Showing 114001 words to 117000 words out of 184071 words

Chapter 39 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

Advertisement

cewa


"kayi min alkawarin duk runtsi duk wuya bazaka rabu da Nadeeyah ba,
bazaka sata kuka ba,
kuma ba---

malam biyu ka fadi ga na uku na shirin biyowa baya,
Musaddiq ya katse shi yana dariya,
bari in sa maka su a one word,


"Nayi maka alkawarin bazan taba cutar da Nadeeyah ba,
bare har abubuwan da ka ambata su faru,

are u happy?


Ajiyar zuciya Hilal yayi yace "sosai,
muje insa kaya,


shaddar shima yasaka milk tasha cofee aiki sannan ya daura coffe hula mai ratsin milk,
sunyi kyau sosai kamar dukkansu ne zasu angwance,

wani bakin glass Hilal ya kwama a idonshi saboda gudun bacin rana......



Mrs Tijjani Shattimah.......
[12/04 7:01 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣7⃣
By *Aysha Ya'u kurah*






Ganin ba kowa a parlon sai tsirarrun mutane ya sanya Musaddiq kama Hilal suka nufi dakin su Nadeeyah..


Zaune suke... kowacce an rufe mata kai da mayafi suna jiran azo a kirasu,
kawayensu na gefe suna daukar hotuna hade shewar murnan first kawance a rayuwarsu,

*Amal Mus'ab* na ganin sun shigo tayi saurin isa gurinsu tana murmushi,

kallon Musaddiq tayi ta miko mishi hannu tace "oya sako first step kafin muje second step,
cikin rashin fahimta yayi dariya yace
"ban gane ba,
hannu Hilal yasa a aljihu ya ciro bandir din yan 200nts ya daura a kan hannun Amal,


"Uhmmm nt bad ta fadi tana juya kudin,
lallai ka iya zuwa ghana,
guys bazamu sha wahala gurin abokan ango ba,
but next time mr man a kara hannu ta karashe cikin zolaya..


Dariya yayi yace
"next step?

Haifa ce ta matso tace
"a cikin su biyun nan ango ya dauki matarshi sai su fita kafin dayan angon ya karaso,
nan dakin ya gauraye da ihun yanmata masu zallar kuruciya wadanda suke kan ganiyar shaukin soyayya,


kallon duk su biyun Musaddiq yayi ya rasa kafar da zata sada shi da Nadeeyah,
domin ko ina nasu a rufe yake, hatta yatsun kafarsu a rufe yake da takalmi,
gefen da yake tsaye yabi dan ya gama sadakarwa itace a zaune a gurin saboda yadda gashi yayi tulluku a tsakiyar mayafin,


Hannunshi Hilal ya janyo yace "kar kayi abun kunya Mr soft,
ga matarka can ya nuna inda dayar take
dariya Musaddiq yayi yace
"har yaushe zaka iya tantance abun da bakayi ma kallo fin goma ko ashirin ba a zahiri,
look Hilal,
nasan komai game da Nadeeyah, everything saboda na ganta har ganin nata ya sanya ni na zamo cikin shaukin sonta,
ganeta a haka bazai taba min wuya ba saboda tana makale a cikin zuciyata...

dariya Hilal yayi a zuciyarshi yace
"cikin jinina,
a mafarkina,
in my every breath kamanin ta kawai nake gani,

Allah ya tsare akwai bakin glass a idonshi,
da idanuwanshi sun nuna ma ma'abocin kallonshi irin tarin son dake dawainiya dashi,


Karasawa kusa da ita yayi ya zauna hade da yi mata rada a kunne

"My Young Barr---
bai karashe ba tayi saurin bude fuskarta,
idanuwanta da suka tsaru da make up suka fara tara ruwa,
saurin girgiza mata kai yayi hade da sakar mata murmushin karfin hali,
wannan bakin glashin makafin ba karamin taimakonshi yayi ba dan da babu abinda zai hanasu ganin sirrin dake cikin kwayar idamuwanshi...

"Ashe kina da kyau har haka kanwata?, ya fadi a hankali yana kokarin gyara mata mayafin kanta,

"Nayi maka laifi ko?

Yadda tayi tambayar ba tare da ta dauke ido akanshi ba ya sa shi saurin mikewa dan gab yake da rasa control din raunanannar zuciyarshi,
da dariya Musaddiq ya karaso yace

"na gama jin kunya,
ace na kasa gane muradin raina, lallai ya kamata aci tarata..


