Showing 138001 words to 141000 words out of 184071 words
Chapter 47 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt
acc no,
sau uku tana yin transfer ana ce mata
"Your account is restricted,
Managern Bankin ta kira dan jin dalilin restricting acc dinta,
nan yace mata Alh ne ya basu umarnin yin hakan tun da safe,
faďa sosai ta fara mishi wanda ya sashi bata hakuri haďe da kashe wayar dan bazai iya budewa ba,
da ya batawa Alhj rai gara nata in sun kai dubu su baci,
Dubu hamsin din cikin account din Raudha dashi sukayi amfani da zummar in sunje gida Mummy zata bata dan tana da kudi a cikin drawer,
kwantar mata da hankali ta dinga yi tace
"Ai naci zaman gidanshi,
a ciki zan zauna saidai shi ya bar min gidan,
in kuma bai iya barin min saidai ya maida ni dakinshi,
da tsufana bazan koma gida zawarci ba wallahi,
yadda take maganar kowa ya ganta yasan bata cikin hayyacinta dan cikin kankanin lokaci komai nasu ya canza...
*Allah kenan mai canza komai cikin kiftawar ido......*
Mrs Tijjani Shattimah
[26/04 7:28 AM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣5⃣
By *Aysha Ya'u kurah*
Dukkan manyan asibitocin dake garin lagos babu wanda basu zagaya ba, haka mutuary,
duk inda sukaje da kwatancenta sai su nuna basu ganeta ba,
A Oxford hospital dake Banana island ne kadai wata Doctor tace
"Accident case daya muka karba daren jiya,
mata da miji ne sukayi accident din,
ita ta bugu da yawa dan har anyi tunanin ta mutu,
shi kuma a kai kawai yaji ciwo, yayi collapse saboda tashin hankali,
suna Vip Amenity, naji ana shirin fitar dasu Canada,
Juyawa Papy yayi yace basu bane,
wannan ita kaďai ce,
dafe kai Daddy yayi hawaye na zuba a idonshi yace
"Ya Allah ka bayyana mana Nadeeyah a mace ko a raye,
Hafeez da jikinshi ke bashi duk inda Nadeeyah take tana kusa dashi yace
"da munje mun duba saman Daddy,
ta yiwu ita ce,
ba suyi mishi musu ba suka fara taka steps din hawa saman...
Da gudu wata Nurse ta ke sakkowa daga sama tana faďin
"Doctor Marly...
she is alive,
ta farfaďo,
and the most surprising thing is that her baby is perfectly fine and healthy, Single Fetus...
"Wow Mashaa Allah..
Doctor Marliyya ta faďi cike da farin ciki,
a gwajin jinin da sukayi mata sun gano tana dauke da karamin ciki shiyasa ma basu tsaurara yi mata allurai ba....
Kallon Hafeez Papy yayi yace
"kaji wannan ciki gareta,
Nad----
wayar Daddy ce ta katseshi daga karashe maganar...
dagawa yayi da sauri saboda ganin sunan Hilal,
"Ya farfaďo Daddy,
kuzo da sauri,
Ajiye wayar Daddy yayi yace
"Musaddiq ya farfaďo...
Alhamdulillah...
Papy ya faďi haďe da sakkowa kasa yace
"mu tafi gurinshi,
in da rabon ganin gawarta zamu gani,
in kuma tana raye Allah zai sa mu ganta,
sai mu tsananta addu'a domin bata faďuwa kasa banza,
tunda har bamu ga gawarta ba, na tabbatar tana raye,
domin jikina bai bani Nadeeyah ta mutu ba,
wannan kalmar itace mafi soyuwa da Daddy yaji tun da yaji labarin sakin Nadeeyah,
Allahumma Ameen ya faďi haďe da damke hannun Papy,
shidai Hafeez kallon saman kawai yakeyi hankalinshi yaki kwanciya har suka fita daga reception din,
shima yasan yar uwarshi na nan da ranta bata mutu ba,
share hawayenshi yayi yace
""Ya Allah ka tsare min Nadeeyah,
ka haďata da alkhairai gabas da yamma kudu da arewa,
Ya Allah ka zama gatanta dan bata da gatan da ya wuce kai....
