Showing 84001 words to 87000 words out of 88777 words

Chapter 29 - SO NE KO KIYAYYA COMPELET BOOK BY MAMAN FAREESA.doc

tasaki ihu zata gudu ya fincikota"ta fad'o Ajikinsa ya murgina yana hayewa saman ta....tana k'ok'arin mgn yahad'e bakinsu Awaje guda..... Awannan dare In'am taji jiki hannun yaya Aliyu"saida yasamu nutsuwa sosai da ita sannan yasahir ta mata sukayi wanka suka kwanta...washe gari suna gama sallar Asuba ya d'ora dg Inda yatsaya"ba k'aramin galabaita In'am tayi ba"Amma ta daure sosai"sai bayan yasami nutsuwa ya fahimci taji jiki"yafara rarrashinta sannan da kansa yamata wanka ya shiryata" shima yayi"sai wajen k'arfe 7:35 am suka fito cikin parlourn"dr Aliyu na sanye da suit dark blue"In'am kuma ta shirya cikin sabuwar dubai Abaya brown colour"batayi make up ba"kwalline kawai da powder yaya Aliyu yashafa mata"Ahankali yace"my Angel muje na rakaki dining Area d'in ki zauna saina d'akko warmers d'in muyi break fast d'in"ah ah yaya muje natayaka d'akkowa"keda bakida lafiya?"nifa lafiyata qlau"wajen yadena zafin?"uhmm kawai ta furta batare data kallesaba"bece komaiba suka shiga cikin kitchen d'in"yaya Aliyu muyi break fast d'in nan kawai"tafad'a tana kallon yadda kukun ya jera komai samqn dining table d'in dake cikin kitchen d'in"to shikenan cewar yaya Aliyu yakama hannunta suka zauna"itace ta zuba musu komai suka fara break fast d'in"wanda In'am daurewa kawai takeyi Amma jikin nata sai Ahankali"bayan sun gama suka fito dg ciki tana fad'in sai mun dawo su Atika sunyi Aikinsu"okay yafad'a ya rufe k'ofar da key suka nufi parking lot"In'am tasaka rigimar itace zatayi driving d'in"bece komaiba yabarta sbd beson tana buk'atar abu ya hanata"sunata firansu suka iso Asibitin"sai sannan tama lura da sunan Asibitin" A& M INTERNATIONAL HOSPITAL"my Lion?"na'am babyn baby"murmushi tasaki har fararen jerarrun hakoranta suka bayyana"pls meye ma'anar A&M"harara ya gallah mata yana fad'in kinfini sani"yafad'a suna fitowa dg cikin motar"ya rik'e hannun ta guda"hannunsa guda kuma ya rik'e hand bag nata"b'ata fuska tayi tana fad'in idan nagane suna nufin ALIYU & MARYAM"dama kinsani kika tambaya?"sai kuma yayi dariya yana fad'in wayyo Allah ummih kizo kice yadena mun"wayyo zan tsaya zafi ke Akwai....fisge hannunta In'am ke k'ok'arin yi tana b'ata fuska"yakama dariya ya rik'eta"dama kana jin rok'on danake maka Amma saika shareni bbu komai??"sorry my Angel inaji Amma bana iya Assala komai"bazaki fahimci dad'in Abin ba sai kindena jin zafi"sauk'ina da Allah yasa kika dena cin yaji"shiru tayi tak'i mgn"yayi lock d'in motar suka wuce ciki yanata tsokanarta"ta kwantar da kanta Ajikinsa ya rungumeta suka nufi office nashi"office d'in k'al Agyare fes yake"yaya Aliyu yace"zauna minti 15 zan dawo my Angel"dato ta Amsa ta zauna shi kuma yafita"In'am ta tashi ta d'akko drinks cikin fridge tanasha tana chats da friends nata agrp"kimanin mintina 20 yaya Aliyu ya dawo cikin office d'in"d'an murmushi yayi yana fad'in ranki yadad'e mrs Aliyu me tubarau"tana dariya tace"pls yaya kadinga sawa yana k'ara maka kyau wlh"shikenan Angama my princess"yafad'a yana jawo wata loka ya d'akko bak'in glass"saida yagoge sannan yasaka" kafin ya zauna yana danna laptop suna fira da in'am"dg bisani yafara duba patient"sai wajen k'arfe 1 yadakata da duba patient yaje yayi sallah"In'am tayi tata Anan office d'in"bayan yadawo suka nufi gida.....

