Showing 1 words to 3000 words out of 48110 words
Chapter 1 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf
TRUE LOVE
__________________
SOYAYYAR GASKIYA
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : Princess Meerah
THE WRITER'S OF
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE
HASKE BIYU ( YAR JARIDA )
TAURIN ZUCIYA ( RETURN )
* Wannan gajeran labari ne , labarin soyayya tsakanin Fari da Baki , Soyayya
tsakanin abun da ba za su taba kasancewa a waje guda ba , ga cin amana , na jinin ka ma ba
zai kyale ka ba , wannan labarin da ga karkashin zuciya ta ya fito , duk wanda ya sauya min ko
da kalma daya cikin abun da na rubuta ban yahe mishi ba , sannan duk wata kalma da na fada
ba dai'dai ba ko na yi kuskure to ku yahe min , Duk kuma wanda ya fadi wata mumunar kalma a
kai na , to shi da Allah *
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb
يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{PAGE 1 & 2 }
▪UNITED STATE OF AMERICA ( U.S.A )
▪NEW YORK STATE
▪GREENWICH STREET
Wata kyakyawar Budurwa ce ke tafe a saman titin waya a kunne
Ta na sanye cikin Wando palazzo Black colour da Shirt Navy blue , ta yi Rowling wani veil navy
blue a kan ta , ta na rataye da wata yar bag Black ita ma , hannun ta na dama ta rike da wani
cup na coffee dayan kuma ta na rike da wayar ta a kunne
Budurwa kyakyawar gaske ce , amma kallo daya za ka yi mata ka san ba jinin turawa ba ce , a
shekaru za ta kai 22 years
Skin din ta fara ce kal amma ba kamar na turawa ba , ta na da dara daren idanun ma su daukar
hankali , farare kal kwayar cikin su kuma Black ce , Black din ya ciza sosai har wani kyali ya ke
yi eyelashes din ta dogaye da su kuma baki kirin , ta na da dogon hanci kamar pencil , design
din lips din ta gwanin burgewa , pink colour da su ga bala'in laushi , sun sha lips balm , ta saka
wasu medical glasses a idanun ta Ta na da shape kamar na coca cola , hips da breast din ta cike su ke bam dai'dai shekarun ta ,
ta hadu iya haduwa kamar ita ta yi kan ta Masha Allah
Wani cool murmushi ta saki cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa ta ce " Momy , ki bari
har na samu hutu , in sha Allah ina nan zuwa , kin San ba yadda za a yi auren Yasmine ba na
nan " ta fada da haoussa , hakan na nufin ita bahaoushiya ce ?
Ta dan dauki lokaci kafin ta saki yar karamar dariya ta ce " Momy , aure fa lokaci ne , in sha
Allah in na wa lokacin ya zo zan yi , amma gaskiya ban da ra'ayin aure a yanzu " ta kai karshen
dai'dai ta sha wata kwana
Kawai sai jin ta ta yi ta bugi mutun har sai da cup din hannun ta ya kubce mata ya fadi kassa
cikin sa'a bai bata mata kaya ba
Da sauri ta dago kai ta ja da baya
Wasu samari ne tsaye a gaban ta , sam ba su yi kama da mutanan kirki ba
Kare musu kallo da kyau ta yi kafin ta ce " momy ina kiran ki " da ga haka ta sauko da wayar ta ,
ta kashe kiran sannan ta ce da samarin nan " How can i help you ? "
Wanda ta yi karo da shi ne ya mika ma ta hannu cikin tsawa ya ce " Give me your phone "
" why ? " ta fada mishi cikin ko in kula
Wata yar karamar dariya ya yi kafin ya fido gun a bayan shi ya saita kan ta , da sauri ya na fadin
" give your phone , give your phone "
Dayan saurayin ne ya katse shi da cewa " and her bag "
Wata yar kara budurwar nan ta yi kafin ta mika mishi wayar ta da sauri hannun ta har kerma ya
ke yi ta fido jakar ta , ta mika musu ta na fadin " please let me , ga su nan na ba ku "
Su na karba su ka yi kwanar da ta fito da gudu
Su na barin wajen ta daura hannayan ta saman kai nan take idanun ta su ka kawo ruwa ta na
fadin " wayooo Allah na shiga uku na , ina zan sa kai na yau ni Esra , duk keys din apartments
di na su na a ciki ya zan yi da raina ni "
Sai sambatun ta ta ke yi ita kadai dan hanyar babu kowa saman ta
Kamar da ga sama ta jiyo Muryar mutun a bayan ta ya na fadin " Miss wannan na ki ne ? "
A dubu dari ta juyo ta na kare mishi kallo