*****
*******
Hannu Husna tasa tana share hawayen dake tseren fitowa a ta gefen idonshi,
kallonsu yakeyi daya bayan daya yana adduar Allah yasa kallon da zaima na karshe ya zamto Nadeeyah ce tsaye tana mishi murmushinta mai matukar kyau...
yana sauke idonshi kan Hilal ya runtse idonshi,
Hilal ya cika masoyi,
Hilal is a real definition of a brother, friend nd a guardian..,
ya akayi bai fahimci son da Hilal yakewa Nadeeyah ba,
lallai ya cika babban sakarai wanda bai iya fahimtar abu..
Hannunshi Hilal ya rike haďe da kwanciya a jikinshi dan ya fahimci tunanin da yakeyi.. murya na rawa yace
"Bakayi min komai ba Musaddiq, u will always be my no 1,
i will always love u,
babu abinda zai canza soyayyata agareka,
u are very nice,
matsalata ďaya ce wacce nake son canza ta a gareka,
u are very soft,
a wannan duniyar ana daukar advantage din irinku,
change!!,
u have to change Kyari..
ya karashe yana kuka sosai saboda baisan yadda zai dauki mutuwar Nadeeyah in an faďa mishi ba..
kukan da sukeyi tare ya sanya dukka mutanen gurin zubda hawaye,
an rasa mai rarrashi a cikinsu,
Hannun Musaddiq Ruwaidah ta kama tana kuka tace
"Ance my sister is no more,
ina ka kaita,?
ba kai muka tafi muka barma ita ba?
Janyota Jamal yayi ya buge bakinta haďe yi mata tsawa,
Shuru Musaddiq yayi yana kallon Hilal wanda ya kasa haďa ido dashi,
Murya Na rawa yace
"Na--aad--
bai karashe ba ya hango hijab dinta a hannun Husna,
Durowa yayi akan gadon haďe da fisgo hijab din,
jinin da ya gani a jikin hijab din ne ya sanyashi sakin wata razananniyar kara ya zube a gurin,
wannan karan faďuwar da yayi tafi ta jiya dan babu inda yake motsi a jikinshi,
Da gudu su Hilal suka fita suna kwala kiran doctor,
nan dakin ya dauki sabon kuka har su Daddy da suka shigo a lokacin,
Faďa sosai doctors din sukeyi suna faďin
"Munce ku barshi ya huta,
kunki,
gashi yanzu kun janyo mishi faďuwar da tafi ta da,
Allah ya tsareshi daga tabuwar zuciya ko stroke...
Dukan Ruwaida Mami ta fara yi tace
"Shegen bakinta yasata fada mishi Nadeeyah ta mutu,
Anni ce ta shiga tsakani cike da faďa tace
"baki san yarinta ba,
duka nawa take?
"Da haka kuke dada maida ita baya,
Jamal ya faďi rai a bace haďe da fita waje,
Su dai su Papy suna can suna leken halin da Musaddiq yake ciki..
Oxygen suka ga an taho dashi da gudu za'a sawa Musaddiq,
Zaman dirshan Daddy yayi a tantagaryar kasa yace
"Shikenan,
Allah ya jikanka Musaddiq,
Allah ya amshi bakuncinka,
na yafe maka duniya da lahira,
na yafe maka...
"Haba Alhj Mukhtar,
ciwo ya taba zama mutuwa ne,
dan Allah karka karya mana zuciya,
Cike da zarewa Daddy yace
"Life Support,
Musaddiq da life Support,
numfashi ma sai da oxygen,
wa aka taba sawa kaga ya mike,
"Suna nan da yawa Daddy,
babu abinda zai sameshi,
wallahi Musaddiq bazai mutu ba,
in kuwa kaga ya mutu to saidai ko mu mutu tare,
yadda Hilal ke maganar ya sanya Daddy fashewa da kuka sosai haďe da rungumeshi....
Likitoci sunfi awa ďaya akan Musaddiq kafin su samu Allah ya basu sa'ar ceto ranshi,
stroke ne ya kusa kama shi,
ga hawan jini da yayi mugun hawa wanda yayi ma shekarunshi yawa,
Cikin ikon Allah bai taba zuciyarshi ba amma fa dakyar yake numfashi shiyasa suka haďa mishi da oxygen...
sosai sukayi ma Daddy kashedi akan kar su sake su faďi abun da zai ďaga mishi hankali dan condition dinshi is very critical,
Shawara sukayi kowa ya tafi a barshi da Daddy da Hilal kawai,
nan Jamal ya bukaci tsayawa saboda ya dinga taimaka musu....
