Showing 6001 words to 9000 words out of 184071 words
Chapter 3 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt
koma,
Ayya mamma ta fadi tana Mai zaunawa kusa da ita, har zaki koma Antyn Yara,
Reemah tace eh zamu koma tare da musaddiq na sama mishi makaranta a can,,
Allah sarki musaddiq zaka bamu kewa ashe, to Allah yasa ka je ka fara a sa'a,
Ameen musaddiq yace yana Sosa keya,
da sauri ta dawo gidan da sabon silifas a kafarta da ledar madara da suga,
ajiyewa tayi a kofar kitchen tace sannunku,
mamma ta kalleta kallon tuhuma tace a Ina kika samo sabon takalmi? ,
canji ta ciro a cikin aljihunta ta mika ma mamma tace Anty ce ta siye duka ta kuma bani kudin takalmi,
shine dan sakarci baki shigo kin fada min ba mamma ta fadi rai a bace,
Anty Reemah tace "kiyi hakuri mamma ni nace tayi sauri ta siyo takalmi,
mamma tayi murmushi tace to mun gode fa Allah ya saka da alkhairi, Ameen anty Reemah tace tana kallon Nadiya da ke rabe tana wasa da hijabinta,
ni ko mamma wace makaranta Nadiya ke Zuwa?
Mamma ta yi murmushi tace ta zana jarabawar aji shida zata cigaba da makarantar gaba in shaa Allah,
to ai mamma naga har an kusa gama third term wace makaranta kuke neman mata? ,
mamma ta kalli gefen da Nadiya take tace makarantar kwana ta Queen Amina dake kakuri,
to har yanzu bata samu bane? Reemah ta tambaya cike da damuwa,
muna ta kokarin har hada abin da zata tafi dashi ne mamma ta fadi cike da Jin kunya,
Anty Reemah tayi ajiyar zuciya tace mamma karatun diya mace nada matukar amfani,
Dan Allah Kar ayi wasa da ita first term din nan da za mu shiga,
ki bar batun queen Amina,
zan ma abban Hilal magana zai sa a bata admission a fgc malali in shaa Allah,
sannan ki turo min hafiz inason ganinshi gobe kafin muje gidan Baffa,
Kasa rufe baki mamma tayi saboda murna,
share hawayen farin ciki ta shiga yi tana kallon Nadiya dake ta dariya,
kai gaskiya nagode Antyn yara, Allah ya biyaki da aljanna, nagode sosai,
anty Reemah ta mike tana fadin haba mamma me akayi ai duk daya ne,
Dan Allah ki daina min godiya,
Godiya ta zama dole Reemah mamma ta fadi tana rike baki, kedai kawai Allah shine zai saka miki,
Ameen anty Reemah tace ta fito da dubu biyar a jaka ta bawa Nadiya tace wannan na auta ne in ta tashi kice mata gashi inji ni kinji,
Nadiya ta karba ta shiga godiya hade da bayyana kyawawan hakoranta,
har gurin Mota suka raka su suna ta godiya kamar bakin su zai tsinke, musaddiq mamma ta kalla tace "me kake so in kawo maka ka tafi dashi? , murmushi yayi yace koma meye mamma nagode,
mamma tace to an gama dan albarka..
Hon Hilal yayi yace muje ko mum, bata bashi amsa ba sai ma harara da ta bishi dashi,
mamma tayi dariya tace Hilal Allah ya kiyaye hanya ka gaida abbanka kaji,
zaiji kawai Hilal yace ya tada motar sukayi gaba.....
Mrs Tijjani Shattima......
