Showing 33001 words to 36000 words out of 88777 words

Chapter 12 - SO NE KO KIYAYYA COMPELET BOOK BY MAMAN FAREESA.doc

da ita tana tsaye jikin wata bishiya"mama gaje ta nufeta tana mamakin dama A wannan k'auyan ne dodon yake?......naso mu taho tare dake to sai kikace sai kin fara zuwa gidan hjy hauwa"cewar hjy wasilah sadda mama gaje ta iso gefenta"kedai bari naje dan ta ganni tasan na sauya nima na samu duniya yanzun"dariya hjy wasilah ta dingayi"kafin su kutsa cikin daji Inda keda dogayen shifkoki suna tafiya"sau 3 mama gaje nayin sartse da k'aya sai mita takeyi tana fad'in itafa ta gaji da tafiya"hjy wasilah na bata hak'uri da sanar mata sun kusan kaiwa...sunyi tafiyar kusan mintina 30 kafin su iso Adaidai bakin wani iccen gawo"suka tsaya suna kallonsa da waige waige sbd kar wani yagansu"wanda da wuya kaga mutum Anan sai idan manomi ne"wasu surutai hjy wasilah tayi.... Atake dg tsakkiyar bishiyar yabud'e "saiga hanya da k'ofa"babu b'ata lokaci suka shiga wajen ya rufe"sai gasu adajin Allah ta'ala "saidai Inda suke zagaye yake k'asa da sumunti"sannan Akwai bukkoki da gulbin ruwa can baya"sai wata bukka babba da'akejin motsin mutane Aciki"hjy wasilah tace"muje can zamu shiga"kowa nacan da mun gama had'uwa dodo zai fito muyi mgn"dato mama gaje ta Amsa suka shiga...bbu jumawa suka fito suda yawa"d'aya bayan d'aya haka suka jera suna dg tsaye"kowane da riga bak'a babba ta yadi Ajikinsa" sun aza saman kayan jikinsu "sai hula jaa duk kowa yasaka"maza su sha ukku ne guda yak'aru"wanda Ada su 12 ne"mata kuma su takwas ne yanzun sun koma su tara"bayan dodo ya bayyana"akace sabbin shiga k'ungiya su fito"Atake mama gaje da safwaan suka fito dg gaba"Aka basu wani Abu kamar jini Acikin wata k'warya sukasha"tunda safwaan yaga mama gaje yaga kamar yasanta"Amma saiya share"mama gaje Aka bata wani dutse ta dafa tayi Alk'awarin kawo mijinta"bayan ta gama Aka bama safwaan yadafa"shima yayi Alk'awarin zai kawo mahaifinsa sati na sama.....bayan kowa yagansu kafin dodo ya sallami kowa"kasancewar kusan k'ofar shigowa matsafar guda hud'u ce"gabas, yamma, kudu, Arawa"ta yamma Anan mama gaje da hjy wasilah da safwan da wani suka biyo"suna fitowa safwann yace"duk A cikin garin kano kuke ko? yafad'a yana kallon su mama gaje"kasancewar shi namijin da suka fito Atare shinema yasaka safwan cikin k'ungiyar"mama gaje na washe baki tace"Eh nida ita duk Anan muke"okay bbu damuwa muje na saukeku Agida nima can nayi"gaskiya ka kyauta sosai"Amma nidai bama gida nayiba"GRA nasssarawa zanje"okay yafad'a"Amma saida yaji fad'uwar gaba sbd yasan Anguwar su dr Aliyu me tubarau ce"bece komaiba suka dinga tafiya har suka iso Inda safwaan yayi parking"mama gaje da hjy wasilah suka zauna a back sit"safwan da gudan suka zauna A front sit"suna fira jefi jefi har suka iso Anguwar G R A gab da magrib... Adaidai bakin k'ofar wancan gidan zan sauka"cewar mama gaje"k'irjin safwan na bugawa yace"me jan get d'in?"Eh nan "Allah sarki Anan kike kenan?"ah ah yayata hjy hauwa ke Aure Agidan"ta k'are maganar tana fitowa dg cikin motar tana musu godiya.... Atake safwan yafahimci mama gaje k'anwar mahaifiyar dr Aliyu ce"wani shegen murmushi yasaki me wuyar fassara"k'asan zuciyarsa yana zargin k'ilan umma bata taimakama mama gaje"ko kuma mama gajen nason tafi umma wadata shiyasa ta zab'i shiga k'ungiyar Asiri....yana wannan tunanin yaja motar yayi gaba"wanda tun lokacin da motar tayi parking Akan idon yaya Aliyu dake zaune cikin mota ya Ajiye In'am harma ta shiga gida"shi kuma zai tafi Asibiti"yana k'ok'arin tashin motar yaga motar dayabi last week har k'ofar gidan safwan tayi parking"gashi me tinted ce ba'a ganin na ciki saidai na ciki yaga na waje"kamar yadda motar yaya Aliyun shima take"gaban yaya Aliyu yayi mugun fad'uwa da yaga mama gaje ta fito dg cikin motar ta shige gidansu....
'?

