Showing 12001 words to 15000 words out of 48110 words

Chapter 5 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf

mu yi maganar mu cikin konciyar hankali "

a hankali Cherry ta dawo wajen Chair din ta ta zauna ta na fadin " okay hakan ma zai fi , kun
san akwai camera cikin office may be maganar nan da mu ka yi ma sun jiyo mu "

a tare Arthur da Esra su ke hada baki su na cewa " da gaske ki ke ? " su ka fada su na zaro
idanu da ga gani sun tsorata

wata yar karamar dariya Cherry ta yi ta na fadin " na so kun ga kawunan ku , wai da gaske ki ke
? , matsorata kawai " ta kai karshen ta na sakin wata dariyar

a tare Arthur da Esra su ka ja tsaki su na cewa " Allah ya shirya ki wlh "
cikin dariyar ta ta , ta ke fadin " da gaske na ke akwai cameras , sai dai ban sani ba in akwai
cikin office din mu ba "

mikewa tsaye Arthur ya yi ya na fadin " ni na tafi Abu na tun da haka ne "

wata yar karamar dariya Esra ta yi ta na fadin " kenan da gaske ta ba ka tsoro ? "

" kin san an ce hanyar lafiya a bi ta da shekara , gwara na tafi kamar yadda na shigo , sai mun
hadu an jima " ya na gama fadar haka ya kafa ya fice

ya na fita Cherry ta kalli Esra ta ce " yau ba ki hadu da dan iskan ki ba ? " ta kai karshen ta na
daga mata gera

tsuke fuska Esra ta yi ta na fadin " kin ga malama tashi fice min da ga nan "
wata yar karamar dariya Cherry ta yi ta na kokarin tashi ta ce " da ga tambaya ? , ni ma na tafi
tun da haka ne ".

" ai dama ban kira ki ba " Esra ta fada ta na kai kallon ta kan laptop din ta
" okay , see you later " Cherry ta fada ta na sa kafa ta fice office din


TRUE LOVE

__________________

SOYAYYAR GASKIYA

( A HEART TOUCHING LOVE STORY )








STORY & WRITING BY : Meerah



THE WRITER'S OF

TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE
HASKE BIYU ( YAR JARIDA )
TAURIN ZUCIYA ( RETURN )



GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN
NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY







TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION



https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb







يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ










BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM








{P A G E 9 & 10 }




a haka Esra ta ci gaba da aikin ta ita kadai cikin Office din , sai da ta share wajen good one hour
a haka kafin ta ja wani dan karamin tsaki ta kai hannu cikin bag din ta ta fido wayar ta , ta saka
karatun kur'ani ta aiki ta na saurare

_________________________________


▪BROOKLYN


wata kyawatencen balcony ne Fari kal , ya sha tiles farare kal ma su mugun kyau da haske
ga wata katuwar Swimming pool , ruwan cikin ta sky blue ne saboda tiles din da ke cikin pool
din blue ne sai ruwan su ka dauki launin tiles din
pool din zagaye ta ke da wasu umbrella irin na bakin beach haka
kassan kowace akwai wasu chair guda biyu dogaye kamar na icce , da ga tsakiya su akwai
wata yar karamar table ta glass saman kowace akwai Towel farare guda biyu ajiye
bayan wadanan chair din dan nesa kadan akwai wani kyawatencen parlour wall din da ke
fuskantar pool din duk da glass ne an rufe shi da wasu curtain farare kal
parlourn ya kawatu da duk kayan more rayuwa , ilahirin abun da ke cikin parlourn Milk color
amma bari mu koma cikin labarin mu dan tukunna ba mu isa parlourn ba
duk balconyn zagaye ya ke da glass ka na iya ganin duk yanayin garin

wani kyakyawan Saurayi ne zaune saman daya da ga chair din bakin pool
saurayin kyakyawa ne , a shekaru zai kai 32-34 years , fari ne kal cikaken bature gaba da baya
, ya na da wani kontancen gashi color din shi baki kirin ne amma harshen su duk blue ne , ya
konta min a baya gwanin burgewa sai wasu da su ka zubo mishi gaban goshi
ya na da kananan idanu farare kal kwayar cikin su kuma Ash ce , ya na da dogon hanci da dan
karamin baki lips din shi kuma pink color ne ya na da wani piercing a kunnen shi da na dama
ya zaune saman chair din ya mike kafafun shi da ga shi sai short , a hannun shi na dama akwai
wani Tattoo kamar flowers haka
ya na rike da wani magazine ya na karantawa cikin konciyar hankali