[04/12 09:45] Meela Adeel: 8⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah
Washe gari karfe 8 a gidan Anty Reemah tayi wa Hafiz,
a kitchen ya sameta tare da Yan aikinta suna ta aikin abun karyawa,
da fara'arta ta tarbeshi tasa ya wuce parlor,
sai da ta kammala komai tasa shi ya karya sannan ta dawo gurinshi,
Wace sana'a kakeyi? Tambayar da ta fara yi mishi kenan,
kanshi a kasa yace "dako nakeyi da wheelbarrow,
wheelbarrown naka ne? Ta sake jefo mishi tambaya,
a'a ya fadi yana mai girgiza kanshi, haya nake daukowa duk yini dari uku nake bashi,
Good anty Reemah tace tana gyara zamanta,
Hafiz ka saurare ni da kyau kanaji ko,
gyada kanshi yayi yace inajinki anty,
da farko dai zanso insan sana'ar da kake sha'awar yi, ka ture batun dako, dan banga amfanin sa ba,
sunne kai yayi yace walhy anty bani da wani idean sana'a yanzu sai dai in kika bani shawara bazanki dauka ba,
ajiyar zuciya tayi tace
"to akwai mijin kawata a railway station yana sana'ar fruits,
zan mishi magana in hadashi da kai sannan zan baka jarin da zaka tsaya da kafafunka ka rike mahaifanka da yan uwanka,
basu da kowa a duniya sai kai Hafiz,
hakkinka ne ka kula dasu da ilimin su,
nasan kana nema, rashin Jari ne ya taushe ka amma inada yakinin in na baka zaka kula da hakkinsu,
Dan Allah Hafiz karka bari suyi kuka da kai ko ba dade ko ba jima na rokeka da Wanda bama gani amma shi yana ganin mu,
mikewa daga zaunen da yake yayi ya durkusa yace wallhy zan rike amanar su in ban rike amanarsu ba tawa zan rike,
nagode sosai anty Allah ya saka da mafificin alkhairi, Ameen anty Reemah ta fadi ta dauki wayarta ta kira Hajiya Maryam,
sun dade suna magana sannan sukayi sallama, tace "gobe in shaa Allah zaka fara Zuwa ka koyi yanda sana'ar take,
zan turo maka kudin a account dinka, in baka dashi ka bude dan gara in baka su a hannunka,
Allah yasa ka fara a sa'a,
Ameen ya Allah nagode kwarai Allah ya kara daukaka,
Ameen ameen Hafiz ban kuma ce ka fadawa kowa ba,
ka rike shi sirri a tsakanin mu,
angama anty babu wanda zaiji in shaa Allah,
nan suka dan taba hira har kusan goma yayi mata sallama ya tafi cike da farin ciki....
Duk nuku nukunki sai kinje Nadiya,
Baffa mahaifina ne duk abin da yake min badan baya sona bane tunda shi ya kawoni duniya,
Nadiya da bata da mafita tace "zanje mamma rigar ce taki shigana,
zama ta shige ki ne matso in zage miki zip,
matsawa tayi badan ranta yaso ba mamma taja mata rigar ta shige tsaf kamar a jikinta aka dinka,
gashi ya shige maza daura dankwali muje,
dankwalin ta daura ta yafa gyale duk ranta a jagule,
ta tsani wulakancin su Badariyya, tasan Sam haduwarsu ba Mai dadi bace kullum suka hadu sai sun tozarta ta kuma babu Mai hanasu,
daukar zainab tayi ta bi bayan mamma suka fita hade da rufe gidan...
Gidan cike yake da 'yayan kawayen mummy da iyayensu da ita kanta,
suna can ciki anata wasa da ciye ciye,
iyayen kuma suna hira hade da Shewa,
can gefe kuwa su Reemah ne ita kannenta sunata hira babu Wanda ya lura da zuwansu,
hakan ya ba Nadiya daman zama can nesa dasu tana kallon yaran dake dakin 'ya'yan hutu kawayen su badariyya,
zainab da hankalinta ya gama tashi da tulin kayan wasan yara sa'aninta ta mike a jikin Nadiya tace anty zanyi wasa,
Nadiya ta zaunar da ita tace ki bari su gama kema sai kiyi kinji,
gyada kanta tayi tanata binsu da ido suna wasa babu kakkautawa,
Mamma kuwa tana can gurin su goggo da mummy da kawayenta sunata hira, tunda ta gaishesu ta nemi guri ta zauna a kasa itama, babu Wanda yace musu ga abinci haka in za'a ba yara barka da sallah babu wanda ke kallonsu,
sallah kadai ke tada iyayen Sannan su dawo su cigaba da hira,