Waje Hilal ya fita ko zai samu zuciyarshi ta dan mishi dama daman nauyin da tayi,

Bq ya nufa inda su Hafeez suka Hinad na biye dashi a baya tana tambayarshi kudin liki,

"kunnenta ya kama yace
"baki damu da ki bani abinci ko wani abu ba,
ke kawai kudin liki,
ina Zee?

"yaya sakar min kunne plss,
Mum ce tace tasan zaka ci abinci fa,
shiyasa ban samo maka ba,
kuma Zee nima tunda na dawo saloon ban ganta ba,

sakin kunnenta yayi ya ciro kudi a aljihunshi ya raba gida biyu ya bata,
"yasan zasu bukaci kudin shiyasa yasa Galadanci yayi mishi canji tun kafin ya iso,


Godiya tayi mishi tace bari ta kawo mishi ko nama ne,


parlon ya shiga ya tarar da Hafeez a kimtse yana zaune yana jiran azo kiranshi,

cike da zolaya ya dan naushi cikin Jamal dake kishingide yana game,
mikewa yayi yana dariya yace
"har ka iso,

"wallahi kuwa.. ban dade da shigowa ba,
mun sameku lafiya?

lafiya lau Hafeez yace yana kallon idon Hilal,


"yaushe ďana ya zama makaho?

Ya tambaya yana dariya,

shima Hilal dariyar yayi yace
"fashion ne kawu karami,
dariya mai sauti dukkansu sukayi suka hau wata hirar ta daban....





Inaa Amaryar take!!!!

Hajiya Aliya ta tambaya hade da bankado kofar dakin su Husnah,

lokacin Musaddiq na manne da ita kamar zai maida ita jikinshi,
samm baiji kunyar kawayensu dake gurin ba,


shigowar su Hajiya Aliya ne ya sanyashi matsawa kadan hade da gaishesu, amma har lokacin hannunshi na cikin nata..


Harara Hajiya Aliya ta watsa mishi sannan ta bude fuskar Nadeeyah da iya karfinta,


"auuu kece amaryar,
iko sai Allah,
ashe Hajiya Zainab munafurtarmu tayi Hajja Asiya,
"ashe dama tasan auren zumunci zasuyi ma dansu shine ta daura ma diyata dakon son da yake neman zamewa zuciyarta illa,


waigowa tayi ta kalli Mummy da tayi tsamo tsamo saboda kunya da takaici tace

"Wallahi tallahi Zainabun Muntari bashi kika ci,
na rantse da wanda raina ke hannunshi ni Aliya bazan kyaleku ba,
sai na sa kun muzanta a idon duniya,
yanda kikayi wasa da rayuwar 'yata kema sai nayi da ta naki yayan,
mu zuba mu gani,

wuce muje Hajja Asiya ta karashe hade da buga kofar dakin tana huci,


Kuka sosai Mummy ta fashe dashi hade da ficewa daga dakin itama,
a rude Musaddiq ya saki hannun Nadeeyah ya bi bayanta hankali a tashe,
itama Nadeeyar mikewa tayi tana share hawayen da ya ziraro mata tana kokarin bin bayan Mummy Anty Raly ta dakatar da ita,

zaunar da ita tayi ta rarrasheta da kalamai masu dadi da kwantar da hankali,
jakarta ta ajiye kusa da ita tace "ki kular min da jakar nan, yanzu zan dawo...




Sau uku wayar dake cikin jakar na ringing Nadeeyah na kin dauka, saboda bata san bude ajiyar da aka bata,
a na biyar ne ta bude ta fito da Wayar,

*Tahir Legacy*
ta gani a rubuce,
da sauri ta ajiye wayar saboda wani irin mugun faduwar gaba da taji,

"uncle Taheer ta fadi a cikin ranta,
gaba daya ta manta dashi a cikin rayuwarta,
gashi yanzu zata sake yi mishi mantuwar din din din,
bai fasa kira ba har saida ta gaji ta dauki wayar zata kaima Anty Raly sai a sannan taga wani suna daban,
*Aunt S 2*
a gaggauce ta dauka tace
"Assalamu Alaikum bari in kai mata...
yadda yayi haddar sanyin muryarta dake yawan yawo cikin kanshi ya tabbatar mishi da itace,

"My omri is going lv me,
dagaske ne?


