Showing 48001 words to 51000 words out of 88777 words

Chapter 17 - SO NE KO KIYAYYA COMPELET BOOK BY MAMAN FAREESA.doc

d'in Abincin yafita"yana A hanya yakoma kiran sulaiman"sai Akaci sa'a yagama wayar"bugu 3 ya d'auka cikin ladabi"sulaiman kana cikin gida ne?"Eh ina ciki rufewama zan sakq masu gadi suyi"okay kaje d'akin maryam ka dubamin ita tayi bacci ko Idonta biyu??"dato ya Amsa"shi kuma yakashe wayar yasaka key yabud'e k'ofar parlournsa yashiga....
sadda yaya sulaiman ya shiga d'akin in'am bacci takeyi harma ta kashe hasken d'akin"yana fitowa dg cikin d'akin yaya Aliyu na koma kiransa...kai yaya Aliyu na rasa wane irin SONE yakeyiwa yarinyar nan Aduniya?"yafad'a yana d'aukar wayar yasanar masa bacci takeyi"dg haka yaya Aliyun yakashe wayar"ummi dai na jin yaya sulaiman batace komaiba"ta fahimci k'ilan Aliyun kiran In'am yayi bata d'auka ba shine yaturo Aga tana lafiya"ita kanta yanzun Abin nasu yafara bata tsoro"ta fahimci kamar shak'uwarsu ta yanzun saima tafi ta da....
yaya Aliyu kuwa yasami nutsuwa da Aka sanar masa tayi bacci"Abincin ya cinye yanata murmushi"sannan ya wuce katafaren bed room d'insa"da k'aton pic nata dake d'akin ya had'a Ido"yasaki tattausan murmushi ya lumshe ido"yana tunanin ranar da Allah zai cika masa burunsa In'am ta zama tashi"yana wannan tunanin yarage kayan jikinsa yasaka kayan wanka yashige bathroom...
washe gari misalin k'arfe 7:28 am"In'am ce da nafeesa tsaye Ak'ofar gidan"kowace tana sanye da yunifoam Ajikinta"sai yaya sulaiman dake k'ok'arin bud'e driver sit yashiga"ya shirya cikin manyan kaya"sosai nafeesa taga yamata kyau"saidai tak'i yarda ta had'a ido dashi"tsaki yaja cikin daka tsawa yake kallon in'am yace"ke wai bakiji menace miki ba?"ko ummi batace miki nizan kaiku ba"ko kuwa ala dole sai yaya Aliyun ne zai kaiki??"kayi hak'uri dan Allah nide shine nakeso yakaini"yanzun zan kirashi....Afusace yaya sulaiman yanufeta da nufin ya mammareta"yayinda nafeesa na front sit zaune tana musu dariya......wani mahaukacin horn sukaji Abayansu! Atake k'irjin In'am yabuga"sbd ranta yabata yaya Aliyu ne"juyawa sukayi Atare suna kallon bayansu"Aikuwa hasashen nasu gaskiya ne"shine cikin had'add'iyar motarsa"Ahankali yabud'e k'ofar motar ya fito cikin nutsuwa"kasancewar yau Friday"ya shirya cikin farar sabuwar shadda"ya Aza hula k'ube"yafito sak A bakanon sa"ya dad'e da farin tubarau" yayi kyau har yagaji"saidai yau da Alama y'an miskilancin sun motsa"yana tafiyar cikin kasaita da shan k'amshi"fuskarsa Ad'aure"tun kafin ya iso mayen mayataccen k'amshin turarensa yarigashi isowa"yaya sulaiman ya harari in'am dake turo baki"itama ta d'aure fuska sbd yadda taga yaya Aliyu yanata wani shan k'amshi"zaki san kin b'atamun lokaci"yanzun befi saura 25 minit ku shiga paper ba"yafad'a yana kallon yaya Aliyu daya iso wajen sukayi musabuha"In'am kuwa k'in kallonsa tayi ta nufi motar yaya sulaiman zata shiga"kin fasa shiga motar yaya Aliyun ne?cewar yaya sulaiman" k'in mgn tayi ta bud'e k'ofar"yaya Aliyu ya saki d'an guntun murmushi ya matso gefenta bece komaiba saidai taji yakama hannunta"d'aure fuska tayi ta tsuke pink lips nata ta fara turjewa tak'i mgn"kuma tak'i yarda ta kallesa"yaya sulaiman yayi murmushi yana kallon su yabud'e motarsa ya shiga....kinga sulaiman d'in yatafi my Angel"ki hak'ura da wannan rigimar muje na saukeki karki makara"kinsan