Adinga shairhi=??

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

d'?=ؓ? SONE KO K'IYAYYA =ؓ?d'?

29&30


......... Shiru kawai yaya Aliyu yayi yana nazarin Abinda yagani"saidai tunanin nasa yakasu kashi daban daban"Abu na farko dayakeso yasani shine waye mamallakin wannan mota?"sbd yasan be tab'a ganin safwaan da wannan motar ba"inma ta safwaan ce to meyasa mama gaje ta shiga ciki??"kodai yaje ya tambayeta waye ya Ajiyeta A mota, kuma ina taje cikin motar??.....tsaki yake ja kamar zai huda harshensa"dg k'arshe ya yanke shawaran bibiyar safwaan da kuma wannan mota" ta haka kawai zai gano bakin zaren kamar yadda brr Ahmed yabashi shawara yayi Abaya.....motar yabama wuta yabar wajen zuciyarsa nasanar masa sai mama gaje ta had'a masa bom Awajen umma.....hakan kuwa ta kasance dan maganganu k'arya da gaskiya mama gaje ta sanarwa umma kan In'am da Aliyu"wai ta ganshi ya sauketa Amota ta fito da manyan ledoji"ta jima tana fad'in k'arairayi sannan ta zauna sukaci Abinci zubaida tayi sallah"Amma mama gaje bata yiba"zubaida kuma na mamakin kusan sati 2 kenan rabon dataga mama gaje tayi sallah"tana so ta tambayeta dalili Amma tana shakka Aranta ...ba sune suka bar gidan ba sai wajen isha'i"sadda suka fito dg b'angaren umma mommy itama ta fito da bak'uwa zatayi mata rakkiya"mama gaje na ganinta ta d'aure fuska tak'i yi mata mgn suka wuce Abinsu"mommy tayi murmushi kawai tana yimata Addu'ar shiriya Aranta.....yaya Aliyu be shigo cikin gidan ba sai bayan yayi sallar magrib"sannan yadawo yayi wanka ya shirya cikin milk d'in jallabiya yanata zabga k'amshi yatafi yayi sallar isha'i"Ana idarwa kai tsaye gidan ummi yanofo"dukda k'asan ransa yana jin nauyin ummin sbd kusan sati 1 bezo ya gaishetaba sai yau zaije...ummi kuwa tunda taga in'am nata walwala kuma tace"tazo taci Abinci tace taci Abinci Awajen yaya Aliyu jikinta yabata da dare koda safe saiya zo....tun bayan in'am ta gama sallar isha'i tayi shirin bacci ta fito tazo ta zauna cikin parlourn da hijab k'arama himar Ajikinta tana kallon yaya mukhtar dake zaune yana kallo"Ahankali tace"yayana nawa shika d'ai"harara ya ballah mata yana fad'in dama ina son mgn dake "meyasa wai idan Abdallah ya miki mgn bakya son kulashi??"cak yaya Aliyu dake k'ok'arin shigowa yatsaya sbd yaji wace Amsa in'am zata bama mukhtar??..."wai bakiji ina miki mgn?"b'ata fuska tayi tace"nidai gaskiya haushi yake bani yayita kallona"kuma nidai bana son na tsaya da wanda ban saniba karatu nakeso nayi.....wata Ajiyar zuciya me tubarau yasaki Ab'oye" Aransa yana mamakin wayon In'am"dama Angel nasa nada wayo haka? Amma take nuna batayi hankaliba"yazata fa zatace shine ya hanata kula maza"fuskarsa Asake yashigo cikin parlourn da ledar tsarabarta A hannunsa"saida In'am taji fad'uwar gaba da taji tattausan muryanshi"mukhtar kuwa had'iye masifar dayaso yima in'am yayi ya Amsa sallamar yaya Aliyu"tunda yashigo idanuwansa k'yam Asaman baby face nata dan ba k'aramin