Showing 15001 words to 18000 words out of 48110 words
Chapter 6 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf
ku idan na zo "
gyada kan shi mutumin nan ya yi a hankali ya na fadin " Masha Allah , ba zan tsayar da kai
ba , dama ni na yi wa mahaifinka magana ya turo ka , mu yi magana , ina fatan za ka saurare ni
da kunnen basira "
cikin girmamawa Irfan ya ce " uncle ba sai kun yi min maganar ba , na riga da na san komai
dan Daddy ya fada min , kuma ina goyen bayan ku dari bisa dari , in sha Allah ba za mu ba ku
kunya ba , zai kara dankon zumuntar da ke tsakanin familyn mu , ni dai ta bangare na ba ni da
matsala , kawai fata na Allah ya tabbatar mana da al'heri "
Hamdala mutumin nan ya yi ya na fadin " Alhamdoulilah , Alhamdoulilah , ka san ni da
mahaifin ka tare mu ka taso , tun muna yara , a tare mu ka yi wassan kassa , a tare mu ka yi
karatu , aiki ne kawai ya raba mu , tun muna matasa mu ka yanke wannan shawarar , ina fatan
hakan zai zama karin dorewar abotar mu , mu zama family guda ta hanyar ku "
wata yar karamar dariya Irfan ya yi kafin ya ce " uncle , ai mu dama family guda ne , kar ka
manta a nan na taso , ina tune lokacin da na ke wassa saman cinyoyin ku , in sha Allah za mu
cika muku burin ku , albarkar ku kawai mu ke nema da addu'ar ku "
" Albarka kullum cikin saka muku ita mu ke yarona "
" na gode Uncle , i'm sorry amma tafiya zan yi , akwai inda a ke jira na "
wani kyawatencen murmushi Mutumin nan ya saki kafin ya ce " no , kar ka damu , amma ka
yi hakuri tukunna ba ta dawo ba , amma zan turawa Daddyn number din ta ya ba ka ko da
gaisuwa ce kafin lokacin ya zo "
" kar ku damu uncle , na gode sosai " ya kai karshen ya na mikewa tsaye
a hankali shi ma mutumin nan ya mike tsaye su ka yi musbaha , da ga nan su ka yi sallama
Irfan ya bar wajen , shi kuma ya koma ya zauna ya fiddo wayar shi ya fara latsawa
ya yi wajen ten minutes a haka kafin wata kyakyawar mace ta shigo garden din rike da wani
tray dauke da wasu glass biyu na juice
matar kyakyawar gaske ce , a shekaru za ta kai 45 to 50 years , kallo daya za ka yi mata ka
san mahaifiyar Esra ce dan su na kama sosai , kawai Esra za ta gwada mata haske , amma da
ga ganin yanayin jikinta ka san ta na samun huta , da kuma kula
ta na sanye da wata Abaya red color mai kyau , da wani Hijab fari da kadan ya wuce kirji ,
fuskar ta dauke da wani cool murmushi , ta na tafiya cike da nitsuwa
a haka har ta karaso wajen dattijon nan ta zauna saman chair din da Irfan ya tashi ta ajiye
tray din a kassa dan babu table a wajen
cikin sanyin murya ta ce wa dattijon nan " Engineer , har Irfan ya tafi ne ? ni da na kawo
muku juice "
[16/02 à 09:38] : __________________
TRUE LOVE
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : MEERAH
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{P A G E 11 & 12 ❤}
wata yar karamar dariya Engineer ya yi kafin ya ce " No , ya ce wai ya na da aiki , may be next
week ya dawo dan gobe zai koma London "
gyada mishi kai ta yi a hankali kafin ta kai hannu ta dauki glass din juice ta mika mishi
hannu ya kai ya karba ya na yi mata godiya
ba ta ce mishi komai ta kai hannu ta dauki gudan ta fara sha cikin nitsuwa
cen sai ta ce mishi " ka na ganin wannan shawarar da ka yanke me bulle wa ce ? "
cikin rudu ya ce mata " kamar ya me bullewa ? ban gane ba "
" ka fi kowa sanin halin yarinyar ka , idan ka ce za ka matsa mata da maganar ba za ta taba
amincewa ba , ni ma ina son ta yi aure but ya kamata mu ba ta damar zabar wanda ta ke so ba
mu cilas ta mata ba , a cikin 21st century mu ke , an daina wannan hadin auren da a ke "
" ni dama na san ba za ki taba amincewa da wannan maganar ba Aysha , amma in ba haka ba
ba za ta taba yarda ta yi aure ba , ki na gani US ta gudu dan kawai kar mu yi mata maganar ,