dai bazaki iya k'watar kanki A wajena ba ko?"yafad'a Ahankali cikin taushin muryanshi yana binta da wani irin mayen kallo yana tsotsar lip nasa na k'asa....ni baran bikaba ka cikani mun b'ata dakai! Akanme my Angel?"yafad'a yana wani marairaice murya kamar wani k'aramin yaro"In'am ta saci kallonsa suka had'a ido"murmushi yasub'uce mata sbd Abinda taga yayi....yes Afad'amun saina dena ko my Angel?"kinga be kamata kiyi fushi da babban Amininki ba"kuma Allah koki yarda mu tafi kona d'aukeki da hannuna tunda kinaso kiyi latti"batayi mgn saidai tadena k'ok'arin k'wace hannun"tana lura da Auwal da mahmood na kallonsu dg can wajen me d'an kes suna mgn k'asa k'asa"ta gallah musu hara sadda yabud'e gidan gaba yasakata"sai bayan yaja motar Ahankali tace"ina kwana?"kin tashi lafiya my Angel?"Alhamdllh! ta fad'a Atak'aice"I'm sorry kinji tawan?"yafad'a murya can k'asa"wanda saida In'am taji kasala"cikin muryar shagwab'a tace"yanzun ka kyauta yaya Aliyu Abinda kayimun jiya?dukda bansan ko kanada uzuri ba"kuma da safe naga miss call naka ai"kai my Angel maimakon ki kira kiji yaya Amininki ya kwana ko?"shiru tayi tak'i mgn...nufashi yasaki kafin yace"jiya bayan sallar magrib Asibiti naje sbd Ammun kiran gaggawa "Amma kina A raina babbar k'awata"d'an murmushi tayi batayi mgn ba"koba haka bane?"eh mana"kai my Angel Ai nabada uzuri ko?"yaka mata ki sassauta mun"shiru tayi kanta Ak'asa tana mamakin yadda yake mata yanzun bbu d'aure fuska balle tsawa....kumafa naci Abincin dakika bama Auwal yakai A Ajiyemun"tattausan muryanshi ta katse mata tunani"ta saci kallonsa"Aranta tace"masha Allah ko wane dressing saima masa kyau"my Angel! na'am"kice wani Abu mana pls"nifa ban hak'ura ba"meyasa?" bakai bane ka fito kanata wani d'aure fuska fisabilillahi"kuma dai kasan Ai bbu y'ar haka tsakanin Amini da Amini ko Aboki da Aboki ko?"my Angel! yaka mata Ace kece kika fi kowa sanin halina"yawan mgn ko fara'a be dameniba kin sani"sai idan ina tare dake ko kuma ina tare dasu Ahmed"ko Abaya time d'in kina k'arama dake kad'ai nake wasa har nayi fara'a" yaka mata kimun uzuri idan kin ganni haka"to Amma Aika ganni kuma baka saki fuska ba"dg yau nadena my Angel"kinga d'azun danaga sulaiman yanufeki k'ilan dokarmun ke zaiyi ko?"Eh wai sbd nace nidai kaine zaka kaini skul"ki rabu dashi bazaiyi gangancin dukarmun keba"y'ar dariya tayi tace"yaya wane irin wasa ne mukeyi Abaya?....cikin wata iriyar murya yace"kinaso yanzun mudingayin irinsa?"jikinta Amace tace"uhmm"Adaidai lokacin da yayi parking"wanda befi saura 8 minit su shiga paper d'in ba"yaya Aliyu na gode bara natafi kar na makara"my Angel! yakira sunanta"batare data kallesaba ta Amsa da na'am"kinyi break fast d'in?"ah ah"saina dawo sbd kaga zuwa 11 :30 am mun gama dama guda 2 ce zamuyi"okay zan dawo na d'aukeku kinji ko?"to shikenan"ta fad'a tana d'an murmushi"to bakice kin hak'ura ko?"kallon kyakykyawar fuskarsa tayi takama dariya"tana fad'in kai yaya sai kadinga yin Abu kamar d'an yaro"ai na hak'ura tuni ko?"yauwa my Aminiyas"tayi murmushi tana cewa"Allah yatsare hanya"ya Amsa cikin jin dad'i yana kallonta ta shige cikin get d'in makarantar"ya lumshe manyan idanuwansa yana sakin Ajiyar zuciya"saima sannan yatuna be bata tsarabar daya mataba a k'asar chairo"kuma ledar daya saka kayan na'a back sit a Ajiye"juya Akalar motar yayi zuwa Asibiti......