Saurayin ya hadu ba laifi gaskiya , a shekaru zai kai 33 years
Fari kal da shi kamar ka taba jini ya fito , ya na da sexy eyes farare kal kamar madara , kwayar
cikin su kuma light Green ce , da dan karamin bakin shi , lips din shi kuma duk pink color ne ,
gashin kansa Darck black curly ne amma bai tara suma sosai ba , ta zubo mishi gaban goshi
kadan ta rufe idanun shi , ya na saka wani earring a kunnen shi na dama ga wani saje baki kirin
konce a fuskar shi , ya na da tsayi ga kuma murdaden jiki sosai allamun ya na yawwan motsa
jiki
Ya na sanye cikin wando Crazy jeans blue color , sai yar singlet fara wadanan karfafun damtsen
na shi duk a waje su ke , kafafun shi su na cikin wasu sneakers ma su mugun kyau farare ,
A hankali ta sauko da kallon ta kan abun hannun shi , ta na ganin bag din ta da phone din ta ta
saki wani kyawatencen murmushi
Da sauri ta kai hannu ta kwace su , ta na fadin " eh , nawa ne , na gode sosai , na dauka na
rasa su kennan har abada "
Hannayan shi ya saka cikin aljihun shi kafin ya ce " sai a bani ladan aiki na ko , ko 100$ ce za ta
ishe ni " ya kai karshen ya na fudo hannun shi ya kai bayan keyar shi
Kare mishi kallo ta yi da ga sama har kassa kafin ta ja wani dan siririn tsaki ta juya ta ci gaba da
tafiyar ta , ta rataya bag din ta
Ta na shirin mayar da phone din ta cikin bag din ta , ta ji an zabce mata ita
A dubu dari ta dago kai ta na fadin " waye ne ? " , nan ta ga saurayin nan ne , ya na zabtar
wayar ta ya yi gaba ya yi wata yar kwana da ke gaban su kadan
Da sauri bi bayan shi ta na fadin " kai malam ban waya ta " dai'dai lokacin da ta yi kwanar ita
ma
Cak ta tsaya ba shiri , ashe ba kwana ba ce , irin dan kwangon nan ne da turawa ke yi dan ajiye
trash bin
Cen ta hango shi zaune saman wasu kwali , ya na rike da wayar ta ya na jujuya ta , hannu
gudan kuma ya na rike da taba ya na busawa
( YANZU DA YIN KWANAR SHI HAR YA SAMU DAMAR KUNNA TABA ? )
A hankali ta karaso gaban shi ta na sa hannu ta janyo veil din ta , ta toshe hancin ta dan wajen
ya na mugun wari , ga kuma na tabar da ya kunna , amma shi sam bai damu ba ya saba da
wannan warin
Gaban shi ta karaso ta mika mishi hannun ta , ta na fadin " give my phone please , wlh na yi late
a wajen aiki "
Ba tare da ya dago kai ya kale ta ba ya ce " cewa na yi ki ba ni ladan aiki na amma ki ka ki , kin
san idan na sayar da wayar nan za ta fi 100$ ? "
Da sauri ta ce mishi " eh na sani , ka yi hakuri ban rike da kudi amma gobe zan kawo maka
please ban waya ta "
A hankali ya kai tabar shi baki ya ja kafin ya sauke ta ya busa hayakin a saitin ta
Da sauri ta kauda kai gefe ta na dan lumshe idanun ta
" What's your name ? " ya fada ya na meda tabar shi baki
Dan tsaki ta ja kafin ta ce " don Allah ka ban waya ta "
" who is Allah ? Ni ban san shi , dan haka in ki na son wayar ki , ki amsa min tambayoyi na " ya
fada ya na kunna wayar ta ya kali screen din , hoton ta ne ke sama , ta na sanye cikin wata
gown pink colour , zaune cikin wani garden ta saki murmushi gwanin burgewa
Da sauri ta ce mishi " Esra Yahaya "
A hankali ya gyada kan shi kafin ya ce " okay , my name is Kim , are you married ? "
" no " ta fada a takaice
" okay zan ba ki wayar ki , but promise me za ki kawo min Chocolate gobe , ko ba ki zo ba ni
zan tarda ki gida " ya fada ya na mika mata wayar ta
Maganar shi ba karamin mamaki ya ba ta ba , ba ta san lokacin da ta ce mishi " me kuma za ka
yi da chocolate kai da ke shan taba , na dauka kudin sayan tabar ka ke so "
Slowly ya sunkuyar da kan shi ya ce " Kudin sayan tabar ba za su yi min wuya ba , kawai
chocolate din na ke so "
Kare mishi kallo da kyau ta yi kafin ta kai hannu ta karbi wayar ta juya ta fara takawa za ta bar
wajen
Ya na jin ta fara takawa ya dago kai slowly ya na kallon yadda ta ke tafiya cike da nitsuwa
Sai da ta kusa fita wajen ta jiyo Muryar shi ya na fadin " Ki daina biyowa hanyar nan , akwai
gangster sosai a wannan lokacin , ba ki ga babu kowa saman hanyar ba "
