana fadin babu wanda ya isa ya taba makka,
"sunan da ta rada mata kenan tun kafin taji sunanta,
ita zuciyarta ta tafi can tunanin in iyayenta suka zo to fa zasu musu alherin ganin sun taimaki yarsu,
kuma zata kafa tarihin ita ta fara taba jikin balarabiya a duk fadin tsirarun musulman da suka musulunta a kauyen,

cire kayan tayi ta dago yayin ta fito da ita tace "sannu hai yar budurwa,
fito muje ki sha fura sai kiyi wanka,
raba dara daran idanuwanta ta fara yi dan ko kalma daya bata dauka cikin kalaman ma'u ba, hannunta ta riko suka fito waje ta shimfida mata sabuwar tabarma ta nuna mata tace "zauna,
bata fahimta ba haka ta kuma kama hannunta ta zaunar da ita,
furar ta mika mata ta dauka ta fara sha hawaye na zirarowa daga cikin idanuwanta,
tunanin kaninta takeyi dan shekara 6 a duniya wanda ta zamo gata a gareshi gaba da baya,
ko a wani hali yake yanzu Allah masani,
ludayi uku tayi ta miko ma ma'u..
Amsar kwaryar tayi tana fadin "hai har kin koshi, da kin kara kadan ta fadi tana miko mata, Girgiza kai tayi saboda ta fahimci nufinta tace "Alhamdillah, Jazakumullah khairan"
yashe hakori Ma'u tayi tana dariya har can cikinta tana kyakyato shi,
dariyar murnan jin yaren larabci, da kuma ganin ita kanta balarabiyar makkan a gidanta takeyi,
saida ta gama dariyarta tace "hai Baffan Boddo an je gidan kawu suwidi in fadowa su inna wuro munyi bakuwa mai tsarki yar Makkah,
takalmin robarta ta janyo me ruwan bula tasa a kafarta, ta yayo dankwalin saka ta rufe kanta ta fara tafiya,
ta kusa taba kofar Baffa yayi saurin tareta yace "A wala hakkilo na" ("baki da hankali ne?)
Kinsan irin halin da zaki samu a ciki in kika gayyato mana mutanen gidan Kawu Suwidi?, kince bazata bar gidan nan ba na hakura ta zauna amma ki sani babu me shigo min gida bare ya ganta ya jaza min masifa,
tana nan zaune nasan za'a zo cigiyarta a lokacin sai in mikata gurin iyayenta,,
kalonshi ma'u tayi fuskar nan cike da gamsuwa tayi kamar ta yarda din da gaske,
yaye dankwalin kanta tayi tace "Haka ne, na manta ne ina ta zumudin kai rahoto dan kawai in burge su inna wuro,
yanzu bari inje in sata tayi wanka sai ta canza kaya a wanke na jikinta, gyada kai Baffa yayi cikin jin dadi ya koma daki kusa da yaranshi ya zauna yana shafa kan karamar dake kokarin tashi..



Murdaddiyar sarkar murjanin gwal din da ta cire kafin ta shiga wanka ma'u tayi ta juyawa a hannunta tana dariyar farin ciki, "Aiya Ya Allahn Hard'ejo,
(sunan yayan mijinta kenan malamin da ya fara kawo musu musulunci kauyen),
ji wani "kuje ndade' (sarka) kamar ba hannun mutum bane ya kerashi, sashi tayi a wuyanta tace "wannan ko matar Ardo Laminu bata da irinshi,
kaii ya zame min dole in je gidan su inna wuro dan bazan bar wannan daddadan labari ya wuce ban basu shi ba,
ai ni ko da wannan maka wuyar aka barni na tsira,
daki tayi da sauri tana magana kamar zararra,

kayanta dake cikin wani akwatin katako ta dauko sababbi na fulani tace " Baffa zan bata wannan kayan nawa tasa saboda a wanke wadancan,
gyada mata kai kawai yayi dan mamakinta bai barshi ya bude baki yayi magana ba,
ma'u da ko dankwalinta bata iya bawa wani aro shine har ta dauko kayanta da bata taba sasu ba zata bawa wata tasa, lallai yar makkah ta ciri tuta..


Sosai kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login