cikin nishad'i in'am tayi paper"koda suka fito break bataci komai ba"tanata game Awayarta"sai k'arfe 10 suka koma shiga wata paper d'in"wajen k'arfe 11:25 am ta fito"ta zauna Awani block tana jiran fitowar nafeesa"bbu jumawa itama ta fito"Atare suka fito dg cikin get.....Allah sarki yaya Aliyu harma yazo d'aukar mu kenan?"cewar In'am data hango motarsa fake"hmm! yanzun kina bani mamaki In'am?"name fa?"Ada kin tsani yaya Aliyu kina masa kallon mug....kinga Adena wannan maganar nafee"ko kuwa nasanar masa"harara ta gallah mata tana fad'in ki sanya niya"in'am na k'ok'arin mgn ta hango motar farooq yana k'ok'arin yin parking"hakan yayi daidai da fitowar yaya Aliyu dg cikin motar"suka had'a ido da in'am"yasakar mata wani irin killer smile "tayi k'asa da kanta tana maida masa da murmushin"ta nufesa tana fad'in yaya ka dawo?"nadawo my Angel ya paper d'in??"Alhamdllh bbu wata matsala"okay kuzo muje"ko kuwa waccan magulmaciyar sulaiman d'in take jira?? yafad'a yana kallon nafeesa dake tsaye nesa dasu bama tajin me suke cewa"In'am dai murmushi tayi ta shiga ciki ta zauna"shima yaya Aliyu yaza gayo ya shigo"nafeesa ma haka.....farooq dake tsaye yana kallon komai"ransa yab'aci matuk'a"wato shine take takawa yadda ta gadama tazo tana washema wani baki"wanda bbu Abinda suka had'a dashi sai zaman unguwa"kasancewar sady ta sanar masa dangantar nafeesa da In'am da kuma yadda yayan nafeesa ke bama in'am kulawa"sosai yaji zafin yaya Aliyu da kishinsa"saidai ransa yabashi bason juna sukeyi da in'am ba"idan yana sonta Aida tuni An saka musu rana"da wannan tunanin yashige mota yabi bayansu.....
Tunda suka hau samqn titi bbu me mgn Acikinsu"jefi jefi yaya Aliyu na kallonta"Amma beyin mgn sbd yaga basu kad'ai bane Acikin motar...suna isowa layin yayi horn bakin get d'in gidansu" Aka bud'e musu get suka shiga"yana gama parking nafeesa ta fice"sai Asannan ya kalli in'am murya can k'asa yace"my Angel ga tsarabarki nan gefenki ki d'auka kije dashi "tunda baza'a cemun yaya Aliyu ina tsarabar tafiyar ba??"uhmm! kamar na baka Ajiya yaya Aliyu?"kin wuce batun y'ar kunya ko jin nauyi Awajena maryam"hakane yaya Aliyu nasani nagode da kulawa dani da kakeyi da yimun hidima me yawa"dan Allah ka rage sbd ummi saita tayi fad'a idan taga kayan nan "yanata kallonta"Ahankali kamar beson mgn yace" tashi kije ki canza kaya kizo muyi break fast ina part d'in mommy"dg haka yafara k'ok'arin fita dg cikin motar"itama batace komaiba ta fito tana turo baki"hannunta rik'e da jakarta da babbar ledar daya bata kayan tsaraba Aciki"ko nazo na rakaki ne my Angel? yafad'a yana tsaye Abayanta" nok'e kafard'arta tayi batare data ce komai ba tayi gaba"ya girgiza kansa ya zauna samqn motar yana danna waya"sbd yafiso yajirata su wuce ciki A tare"danma umma ta hanashi shiga gidansu Aida rakata zaiyi ma....