Dan karamin murmushi ta yi mishi kafin ta ce " na gode , gobe zan kawo maka chocolate din ka
" da ga haka ta juya ta fice wajen
Har ta bar wajen bai janye kallon shi ba , sai da ya dauki lokaci kafin , ya sa hannu cikin gashin
shi duk ya cakuda , ya sa hannu cikin aljihu ya ciro kwalin tabar shi ya ciro guda ya kunna ya ci
gaba da aikin shi
Esra kuma ta na barin wajen ta fara tafiya da sauri sauri ba ta dauki 6 minutes ta iso bakin wani
tanpasheshen building duk na zallar glass
▪ONE WORLD TRADE CENTER
ya na da ga cikin jerin manyan building goma na cikin New York , ya na dauke da hawa dari da
hudu , wannan ginin sai da ya dauki wajen shekara 7 a na yin shi , sannan an kashe mishi
makudan kudade wanda za su kai 3,9 milliards na dollars
Da sauri ta shiga cikin building din ta na duba watch din hannun ta
Kawai sai jin ta ta yi ta bugi kirjin mutun , har sai da bag din ta , har takardun da mutuman ke
rike da su ka zube
Ba tare da ta dago kai ba ta ga wanene gaban ta ba ta duka da sauri ta dauki jakar ta , ta rataya
sannan ta fara tatare takardun shi ta na fadin " yi hakuri don Allah , wlh sauri na ke tun Sir Kevin
bai gan ni ba , na....... " kut maganar ta yanke sakamakon dago kan ta da ta yi ta ga wanene ke
gaban ta
Tsaye ya ke cak cike da kwarjini ya na sanye cikin Suit farare kal gwanin burgewa
Cikeken bature ne fari kal da shi kamar ka taba jini na hito , ya na da dan tsayi amma ba sosai
ba , da murdaden jiki , ya na da kananan idanu farare kal kwayar cikin su kuma black ce , ya na
da dogon hanci , da jajayen lips shape din su kamar heart , bai wani tara gashin kai ba shi ba
baki ba , shi ba brown ba , sumar shi a konce ta ke lufff gwanin burgewa , gayen ya hadu sosai
amma fuskar nan ta shi a daure ta ke tamau kamar hadari
Murya na kerma Esra ta shiga fadin " So.......sorry sir " ta kai karshen ta na mika mishi takardun
shi da ta su ka fadi
Hannun ya sa ya karbi takardun shi ya na tsare ta da wadanan kananan idanun shi
Ya na karba ta yi sauri ta raba ta geffen shi ta wuce
Ba ta yi wani taku biyu ya kira sunan ta cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa da izza , cak
ta tsaya ta lumshe idanun ta na karanto duk wata adu'ar tsari da ta fado mata a zuciya
A hankali ya daga kafa ya dawo gaban ta ya tsaya ya na ci gaba da kallon ta
Sai da ya dauki wajen good ten minutes a haka kafin ya bude bakin shi a hankali ya ce " open
your eyes "
Dum ta ji gaban ta ya fadi , zuciyar ta ta shiga duka uku uku , a hankali ta fara bude idanun ta ,
sai cikin na shi , da sauri ta sunkuyar da kan ta , dan ba za ta iya jure kallon cikin idanun shi ba
A hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce mata " me ya tseda ki , yanzu karo na hudu ki na
zuwa a makare cikin satin nan , apartments din ki fa just behind ya ke , ba zai wuce ki dauki 15
minutes cikin kin jima kafin ki zo , amma kullum sai kin yi late "
Wasu yawu ta hadiye kafin ta bude baki lips din ta har kerma su ke yi wajen cewa " I'm so sorry
, wlh wasu........ "
A hankali ya katse ta ta hanyar daga mata hannu ya daura da cewa " ki bi a hankali Miss Esra ,
in har ki na son aikin ki , dole ki kiyaye nan gaba ba zan iya daukar wannan late ba "
" nagode Sir in sha Allah zan kiyaye " ta fada cikin girmamawa
Sai da ya tsaya kallon ta da ga sama har kassa sannan ya raba ta geffen ta ya fice abun shi
Ya na fitowa sai saman wata dankareriar mota baka kirin har wani kyali ta ke yi kamar mirror ,
kudin motar nan kadai ya isa mutun ya yi lafiyayen gida har ma ya ja jari
Da sauri driver din shi ya bude mishi kofar baya , ya na shiga ya meda kofar ya rufe ya koma
wajen shi da sauri ya tada motar su ka bar wajen da gudu
Da kallo Esra ta raka shi sai da ya bar wajen sannan ta sauke nanauyar ajiyar zuciya har sai da
ta dan lumshe idanun ta ta na dafe saitin zuciyar ta ta na fadin " Allah na gode maka " da ga
haka ta daga kafa ta nufi