kyau tamasaba"itama satar kallon sa tayi suka kuwa had'a ido"yaya ina wuni?"tafad'a tana sunkuyadda kanta ak'asa"lafiya qlau"yafad'a yana mik'a mata ledar hannunsa yace"ummi fa?"tana ciki tana sallah"ta fad'a tana Amsar ledar da hannu biyu"kije ki kamun littattafanki na islamiya"yafad'a kamar an masa tilas yana zama kan kujera"mukhtar ya gaishesa"in'am kuwa bata wani damuba sbd tasan ta iya komai Aka koya musu"d'akinta ta shiga"ta duba ledar taga tsirene da zafinsa da ice cream"wayyo yaya me tubarau d'ina yanzun yana jidani "ta fad'a tana murmushi ta Ajiye ledar dukda tanaso taci saidai yanzun tarasa meyasa takejin nauyin cin wani abu Agabansa??"littattafan ta d'akko ta dawo parlourn ta sami yaya Aliyu da ummi suna fira"Agabansa k'asa kan carpet ta zauna saitin k'afafuwan sa tana fad'in gasu yaya"ummi dai na kallonsu batayi mgn ba"yaya Aliyu ya karb'i jakar yana zaro books d'in ciki yafara bud'e *sa'al wajawab* yana dubawa can yafara karanto mata da larabci tana fassarawa"ummi ta tashi tana murmushi tabarsu sbd suyi karatun" wanda hakan ba k'aramin dad'i yamata ba"ta tabbatar idan Aliyu shine miji ga In'am lallai in'am ta gama dacewa da miji na k'warai.....sunfi mintina 30 suna karatun"kusan book4 sukayi" *sa'alwajawab, Arba'una hadiz,kitabul tajweed,talbiyatul Aulad* "....hamma in'am tayi tana fad'in wayyo Allah yaya bacci gashi gobe Akwai skul"kuma kace na shirya da wuri ko?"yaya Aliyu dake kallonta yana k'ok'arin mgn Aka turo k'ofar parlourn da k'arfi"haka nan k'irjin yaya Aliyu yabuga!"yajuyo kansa yana kallon k'ofar sbd yaga waye??umma ce tsaye da dogon hijab Ajikin ta" tana huci tana jifar In'am da wani irin mugun kallo"wanda In'am d'in tayi saurin yin k'asa da kanta jikinta har rawa yakeyi....wato maganar gaje ya tabbata kenan??"ni ina nan na d'auka ka tafi Asibiti ko kana can part naka" kana hutawa Ashe kana nan katare??"bansan miye Aka baka kaciba"to wlh Ahir d'inka"zaka tashi kafita ko kuwa??duk ranar dana koma ganin kazo wannan shegen gidan wlh saina baka mugun mamaki"mutumin banza da baida kishin kai"ke kuma munafuka kina k'asa da kai kamar ta Allah"dg ke har uwar taki nafi k'arfin bokanku....rintse idanuwansa yaya Aliyu yayi yamik'e tsaye har jiri yake gani ya dafe bango"cikin wani irin yanayi yace"umma dan Allah muje bazan koma shigowa ba kamar yadda kikace dg haka yafita yana waiwayen In'am dake k'wallah....kama koma dawowa kaga yadda zanyi dakai"kana nan Anata ta tsarka Atatsi ubanka"to wlh d'ana yawuce haka....sannu me Abin haihuwa wacce tafi kowa iya haihuwar!"Ada naso na barki kiyi hargowarki kije "saidai naga Abinki yayi yawa"Aliyu banice ke kiran saba shine ke kawo kansa"kuma bazan koresaba idan yazo kodan sbd mutuncin sa dana mahaifinsa"cewar ummi cikin fad'a"kasancewar me hak'uri be iya fushi ba"umma na hararanta ta tab'e baki tace"Ashe ba kece ke kiransa ki cusa masa wannan me kama da muciyar ba? murmushi ummi tayi tana fad'in inaso ki