ya na a haka wani server ya shigo wajen ya na sanye da wasu Suit bakake hannun shi rike da
tray dauke da glass biyu ya juice da wani dan plate na fruits

kai tsaye wajen wannan saurayin ya nufa ya kai hannu ya dauki glasses din nan ya ajiye saman
table din geffen shi da plate din fruits din sannan ya mike ya koma dayan geffen saurayin ya ce
" sir , ku na bukatar wani abu ? "

a hankali Saurayin nan ya girgiza mishi kai ya na murmushi ya ce "No , za ka iya tafiya na gode
"

gyada mishi kai kawai server din nan ya yi kafin ya juya ya bar wajen
wani dan karamin tsaki saurayin nan ya yi kafin ya ce " wai kai malam ba za ka fito ba , ka yi
wajen two minutes a ciki fa " ya fada da turanci

ya na gama fadar haka wani saurayin ya fito da ga cikin pool din ya juyawa saurayin da ke

zaune baya , Babu riga a jikin shi , gashin kan shi kawai a ke iya gani ya zubo mishi har baya
keya ya konta mishi luf amma light green ne , amma da ga gani ba karamin namiji ba ne dan
damtsen shi a murde ya ke kamar dan dambe ,

a hankali na jiyo Muryar shi ya na fadin " lafiya ka fiddo ni ? " cike da nitsuwa ga murya ta shi a
sanyaye kamar an busa sarewa
" Ayden wai yaushe za ka daina harkar restaurant ka kama companyn ka , ka fi kowa sanin
satar da Kevin ke yi maka amma ka yi shiru "

ko sannu Ayden bai ce mishi ba ya koma cikin ruwan
wani dogon nunfashi saurayin nan ya ja ya na cewa " oh ni Adrian , ba da kai na ke magana ba
? "

Ayden ya na jin shi amma ya share ya ci gaba da yawon shi cikin ruwan

wani dan karamin tsaki Adrian ya ja ya na fadin " shikenan amma kar ka ce ban fada maka ba "
ya na gama fadar haka ya kai hannu ya dauki glass din juice ya kai baki ya surba Kafin ya
mayar ya ajiye

sai da ya yi wajen two minutes a haka kafin ya sake fitowa da ga cikin ruwan , yanzu ma ya
juyawa Adrian baya
a hankali ya kai hannu ya yi baya da gashin kan shi da ya jike
cikin nitsuwa ya ce " Guy , don't worry , na kusa gamawa da Maganar Kevin , kawai ina son na
gama da Business din restaurant din nan ne , da kai na zan koma Companyn , yanzu ka yi
kawai abun da na saka ka "

sai da Adrian ya dan jinkirta kafin ya ce " na shirya ground plan din companyn , sign din ka
kawai na ke jira "

" okay " ya fada a takaice kafin ya yi kassa ya koma cikin ruwan
wani dan karamin murmushi Adrian ya saki kafin ya ci gaba da karatun shi


▪ESRA


Zaune ta ke cikin parlourn su , ta na sanye da wani dan karamin wando dai'dai cinya , da
wata t-shirt white color mai kyau
ta mike kafafunta saman sofar , ta daura laptop a sama ta na latsawa cikin konciyar hankali

ta na a haka Safna ta turo kofar part din ta shigo ta na sallama , ta na sanye da uniform din
restaurant din su
amsa mata sallamar ta Esra ta yi ta na fadin " sai yanzu ki ka dawo ? "

da murmushi a face din ta Safna ta karaso cikin parlourn ta ajiye bag din ta saman table
sannan ta zauna ta na fadin " kin dai gani "

" okay , je ki yi wanka , na shirya mana diner " Esra ta fada ba tare da ta kalle ta ba
wata yar karamar dariya Safna ta yi har da tapi ta na fadin " iyeeeee , wai Esra da gaske kin
shirya mana diner ? lafiya ? ko dai tsintuwa ki ka yi ? "

wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " ba abun da na yi kawai dai na dawo ne ina jin
yunwa shi ya sa na shirya mana "

