Showing 36001 words to 39000 words out of 48110 words
Chapter 13 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf
,
sannan ya dauki tray din ya kai wajen washbasin ya ajiye
MY BOOK IS ₦500
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
SOYAYYAR GASKIYA
__________________
TRUE LOVE
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : MEERAH
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{P A G E 25 & 26 ❤}
bayan ya ajiye ya dawo ya tsaya geffen ta ya ce " here is , ga shi na kammala "
da murmushi a face din ta ta ce " gaskiya da ga gani zai yi dadi , Yanzu ka iya girki haka ka
ke neman bata wa kan ka lokaci wajen yin security a nightclub , why ba za ka nemi aiki ba a
wani restaurant ba ? "
" na nema , amma duk restaurant din da na je sai su ce na gwada musu takardun karatu na
ko certificate din kwarewa ta a girki , ni kuma ko primary school ban yi ba , shi ya sa na hakura
na daina nema "
har cikin zuciyar ta ta rasa dalilin da ya sa ta ke mugun jin tausayin Kim , he look so innocent
, amma rayuwar shi ta na neman ta ruguje haka , gaskiya ya kamata ta gyara mishi rayuwa ko
da shi ne abu na karshe da za ta yi a ta/ta rayuwar
wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce kai hannu ta dauki plate din Apple pie ta
na fadin " okay , let's go and eat " ta kai karshen ta na fara takawa ta nufi parlour
ba musu ya dauki dayan plate din ya bi bayan ta su ka nufi yar dining table din su ta ajiye a
sama sannan ta zauna saman chair guda ta na ce mishi ya zauna
ajiye plate din kawai ya yi kafin ya dan ja da baya ya na ce mata " no , lokacin hawa aikina ta
kusa , tafiya zan yi "
marairaice fuska ta yi ta na mikewa tsaye har ta bude baki kawai ta ga ya juya ya fara takawa
zai fice
da sauri ta ce mishi " Kim , ka tsaya na zuba maka cikin box kar ka tafi da yunwa "
ko juyowa bai yi ba ya sa kafa ya fice ya janyo mata kofar
ita dai da kallo ta raka shi har sai da fita sannan ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya ta
koma zauna ta so ya tsaya su ci abincin tare ko da pie din ce tun da ita ce favorite dessert din
shi , amma yanzu ya tafi
a hankali ta kai hannu kai tsaye ko spoon ba ta saka ba ta dauki Apple pie din nan guda ta
kai a baki ta na bismillah sannan ta fara ci
a hankali ta sauke wata boyayyar ajiyar zuciya kafin ta lumshe idanunta a hankali , gaskiya
taste din da yi mata mugun dadi , ita ba ta ma taba cin Pie din da ta yi mata dadi irin wannan ba
, ga shi abun so easy amma taste din duniya ne guda , gaskiya Kim ya iya girki
cikin kankanan lokaci ya shirya wannan abun ina ga an ba shi isashen lokaci abun da zai yi
sai ya fi hakan
sai da ta gama cinye sannan ta tashi a hankali ta nufi corridor ta shiga
a hankali ta kai hannu ta tura kofar bedroom din Safna ta na sallama kassa kassa
a konce Safna ta ke saman bed din ta , ta na rufe da duvet
ta na ganin Esra ta dago kai a hankali ta na amsa mata sallamar ta
a hankali Esra ta karaso cikin dakin ta zauna bakin gadon ta na fadin " ya jikin naki ? "
wata yar karamar ajiyar zuciya Safna ta sauke kafin ta ce " da sauki , amma yunwa na ke ji ,