***********
Kwanci tashi Asaran me rai"rayuwa tayi dad'i ta kuma lula" dukda wata ran Ana samun sab'ani"ummi dai sunyi Aurensu da Alh musa"An kuma saka ranar auren yaya seif da sady,yesmeen da yaya mukhtar"yayinda matar yaya isma'il keta laulayi"dan yanzun watansu na biyu kenan da Aure"su in'am sarakan soyayya"basuda Aiki sai zuba love"tuni tafara zuwa skul of nursing"wani time d'in tare suke fita da yaya Aliyu wani lokacin kuma yarigata fita"sosai In'am ta k'ara haske da k'iba"yanzun ta zama y'ar hannu dagewa takeyi tana faranta ran yaya Aliyu sosai.....Ayau tun wajen 2:30 pm ta dawo gidan"tayi wanka ta shirya cikin k'ananun kaya ta shiga kitchen"komai ta d'akko ta jera dining area"saidai koda ta duba Abincin taji be mataba"tarasa meyasa Acikin kwana 2 nan ba kowane Abinci ke burgetaba"ga yau saiji takeyi zuciyarta na tashi"tana nan zaune parlourn su Atika suka shigo"bayan sun gama gaisawa suka fara Aikinsu"In'am kuwa wayarta ta d'auka da nufin ko text message ta turama yaya Aliyu sai taga text message nashi"tayi d'an murmushi tana fad'in Allah sarki my Lion"duk yau kana raina wlh"ta fad'a tana karanta message d'in tayi murmushi kawai"saida taga lokacin sallar la'asar yayi sanann tabar parlourn taje tayi sallah"ganin kar yunwa tayi mata illah yasaka ta d'akko fresh milk ta zuba cup 2 tasha"bayan ta gama ta sallami su Atika suka tafi"kwanciya tayi samqn 3 seeter"bbu jumawa bacci yayi Awon gaba da ita..... k'arfe 4:15 me tubarau ya shigo cikin parlourn"yasha gayunsa tamkar d'an saurayi yanata k'amshi "yatsurama In'am dake kwance ido yana binta da kallo har ya iso gefen kujerar datake kwance" ya Ajiye ledojin hannunsa"ya shafi fuskarta"ta bud'e idanuwanta suka sark'e da nashi idon"Ahankali ta motsa lips nata tana fad'in my Lion kadawo ??"beyi mgn ba sai hannunta guda yakama yana duba yatsun hannunta"sannan yatale mata ido guda"kafin yatayar da ita zaune ya zuge mata zif d'in rigarta ta baya "da mamaki In'am ke kallonsa batayi mgn ba dai"breath nata guda yafiddo yaduba kan napple d'in"girgiza kansa yayi yana fad'in tunda kikazo gidan nan bakiyi period ba ko?"yak'are maganar yana mayar maya da zif d'in riga"Eh banyiba menene wai yaya?"beyi mgn ba sai shafa gashin kanta yayi ya janyota jikinsa yana fad'in meyasa baki ci Abinci ba?"k'ok'arin mgn takeyi taji Amai nataso mata"Aguje ta nufi cikin toilet d'in dake parlourn"yaya Aliyu ya mik'e tsaye gabansa na fad'uwa yabiyo ta"domin zarginsa ya tabbata"In'am ciki ne da ita"beso ta haihu yanzun sbd yana ganin tayi k'aranta da haihuwa"yana kuma zargin bore zata masa idan ta gane tanada ciki"saidai yaji dad'in kyautar da Allah ya musu"shigowa yayi ya d'agota ya taimaka mata ta wanke bakinta suka fito"dama baki lafiya??bansan meke damuna ba yaya kamar dg jiya zuwa yau"Abincin da Aka dafa bemun ba"ni taliya da manja da yaji nakeso y'ar hausa"ita kawai kikeso?"Eh ita kuma yanzun nidai...ta fad'a cikin shagwab'a"sorry zan kira umma ta dafa mahmood ko Abdul hakeem wani yakawo"zoki kwanta"to yaya kadubani saika gane meke damuna ko?"to fad'amun meke damunki?"yafad'a yana zaunar da ita Ajikinsa"ya shafi wuyanta yaji da zafi"kafara