" okay bari na je na yi wanka " ta fada ta na kokarin tashi
da sauri Esra ta tsayar da ita ta na fadin " please , zauna ina son na yi miki wata tambaya "

ba musu Safna ta koma ta zauna ta na fadin " wace tambaya kuma ? "

a hankali Esra ta rufe laptop din ta sannan ta sauko da kafafun ta kassa ta zauna bakin sofar
ta na fadin " dama a kan restaurant din ku ne , na ce kin taba ganin mamallakin wajen ? "

a hankali Safna ta girgiza mata kai ta na fadin " no gaskiya ban taba ganin shi ba , but ba
restaurant guda ba ne , restaurant din shi su na da yawa gaskiya , wanda na ke aiki ciki karami
ne ma sosai , na so ki ga restaurant din shi na Washington , sai ki rantse da glass a ka yi shi ,
musaman sai manyan ministers da yan kasuwa ke shiga restaurant din , shi ma sai sun yi
booking one week before , ba karamin mutum ne ba wlh "

cikin nitsuwa Esra ta ce mata " but , ko so guda bai taba zuwa restaurant din ya duba ba ? "

girgiza mata kai Safna ta yi ta na fadin " no gaskiya , ko so guda ban taba ganin shi ba , ni ko
sunan shi ma ban sani ba wlh , kawai dai in mu na meeting ne manager din mu na maganar shi
amma bai taba fadin sunan shi ba "

" okay , na gode " Esra ta fada kafin ta bude laptop din ta ta ci gaba da aikin ta

ita dai Safna ta tsaya ta kurawa waje guda ido kamar mai tunanin wani abu

cen sai ta ce wa Esra " Esra , kin san wani abu ? akwai wani mutum da ke yawan zuwa
restaurant din duk Monday , kullum shi ne first client din mu , kuma kullum in ya zo coffee ne
kadai ya ke sha ya yi tafiyar shi "

a Hankali Esra ta dago kai ta kalle ta ta ce " ki na iya gane shi idan kin gan shi ? may be shi
ne mai restaurant din ba ki taba sani ba "

" Eh zan iya gane shi , sosai ma , kin ga ko wlh kullum in ya zo da laptop a hannun shi ya na

typing , sai wajen karfe 9 sannan ya ke barin restaurant din , watarana su biyu ma su ke zuwa ,
amma gudan ban taba ganin face din shi ba gaskiya "

" okay , yanzu je ki yi wanka mun yi maganar da ga baya "

da to kawai Safna ta amsa mata kafin ta tashi ta dauki bag din ta , ta nufi corridor ta shiga
bedroom din ta , ta bar Esra nan zaune ita kadai ta na aikin ta



____________________________________



▪LAGOS ( NIGERIA )


wani kyakyawan matashi ne zaune saman chair , tsakiyar wani kyawatencen garden
matashin kyakyawa ne ba laifi , a shekaru ba zai wuce 36 years ba , skin din shi chocolate ce
, da ga gan shi ka ga cikaken bahaushe gaba da baya
ya na sanye da wasu suit khaki , ma su mugun kyau sun zauna mishi a jiki
ya na rike da wayar shi ya na latsawa ya na sakin murmushi

ya na a haka wani kyakyawan dattijo ya iso wajen ya na sallama , ya na sanye da wata
jallabiya white color mai dogayen hannu , fuskar shi babu yabo babu fallasa , a shekaru zai kai
60 haka , amma da ga ganin yanayin jikin shi ya na samun hutu dan har ya fi saurayin da ke
zaune haske , ga shi kuma bai tare kyasumba ba sai ka yi tunanin kamar dan shekara 40 ne
a hankali matashin nan ya dago kai ya na amsa mishi sallamar shi kafin ya mike tsaye ya na
mika mishi hannu ya na fadin " Barka da fitowa uncle "

wani dan karamin murmushi mutumin nan ya yi , ya na mika mishi hannu su ka yi musbaha
sannan ya zauna saman dayan chair da ke geffen ta matashin nan

sai da ya zauna sannan ya ce " Irfan , sai yau ka tuno da ni ko ? "
komawa Irfan ya yi ya zauna ya na dan sunkuyar da kai ya ce " a'a wlh uncle , kun san
yanayin aiki ne , ko wannan zuwan na tsaye ne komawa zan yi dan gobe zan koma London "

" Masha Allah , Allah ya taimaka , Allah ya kara daukaka "

" Ameen ya rabbi , na gode uncle " Irfan ya fada cike da girmamawa

wani kyawatencen murmushi mutumin nan ya saki kafin ya ce " ya ka baro mahaifin naka , da

momyn ka da sauran yan uwan ka ? da fatan ka baro su lafiya ? "

" Alhamdoulilah uncle , su na nan lafya , sun ma ce na gaishe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login