sani bana takara da hukuncin Allah hauwa"idan Allah yayi In'am matar Aliyu ce ke baki isa ki hanaba"haka nima"dukda bazanso haka yafaruba" Amma Allah shine yabama kansa sani.... Allah yakiyaye"kinaso kenan tunda kikace haka?"wannan kuma ke yadama"dg yau karki koma zuwa min gida"mijinki kuma badan sbd tsoronki yasaka nak'i Aurensaba saidan sbd bana ra'ayin auren nasane"zan kuma Auresa Ayanzun saiki mutu idan mutuwa zakiyi.....tsaki umma taja tana fad'in mu zuba ni dake"dg haka ta fice"in'am dake zaune tana kuka ta tashi ta fad'a jikin ummi tana fad'in ummi na shiga rud'ani me kalaman ku suke nufi?? Kije kiyi bacci in'am"da sauran lokaci har yanzun"Amma insha Allah zan sanar miki wace gudun muwa Aliyu yabama rayuwarki.....cika ummi In'am tayi batace komai ba ,ta d'auki littattafan ta shige d'akinta" ta Ajiye books d'in tana tunani"duk yanda taso taci tsiren nan fita ranta yayi ta d'auka ta mayar A fridge"tazo ta kwanta bacci.....
washe gari misalin k'arfe 7:15 am"yaya Aliyu ne zaune cikin motarsa dg wajen get d'in gidansu"kallo d'aya zaka masa ka fahimci yana cikin damuwa"yab'oye jajayen idanuwansa Acikin bak'in tubarau nasa"yatsare k'ofar gidan su in'am da ido yanaso yaga fitowarta ko yaji sanyi Azuciyarsa...damuwar da yake ciki Ajiya ta saka ko baccin kirki beyiba"ya zauna yayi iya tunani da hangen nesa sbd yagano makusa ko Aibun ummi Amma be ganiba sai Alkharinta yake gani"ya tabbatar da cewa"mama gaje ba k'aramar shed'aniya bace sbd itace sanadin duk wata gaba da b'atancin tsakanin umma da ummi da kuma mommy"zai cigaba da Addu'a idan In'am Alkhairi ce ga rayuwar sa Allah yabashi ita"idan kuma ita ba Alkhairi bace Agaresa Allah yabashi juriyar rashinta"yaja doguwar Ajiyar zuciya yana fesar da wani zazzafan huci dg bakinsa yana tuna yau da safe da k'yar umma ta Amsa gaisuwarsa"tana k'ara masa warning karya koma shiga gidan ummi....be gama wannan tunanin ba ya hango In'am ta fito dg cikin gidan"tana sanye da yunifoam da socks da sendel"ta ratayo skul bag nata Agefen kafad'arta"fuskarta bbu walwala ko kad'an"kamarma tayi kuka"da kallo tabi motar yaya Aliyu"saidai batayi zaton yana ciki ba"yana lura da ita harta bud'e gaban motar yaya yusuf ta shiga"nafeesa ma tazo itada yaya sulaiman ya bud'e mata back sit ta shiga"yamik'a mata skul bag nata yana murmushi"wanda yanzun kusan kowa yafahimci suna son juna shida nafeesa...yaya Aliyu yabi motar da kallo harta b'acewa ganinsa"wani irin tausayin kansu shida In'am yaka mashi"yasan koda bata sonsa to tayi sabo da shak'uwa dashi"fatansa Allah yazab'a musu mafi Alkhairi"yana wannan tunanin yabud'e k'ofar fuskarsa bbu walwala ko kad'an yafito yashiga cikin gida....
