Showing 36001 words to 39000 words out of 88777 words

Chapter 13 - SO NE KO KIYAYYA COMPELET BOOK BY MAMAN FAREESA.doc

Aureba tunda beda niya"hmm! Alh kenan! Aliyu In'am yake mutuwar SO Amma tsoron mahaifiyarsa ya hanashi yanuna hakan"wlh tun yarinyar nan tana k'arama bata san kantaba na fahimci yana sonta....zancen banza! yana son nata shine yayi shiru beyi mgn ba?"to zan ganshi idan sbd hauwa yab'oye...karkayi haka Alh dan Allah"mu bisu da Addu'a ne kawai"karka manta koma miye mahaifiyarsa ce tanada iko Akansa"matsalar kawai datake nuna k'iyayyar ta badan Allah! tunda ba'a mata komai ba"yanzun haka bawai sonake na had'aka da matar kaba Alh mgn ce ta gasky"d'azun nake tambayar nafeesa In'am kwana 2 nadena ganinta"saita kama kuka sbd kasan sun shak'u"fad'a nakama yi mata da tambayarta ko fad'a sukayi?sai take sanarmun.....ta labarta masa zuwan umma gidan ummi"da korar data yiwa yaya Aliyu data samesa Acan"harda gargad'in karya koma zuwa gidan.....cikin b'acin rai Abba yace"wlh dani take mgn tunda dama tana d'aukar hud'ubar gaje y'ar uwarta"haka kawai tasamun yaro Adamuwa duk irin b'oyayyar da yake yi mana dg ni har ita"lallai Abin da mamaki"ni kaina wani lokacin idan naga yadda yake kulawa da ita ina zargin ko SONE"sai kuma naga Aliyu shi baya sakarma kowa fuska"ai wlh Alh yanzun haka In'am dai da girmanta ko?"to tsab Aliyu zaizo mun da ita yace"gata nan taci Abinci"koya saka Azubo Abinci yatasata gaba yace"saita ci sbd yasan bata son cin Abinci"shiru Abba yayi yana tunani can yace"bbu damuwa zamuyita Addu'a d'in mugani zuwa sadda zasu gama makarantar"to Alh yabatun Aurenka da ummin yaran? hmm !binta kenan kema kinsan Ai bata so ko?"na kuma sanar mata bazan bari ta Auri wani ba tunda bata sona.... murmushi kawai mommy tayi ta tabbatar Inda Agaban umma ne yafad'i hakan sai sunyi tashin hankali da ita kan wannan y'ar maganar"dan ita tanada zafin kishi...
Ayau yakama week end"misalin k'arfe 12 na rana"garin yayi zafi sbd hadarin da yayi k'asa"In'am ta shigo cikin layin Anutse"tana rik'e da leda bak'a Ahannun ta"tana sanye da dogon hijab har k'asa, gogagga morish maroon colour"tayi kyau gwanin ban sha'awa"saidai tunani takeyi dan kanta Ak'asa yake......tunda ta doso cikin layin yaya Aliyu dake k'ok'arin shiga get d'in gidansu ya hangota ta madubi"hakan yasa ya fasa ya kashe motar"yabi d'an mitsitsin bakinta da kallo yana lumshe ido" yana tuna ranar da Allah zai nuna masa In'am ta zama mallakinsa idan yasami d'an bakin nan nata bazai masa da wasa ba.....saurin bud'e lumsassun idanuwansa yayi yazuge glass d'in motar"kyakykyawar fuskarsa ta bayyana "hakan yayi daidai da in'am ta d'ago kanta karaf idanuwanta suka sark'e dana yaya Aliyu....cak ! ta tsaya ta sunkuyadda da