Koke koke babu irin wanda ba'ayi a gidan Musaddiq ba,
isowar su Anty Reemah da Raliya ya kara ďaga hankulan yan gidan dan sunyi kuka har sunji ba daďi...
Dakin da aka maida Musaddiq guri ne da daga doctors sai mutum ukun dake jinyarshi kaďai ake bari su shiga..
A gidanshi sauran mutanen suka zauna suna jajanta lamarin haďe da yi mishi adduo'i na neman sauki da kuma na bayyanar Nadeeyah....
Dubu biyun da ta rage musu ita suka dauko drop suka iso gida,
A garkame suka samu gidan da kwaďo ga kuma police guda biyu zaune akan kujeru suna gadin gidan,
*(Shirin da Daddy yayi a waya kenan tunda yaga sun tafi, yasan gidanshi zata wuce shiyasa ya kira abokinshi commissioner dan ya tura a rufe mishi gida ayi gadi, kuma kar su bar kowa ya shiga)*
jiki a sanyaye Mummy ta karasa haďe da gaida Police din,
amsa mata sukayi gami da kallonta,
"Ina zaki?,
"Gida na ne,
ina son zan shiga ne,
juyar da kai sukayi sukace order aka basu na kar su bar kowa ya shiga gidan,
ganin babu alamar rahama a fuskarsu ya sanyasu juyawa cike da tashin hankali,
"Ta inda ya bullo kenan?
kaya kala uku kadai gareta,
gashi bata da kudi a hannunta, ba mota,
babu komai na jin dadin rayuwa,
Gidan Goggo suka nufa dan nan ne ya zame musu dole.....
Mummyyyy oyoyo.....,
Raees ya faďi haďe da rugowa da gudu ya rungumeta,
ajiyar zuciya tayi tana faďin
"Alhamdulillah,
aurena is safe,
yanzu zan gyara zamana da mijina da yan uwanshi kar Allah yayi min mugun kamu..
wucewa ciki tayi tana godewa Allah da irin son da yakeyi mata..
Yaranta kanana biyu take son gani dan ta jiyo dariyarsu a parlor..
Turusss..
taja ta tsaya ganin Shamsu goye da Adeel ita kuma Fatima goye da Amma suna rarrafe suna zagayen parlon suna bangazar juna..
Wani tsawa ta dakawa Fatima wanda yasata saurin sauke Amma a bayanta,
"Sannu da dawowa Anty,
"Gyatummm..
gyatummm..
Radiya ta shiga kwala kiran ta da karfin gaske,
"Mama bata nan,
ta koma gida... Fatima ta amsata cikin ladabi
"Sai ta barki kina min aiki kina wasa da mijina?
Mijinta ne itama..
mai sukuni,
Inna indo ta faďi tana dariya,
"Whatt?
Mijinta?
"Kwarai kuwa,
mijinta nake, ko kinada matsala da wannan me?
Wani irin sarawa taji kanta nayi tayi saurin zama akan kujera,
"Ni zaka ciwa Amana Shamsu?
"Auren ne cin amana? Inna indo ta tambaya tana zama a gefen Radiya,
"Ke dallah can rufe min baki,
ina magana ne da mijina ba dake gayyar na aiya gayyar tsiya ba..
"Aheeee yayanki ma gayyar tsiyace tunda abun da yayi ni hi yayi su,
"Shamsu kayi warning matar nan,
kasani sarai bani da mutunci,
"Rashin mutuncinki ya tsaya akanki,
kinga na samu nutsuwa a gidana,
karki zo ki nemi tarwatsa min,
Fatima shiga da yara ciki,
ki sirka min ruwan wanka kuma ki jirani a bayin..
A fusace Raudha ta mike ta fisgo hannun Adeel haďe da kwada ma Fatima mari,
nuna ta da yatsa tayi tace
"in baki fita a cikin gidannan yanzu ba, wallahi sai na kasheki, zo ki wuce, munafukai maciya amana,
Marin da tayi mata shamsu ya mayar kan fuskarta yace
"saidai ke ki fita,
in har bazaki yarda da fatima a matsayin matata ba saidai ki fita ki barmin gida,
"Wallahi shamsu kai baka isa ka haďa ni kishi da wannan kucakar ba,
wallahi kayi kaďan,
Rungumo Fatima yayi sosai yace
"wannan kucakar ta shayar dani kaunar da wayayya ta kasa shayar dani,
ta kula da mahaifiyata cikin kankanin lokaci,
mai rabani da ita saidai mutuwa...