A skul kuwa tun kafin Afito break farooq ya iso sbd da an fito break yayi mgn da In'am"saidai Ana fitowa break d'in In'am class tayi zamanta"ko break fast dg gida batayiba"dama inba ummi da yaya Aliyu ba bbu me tursasata taci Abinci"tagumi tayi tana tunanin warning d'in da ummi tayi mata d'azun"Akan karta koma shiga gidansu nafeesa saida dalili me k'arfi"idan taga Aliyu iyakarta dashi gaisuwa"ko Abu yabata karta koma Amsa ,kuma karta koma shiga motarsa"dato kawai ta Amsa Alokacin batace komaiba"sbd tasan mutuncinta ummi keso ta kare"saidai gaba d'aya idan ta tuna yadda taga yaya Aliyu yafita jiya dg cikin parloursu" sadda umma ke masa fad'a sai taji wani iri"gaba d'aya kewarsace ke damunta"tasan idan shine yakawosu skul saiya tursasata taci wani abu kuma saiya bata chacoolates da sweets ko biscuits.....wai dama kina nan inata nemanki muje muci i?"taji muryar nafeesa"d'ago kanta tayi ta kalleta tace"Azumin litinin nakeyi kuma kaina na ciwo"subahanallahi sannu"sady nata nemanki zakuyi mgn da yayanta farooq"nima mun gaisa da Abokinsa Abdul"ya nuna mun sona yakeyi"nasanar masa inada wanda zan Aura yayi hak'uri"harara In'am ta gallah mata tana fad'in wai wannan mugun yaya sulaiman d'in kike nufi?"wlh ya isheki karki koma ce masa mugu"nace mugu ki sanar masa mana"shi kuma wlh yafita harkata"karatu nazoyi ba shirme ba"nima dai Abinda nagani kenan"kuma kinsan halin yaya yasan da hakan wlh mun shiga ukku"kukan da In'am ke rik'ewa ta fashe dashi tana fad'in ai yanzun umma ta rabani dashi ta hanashi zuwa gidanmu nafeesa"bansan wace irin k'iyayya matar nan ke mana ba?"ta fad'a tana kuka tana sanar mata Abinda yafaru"da kuma warning d'in ummi Akanta..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! kiyi hak'uri In'am"nidai bbu wanda ya isa yaraba Abotarmu dake"yaya Aliyu kuwa ni kaina na kasa fassara Abinda ke tsakaninku"Amma komai daren dad'ewa komai zai bayyanah....bata kai Aya Azancen taba sady ta shigo Ajin tana kiran In'am"had'e rai tayi tana kallonta tace"nafee ta sanar mun komai kuma bazan jeba sbd karatu nazoyi nan ba shirme ba"dg haka tayi shiru"sady kuwa haushine sosai taji Abin yabata"sai batace komai ba tabar Ajin......
sannu Ahankali rayuwar ke tafiya"yaya Aliyu yadena zuwa part d'in ummi"idan sun had'u Awaje idan zata fita Anguwa ya gaisheta cikin jin nauyin Abinda umma tayi"ita kuma bata nuna masa komai zata Amsa"In'am kuwa kullum kan idonsa take tafiya skul da islamiya yana dg cikin mota me tinted"saidai yafi sati 1 rabon da yaganta ido da ido"to itama In'am d'in tana jin kewarsa Amma bata nunawa hidimar gabanta takeyi....gefe guda kuma safwaan yafara canzawa"wajen hawa manyan motoci da sakq manyan surutu"sannan yafara gidana tashi Asibitin"yayinda saiya gadama yake zuwa Asibitin dr Aliyu"shi kuma dr Aliyu yasan da haka Amma yabarsa"idan sun had'u saidai kawai Agaisa"dr Aliyu be mamakin yadda safwaan ke masa faran faran tamkar masoyinsane shi"saidai yabasar Awuce wajen.....duk Abinda ke wakana brr Ahmed da dr Aliyu suna saka ido sosai kan safwaan"yanzun haka dr Aliyu yakori dr salma dg Asibitin last 3 days....