kanta k'asa idanuwanta na cikowa da k'wallah"maryam! yakirata cikin sanyin muryarsa"bata d'ago kanta ba ta russinah tana fad'in yaya Aliyu ina wuni?"bazan Amsaba?"shiru tayi still kanta Ak'asa"zonan! da sauri ta d'ago kanta tana kallon k'ofar gidan su"sai kuma ta matso Asaitin Inda yake"ina kikaje yanzun cikin rana?ummi ce ta Aikeni bakin titi"to wannan k'wallah d'in dake idonki na meye?"babu komai yaya"dama zanje karta jirani"shiru yayi can yace"kinaso na siya miki waya?"da sauri ta girgiza kanta"bakya son Abinda yafito dg hannuna ko?"yafad'a yana d'aure fuska"bafa haka bane yaya Aliyu"yanata kallonta beyi mgn saidai yana nazarin kamar bataso wani yaganta tana tare dashi"sweets da chacoolates da big boom masu yawa ya mik'o mata yana fad'in Amsa ki tafi"d'ago kanta dake Ak'asa tayi ta saci kallon sa...suka koma had'a ido"sai A sannan ta lura yayi y'ar rama"Amma ba k'aramin kyau yamata ba"yana sanye da k'ananun kaya"k'amshin turarensa har Inda take tana jinsa"yayinda gabanta keta fad'uwa" dan yanzun data gansa ta rasa dalili sai taji fad'uwar gaba..... Maryam bakyaso?"ya tambaya yana katse mata tunanin ta"da sauri ta matso ta mik'a masa hannayenta duka biyun batayi mgn ba"yabud'e k'ofar motar yana Aza nasa tafikan hannun Asaman nata, yazuba mata su chacoolates d'in"tabi dogayen yatsun hannunsa da damtsen hannunsa duk gashi da kallo kafin tace"yaya nagode"ta fad'a Ahankali"beyi mgn ba yarufe k'ofar yazuge glass d'in motar"yabita da kallo tana tafiya Anutse harta shige cikin get d'in gidansu"tana shiga ciki ta b'oye chacoolates d'in cikin Aljihun doguwar rigar Atamfar jikinta sbd kar ummi ta gani"sannan ta wuce ciki.....
Awashe garin ranar Aka tashi dajin rasuwar mahaifin safwan Alh d'ahiru"Abin mamaki kuma da yamma Akace mijin mama gaje yarasu"Abin yabama dr Aliyu tsoro"yanaso yasanarwa brr Ahmed ganin mama gaje dayayi ta fito A wannan motar ,ga kuma rasuwar mijinta data mahaifin safwaan yakama rana guda"beso ya zurfafa zaton Abinda beda tabbas Akansa"hakan yasa bema brr Ahmed zancen ba"saidai mutuwar mahaifin safwan da Aikin daya Ajiye yak'ara tabbatar musu yana cikin k'ungiyar Asiri tayin kud'in jini dumu dumu...tun bayan rasuwar mlm lawal mama gaje taci gaba da facaka da kud'i"Hamza da zubaida na yawon tambayarta wane irin kasuwancine takeyi haka?? Amma saita nuna musu kud'i Ai Aliyu ya bata tayi had'in gwiwa da wasu y'an company suna kasuwanci"dg zubaida har Hamza basu yardaba"sannan kuma suna mamakin yadda ta nuna mutuwar ubansu ko Ajikinta"Asalima da gari ya waye sukaga gawarsa sai Akace Akaishi Asibiti"ta dinga fad'a tana cewa jayayya sukeyi da hukuncin Allah.... Ayanzun y'an Anguwar suna yawon zund'enta sbd ganin ta canza Amma basuga tana wata sana'aba....