In'am na fitowa dg gidan gabanta yayi mugun fad'uwa sbd Arba datayi da farooq yana zaune samqn motarsa"yaci wankan k'ananun kaya yana girgiza k'afafuwansa"fuskarsa bbu walwala"kallo d'aya ta masa ta d'auke kanta tana mamakin meya kawosa k'ofar gidansu? bayan tunda take dashi be tab'a zuwa ba"in bacin bbu kyau wulak'anci"dako kallo be ishetaba"Amma datayi wannan tunanin kuma matsayinsa na bak'onta saita masa sallama"yana yatsina fuska ya Amsa ciki ciki"dan Allah bara na shiga nakai kayan nan ciki saina dawo muyi mgn"ta fad'a batare data kallesaba"okay kawai ya fad'a yana dirowa dg samqn motar"ita kuma ta wuce cikin gida....kimanin shud'ewar mintina 10 "In'am ta fito da dogon hijab har k'asa Ajikinta"wanda tayi matuk'ar yimata kyau"farooq na tsaye yana niyar tafiya sbd Azatonsa bazata fitoba"yana ganinta ya tab'e baki yana fad'in nazata bazaki dawo ba In'am?"ni kuwa meye zai sakq nak'i dawowa?"nasan kodan sbd wancan doctor Aliyu yake ko waye zaki k'i dawowa?"kin bani mamaki maryam"idan bakya sona sanarmun yaka mata kiyi bawai ki dinga jana ak'asa ba"tun jiya nake kiranki kika mun banza why??"duk Abin be kai hakaba bana kusa da waya duk jiya sbd ina karatun exams"Allah ko?"to yanzun wane matsayi kika Ajiyeni Azuciyarki?"gara nasani tun kafin sonki yayi Ajalina beauty"bakya sakarmun fuska"Amma Abin mamaki d'azun kina washema wani banza hak'ora! waye shi,me kuka had'a dashi dayake wata isa dake"bayan bbu dangin iya balle na baba da kuka had'a dashi???.....ran In'am Ab'ace ta d'aga hannunta cikin rufewar ido ta d'auke farooq da wani irin lafiyayyen mari.....wanda hakan yafaru A kan idon yaya Aliyu daya turo get zai fito "sbd yaje ydubata yaji shiru bata dawo ba"cikin tsananin b'acin rai da.......
'?

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

d'?=ؓ? SONE KO K'IYAYYA =ؓ?d'?

43&44


........Cikin tsananin b'acin rai da fusata In'am ke nuna Farooq da yatsa tana fad'in i hate you farooq! waye kai mekake tak'ama dashi da zakazo kamun irin wannan cin fuskar har k'ofar gidanmu?? kasan waye shi Awajena,kasan matsayin dayake dashi Aguna ?? Daka zagesa gara Ace nice ka zaga dan bazan maka komai ba"Amma yanzun ko ganinka bana sonyi"ka d'auki duk matakin dakake ganin zaka iya d'auka sbd na mareka"ta fad'a hawaye masu zafi na wanke mata fuska....ta cigaba da cewa"bansan meyasa da yawan mutane suke yima Alak'ata da yaya Aliyu kallon k'aramin Abu ba?"koma miye ina ruwan wani damu? kafita dg rayuwata farooq tun kafin yaya Aliyu yayi maganinka"domin zai i ya....shiru tayi sbd lura datayi yaya Aliyu na nufosu fuskarsa tamkar hadarin gabas"sbd tsabar yadda ya had'eta bbu Annuri ko kad'an "farooq na tsaye kamar An dasashi Awajen yana dafe da kuncinsa"zuciyarsa na k'una sbd b'acin ran Abinda in'am ta masa"ni kika mara In'am??"yafad'a Afusace yana kallonta da idanuwansa da sukayi jajir yana "kasa mgn tayi ta d'auke kanta tana sakin shashshekar kuka.....yaya Aliyu yatsaya dab da ita har tana jin hucin numfashinsa"fuskarsa bbu Alamar rahama yake bin farooq da wani irin mugun k'ask'antaccen kallo"wanda Atake Farooq yaji mugun shakkarsa"cikin dakakkiyar muryarsa me bama marar jin mgn tsoro yace"waye kai?"miye dalilinka na zuwa nan har kayi sanadin zubar hawayen ta?? yafad'a