"To ko saidai ka zaba koni ko ita... Radiya ta faďi tana huci..
"A bayyane yake Radiya,
na zabi Fatima,
saboda ta haďa abubuwa da dama,
wayewa ce bata da ita,
zan siyo mata a kanti tunda akwai su da dama kantin wayayyu,
zan maida ita first class lady wacce zakiyi mamakinta,
ban ce zan sake ki ba,
amma in kina bukata ina iyawa,
"Aiko dole ka sakeni,
me zanci da kai,
kaje can ka karata da yar talakawa yar mai min hidima, kazami kawai..
"Nagode mai tsafta ya fadi yana dariya,
"Kije na sakeki,
amma duk ranar da kikaji kina muradina kafin ki gama idda ina iya maida ki saboda darajar 'yayanki da mahaifinki,
yana kaiwa nan yaja Fatima suka wuce daki..
Yana jiyo ihunta tana zaginshi da mahaifiyarshi,
babu wanda a cikinsu ya tanka ta dan anyi mata mai kankat....
Dakinta ta shiga ta tattare kayanta da gwalagwalanta ta fice ta bar mishi gidanshi....
*********
Saida Musaddiq ya kwana uku a asibiti, lokacin ya farfaďo yana gane duk wanda ke kanshi,
babu abinda yakeyi daga kallon su Daddy sai bacci in allurai sun ratsashi,
tunda ya farfaďo kamar an tafi da hawayen da yakeyi,
magana ba ya yinta ko kadan sai dai in sunyi ya bisu da ido,
Da support yake zuwa yayi alwala da wanka saboda jikinshi samm babu kwari,
a wannan lokacin ne aka yarda kowa yazo ya ganshi dan jikinshi yayi kyau matuka,
abinci da ya zamo aminin Musaddiq yanzu ya maidashi babban makiyinshi domin sai anyi bacin rai kafin ya yarda yayi cokali daya,
kowa burinshi ya farantawa Musaddiq dan dai kawai su samu ya saki jikinshi ya cigaba da Mu'amala kamar yadda ya saba,
Zainab da Ruwaida ne samm ba'a yarda suje inda yake ba saboda har yanzu bakinsu bai bar tambayar inda Nadeeyah take ba...
A cikin kwanan shi na bakwai aka sallameshi,
har wannan lokacin babu wanda yayi mishi maganar inda Nadeeyah take,
shidai yafi bada an binneta shiyasa ma baiyi yunkurin tambaya ba, dan kar ya sake tayar wa da hankalin su Daddy,
Suma kuma har lokacin basu bar neman Nadeeyah ba,
dan har police station suka kai,
tunda Allah baiyi sunga gawarta ba sunsan tabbas tana raye,
in da rai wata rana dole su haďu in shaa Allah....
****
"Karka damu Daddy,
i will take care of myself,
Kallon Zubair Daddy yayi yace "Dan Allah ka kula dashi,
karka barshi ya dinga tunani, ka----
"Nace i will take care of myself,
i'm nt a kid,
yadda yayi maganar da tsawa ya sanya Anty Reemah matsowa kusa dashi,
Dafa kafaďunshi tayi tace
"Laifi ne dan ance a kula dakai,
tafiyar nan ance ka hakura da yinta,
baka da lafiya, ka dage sai kayi ta,
dole a nemi mai kula da kai..
Hannunta ya cire a kafadunshi ya dauki brief case haďe da kallon Daddy yace
"kayi min addu'a in shaa Allah babu abinda zai sameni,
tunani shi ke yin kanshi,
with ur Du'a komai zai daidaita,
Murmushi Daddy yayi yace
"In shaa Allah son,
Allah ya tsare ku ya bada sa'ar abinda aka je nema...
Gurin da Hilal ya ke tsaye Musaddiq ya kalla,
suna haďa ido ya karaso inda yake ya rungumeshi,
rashin walwalar Musaddiq na matukar damunshi,
babu abinda yake sanya shi farin ciki,
dariya kanta ya manta yadda akeyinta, domin wani sashi na yin dariyarshi ya mutu a ranar da ya rasa Nadeeyah,
"Take care kaji,
in na gama project zanzo Singapore inyi keeping dinka company,
gyaďa kai kawai Musaddiq yayi suka fita,
dukkansu yan parlon kowa na mishi fatan alkhairi haďe da adduar Allah ya kara sanya farin ciki a cikin zuciyarshi......