sanarmun meka gani daka dubamin abuna mana"dariya yayi yace"juna biyu nagani kina dasu....ihun murna tayi ta rungumesa"wanda yaya Aliyu yayi bala'in mamaki"be gama wannan tunanin ba yaji tace"wlh dama yaya nayi zaton shine dakace banyi period ba tunda nazo"Allah yasa na haifi baby girl"Ameen my Angel"da duk naji wani iri karkice bakyason baby nah"inafa so yaya"ta fad'a tana rufe fuskarta wai kunya"su my Angel An kusan zama uwa ko? to yaya kamar haihuwar da wahala sbd naga Anty tasleem da zata haihu duk yaya Ahmed yadamu"karki damu my Angel C's zqn sakq Amiki A london bazan bari kisha wannan wahalar haihuwar ba gsky"to yaya Allah dai ya inganta mana"Ameen yah Allah"Amma dole ki rage guje guje da shan Abu me sanyi"to dukfa zan kiyaye"bance kisanarwa nafeesa ba da kowa ma"da mamaki tace meyasa yaya?"sbd banaso su sani"Amma kuma yaya Abin farin ciki ne idan nasanarwa nafeesa ita kad'ai laifi ne?"d'aure fuska yayi yace"okay sanar mata zakiyi kenan?"kayi hak'uri ba nufinah kenan ba"saidai naga Alamar kamar baka son cikin ko?"bansani ba"yafad'a fuska Ad'aure"In'am batace komaiba ta janye jikinta dg kusa dashi ta koma kan 2seeter ta kwanta"hawaye na zubo mata ranta na bata tabbas yaya Aliyu beson cikin shine zaice karta sanarwa kowa"k'ilan ma salwantar mata da cikin zaiyi tunda likita ne ,shine zai mata dubara wai karta sanarwa kowa"yaya Aliyu kuwa ransa ya sosu da Abinda tayi sai yaga kamar laifinsane dayake bari tana yadda takeso shiyasa take neman rainashi"tsaki yaja ya mik'e tsaye ya nufi upstairs"zuciyarsa bbu dad'i yatashi ya shiga wanka"bayan ya fito ya shirya cikin wando 3 quarter black da farar t shirt" sakkowa down stairs d'in yayi yasamu In'am bata cikin parlourn"saima sannan yatuna datace taliya takeso"saiya tuna daya sanarwa umma adafa zatayi zaton ciki ne"shi kuma yana jin nauyi"tashi tsaye yayi dukda yana jin haushin Abinda ta masa haka yanufi cikin kitchen Inda yaji motsinta"samunta yayi zaune kan kujera gaban dining table" taliya ce super getting da manja"sai yajin jego gefe da lemo fanta tanaci"tana ganinsa ta had'e rai ko kallo be isheta ba"Afasa Amso waccan da kikace kinaso?banza ta masa tak'i mgn"Atsawace yace"bakyaji ne?"yafad'a yana k'ok'arin isowa gefenta"kuka ta fashe dashi tana fad'in sbd dan baka son cikin shine zaka wulakan tani"wata biyu duka shine zaka nunamun halin maza?"bbu komai zan nemi mafita"tana fad'in hakan ta cire hannunta dg cikin Abincin ta nufi wajen sink tana wankewa"shi kuma zak'in fama yayi tsaye yak'i mgn fuskar nan ya daureta...wlh kika fita ina miki mgn saikin sani"yaushe kika rainani har haka maryam??"sbd ina miki gata shine kike Abinda kika gadama"idan nace karki sanar shine zaisaka ki d'auka bana son cikin?"lallai maryam har yanzun bakisan wane irin matsayi kike dashi Azuciyar Aliyu ba"sbd gudun karki damu yasaka nayi zaton b'oye miki"to bari kiji bazan lamunci kina mun musu ba"zakizo kibani hak'uri ko kuwa??"tana tsaye tana share hawayenta ta iso gefensa kanta ak'asa ta duk'a tace"kayi hak'uri dan Allah bazan koma ba"shikenan"Abinda yace"ya matso ya kama hannunta suka fito dg cikin kitchen d'in"d'akina zanje ni"su wa'annan