tun dazu na ke jin wani qamshi na tashi ban san da ga ina ya ke ba , please gyara min wani abu
na ci "
wani dan karamin murmushi Esra ta saki kafin ta ce " tashi mu je ki ci , shi ya sa ma na zo na
kira mu je mu ci abinci " ta na gama fadar haka ta mike ta nufi kofar fita
a hankali Safna ta janye duvet din jikin ta , ta mike zaune ta sauko da kafafun ta kassa ta
mike tsaye ta fara takawa a sanyaye ta fito dakin
ta na fitowa ta isko Esra zaune saman yar dining table din su
dan zaro idanu ta yi ta na kallon abincin da ke sama ta karaso wajen ta janyo dayan chair din
ta zauna ta na fadin " Esra , ina ki ka samo wannan abincin ? "
wani dan karamin murmushin geffen fuska Esra ta yi kafin ta ce " kamar ya ? ni na shirya "
a hankali Safna ta girgiza mata kai ta na fadin " fadi gaskiya , na san kin iya girki amma ba ki
taba girka irin wannan abincin ba , asali ma ban taba ganin ki gyara fish ba , ko dai sayo wa ki
ka yi ? "
wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " kin yi gaskiya , ina saurayin nan da mu ka
taimaka a garden ranar nan ? "
a hankali Safna ta gyada mata kai allamun ta gane shi
" To shi ne ya zo ya girka mana , kuma da yay duk karfe 8 zai zo mu yi girki tare "
dan tabe baki Safna ta yi ta na kai fork din da ta debo fish da potato a ciki ta kai baki
sai da ta gama ta hadiye sannan ta kalli Esra ta ce " Yanzu saurayin nan ya yi wannan girkin
? "
gyada mata kai Esra ta yi ta na fadin " ni kaina na yi mamakin yadda a ka yi ya iya girki haka ,
kuma wlh ko one hour bai yi ba "
" gaskiya ya fi shirmen da ki ke girka mana " ta qarashe maganar ta na wata yar karamar
dariya , kamar ba ita ba ce dunkule kamar an aiko mata mutuwa
ita ma Esra wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mata " wannan karan zan yarda da ba ki
yi karya ba , amma ai koya min zai yi nan gaba kadan sai na fi shi kwarewa "
ita dai Safna ba ta ce mata komai ba ta na cin abincin kawai ba karamin dadi ya yi mata ba
Esra na ganin ta yi shiru ta gane ta tafi , hakan ya sa ta ja bakin ta ta yi shiru ta ci gaba da cin
abincin
sai da su ka cinye komai har Apple pie din ba su rage ba sannan su ka tashi su ka gyara
wajen Safna kuwa har ta dan ji karfin jikin ta
bayan sun gyara table din su ka wanke plates din a tare sannan Esra ta dawo parlour ta
zauna
Safna kuma ta koma bedroom din ta , ciki ya cika sai barci
_________________________________________
▪AYDEN
konce ya ke saman wata doguwar sofa fara kal , ya daura hannun shi guda saman cikin shi ,
gudan kuma saman idanun shi , wa ya sani ya na farke ko barci ya ke
ya na a haka Adrian ya shigo parlourn da ga shi sai short da singlet fuskar shi da damuwa a
kai ya nufi wajen kafafun Ayden ha na zauna
murya a sanyaye ya ce " Ayden , ba ka ce komai ba dangane da paper din nan ba ? "
shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai amma ya na jin shi dan ba barci ya ke ba
a hankali Adrian ya kai hannu ya buge shi a cinya ya na fadin " bro , da kai na ke magana
please ka ce wani abu mana "
wata boyayyar ajiyar zuciya Ayden ya sauke kafin ya ce " Please ka bar ni da abun da ke
damu na "
cike da kula Adrian ya ce " Oh my God , damuwa kuma ? wace irin damuwa kuma Ayden ?