amma ina jiran ta dawo auren Yasmina , ba zan bari ta koma ba "
wani dogon nunfashi Aysha ta ja kafin ta ce " ka yi dai tunani mai kyau , ba dan ka na son
abotar ku da Wadi ta daukaka za ka hukuntar da yarinyar mu , kuma ba na tunanin za ta amince
da auren nan , ni dai zan so ka zauna ka kara tunani , rayuwar ta ce baki daya ka ke shirin yin
wassa da ita "
shiru Engineer ya yi bai ce mata komai ba ya na ci gaba da latsa wayar shi , shi dai a wannan
maganar ba gudu ba ja da baya duk abun da a ka yi sai ya yi auren Esra da Irfan dan shi ne
babban burin shi a rayu
________________________________________
▪US ( NEW YORK CITY )
▪GREENWICH STREET
a hankali ta ke tafiya cike da san'da kamar barauniya , ta na sanye da wata gown white color
mai mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta Purple a kai , ta na rataye da bag din ta kamar kullum
tafiya ta ke ta na waiwaye kar a je akwai gangs din da su ka fito a wannan lokacin
cikin sa'a ko ba ta hadu da kowa ba har ta karaso wajen wannan kangon da Kim ke rama
ta na shigowa ko ta hango shi cen zaune saman wasu box , ya na sanye da wani short white
color da shirt Red color babu takalmi a kafafun shi , ya na rike da taba ya na sha cikin konciyar
hankali
a hankali ta karaso wajen ta na yi mishi sallama duk da ta san ba zai iya amsa mata ba
ko sannu bai ce mata ba ya ci gaba da shan tabar shi
a sanyaye ta ce mishi " Hi , Good morning "
" Hi ! " ya fada a takaice ya na kai tabar a baki ya kara sha
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " Kim , tun da safe ka na shan taba ? ka yi
breakfast ko ? "
a hankali ta saki tabar ya sa kafa ya murje ta , ko zafin wutar bai ji ba , Esra kuwa har wani dan
lumshe idanu ta yi ji ta yi kamar ita ta taka wutar
shi kuwa ko ajikin shi kamar ba wuta ba ce ya taka
a sanyaye ya ce mata " wai me ki ke yi a nan ? a sani na chocolate ne ya hada mu , kuma kin
ba ni shikenan , why za ki takura min ? "
wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " ni kai na ban san abun da ya sa na takura maka haka
ba "
" to ki rabu da ni mana " ya fada ya na kai hannu cikin aljihun shi ya fiddo wata sabuwar tabar
da sauri ta kai hannu ta buge tabar ta na fadin " Please , stop , ka san irin illar da abun nan za
ta yi maka ba , tun safe ka na sha "
" breakfast ne na ke " ya fada ya na sake kai hannu ya fiddo sabuwar tabar
yanzu ma hannu ta kai ta buge ta na fadin " mu je na saya maka breakfast to "
" da kuma tabar da ki ka buge min " ya fada ya na kai bayan trush ya fiddo wasu sneakers
purple ma su kyau , ya saka a kafafun shi kafin ya mike tsaye
wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " na yarda , amma bisa sharadi guda "
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " wane sharedi kuma ? "
" can i be your friend ? " ta qarashe maganar ta na mika mishi hannu
kallon hannun nata ya yi na dan lokaci kafin ya girgiza mata kai a hankali ya ce " kin taba ganin
duhu da Haske sun hadu a waje guda ? ni kamar duhu na ke , ke kuma haske , ba za mu taba
kasancewa a tare ba , haka tsarin rayuwa ya ke "
" to ka ba ni dama , na mamaye duhun rayuwar ka da haskena , ka ba ni dama na sauya
wannan tsarin , kai ma ka na da izinin samun abokin da zai taya ka kuka , wanda zai taya ka
dariya , wanda zai sauya maka rayuwa , ka ba ni damar kasancewa wannan abokin "
sai da ya kare mata kallo da kyau kafin ya ce mata " shikenan , na yarda mu zama abokai just
for two weeks , cikin satin nan biyu in har ki ka yi nassarar sauya min rayuwa , abotar mu za ta
kasance ta har abada "
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ce " Eh , na yarda just two weeks , zan sa ka daina
shan wine da taba , zan gwada maka colors din rayuwa , idan ban yi nassara ba zan kyale ka
har abada "
" All right ! " ya fada ya na riko hannunta su ka yi musbaha