Chakkk ta tsaya da tafiyar da ta farayi,
cire wayar tayi a kunnenta ta sake kallonta dan ta tabbatar da ko dai sunan gizo yayi mata,

maida wayar kunnenta tayi zatayi magana yayi saurin cewa

"tell me plss,

zama ta koma tayi tace
"ina wuni,

"Nadeeyah plss answr me,


"ummm dagaske ne, ta bashi amsa a hankali...

ji yayi gaba daya ya kusa zubewa a kasa,
dama lokacin da yagani a status din sabrinah saida yayi jinyar magudanar jininshi na dan lokaci,

hawayen da ya ziraro mishi ya share,
yace
"but why Nadeeyah,
why??


Cikin rawar Murya tace "Kaddara ta ce haka,
kayi min addu'a Allah yasa auren ya zame min alkhairi,
kayi hakuri uncle,
Allah ya baka wacce ta fini a komai da kake so,
bata jira jin amsarshi ba ta kashe wayar ta dunkule kanta guri daya, dama dakin babu kowa dan Husna sun fita da Hafeez da kawayensu.....





Kaga abun da ka janyo min ko Musaddiq,
kaga irin cin mutuncin da ka janyo min gurin aminai na,
yanzu gaba daya kawayena zasuyi Allah wadai dani,
saida na fada maka Nadeeyah ba alkhairi bace a gareni ka nace saboda kaga jar fata da kyawun dan maciji wanda zai diga maka dafin sa ya tafi ya barka da ciwo,


Wallahi Musaddiq ka cuceni kuma ka cuci kanka....


Anty Reemah ce ta zauna kusa da ita tace haba Mummy,
matar mutum fa kabarinsa,
kuma babu wanda yasan alkhairin dake tattare da auren Nadeeyah sai ubangijin halittu,
yanzu ita wacce kike so din me tafi Nadeeyah dashi,


"Gata da hanyoyin alkhairi, Mummy ta bata amsa tana harararta,



"Hanyoyin alkhairi ai na ubangiji ne,
shi ke budeshi ga wanda yaso,
sai kiga auren Nadee---
a harzuke ta katseta da cewa
"in kika kara magana zan balain saba miki,
mahaukaciyar banza sakaryar hofi,
tashi ki fita ki bani guri, shashasha kawai...

Rai a bace Anty Reemah ta tashi ta fita daga dakin,


Matsowa Musaddiq yayi ya share mata hawaye hade da kwantar mata da hankalin cewa ta kwantar da hankalinta,
babu abun da zai faru,
domin shi zai gyara komai,


Hannunshi Mummy ta kama tace
"Little ka taimakeni,
bayan auren da kake so kayi wanda nake so,
ka auri Faida,
shi kadai ne zai sanya hankalina ya kwanta, in kuma aminta da Nadeeya a matsayin matarka,


shuru yayi na dan lokacin zuciyarshi na harbawa da karfi,
tunanin mafita ya shiga yi,


Dakyar ya sama wa kanshi mafitar amincewa,
dan a samu zaman lafiya,
amma ko yayi hauka bazai auri Faida ba,
daga ya tafi da Nadeeyarsa lagos bazai kara waiwayosu ba sai yayi shekaru,
ganin ya amince zai auri Faida yasa Mummy farin ciki sosai har ta kira aminanta ta fada musu.....





Sai bayan Magriba akayi kamun amare,

"Mami da Anni su suka kama Husna,
sai Anty Reemah da sauran yan uwanta sukayi ma Nadeeyah,

Mummy ma in ka ganta zaka dauka albishir akayi mata da gidan aljanna saboda murna,


Rawa kam kawayen Amare da yan uwa suyi ta sosai har saida suka kure mawakin,
sai kusan goma makadin ya tattara kayanshi yayi gaba da tarin alkhairai masu yawa,

su kuwa kawayen suka koma dakin kwanansu suka cigaba da hirarsu ta yammata,
rabin hirar tasu ma akan Badar ta kare saboda sun so tana nan akayi bikin.....






Rana bata karya....


A ran 23 ga watan yuli..
ranar sati da safe dubban jama'a suka shaida daurin auren

*Musaddiq Mukhtar Kyari* da *Nadeeyah Adam*

da kuma auren

*Hafeez Adam* da *Husnah Mukhtar Kyari*...