"Suwaiba tashi ki tattara gidan nan tunda baki San abinda ya kamata ba sai an fada,
muryar goggo ta dakin kunnen daukacin mutanen dake cikin parlorn,
da sauri mamma ta mike tana murmushi ta fara tattare kwanukan da suka ci abinci,
kwala Kiran Nadiya tayi tace taho ki fitar min da kwanukan nan,
zaunar da zainab tayi ta mike sum sum ta karbi kwanukan hannun mamma tayi waje dasu,
Badariyya dake kwance tana game a iPad dinta ta bita da ido cike da rainin wayau,
tsaki taja ta cigaba da danna iPad dinta,
ta rasa dalilin dayasa ta tsani Nadiya,
bata jin ko digon kwayar Santa a cikin zuciyarta,
tasan tafi Nadiya dukkan gatan rayuwa, haka kyau karyarta ta nuna mata, can kasan zuciyarta ta jiyo yayi amsar kuwwar "KYAWUN JIKIN FA" tsaki taja tace saidai jikin Shima dan bamu gama girma bane amma Nadiya babu abin da ta fini dashi,
Husna da Laila yar kawar mummy suka bita da kallon mamaki sukace to waye ya ce Nadiya tafi ki wani abu,
gimtse fuska tayi hade da runtsa ido dan bata San maganar zuci ta fito fili ba,
A ranar babu wani abu da ya shiga tsakaninta da badariyya saboda Hilal da yayi kaka gida a parlorn, Kasa katabus tayi saboda tsoron Kar ya sake marin kyakykyawar fuskarta,
ta tsani abin da zai taba fatarta koda kuwa kuda ne,,
Yaji mamma tayi ma Reemah da yawa na tafiya sannan tayi ma musaddiq dambun kifi da nama,
murna sosai sukayi sunata godiya,
sai bayan Isha mamma ta fara shirin tafiya,
dakin Baffa ta shiga Wanda yake cike da 'ya'yan mummy da ita kanta suna meeting ana ciye ciye,
durkusawa tayi tace Baffa mu zamu tafi sai da safe, to madalla sai da safe suwaiba,
yaki taho zainabu ki karbi kudin mota,
nokewa zainab tayi saboda rashin Sabo,
mamma tayi murmushi tace "quiwa gareta, ,
toooo... to ta rike kanta ta cinye, sai Allah ya tashe mu ki gaida Adamun,
to zaiji Baffa,
ta waiga tace masu sai da safenku,
to sai da safe duk sukace suna masu kai nama bakinsu..
Reemah dai kai kawai take girgizawa cike da takaici,
yafito Hilal tayi da hannu tace maza yaje ya sauke su a gida,
kunkuni ya fara yi yana buga kafa,
musaddiq ya mike yace bani mukullin,
da sauri ya wurga masa ya koma ya zauna ya cigaba da latsa wayarshi, a can bakin gate ya tarar dasu suna kokarin fita,
Mota ya bude yayi musu hon yaja ya isa gaban su,
bude musu yayi yace mamma muje in kaiku,,
ayi haka.... mamma ta fadi tana rike baki,
bakomai ku shiga muje,
baya suka shiga ya ja motar suka wuce....
********
Tun daren suka gama shirye shiryen komai na tafiya,
ba kananan kudade daddyn shi ya turo na siyayyar tafiyarshi ba, mummy da kanta ta shirya mishi kaya suna ta hira cikin farin ciki,
Yaya wata nawa zakayi? Husna ta tambayeshi tana bude ledar dambun naman da mamma tayi mishi,
mummy tayi dariya tace shekara nawa dai, ai sai kin ganshi kawai, Husna tace "tabdi har shekara anya mummy zai iya zama kuwa, shi da baya ko iya kwana a wani gari,
shafa kanshi mummy tayi tace "can ma ai gida ne ko little? ,
gyada kai yayi ya kwanta kan cinyarta yace but I will miss you so much mummy,
i will miss u more my baby,
ka kwantar da hankalinka zan dinga zuwa ganin ka a kai kai kaji,
um kawai yace yana kallon Badariyya dake mishi kallon shi din baida wayau,
tsaki yaja ya mike ya nufi dakinshi,
rainin Badariyya a gareshi yayi yawa,
lallai taga gadon barcinshi amma babu komai with time Shima zai zama jajirtacce marar daukar raini in shaa Allah ya fadi yana mai karfafa zuciyarshi.....
Mrs Tijjani Shattima....
[04/12 09:46] Meela Adeel: 9⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah
HAPPY NEW YEAR, Allah yasa mun shigeta a sa'a AMEEN....
2017 is unforgettable... Allah yayi Maka Rahama Babana...
"Kilode sis"...