************
kwanci tashi inji masu iya mgn sukace Asaran me rai"In'am da nafeesa na karatu bbu kama hannun yaro"sun gama first term sun shiga second term har Anyi hutu"yanzun da sun koma zasuyi last exams su gama"tsakanin yaya Aliyu da In'am sai hange daga nesa"sai suyi sati 2 basuga junaba"saidai shi kullum saiya ganta lokacin tafiyarta islamiya ko kuma dawowarta"zai zauna Amota yaganta sannan yatafi"Amma yadena shiga gidansu sbd bin umarnin ummansa"gaba d'aya yaya Aliyu yak'ara komawa shiru shiru"ita kanta umma Abinda tayi yadameta"sbd Aliyu dg gaisuwa da tambayarta Abinda take buk'ata bbu Abinda ke k'ara had'asu"sai da dare yazo yamata saida safe...to kusan Abba ma haka yake mata"baya sake mata fuska ko fira da ita"Abincinta baya ci"gaba d'aya itama cikin damuwa take"shi kuwa Abba Aganinsa yi mata zancen Abinda tayi yanzun bashine fa'idaba yabarta sai nan gaba tukum"idan yamata maganar yana ganin zatayi zaton ummi ce tasanar masa da wani Abu game da ita"shiyasa gaba d'aya ya d'auke mata wuta....Abangaren farooq da in'am kuwa duk yadda take k'in kulashi baya fushi haka yake bibiyarta"bbu laifi kuma yanzun tana d'an kulashi"yanaso yafara zuwa gidansu fira wajenta tace"yabari suyi SSCE"yanzun haka Abba yabama yaya sulaiman kud'i dasun koma hutu yasiya musu wayoyi sbd exams......Ayau misalin k'arfe 10:11 am"ummi na zaune a parlourn ta ita kad'ai tana kallon tauraruwa TV"Aka turo k'ofar parlourn Ahankali"mayen k'amshin turaren Aliyu me tubarau yacika parlourn"ummi ta kalli k'ofar da mamaki tana Amsa sallamarsa"ya wanku cikin sabbin suit dark blue"wanda sukayi bala'in haska choco colour d'in fatar jikinsa"kallo d'aya zaka masa kasan hutu da jin dad'in rayuwa had'e da wayewa na yawo A jinin jikinsa"tun dg bak'ar suman kansa zuwa lallausan zagayayyen sajen fuskarsa selk'i da d'aukar ido sukeyi sbd gyaran da suke sha"yana sanye da takalmi sawu ciki dark blue da Agogon fata d'aure A hannunsa"yadad'e da tubarau bak'i"ummi fuskarta Asake take fad'in Aliyu ne?"Eh nine ummi"yafad'a yana d'ukawa ya dafa kujerar dake gefensa yaz are glass d'in yana fad'in ina kwana ummi??lafiya qlau Aliyu fita zakayi ne?"yana satar kallon k'ofar d'akin in'am yace"Eh sallama nazo yimiki ummi"zanje k'asar Cairo nayi wani course na wata ukku nadawo"masha Allah! Allah yatsare yabada sa'ar Abinda Akaje yi Aliyu"ya Amsa da Ameen cikin jin dad'in Addu'ar tata da ganin k'imarta Azuciyarsa"ya mik'e tsaye yana k'ara kallon k'ofar d'akin In'am Akaro na biyu"ummi na lura dashi tace"kuma baka kirani kasanar mun ba"dako dambun nama ne namaka katafi dashi ko?"karki damu ummi Addu'ar ma dakika mun tayi dan ita nafi buk'ata dg haka yajuya tanata masa fatan Alkhairi yafita....ke In'am! kina ina?"gani ummi"cewar In'am dake lab'e d'aki tana jin maganar yaya Aliyu"fitowa tayi tana gyara d'an kwalinta"maza kije ga yayanku can zaiyi tafiya ki masa fatan Alkhairi ki dawo"dato In'am ta Amsa ta fita k'afarta ko takalmi bbu"tana sanye da lace d'inkin doguwar riga....saida ta had'a da gudu"sannan ta hango yaya Aliyu gab dazai isa bakin get"wanda kuma koda yafito dg cikin parlourn saida ya juyo yaga zaiga in'am? sai "yaga bbu ita"kuma beso yatafi be gantaba"kawai saiya Ayyana Aransa yanzun idan yafita zai turo Auwal yakira masa ita"sbd yaga su Auwal d'in zaune k'ofar gida....yaya Aliyu! takira sunansa da d'an k'arfi"cak! yatsaya"kusan second 5 kafin yajuyo cikin nutsuwa yana kallonta ta cikin eye glass nasa"tamkar tasan kallonta yakeyi"sai tayi k'asa da kanta tana wasa da yatsun hannunta"maryam! yafad'a tamkar bashine yayi maganar ba"d'ago kanta tayi taga ya mik'o mata dogon hannunsa guda.....bata san lokacin data tafo Aguje ba ta fad'a Ajikinsa ta fashe da wani irin kuka"wanda kawai tsintar kanta da yin kukan tayi Amma bata san dalili ba......yaya Aliyu wata iriyar kasala da mutuwar jiki yaji lokaci guda"kasan ransa kuma farin cikin kasancewar Ahaka ne"yashafa bayanta cikin tattausan muryanshi yace"kukan na meye my Angel?"idan natafi Ai zan dawo ki dinga ganina ko?....