Marokin gurin na gama sanarwa Jamal yayi dariya sosai yace
"vice versa,
gyara bakin madubi Hilal yayi yace
"ai fa, abin ya burgeni,
Allah ya basu zaman lafiya..
saura mu,

matsowa Jamal yayi yace
"ai ni nama gama samu,
saidai fatan dacewa,
jira kawai nakeyi komai ya lafa in aika sakon zuciyata,
bazan tsaya kallon ruwa kwado yayi min kafa ba....



"Kamar yadda Nayi Hilal ya fadi a cikin zuciyarshi..
amma a fili cewa yayi

"woww kace anjima akwai gist,


"Sosai ma In law...
au My son ya karashe yana dukan bakinshi..



Mikewa Hilal yayi yana kyakyata dariya yace
"ka tona kanka malam,
muje gurin walima kafin mutumin ya fara kumburi.....





Wannan kukan da kikeyi bazai taimakeki ba Amarya,
dama kinci abinci,
da kin samu sauki,


"Kinsan adadin matan da suka shigo gidannan ta haka kuwa?

to ki sani bake bace ta farko kuma bana tunanin zaki zamo ta karshe,
da yawa irin ku son duniyan iyayenku ke ja muku,

saboda son abun duniya sai idonsu ya rufe suyi kyautar da zata damesu nan gaba,
ta shi kici abincin,


kingani harda Farfesun Zomo,
ga tuwon lapshi miyar yauki gaskiya ke yar gata ce, dan abin bauta Garzar ki rage min, ta karashe tana turo langar tuwon gabanta,

Kafa Badariyya tasa ta ture langar tuwon,
nan naman ya zube a kasa,
komai ya bayyanar mata,

kan zomo ne da kayan cikinshi,
sai tsirarrun nama,
da sauri kande da ta durkusa tafara kwashe naman tana suďe hannu kamar mayya wacce tayi sabon kamu,

Idon da ya soye da bakin ciki Badariyya ta bita dashi tana hawayen zuci,

"wannan wace iriyar jarabawa ta fado,
kalmar na shiga uku har lokacin bata bar fita daga bakin Badar ba,
tana kallo kande ta sude gurin tass kamar an goge sannan ta russuna tace
"Ranki ya dade,
ko bakya jin yunwa bai kamata ki wulakanta abinci ba,

wannan naman yanzu da zan fita dashi tsakar gida sai an kusa kaini kasa saboda wawason shi,
ki daure kici ko kadan ne saboda kar yareemah yayi fada,

tsakii mai karfi Badariyya taja hade da sake yin tagumi tana tunanin way out..



Shigowar Yareemah ne yasanya kande fita da sauri bayan ta gaisheshi...


Zama yayi a gefen Badar hade da dauko langar farfesun...


"Sauka ki zauna a kasa ki cinyeshi tass domin ki samu karfin jikinki,


a fusace Badar ta mike tace "wannan kazantar ce zata sa in samu karfi a jikina,
wallahi kaji na rantse bazan zauna a gidannan ba,

kukan bakin ciki ta fasa mishi tace
"wallahi in na fita a gurin nan sunanku sorry, domin sai na gayyato muku sojoji sun tada wannan tsinannan kau----


"keeee...

ya katseta cike da tsawa,
nan take fuskarshi ta sauya yace "Zauna maza ki cinye abin dake cikin kwanukan nan,


"Bazan ci ba!
Nace bazan ci ba ka kashe n----


wani farin haske ne ya wuce ta makogoronta ya hanata Magana,
sai ma bin umarnin shi da ta fara yi...
tare suka zauna ya bata abincin a baki ta cinye tass cikin ficawar hayyaci,
tana gama shan ruwa ya umurceta da ta fitar da kwanukan waje,
ba musu ta kwashesu ta fitar dasu ta dawo dakin ta zauna a nutse,



mikewa yayi ya dawo inda take hade da kamo hannuwanta,

"ki kwantar da hankalinki, nima mutum ne kamar ki,
saidai mu Allah yayi mana baiwar sanin wasu abubuwa,


Tun kafin nayi auren farko lokacin ina yaro mahaifiyarki ta bani ke saboda jin dadi wani aiki da mahaifina yayi mata,
tun daga ranar muke kula da duk wani motsinta,
a ranar da aka haifeki mahaifina yayi murna domin a tunaninshi namiji zata haifa,
tun daga wannan lokacin muke bibiyar dukkan sawunki,


kina shekara tara a lokacin naga zuciyarki ta fara darsa wani abu game da dan uwanki,
a sannan ne muka turo lawisa ta shiga rayuwarki,
in kin lura a duk tarin kawayenku babu mai shiri da Lawisa sai ke,
abun da yasa kuwa shine ba dan su tazo ba,
domin ki tazo,
a duk lokacin da ta kawo min batunki da Musaddiq,
nakan ji kamar in kashe shi saboda kishi,
mahaifina kan bani hakuri akan duk rintsi ke din tawa ce,
yanzu gashi na sameki bayan shekaru 18 na jira...