Husna ta fadi tana zungurar Badariyya da tayi tagumi tana kallon Kasa,
tsaki Badar ta ja tace "nothing bacci kawai nake ji,
Husna ta tabe baki hade da kwanciya tace
"to ai sai ki kwanta,
Badar ta dan kashingida ta runtse ido kamar mai bacci,
har cikin ranta bata son tafiyar Musaddiq,
duk da yawan samun sabanin da sukeyi tafi son kasancewarshi kullum a gida tana mishi koda kallon raini da wulakancin da ta saba ne,
to in ya tafi wa zata dinga gani,
Husna tayi mata kadan a cewarta,
duk da sa'oin juna ne amma a koda yaushe Badar gani takeyi ta girme ma Husna nesa ba kusa ba saboda tsantsar sangarta da d'agawa,
tunanin hanyar da zata bi ta hanashi tafiya ta shiga yi,
ta dade tana tufka da warwara kafin daga karshe ta samo mafita,..
a hankali ta Mike ta murda kofa ta fita ,
dakin mummy ta nufa dan tasan bata ciki tana can gurin musaddiq,
drawers ta fara janyowa ta shiga binciken visan musaddiq da aka kawo mishi jiya,
da kyar ta gano inda take cikin wata karamar jaka,
dariyar farin ciki ta shiga yi a ranta tace zanga yadda za'ayi ya tafi ba wannan,
hannu tasa zata fara yagawa taji an Fisge visan a hannunta,
saurin waigawa tayi dan ganin ko waye,
Husna ta gani tsaye tana kallonta cikin ido,
"haba Badar yanzu muguntar taki har ta kai haka,
meye amfanin yaga mishi visa,?
tun fitar ki na biyo ki dan nasan ba fitar alkhairi kikayi ba,
akwai abin da kike shirin kulawa da shurun da naga kinyi,,
mtswwwwwwwww Badar taja dogon tsaki tace "dalla malama bani,
ni nace miki yagawa zanyi,
to me zakiyi dashi? husna ta tambaya fuskarta dauke da mamaki,
ban sani ba Badar ta fadi tana mik'a hannu zata kwace,
kaucewa husna tayi tace wallahi bazan baki ba,
sai dai ki kwata ta karfin tsiya,
nan suka fara kokawar da ya janyo hankalin su mummy,
Kaiiii, kaiiii,
lafiya menene haka, mummy ta fadi da karfi tana shiga tsakaninsu,
Husna tasaki wahalalliyar ajiyar zuciya hade da haki tace mummy visar Yaya zata yaga,
Visa kuma, to me yasa??
mummy ta tambaya cike da mamaki tana kallon Badar,
Cike da shagwaba Badar tace
"mummy karya fa takeyi wai dan taga na dauko na rike a hannuna ina karantawa shine tace wai zan yaga,
akan me zan yaga mishi visa,
me yaga war zai amfane ni dashi,
kawai dai sharri zata min dan taga ba k----- mummy tayi saurin rufe mata baki ta rungumeta tana rarrashinta,
yi hakuri Badar din mummy,
nasan karyar husna ai, in mafadin magana wawa ne majiyinta bazai zama wawa ba,
Husna ta fito da ido waje cike da mamaki tace Badar kiji tsoron Allah,
tabdi!!!! ta kara fadi cike da kullewar Kai tana tsananin mamakin halin Badariyya a Yan Kananun shekarunsu,
ajiye visar tayi a kan madubi ta raba ta gefen musaddiq da ya nade hannayenshi yana kallon ikon Allah ta wuce rai a bace,
rufa ma Husna baya yayi hade da hararar Badar yana fadin Allah dai ya kyauta,
"Ameen"
mummy ta fadi a fusace tana sharewa Badar fuska tana kara bata hakurin abinda husna tayi mata,
Sam bata son bacin ran Badariyya,
wata iriyar kazamtaciyyar soyayya takeyi mata wanda bata da masaniyar wannan zurfaffan son zai mata illah marar misaltuwa anan gaba.......
********
"Babu sallama......"