Mutum kamar Musaddiq wanda baisan menene bacin rai ko fushi ba a ganshi a haka dole hankalin makusantanshi ya tashi dan sun san ba karamin abu bane yake sanya Musaddiq fushi,
Daddy yaso yayi quiting aikin da yakeyi amma Musaddiq sam yaki, saboda shi kadai ne yake ganin zai dabe mishi kewa,
badan Daddy yaso ba haka nan ya yarda dan yaso ya zauna tare dashi har ya samu sassauci a zuciyarshi...
Duk wani shiri na barin gidan su Badariyya sunyi domin abun kawai da ya rage musu shine su tarwatsa kuttun tsafin Bokan gaba daya,
layar dake bakinsu suka matsa dan bacewa suka ji su har lokacin a gurin,
cike da tashin hankali suka kalli juna haďe da sake latsata,
hankalinsu bai kara tashi ba sai da sukaji damka a bayansu,
waigowa sukayi dan ganin mai ganinsu a wannan lokacin da suka san sunyi komai dan bacewa ganin mutanen gidan,
Yareemah Suhail suka gani gefenshi kuma duk wasu kulli da sukayi ne wanda ya warwaresu ya sanya musu wuta,
Dariya sosai yayi yace
"kun taba jin labarin wanda ya shigo gidannan ya fita shi kadai,
shafa kanshi yayi ya cigaba da cewa
"Badariyya nasan da hatsabibancinki kika zo,
sai kuma kika kara da na Marakisiyya,
da nice ke zanyi biyayya domin cikin biyayyar wata rana in da rabo ina iya kaiki gida ki ga yan uwanki har kiyi musu sati in kinaso,
amma tunda kin biyewa wannan hatsabibiyar sai kuyi ta zama da taurin kanku,
duk ranar da kuka ga kun amince da zaman gidan nan sai kuyi biyayya, in kuna da rabo sai kuga na kaiku gida dan ziyara,
yana kaiwa nan yayi wurgi dasu cikin wani dakin da basu san da zamanshi a gidan ba..
Kukan jini ne kadai Badariyya batayi ba dan ta ga koshi ya rikide ya zame mata kwanan yunwa,
tayi shirin komawa ta shiga Musaddiq sosai har ta kai ga aurenshi hankali kwance ba tare da kowa ya zargeta ba...
Taci kuka sosai har saida faďa mai karfi ya kacame musu ita da Marakisiyya,
faďan da ya sanya zubewar hakoran Badariyya na gaba, dan Sosai Marakisiyya tafi karfinta.....
*6months later...*
*******
Radiya..
bani dubu biyu zan baki gobe in Reemah ta turo min,
Buďe baki Radiya tayi tace
"ina na gansu Mummy,
nawa nake binki?
kusan 30k fa,
ina zanga dubu biyu yanzu,
Raudha dake kwance akan kujera tace
"Ki bata mana,
jiya fa kika siyar da zobenki,
meye a ciki dan kin bata,
kika san abunda zatayi dashi...
To munafuka,
da na siyar da zoben baki faďa mata abun da nayi dashi ba,
saida zoben kaďai kika iya faďa mata,
ni fa na gaji da wannan rayuwar,
duk wani abu nawa ya kare,
kullum ni kenan cikin bada kudi sai kace wata banki,
na gaji wallahi ta mike fuuuu tayi cikin daki....
Share zufa Mummy tayi haďe ficewa daga dakin tana mamakin hali irin na Radiya,
kwallar da ta fito a idanunta ta share haďe da yin tagumi tana tunanin a wani hali Musaddiq yake yanzu,
rabon ta da ta sashi a ido tun daren da suka fita nemo Nadeeyah,
ko sau ďaya bai taba tunanin nemanta ba,
ta sani ta bata mishi matuka,
a yanzu dana sani takeyi sosai na biye wa san zuciyarta da tayi,
kawayenta da a da suke like mata kaff dinsu sun guje ta saboda halin da take ciki,
Nairah dari yanzu mugun sha'awa take bata,
ga Baffa ya dauke Anni ya maida ita gidan da Papy ya siya saboda ya dinga sauka in yazo,
ko ganinshi basa yi a gidan saboda a cewarshi basa girmama matarshi,
Daddy kuwa ko ta kirashi bata samu dan ya sanyata a black list,
samm bata samunshi, koda text tayi mishi saidai ya dawo mata dan