please tell me , mi ke damun ka ? "
dan jinkirtawa Ayden ya yi kafin ya ce " Adrian , son yarinyar nan ya na neman ya min illa ,
ban san ya a ka yi na kamu da son ta ba , wai ko na haukace ne ban sani ba ? "
wani kyawatencen murmushi Adrian ya yi kafin ya ce mishi " no , ba ka haukace ba , amma
nan gaba za ka haukace in har ka ci gaba da rejecting abun da ke cikin zuciyar ka , ka san
minene love at first sight , shi ne kawai ya kama ka , yanzu kuma sai ka yi kokarin ka bawa
zuciyar ka abun da ta ke so " cikin zuciyar shi kuma ya ce " ko da ba ka yi kokarin bawa zuciyar ka abun da ta ke so ba ka
tabbata ni sai na mallaka maka ita "
shi dai Ayden bai ce mishi komai ba da allamun ya tafi duniyar tunanin shi
wata yar karamar dariya Adrian ya yi ganin yadda abokin shi ya damu kawai saboda mace ,
abun da bai taba gani ba
hannu ya kai ya bugi cinyar shi ya na fadin " yanzu tashi ka gyara mana wani abu mu ci dan
ni yunwa na ke ji "
wani dan karamin tsaki Ayden ya yi ya na fadin " ba ka san hanyar kitchen ba ? "
" na sani amma ka san ni ban iya girki ba kamar kai , please tashi ka gyara min wani abu ,
tun safe ban ci komai ba , please bro " ya kai qarshen a sanyaye
wani dogon tsaki Ayden ya ja kafin ya juya ya shige cikin sofar ya na fadin " in dai ni zan girka
maka ka mutu da yunwa "
hannu Adrian ya kai ya buge shi a baya kafin ya mike ya bar wajen da gudu kamar wani
karamin yaro
ko motsi Ayden bai yi ba amma ya na jin shi , kawai ba ya da karfin tashi ne ya na tunanin
Esra , ya rasa yaya ya kamu da son ta lokaci guda haka , shi dai ya san lokacin da su ka yi karo
ne ya taro ta kar ta fadi har su ka kalli juna cikin ido , a lokacin ne Cupid ya samu damar harba
mishi kibiyar son ta a cikin zuciya , kuma ya saita dai-dai dan bai taba jin ya so abu kamar irin
son da ya ke yi wa Esra ba a yanzu
To ya za ta kasance Ayden fa ya kamu da son Esra har cikin zuciyar shi , ita kuma musulma
ce , ya za ta kare ga kuma Kim a gefe dan ga dukkan allamu Esra ta fara kamawu da son shi
yanzu dai bari mu ci gaba da labarin za mu ga in da ya dosa
_______________________________________________
▪AFTER ONE DAY ( MONDAY , misalin karfe 8 )
▪ONE WORLD TRADE CENTER
▪ESRA ❤
da sauri sauri ta shigo building din , dan yau da ga gani ta yi late
ta na sanye da wata gown white color har kassa mai mugun kyau ta yi Rowling veil din black
color , ta na rike da bag din ta , amma sam hankalin ta ba ya tare da ita
ta na tsaka da tafiyar ta kawai ta ji ta bugi mutun har ta fadi kassa ta na sakin wata yar
karamar kara
nan take duk takardun hannun shi su ka zube a kassa
wani dan karamin tsaki Ayden ya ja ya na kai hannu ya dafe kan shi da ke mugun sara mishi
dalilin da ya sa ma bai zauna ba zai koma gida ya huta
Esra kuwa ta na ganin kafafun shi cikin wasu bakaken sneakers ma su mugun kyau tsadadu
ga kuma trouser din suit da ta gani nan take ta ji zuciyar ta ta buga dan a tunanin ta Kevin ne
da sauri ta fara tattare takardun kamar ta yi kuka ta na fadin " i'm so so sorry sir "
Ayden bai ce mata komai ba ya raba ta geffen ta ya wuce ya bar ta nan har da takardun
tsab Esra ta gama tattare takardun ta na dago kai za ta mika mishi ta ga babu kowa a wajen
da sauri ta kalli damar ta ta kalli hagun ta ba ta ga kowa ba
ta na juyowa ta ga hannun mutum a gaban ta
slowly ta dago kai ta ga Adrian ya na miko mata hannu da wani dan karamin murmushi a face
din shi allamun zai taimaka mata ta tashi
ita kuwa kawai