yana tun karo farooq"yana jin wani irin bak'in kishi na taso masa"k'asan zuciyarsa yana jin sanyi da dad'in kalaman In'am data nuna yanada daraja wajenta"yafahimci yanxun yanada matsayi me girma A wajenta...da sauri In'am ta rik'e hannunsa guda murya na rawa tace"ka barsa yaya Aliyu pls! No my Angel ki barsa naji idan wata rashin kunya yakeji da ita... tab'e baki farooq yayi yana bud'e k'ofar motar sa ya kalli yaya Aliyu yana fad'in sanina bazai Amfaneka da komai ba"ke kuma ki rubuta ki Ajiye wallahil Azim sai kinsan kin d'aga hannu kina mace kin mareni"yana fad'in hakan yayi k'ok'arin shiga cikin motar"yaya Aliyu na huci ya fisge hannunsa dg cikin na In'am ya finciko farooq.... wata wawar chakuma yamasa yana huci cikin zafin rai yace"ka isa kazo har nan kayi sanadin zubar hawayenta ka tafi salin Alin??"idan kana zaton hawayenta dakayi sanadin zuba kaci bulus kayi kuskure...subahanallahi! meke faruwa haka Aliyu??"cewar Alh d'ahiru Abayansu (k'anin mahaifin In'am)"cika farooq daketa son fisge hannunsa yaya Aliyu yayi"yana binsa da wani irin kallo cikin kakkausar murya yace"ka guji had'uwarmu dakai Alokaci na gaba"dan ta haka ne kawai zanyi maganin rashin kunyar taka ta cikin cokali"yafad'a cikin izzah yana hura hanci"yayinda In'am ke share hawayenta ta shige cikin gidan da sauri"yaya Aliyu yayi k'asa da kansa yana fad'in Abba sannu da zuwa!... farooq kuwa ya shige mota yabaza k'ura Awajen yayi gaba.... Aliyu Adinga hak'uri da kai zuciya nesa dan Allah"wannan ai yaro ne k'arami bama sa'anka bane ga yadda naga idonuwansa"hakane Abba ina wuni??"lafiya qlau Alhamdllh"ina Alh (Abba) kwana2 mun rabu da gaisawa"yana nan lafiya qlau yana kasuwa "to masha Allah"dg haka Alh d'ahiru ya tura k'ofar get d'in gidansu In'am yashige ciki"yana k'ok'arin shiga cikin parlourn gidan in'am ta fito"gaidashi tayi ta wuce"shima dama kwana 2 yarabu da zuwa yaga family d'in d'an uwan nasa"suma kwana kuma 2 basu lek'a suba"shine yau yalek'o su Ayi zumunci.... In'am cikin nutsuwa ta fito k'ofar gidan"ta sami yaya Aliyu tsaye jikin bangon gidan yana waya da brr Ahmed"tsayawa tayi gefensa tayi k'asa da kanta tana tunanin itada farooq har Abada"tasan insha Allah tunda yaya Aliyu na nan be isa yacutar da itaba.....my Angel shine kika tafi kika barni ko?"taji Amon tattausan muryanshi Abayanta"Ayya yaya Aliyu wajenka fa zanje dana fito yanzun sai kuma na ganka"ta fad'a cikin shagwab'a batare data kallesaba"lumshe ido yayi sbd jin tsikar jikinsa na tashi sakamakon jin muryarta"murya can k'asa yamatso dab da ita yana cewa"wannan yaron shine farooq?"Eh shine"meyasa kika maresa my Angel?"ina ganin fad'anki yayi sauk'i Ashe baki dena ba?duk yafad'a yanata kallonta"kanta Ak'asa tace"laifinsane yaya Aliyu"kuma ni yanzun bbu ruwana dashi nama goge number d'insa bayan nayi blocking"duk wanda zai fad'i magana marar dad'i Akanka koya nuna jin zafinsa Agareka! banida mak'iyin daya wucesa Aduniya yaya Aliyu"bansan meyasa da yawan wasu mutane sukeyima zumuncinmu kallon ba zumuci bane kare kare ne??.....ajiyar zuciya yasaki domin kalamanta ba k'aramin dad'i da kwantar masa da hankali sukayiba"cikin taushin murya yace"dama haka nake da irin wannan matsayin Awajen Aminiya ta?"tana d'an murmushi kanta