*my Angel*? in'am ta maimaita sunan Aranta"shi kuwa sai bayan ya furta yatuna bata sanba yasaka mata wannan sunan "d'ago hab'arta yayi ta lumshe idanuwanta tana tsuke d'an bakinta"yaja karan hancinta yana fad'in kukan ya isa haka"yafad'a yana saka tafin hannunsa yagoge mata hawayenta"sosai In'am taji kunyar rungumesan datayi"da sauri ta fara k'ok'arin janye jikinta dg nasa"saiya rik'eta yana fad'in harkin gama yin sallamar da yaya Aliyu naki?"turo baki gaba tayi tace"to Amma ai yaya bakace ina nake ba ko?"ta fad'a b'ata fuska"beyi mgn ba yacikata ta dawo gefensa"yazare glass d'in dake fuskarsa"tayi saurin yin k'asa da kanta"gaba d'aya yanayin dayake jin kansa Aciki yahanashi iya furta mata komai"saidai yana ganin tabbas Angel tashi itama tafara jin makamancin Abinda yakeji Akanta....ya d'auki kusan second 10"kafin ya tattaro jarumta cikin cool voice d'insa yace" "maryam! I'm sorry kinji?"koda baki zoba inada niyar turowa Akiramun ke"da mamaki ta d'ago kanta ta kallesa sbd tunda take dashi be tab'a fad'a mata wannan kalmar ba"yes kiyi hak'uri bance kizo muyi sallama ba ko?"shiru tayi tak'i mgn"to fad'amun waye yaturoki muyi sallamar?"ummi ce"iya Abinda ta fad'a kenan tayi shiru"ki koma gida nizan tafi"Allah yatsare hanya yabaka nassara yaya Aliyu"Ameen" thank you my lil sis"tayi d'an murmushi har beauty point d'inta na lotsawa"ta juya Aguje tabar wajen tana murmushi"shima murmushin yasaki yanajin kamar yabita ya rungumeta"dan wannan hugging d'in nasa datayi sai yaji kamar karta bar jikinsa" saidai yasan rashin dacewar hakan data tuna yasaka ta cikasa...gaba d'aya jinsa yayi cikin farin ciki dajin k'arfin gwiwar tafiyar"yana fitowa dg cikin gidan"mahmood da Abdul hakeem da Auwal suka biyosa suna masa fatan sauka lafiya yamusu Alkhairi me yawa"ya shiga back sit driver yaja suka nufi air port.... In'am kuwa daidaita nutsuwarta tayi sannan ta shigo cikin parlourn"dataga ummi bata nan zaune"saita nufi d'akin ta"samqn bed ta fad'a tayi kwance ta lumshe ido"jikinta nata k'amshin turaren yaya Aliyu"kodai yaya watace dai yake nufi da my Angel??ta fad'a Afili tana tashi zaune"sbd tayi mamakin jin sunan"sannan Ayau yadda yamata mgn cikin taushin murya da sakin fuska Abin yabata mamaki....sai kuma ta tuna kalaman ummi datake fad'in"idan dai Allah yayi Aliyu shine mijinta baki isa ki hana ba.....wai suna nufin sona yaya Aliyu keyi??kai ba haka suke nufi ba"nida yau ne kawai yama fara sakemun fuska"sai kuma tayi shiru tana tuna yadda Asiya y'ar Ajinsu ke yaba kyawunsa da had'uwarsa"har tana fatan inama zai sota"tsaki taja sbd bata san meyasaba idan Asiyar na irin wannan zancen haushi take bata....bata gama wannan tunanin ba nafeesa ta shigo d'akin da murna tana k'wala mata kira"ta kalleta tana fad'in lafiya irin wannan kira??"kefa ba'a miki gwaninta"to yaya Aliyu ne yabani leda biyu d'azun"yace"na baki guda na d'auki guda Amma sai yatafi zan baki"ta fad'a tana mik'a mata babbar leda fara tayin shopping"jikin In'am A sanyaye tace"Amma nafee kinsan ummi fa ta hanan...kinga basai kin nuna mata ba ki Ajiye cikin ward rope naki kawai"tunda dai yatafi babu zancen ki mayar masa"shopping ne yamana wlh"kai yaya yanada kirki sosai"duk wacce ta Auresa taji dad'i"sbd ya had'u ga iya d'aukar wanka"kawai matsalarsa rashin mgn da fara'a da bayayi...shiru dai In'am tayi batace komaiba tana tunani ta fara duba ledar"nafeesa kuwa fita tayi"biscuits, chacoolates,sweets, chiweengum dasu big bom,da snacks"sai turaruka"sai rafar y'an 200 guda 1 daga k'asa"Allah sarki yaya Aliyu"ada ina maka kallon mugu"Amma yanzun kanada kirki"dama banida kud'i"kosu yaya sulaiman nace su bani kud'i sai Anjamun rai"idan kuma nace ummi ta bani tayita tambayata miye zanyi da kud'i?"ta k'are maganar tana sauka dg samqn bed d'in ta d'auki ledar tasaka A ward rope ta rufe......ta nufi bathroom sbd tayi wanka....