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " shikenan , my new friend , mu je na saya maka
breakfast , ina da sauran lokaci kafin karfe 8 ta yi ni ma zan samu na yi breakfast "
bai ce mata komai ba ya janye hannun shi ya fara takawa zai bar wajen
da sauri ta bi bayan shi ta na sakin murmushi su ka bar wajen , sai tafiyar shi ya ke cike da
nitsuwa , ya na kallon gaban shi
ita dai Esra sai satar kallon shi ta ke ta wutsiyar ido
a haka har su ka karaso restaurant din da Safna ke aiki , cike da mamaki ta shiga restaurant din
ta na tunanin yadda a ka yi ya san wajen nan
amma ba ta ce mishi komai ba , su ka shiga restaurant din , su ka zauna saman chair
sai da su ka zauna sannan Esra ta fara bin wajen da kallo , ta ga su kadai ne babu kowa a
wajen , sai servers din da ke kula da wajen
a ta mike ta na fadin " bara na yi mana order "
gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba
wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta fara takawa ta nufi reception
ta na barin wajen ko Adrian ya shigo restaurant din , ya na sanye da wasu suit bakake ,
hannayanshi rike da wasu paper da laptop , ya na taku cike da nitsuwa
tun da ya shigo Kim ya tsare shi da ido babu ko kiftawa , har ya nufi VIP space ya zauna , ya
bude takardun shi ya fara aikin shi
a hankali ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ya kauda kan shi , dai'dai lokacin da Esra
ta dawo wajen ta zauna saman chair din ta , ta na fadin " hope ka na shan coffee ? "
" Coffeeeeee ? , na yi miki kama da me shan coffee ? may be ice tea zan iya sha , amma ban
da coffee gaskiya " ya kai karshen ya na kauda kai
wata yar karamar dariya ta yi , ta na shirin magana idanun ta su ka sauka saman Adrian da ke
zaune bayan Kim , a VIP space
nan take yanayin face din ta ya sauya , ta karewa Adrian kallo da kyau , nan take kalaman
Safna su ka dawo mata a kai na wani da ke zuwa ko wace safiyar monday restaurant din
amma ya a ka yi , yau Friday ba monday ba
da sauri ta kai hannu cikin bag din ta ta fiddo wayar ta ta saita Kim akwai ta danna ta yi mishi
pic , ga shi ko shi ma ita ya ke kallo pic din sai ya yi kyau gwanin burgewa
wani dan karamin tsaki ta yi ta na fadin " Kim , yi gefe guda please "
ba musu ya yi gefe kafin ya juya ya ga abun da ta ke son gani
a hankali ya juyo ya na kallon ta ya ga Ta na yi wa Adrian Pic
cikin rudu ya ce mata " celebrity ne ? why ki ke yi mishi pic ? "
ba ta ce mishi komai ba ta sauko wayar ta , ta meda cikin bag din ta , dai'dai lokacin da Server
ya iso wajen rike da tray din order da Esra ta yi , ya shirya musu abincin saman table din su
sannan ya juya ya bar wajen
ya na barin Wajen Kim ya kai hannu ya dauki Fork ya fara cin toast din da a ka shirya da Eggs ,
ita dai Mug din coffeen kawai ta dauka ta fara sha ta na kallon shi
ya na cin abincin cike da nitsuwa , ga shi ko yadda ya ke aiki fork din sai ka rantse da Allah shi
ne jikan Sarauniyar UK Elizabeth
amma ita duk da idanun ta na saman shi , hankalin ta na kan Adrian , shi ko bai ma san abun
da ke faruwa ba , sai aikin shi ya ke cikin konciyar hankali
a haka har Kim ya kammala breakfast din , ya sha ruwa ya na yi mata magana amma ba ta ji shi
ba
a hankali ya kai hannu ya kyasta mata yatsu saitin face din ta
a razane ta dawo cikin hayacinta ta kalle shi ta na fadin " What ? me ya faru ? "
" za ki yi late wajen aikin ki " ya fada dan ya na son ya dan tsoratar da ita
a razane ko ga dauki bag din ta ta mike ta na fadin " wayyooo ni Esra na shiga uku wajen Sir
Kevin , na tafi "
" wait , bari na raka ki " ya fada ya na mikewa tsaye
ina ko sauraron shi ba ta yi ba ta nufi kofar fita , Kim kuma , a hankali ya juya ya kalli Adrian
kafin ya juya ya bi bayan Esra su ka bar wajen
su na barin wajen ko Safna ta shigo sanye da uniform din ta
bangaran Esra kuwa , tafiya ta ke da sauri da sauri