ak'asa tace"kaa wuce haka yaya Aliyu" hakane my Angel"idan munga hakan saimu share komu d'auki matakin dayake daidai"iya Abinda nasani ban damu da rayuwar kowaba balle har na zauna nayi tunanin ya wane ke rayuwa"dama yana zuwa wajenki?"ah ah be tab'a zuwaba sai yau"kawai dai skul yake zuwa idan zai d'auki k'anwarsa"shiru yayi yana nazari"sbd bejin zai iya barin yaron hakanan tunda har yayi sanadin zubar hawayen ta"karki koma kuka sbd wani banza dg yau kina jina?"yabani haushine yaya shiyasa"bana son ganin kukanki my Angel"yanzun yaushe zaku gama paper d'in?"saura 5days fa yaya"ranar Wednesday in sha Allah zamuyi final"d'an murmushi yayi yace" Allah yakaimu lafiya"saidai baza kuyi wasu bidi'oi ba"batace komaiba tayi shiru"muje my Angel Asibiti nakeso na koma dg can zan tafi masallaci"yak'are maganar yana k'ok'arin kama hannunta"tayi saurin b'oye hannun nata tana murmushi"yatab'e baki yayi gaba ta biyosa Abaya"parlourn mommyn yanufa"yasami ta shirya masa komai kan carpet"nafeesa na zaune a parlourn tana chats"kallonta yayi yace"ina mommy?"bacci ta kwanta"okay yafad'a ya zauna"In'am ta shigo da sallama"suka had'a ido da nafeesa"ta gallah mata harara"ita kuma tayi murmushi ta tashi tsaye tabar parlourn"satar kallon sa tayi yana danna waya"wai yaya Aliyu koda yaushe kana latsa waya dan Allah?"beyi mgn ba yadai d'ago kansa ya kalleta yaga tayi k'asa da kanta"d'an murmushi yasaki yana tunanin tunbe furtaba yafahimci tana jin kunyarsa inaga yafurta to??.....yaya mezan zuba maka kaci? ta katse masa tunani"Aransa yace"my Angel tayi hankali kenan?"be gama wannan tunanin ba ya ganta tsugunne tana duba komai cikin nutsuwa ta fara seving nashi"shidai yana binta da kallon k'asan ido"tamkar hankalinsa ba'a wajenta yakeba"bayan ta zuba masa komai ta tura masa gabansa"ita kuma ta zuba kunun gyad'a cup guda da chips rabin plate"batare data zuba farfesun kayan cikin sanuwa ba.....yaya pls bissimilah! kallon komai yayi ya kalli na gabanta"d'aure fuska yayi yana kallon ta"tayi k'asa da kanta Ahankali tace"dan Allah wannan ya isheni yanzun"kasan banacin Abinci da yawa "kuma yajin danaga baka so shima bana ci sai idan yazama dolene nakeci kuma kad'an nake ci.... shikenan my Angel"Amma kinsan inaso ki zama y'ar lukuta kina gudu da k'yar"dana biyoki sainayi saurin kamaki ko?"Amma ke baki son cin Abinci"kai yaya sbd kamun mugunta shiyasa kakeso nayi jiki?"ta fad'a tana fara kurban kunun Akunyace"shima yana murmushi yayi Bismillah yafara cin Abincin"Ahaka seif yaturo k'ofar yasamesu"gaida yaya Aliyu yayi"in'am ta gaidashi yashiga kitchen"Aransa yace"dama nasan sonta yakeyi shiyasa ya hanani kulata"da wannan tunanin ya d'akko ruwa da lemo a fridge yafita"In'am kuwa cin yanga takeyi"harma yaya Aliyu yagama sannan ta idar"da kanta ta kwashe kayan ta mayar kitchen"ta dawo parlourn tayi tsaye"zoki zauna mana"yaya gida zan tafi kar ummi ta nemeni"shiru yayi bece komaiba"yaya ! Yes"yafad'a yana k'ok'arin sqka k'wayar idonsa Acikin nata"ita kuma tak'i yarda"tanata kallon k'asa"shikenan kije kibar Amininki da kewarki"idan natafi masjeed wace Addu'a zan yimana??"duk wacce ta dace damu mana"shikenan kingama mgn"yafad'a yana danna waya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login