Bayan wata 3
'?

Tofa yanzun fa za'a fara zuba love guys Ashirya zafafan comments >?*?=??

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

d'?=ؓ? SONE KO K'IYAYYA =ؓ?d'?

33&34


*Bayan wata ukku*
tun bayan tafiyar Aliyu k'asar Cairo yaya sulaiman yasiyama nafeesa da In'am waya suka koma hutu"yayinda In'am har yanzun sai jifa jifa take shiga gidansu nafeesa...to itama nafeesar kusan hakan sai yakama take shiga gidansu In'am sbd kunyar ummi "dan yanzun kowa yasan suna son juna itada yaya sulaiman"yanzun sai idan zasuje skul suke had'uwa ko zuwa wata Anguwa"saidai kawai suyi mgn ta chats"kasancewar suna yin wayar suka fara what's app, snapchat, extergram da sauransu....Anan In'am kecin karo da zafafan hausa novels tana karantawa"tuni ta k'ara wayewa da gogewa da kuma kamun kai da Aji"sosai tayi wata irin canzawa"dan yanzun bata wannan surutun kamar da saiya kama take mgn"yayinda maza masoya keta yimata caa"bata kuma cika yawan kula suba"sbd gargad'in da yaya Aliyu yamata.farooq ne kawai suke waya da chats dashi"Ayanzun k'agare yake In'am ta gama skul yaje yanemi ison fara zuwa fira gidansu"dukda dama ta sanar masa karatu zata cigaba datayi SSCE...sau tari In'am na tuna yaya Aliyu"sai taji kamar ta Amshi contact nasa wajen nafeesa" Amma sbd yanzun tana jin kanta Asama ta k'ara zama cikakkiyar budurwa saita basar "tana ganin Ai bema damu da itaba"idan yakama ta had'u da umma tana gaida ita koda bazata Amsaba wannan kenan...Afannin yaya Aliyu kuwa da tunanin In'am yake rayuwa Ak'asar cairo"ko kuma yayita kallon pics nata da vedios d'in dayake yimata bata sani ba"Ahaka yayi wata ukku cikin matuk'ar samun nassara"wanda k'asar basu bari yatafo ba saida suka Amfana dashi da course d'in daya karanta" sbd k'warewarsa Afannin komai daya shafi mata"sunso ya zauna Anan k'asar yana Aiki"shi kuma ya nuna beso yafison yatafo k'asarsa ta haihuwa Nigeria"wanda Ayanzun haka Asibitinsa An sake zuba k'wararrun ma'aikata"daya dawo zai koma d'aukar wasu"sbd duk Abinda ke wakana Acikin Asibitin yana sane da komai ta waya....