Ta ji an fadi a bayanta,
da sauri ta waigo a firgice ta kalli motar,
kwantar da sit yayi a gaggauce hade da karasa bude tint glass din,,
nan da nan ta saki murmushi mai sanyin kyau,
tace "ina kwananku,
Hinad ta turo kanta daga baya tace "leko kiga mai magana Nadiya,
Yaya Hilal ne yake bukatar yin sallama dake,
Hilal ya chire hular da ya rufe kanshi dashi ya dago sosai ya hade girar Sama da kasa yace wallahi zan karya yarinyar nan,
Hinad ta zaro ido ta kalli drivern mummy tace dan Allah mal---- bige bakinta yayi yace dan Allah Malam ja muje inda mum ta aike ka,
Hinad ta turo baki tace "Nadiya bani milk candy pls Kinga yau zan tafi,
Nadiya tayi saurin juyawa shagon tasi ta dauki robar da ko minti biyar batayi da bashi ba ta miko ma Hinad tace gashi ki tafi dashi duka,
Allah ya kaiku lfy,
ki gaida anty da Yaya Musaddiq,,
ta cikin bakin glass Hilal yake satar kallonta,
duk tunanin shi ba wanda ke ganinshi bai San drivern mummy idanshi kyar akanshi ta mudubin motar ba,
sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa ya biyoshi kuma ya tursasa mishi biyowa ta layin dan ko kusa ba hanyar inda zasu bane,
murmushin zuci yayi yace
"yarinta hooo,"
in ba yarinta me wannan dan yaron ya sani akan mace,
macen ma jaririya,
ko da yake akwai Soyayyar yarinta da kuma ta jini,
muryar Hilal ce ta maido shi daga duniyar zancen zucin da ya tafi,
da sauri ya tada motar suka fara tafiya,
daga musu hannu Nadiya ta shiga yi alamar bye bye,
suna gab da kure layin ya sake kallon madubin gefenshi karo na barkatai ya hangota tana juyawa gurin mai shagon,
kwantar da kanshi yayi kan sit hade da lumshe ido yana Nazarin abubuwa da dama....
LARNACA INTERNATIONAL AIRPORT CYPRUS
2:27am daidai,, agogon kasar Cyprus ya buga,
daidai da karfe 1:27am na agogon kasarmu Nigeria,,
Hayaniyar mutanen cikin jirgin ne ya farkar da musaddiq da bacci yayi can wata kasar dashi,
mik'a yayi ya sake gyara seat belt dinshi, ya kalli Hilal yace
"har mun iso? ,
da kai Hilal ya bashi amsa, alamar eh,,
Alhamdulillah Ala kulli halin musaddiq ya fadi yana mai gyara zamanshi kafin jirgin ya karasa tsayawa,,,
"Welcome to the third largest nd third populous island in the Mediterranean uncle"
Hinad ke maganar cikin kwarewa tana bude hannayenta hade da lumshe idanunwanta a Saman matattakalar benen jirgi,
thank u my darling daughter, musaddiq ya fadi yana mai sunkuyawa dai dai kumatunta yayi mata peck,
saukowa sukayi kowa rike da Jaka suna ja, suna baza idanuwa,,
daga can nesa suka hangoshi tsaye cikin ash jallabiya yana hamma hade da duba agogo,
a guje Hinad ta ruga tana kwala kiranshi da karfi, "PAPA",
bude hannayenshi yayi yana murmushi ta shige jikinshi ya dagata Sama yana juyata,
" I MISS U SO MUCH PAPA"
misd u more more more angel,
Hw waz ur trip? , boring ta fadi tana tabe baki,,
ohhh why my dear? Ya tambaya yana Jan kumatunta,-----
for crying out loud PAPA abinda kazo yi nan kenan, anty reema ta fadi cikin katse musu hanzari,
sauketa yayi yace come on my dear Reems u knw am here for u,
kallon musaddiq yayi cike da murna yace welcome broo, ya hanyar? ,
"lafiya lau alhamdulillah, mun sameka LFY? musaddiq ya tambaya yana murmushi,,
fine fine ka dai ganni sai dai dan wuya na rashin girkin yayarka ya fadi cikin zolaya,
dariya musaddiq yayi yace I cee,
Gud morning father,
PAPA ya fadi yana mai tsugunawa HILAL dake ta faman latse latsen waya,
ohh dad neman magana ne kawai kasan zan gaisheka ai,
just don't want to interrupt you,
you knw i miss u,,
gaisuwar mu dabanne,
harara Papa ya bishi dashi ya karbi jakar hannun matarshi yace
"oya lets go bacci nake ji sosai sosai, kama hannunshi Hinad tayi suka nufi hanyar waje....
Mrs Tijjani Shattima......
[04/12 09:46] Meela Adeel: °ZUMUNCINMU A YAU°
By Aysha Ya'u Kurah
1⃣0⃣
Agios tychonas, limassol..
Estate ne gari guda na ma'aikata,
da yawansu turawa ne yan kasashe daban daban,
yan kasar turkiya sunfi kowa yawa a cikin estate din,
sai tsirarrun bakaken fata yan Africa,,
A katafaran parking space din harabar gidan sukayi parking motar,
fitowa sukayi kowa na mik'a suka nufi cikin gidan,
lift suka danna suka