Ayau yakama friday misalin k'arfe 10:35 am"dr Aliyu na zaune A office nashi yana duba patient"sanye yake da wani lallausan yadi brown colour Ajikinsa"kansa bbu hula yayi haske da kyau"saidai yayi y'ar rama"fuskarsa bbu walwala ko kad'an"Ahaka safwaan yaturo k'ofar yashigo cikin shan k'amshi yana yin sallama can k'asan mak'oshi"yaya Aliyu yabishi da kallo Acikin second 5"kafin ya maida kallonsa ga patient d'in dayake dubawa Anutse yace"kije pharmacy ki Amshi magani natura musu sunanki Acan....iya nan yayi shiru"ita kuma matar ta Amsa dato tana mik'ewa tsaye ta fita"safwaan yatab'e baki yana sakin wani shegen murmushi yace"koda bazaka tanka niba yaka mata ka Amsa sallamata! zare Eye glass d'in dake kan fuskarsa dr Aliyu yayi ya Ajiye yana fad'in meke take da kai?"me kuwa zai kawoni inba dalili me k'arfi ba?"sanin kankane bakada Abinda zan nema Awajenka me tubarau"dama nazone na sanar maka na Ajiye Aiki a Asibitin nan dg yau"na kuma yafe kud'in sati 2"sbd saura sati 2 Ayi Albashi..... murmushin gefen baki dr Aliyu yasaki"ya d'auki kusan second 10 kafin ya kalli safwaan ido cikin yace" gaskiya na maka murna daka Ajiye Aiki sbd kasamu hanyar datafi Aikin saurin samun kud'i"saidai wani hanzari ba gudu ba"Aliyu baya son yafiyar kowa sannan baya yafewa wanda yacucesa koda Ab'oye ne ya cucesan" batun kud'i kuma karka damu zan baka kud'in sati 2 koda sadaka ne kayi dashi"zancen banida Abinda zaka nema Awajena ai tsohon zance ne"tunda kazo ka nemi aiki an baka zancen neman Alfarma yak'are" Iya Abinda na sani zaki baya fitowa farauta saiya shirya"idan yafito kuma baya tak'ama da kowa sai k'arfinsa "domin dashine yake isa harya nemi na kansa Acikin jeji"baya zama sai yabada wani Abu sannan Abashi wani Abu dan Amfanin kansa......dr Aliyu nakai Aya Azancen sa yarab'a safwaan yanufi toilet cikin izzah da gadara"safwaan ya sauke numfashi sbd beda tacewa"jikinsa yayi bala'in yin sanyi da wa'annan maganganu na dr Aliyu me tubarau" masu kama da gugur zana da habaici"hankalinsa yakasu gida biyu"na farko kodai Aliyu me tubarau yasan yashiga k'ungiyar Asiri?"sannan yagano shine yasace masa kud'i million 4 da rabi sadda yana london??ganin bashida Amsar wannan tambayar kawai yafice dg cikin office d'in da sauri yana jin tsananin zafin dr Aliyu Azuciyarsa...

zaune mommy take A parlourn Abba.....
'?


wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

d'?=ؓ? SONE KO K'IYAYYA =ؓ?d'?

31&32


.........Zaune mommy take A parlourn Abba misalin k'arfe 8 na dare" kasancewar itace da girki"Abban na zaune Agefenta yana cin Abinci?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? suna fira"can yace"wai binta dama sulaiman nafeesa yakeso??kai Alh "ta fad'a tana d'an murmushi"kafin tace"kusan wata 3 kenan dana fahimci hakan nima"naji dad'i sosai sbd sulaiman yanada tarbiyya"wannan gsky ne in sha Allah da sunyi SSCE tunda yasami Aiki sai Ayi Auren "idan zai barta ta ida karatun Agidansa saita cigaba kawai"shi kuwa Aliyu bazan ma koma yi masa zancen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login