ledojin tsarabar taki waye kika barmawa??"ni banaso ka cikani tunda dai na baka hak'uri"kuma Allah yasan ni bbu laifin danayi kanata mun tsawa ko?"ta k'are maganar tana gartsa masa cizo me rai da lafiya ga hannu"Amma yak'i cikata saima murmushi yasaki yana fad'in bara na d'auka na kira budurwata tazo ita na bata"ina ruwana da wacce zaka bamawa?"iyaka yarinya ta shigomun gida na fashe mata baki"bece komaiba yajata tana turjewa suka zauna kan kujera ya rungumeta yana fad'in Im sorry Ai kece budurwar tawa ko?"banji dad'in Abinda yafaruba"komai nace banaso kidena"karki koma cewa zan nuna miki halin maza"Amma yaya koma miye Ai Ahankali zakabi kamun bayani yadda zan fahimta ko?"shikenan Adena zancen"ina son cikin sosai wlh"dani dashi wakafi so?"hancinta yaja yace"wa nariga samu?"d'an murmushi tayi duk Idonta yayi jaa"kinga kinyi kuka sbd dad'i yamiki yawa ko?"shiru tayi tak'i mgn tajawo ledar tafara dubawa"kilishine sabo dasu chacoolate masu tsadar gske"godiya ta masa tafara ci"yanata kallonta yayi shiru yana tuna ikon Allah"sunyi fad'a sun shirya kansu kuma"yaya tashi muje kaci Abinci"dato ya Amsa suka wuce dining area d'in....

Haka rayuwar taci gaba da wakana"wata ran da dad'i"wata ran Akasin hakan"In'am tun bbu wanda yasan tanada ciki har kowa ya farga"kuma kusan wata guda suke haihuwa da matar yaya isma'il"nafeesa kuwa sai dg baya ta fara laulayin nata"gaba d'aya iyayen suna cikin farin ciki dajin dad'i k'aruwar da suka samu"yayinda hjy yau lafiya gobe babu haka dai ake..... In'am kuwa cikin saurin fushi yasaka mata da gudun yaya Aliyu"sai yajima be Amshi hakk'insaba"saida rarrashi yake biyan bukatarsa da ita"idan kuma tayi fushi ya rarrashi kayarsa"tun cikin nada 5 month yafara yimata Awo"skul kuma tana zuwa bata fasaba...zubaida kuwa tana gidan hamza bbu laifi hankalinta ya d'an kwanta"kuma maneman idan sun fito bata kulasu sbd tasan ko Anfara zancen Aure sukaji labari zasu gudu"duk idan ta tuna mama gaje ta kashe mahaifinsu sbd tayi dukiya sai tayi kuka kamar ta mutu.....
Ayau yakama juma'atu babbar rana"tun bayan Antashi dg masjeed yaya Aliyu yadawo gidan yake tare da In'am"tana bashi hadin kai sbd yana tausaya mata saiya jima be buk'aci hakk'insa ba"Amma yau yakasa jurewa"gashi cikin yashiga watan haihuwa"shirye shiryen tafiya sukeyi ma london ta haihu can"be kuma sanarwa kowa cs zai sakq Amata ba.....sai Ana ta sallame sallar la'asar sannan yaya Aliyu yabarta"tayi dai kwance itace kawai tasan metakeji"ga gajiya ga cikin nata juyawa ga ciwon mara"haka dai ta d'aure da taimakonsa tayi wanka da sallah"suna zaune bayan sun idar da sallar yaya Aliyu yadubeta yana fad'in muje parlourn na busar miki da gashin" sai muje can lambu kiyi tafiyar ko mintina 30 ne kinyi exercise d'in"girgiza kanta tayi tace"Abarshi yaya bana jin dad'in jikin nawa"gaban yaya Aliyu ya fad'i yace"kodai Abinda mukayi yanzun yasaka natado miki wani ciwo??"girgiza kanta tayi"pls my Angel sanar mun mekikeji kinjiko?"batayi musu ba tasanar masa"wajen ward rope yanufa ya d'akko mata hijab yasa kata mata yace"muje Asibiti nadubaki"bana zaton haihuwa ce sbd saura 2weeks edd naki yacika kuma wasu har