share hawayen dake gudu a idonta tayi a zuciyarta tana maijin tsanar fitowa daga kasan mahaifiyarta,

a hankali tace "ka taimakeni ka maidani gida in aiwatar da abu daya,
zan dawo daga zarar na gama aiwatarwa,


Dariya yayi yace
"Hana auren masoyinki?
Da sauri ta gyada mishi kai,


wani guri ya buga a gefen dakinshi nan take Hoton Musaddiq da Nadeeyah ya bayyana,

zaune suke ta sanya rantsatsen leshi ja mai ratsin green,
sai gyale green da ta rufe kanta dashi,
gefenta Musaddiq ne shima yayi kyau har gaji yana yi mata mayataccen kallon kauna,
Daddy da papy ke zaune bisa kujera suna musu Nasihar zaman aure saboda za'a tafi kaita gidan mijinta....




Kin ganshi, aikin gama ya gama, auren nasu ya tabbata,
sai ki kwantar da hankalinki muyi zaman aurenmu,
zaki ji dadi in kinso kiji,
in kuwa kinso akasin haka duk zaki samesu a gidan nan...
yana kaiwa nan ya mike hade da umurtarta da ta cire kayan jikinta........





Mrs Tijjani Shattimah.......
[14/04 8:11 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣8⃣
By *Aysha Ya'u kurah*







Sake duba agogo yayi karo na ba adadi yaga karfe goma da rabi,

Rai a bace ya mike ya fara rufe kofofin gidan hade da wutar globe,

kitchen ya nufa dan duba ko an kashe kayan wuta,
wutar corridor din kitchen ya kashe hade da faďawa ciki,

Tozali yayi da Fatima tsaye tana fere dankalin da za'aci da breakfast,
gyaran murya yayi wanda yasata juyowa a dan firgice,
hada ido sukayi tayi saurin sunkuyar da kanta hade da tsuguwa kasa ta gaisheshi,

"Tashi Fadima, aikin ne kikeyi har yanzu??
bakya jin jikinki,


murmushi tayi tace "naga gobe da wuri su Ummah zasu tafi shiyasa zan rage aikin da asuba sai in karasa,
gyada kanshi yayi hade da fita parlon cike da tunani iri iri,

A parlon ya zauna zuciyarshi na ta kitsa mishi abubuwa da dama, motsin fitowa yaji daga dakin dasu Ummah suke,
Kanwar Umman ce ta fito da kofi a hannunta,
ganinshi a zaune yasata zama kusa dashi itama tana dan janshi da hira,

"Bakiyi bacci ba Inna?

"ruwa zansha Shamsu,
kaima baka kwanta ba,
ga yar lelenka bata dawo ba,

dariya yayi yace
"kinsan biki,
inaga a can zata kwana,

"auu kana gani ne ma?
Lallai kana da aiki shamsu, watanmu biyu a gidannan yarinyar nan bata taba zama ta kula damu ko na second daya ba,

wallahi in zaka hankalta ka nemi macen mutunci ka nemeta ka aura,
wacce zata zame maka macen gida ba ta titi ba,
tana kaiwa nan ta fara kokarin mikewa,
ganin Fatima ta fito yasa ta zama tace "yar albarka,
zo ki bani ruwa,
da sauri ta karbi kofin ta wuce kitchen ta dauko ruwa a gora ta kawo mata hade da yi musu sai da safe,


Kallo suka bita dashi har ta kurewa ganinsu,

Inna Indo ce ta fara dauke idonta tace
"badan son duniya irin na 'yayan zamani masu son 'yayan masu kudi ba,
da sai ince wannan yarinyar itace tayi daidai da tsarin macen aure mai mutunci da kamala,
to saidai ita ba yar kowa bace, face yar mai aiki,
Allah ya saka musu hidimar da sukayi mana ya kuma bata miji nagari,
mikewa tayi tace
"sai da safe,


"Allah ya tashemu lafiya..
ya fadi yana cigaba da nazarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login