A safiyar yau Alhamis misalin k'arfe 12:15 pm"yaya sulaiman yayi parking d'in motarsa A airport d'in mlm Aminu kano"sbd yaya Aliyu yakirashi yazo yanzun ya d'aukesa karkuma yasanarwa kowa yadawo"sbd zaiyi suprise d'in kowa"sadda sulaiman yafito dg cikin motarsa Alokacin fasin jas keta fitowa dg cikin jirgin....cikin nutsuwa yake sakkowa dg matattakalar jirgin"yana sanye da suit bak'ak'e"saidai suit coat d'in ya ratayeta Agefen kafad'ar sa"sai y'ar ciki fara k'al Ajikinsa"ya tsuk'e k'ugunsa da black belt"yadad'e da eye glass bak'i"yanata zuba wani irin fitinan nan k'amshi"yayi kyau da haske"fatar jikinsa ta koma murjewa da gogewa tana shek'i sbd samun hutu da jin dad'in rayuwa"fuskarsa bbu yabo bbu fallasa yashak'i iskar k'asar sa ta haihuwa ya fesar yana jinsa cikin farin ciki sbd nassarar daya samu Akaratun da yayi k'asar Cairo "game da breath cancer"tun kafin ya Ida isowa y'an jarida sukayi masa caa"kasancewar Ansan Inda yaje da kuma course d'in dayaje ya karanta yayi bincike Akai Amatsayinsa na babban likitan mata...bbu wanda yakula yana janye da troley d'in kayansa yanufi wajen sulaiman"dake nufosa yana murmushi yace"yaya Aliyu welcome back! thank you! yafad'a yana sakin d'an tak'aitaccen murmushi"yaya kaga yadda kayi masha Allah?lallai k'asar ta Amsheka k'ilan In'am bazata ganeka ba?"yafad'a yana Amsar troley d'in"yad'auki kusan second 5 kafin yana d'an murmushi yace"uhmm! bana zaton my Angel zatak'i ganeni ko yaya na koma kuwa sulaiman"ina fatan kana sauke Amanarta dana tamk'a mak'a?"yafad'a sadda suke shiga cikin mota...ina saukewa sosai yaya"wata ran kuma na zazzageta sbd y'ar rainin wayo ce"zalin d'inta kake ci kenan?"yafad'a fuska Ad'aure"wlh ba haka bane yaya Aliyu"yanzun ta d'akko wani sabon hali na k'yaliya Ayita yimata mgn tayi banza da mutane sbd taga ta k'ara girma "shiyasa kwanaki danace zan turo maka pic nata kaji shiru ban turoba batama tsaya nayi mata ba"shiru yaya Aliyu yayi yana tunanin my Angel tashi ta koma shiru shiru kamarshi kenan??"k'ilan yanzun ta k'ara girma sosai sbd saura sati 2 bathday nata yazo ta cika 17yrs....da wannan tunanin suka shigo layin nassarawa"yi parking na fita! saika shigarmun da motar gida ka kai mun kayana part nawa ga key"yafad'a yana mik'a masa"yaya sulaiman ya Amsa yana gyara parking d'in"ransa na bashi yaya Aliyu In'am zaije yafara gani sannan yashiga gida"yayi d'an murmushi sbd tuni yasan yaya Aliyu son Autar tasu yakeyi...cikin nutsuwa yafito dg cikin motar tyana k'arewa layin kallo"me d'an kes na nan yana siyar da kati sai masu wucewa jefi jefi cikin manyan motoci na Alfarma"batare dayayi tunanin komai ba yatura get d'in gidan su in'am ya shigo"masu gadi da masu bama flowers ruwa duk suka zagayesa suna mik'o gaisuwa da masa fatan dawowa lafiya"sannan ya wuce cikin gidan..... in'am ce duk'e A parlourn ummi"ta Ajiye plate d'in Awara soyayya da taji k'wai, ga yanke yanke Agefe" sai robar yaji dakakke shima Agefe duk ta Ajiye"ta nufi kitchen sbd ta d'akko ruwa"ummi na kitchen da laure me Aiki suna girkin rana"In'am na sanye da doguwar riga ta kanti kanta bbu d'an kwali ta d'aure dogon gashinta Abaya"wanda ba shida yawa saidai tsawo....kina nufin da ita Awarar kad'ai zaki karya?cewar ummi tana kallonta"b'ata fuska tayi tana fad'in nidai da ita mana ummi"maimakon ki fara shan tea me zafi"turo baki tayi tak'i mgn"ummi nata kallonta tana murmushi batace komaiba"In'am ta d'auki ruwa ta fita dg cikin kitchen d'in.....turuz tayi sbd ganin mutum zaune kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login