wucewa sunayi"kasancewar ko kayan baby dg waje yayi order yaturasu can landon sbd yagane mace zasu Haifa"Amma be sanarwa In'am ba"yana rik'e da hannun ta suka iso parking lot"ya bud'e mata k'ofar yanata yimata sannu"karka damu my Lion ba sosai nakejin ciwon ba"insha Allah yanzun idan nadubaki zai dena"gaba d'aya ke ko duhun da masu ciki keyi bakiyiba my Angel"saidai kin zama y'ar lukuta ko?"d'an murmushi kawai tayi batace komaiba"yashigo cikin motar yaja suka bar gidan.....bayan sun iso Asibitin kai tsaye office nashi suka nufa yafara dubata"saidai lokacin da dr Aliyu ya gama bincikar In'am har nakudarta takai 4cm"tanata fitar da brown d'in ruwa da sperm nasa"dukda dg ita saishine A office d'in saida yaji bbu dad'i"sbd tasan shine yatado mata nak'udar"Ahankali yace"my Angel kiyi hak'uri labour ne harma yayi nisa in sha Allah lafiya zaki haihu"dg baya munje yawan shak'atawa"kayan baby zanyi mgn yau zuwa gobe aturosu"idan kin haihun An siyi wasu nan"yafad'a yana d'aukar wayarsa ya kira dr Amina yasanar mata duk nurses d'in dake cikin labour room su fito zai shigo da madam"yana gama wayar yace"my Angel bara na ams....be Ida mgn ba in'am dake kwance samqn gadon da Akeyin scanning tasaki k'ara"da sauri ya dauketa yafita dg cikin office d'in da ita.....
'?

Mu had'e last page da dare insha Allah
d'?=ؓ? SONE KO K'IYAYYA =ؓ?d'?

79&80


......... Arikice yaya Aliyu yanufi labour room da in'am"jama'a nata kallonsa"be bari kowa yashigo ciki ba"yanata rarrashinta yasaka safa yasanya hannu yaji kan babyn yataho"shiru yayi yana tunanin in bacin nakud'ar takai 6cm da C's zai mata yanzun"Ahankali yace"atddu'a zakiyi my Angel kinjiko?"nidai yaya dan girman Allah kaciremun cikin nan kona huta da Azabar dana keji"inba hakaba mutuwa zanyi wlh"ka kira ummi tazo muyi sallama"ta fad'a zufa na keto mata"yaya Aliyu ya girgiza kansa yana k'ara gyara mata kwanciyarta sbd ganin Abin yataho gadan gadan"Ihu In'am tasaki ta rirrik'esa tanaso ta tashi zaune"shi kuma yak'i barinta"wayyo ummi zan rabe biyuuuuuuuu! ta furta da k'arfi tana sakin wani uban nishi"baby girl ta fad'o tana sakin kuka sbd iskan duniya dataji"yaya Aliyu yad'aga hannu sama yana fad'in Alhmdllh! yayinda In'am ta sume"ko kallon babyn beyiba yafara dubata yaga normal"kafin ya d'auki wayar sa"yakira dr Amina yasanar mata taje shop"yana son kayan baby cmplt na mata da shawul"dato ta Amsa masa"sai sannan ya kalli yarinyar datayi shiru"masha Allah! yafad'a yana d'an murmushi"domin yarinyar kamanninsa sak ta d'akko" sai kuma ta kwaso farin In'am da gashinta"cibi ya yanke yafara k'ok'arin goge babyn"Ahaka yaji knocking"yaje ya bud'e ya Amso kayan ya shirya yarinyar"ya kwantar da ita samqn wani gado na yara dake cikin d'akin"sannan yayima In'am kwalfar jini ,yamata Allurai sbd bata samu k'ari ba be mata d'inki ba"wasu nurses yakira Aka turo gado ya Aza In'am da babyn ya turasu zuwa d'akin hutu"ya zauna gefen bed d'in yanata kallon in'am dake kwance"Ahaka dr Amina ta turo k'ofar ta mik'o masa ledar ruwa dazai d'aurama In'am"bayan ya Amsa ta masa barka ta fita"ruwan ya d'aura mata sannan ya d'auki wayarsa yakira mommy yasanar mata"Ada ta zata kodai wasa yakeyi saida ya rantse mata sannan ta yadda"sai kuma yarinyar tayi kuka hakan yasa ta kashe wayar da sauri"hakan yayi daidai da farkawar In'am daga suman datayi"shi kuwa yaya Aliyu brr Ahmed yakira yasanar masa haihuwar"In'am ido ta tsurama yarinyar tana murmushi sbd ta fahimci mace ce dan kayan jikin babyn na mata ne"my Angel kin tashi?"uhmm"ya jikin naki?"da sauk'i"kina jin yunwa ko?"harda bacci"Alluran dana miki ne"yafad'a yana k'ok'arin taimaka mata ta tashi zaune ya d'ora mata babyn samqn cinyarta yana fad'in sannu my Angel, kinga Allah yacika mana burunmu mun sami baby girl ko?"Eh yaya kaga saina dinga yimata kitso ko?"murmushi ya saki yana fad'in wai gaba d'aya naga bakima ta tawa duk yarinyar nan ta d'auke miki hankali"ya fad'a yana b'ata fuska kamar wani k'aramin yaro"kai yaya taya zank'i ta rabin raina"to nida ita wakika fi SO?"dariya tayi ta nuna babyn"ya had'e rai yana mik'ewa tsaye zai fita....kai yaya wasafa nakeyi"kajiyo kadawo dan Allah"juyowa yayi ya gallah mata harara yana fad'in nidai ka kiramun ummi mutuwa.....kukan shagwab'a tasaka yadinga dariya ya zauna gefen ta yace"sonakeyi wani yazo sai naje na d'akko miki kayanki da Abinda zaku buk'ata zuwa dare insha Allah saimu koma gida"Amma my Angel karki yadda suce zasu tafimun dake gida wanka"to yaya nima banaso Arabamu"Allah sarki my Angel zan kula dake da babyn mu ko?"d'an murmushi tayi tace"wane suna zaka sakq mata?"fad'amun wane kikeso?"zab'in ka shine nawa my Lion"shikenan zan mata hud'uba da sunan ummi saiki sami nick name d'in da zaki samata Akirata dashi....tana k'ok'arin mgn mommy da umma suka turo k'ofar d'akin suka shigo da kayan Abinci da ruwan zafi A hannunsu"ya mik'e tsaye yana Amsa sallamarsu yace"bara naje na d'akko miki kayanki"dato In'am ta Amsa tana d'an murmushi ta gaida su umma"ya jikin naki In'am?"cewar umma tana kallonta "yayinda mommy ta Amshi babyn"da sauk'i umma"bbu Inda ke miki ciwo?"Eh"kai ina zakaje?"kayanta zan Amso mata"okay kabiya ka Amso ruwan zafin daza'a yima babyn wanka"ita kuma nan sai mommy tayi mata"dato ya Amsa ya fita"sai sannan umma ta Amshi babyn ta gani...mommy ta had'ama In'am tea me kauri da Abinci shak'e da nama tace ta cinye"bbu musu taci ta k'oshi sbd yunwa takeji"bata jimaba da gama cin Abincin ta kwanta baccin gajiya.....cikin k'ank'anin lokaci dangi da y'an uwa sukaji haihuwar In'am"yaya Aliyu kuwa sai wajen k'arfe 6 ya dawo Asibitin"lokacin in'am na toilet itada mommy tana mata wanka da sabon towel"d'akin cike yake da yaran mata"tasleem,nafeesa da nata cikin 6month"wanda zainab ita ta rufe fitama"sai matar hamza hafsat da zubaida "sai Anty d'ayyaba ba da yesmeen"yaya Aliyu yashigo da kaya nik'i nik'i Ahannunsa"tasleem ta tashi ta Amsa tana fad'in sannu da k'ok'ari Angon jego"ya amsa yana murmushi duk suka gaishesa"ya tambayi In'am?" Akace wanka takeyi"fita yayi sbd shima yaje yayi wankan da sallar magrib ya dawo idan yaga jikinta normal yabasu sallama.....
misalin k'arfe 7:48 pm tafiya sukeyi cikin motar fuskar yaya Aliyu Agimtse take bbu Annuri sbd umma tace" gida za'a wuce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login