Showing 9001 words to 12000 words out of 48110 words

Chapter 4 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf

da ya bude idanun shi ba ya ce mata " What are you doing here ? " ya fada cikin sanyin
murya

da sauri ta yi baya kadan , ta janyo veil din ta , ta toshe hancin ta
" Kim , wine ka sha amma ko ? " ta fada dan ta jiyo warin ta cikin breath din shi

gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba
" Why ? " ta fada mishi cikin sanyin murya

wani dan karamin murmushi Geffen fuska ya yi kafin ya ce mata " ke ni fa dan iska ne , shan
wine karamin abu ne waje na , wai me ya kawo ki nan ma please let me "

cikin Sigar rarrashi ta ce mishi " please ka daina , wlh za ta iya maka illa ba kadan ba "

irin wannan murmushin Takaici ya yi kafin ya ce " please ki daina nuna kin damu da ni , ba ki
san ni ba , ba ki san ko wanene ni ba , ki na ganin wajen da na ke zaune , kullum cikin
tsangwamar mutane na ke , su na zagi na , Kalle ki , ki kale ni rayuwar mu ba daya ba ce , dan
haka ki daina kula ni please ba na bukatar kindness din ki , ki tafi ki kyale ni "
" tabass ban san ka ba , ba ka san ni ba , amma ai ka taimake ni duk da ba ka san ni ba , ka ga
ko dan hakan zan iya nuna damuwa gare ka , ni gaskiya ce na fada maka , shan wine babu
kyau , ta na iya janyo maka cancer , sannan cikin adinin mu , shan wine Haramun ne " ta fada
dan ita sam ta manta da shi ba musulmi ba ne
murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " Ke ki ka san wani addini , Ni ba ni da wani Aboki
duniyar nan kamar Wine , duk lokacin da na sha ta na kan ji damuwa ta ta fi , na kan ji na daina
kewar ta , please and please let me ki na damu na "

tsaya wa ta yi ta na kallon shi ba tare da ta ce komai ba
tabass akwai wani boyayen al'amari tare da shi , amma minene wannan abun ? ita ta ma rasa
dalilin ya sa ta damu da shi lokaci guda haka , musaman dan ta gan shi yau ta fito tun karfe 7
ga shi kuma ya ce ta kyale shi , ko bude idanu bai yi ba bare ya kale ta

a haka dai jiki a mace ta juya ta fara takawa ta bar wajen
ya na jin ta fara takawa ya bude idanun Slowly
sun yi jazir ko , lalle ya na cikin maye
wani dishi dishi ma ya ke gani , amma a haka ya raka ta da kallo har sai da ta bar wajen ,
sannan ya meda idanun shi ya lumshe


a hankali ta ke Tafiyar ta duk ta yi nisa duniyar tunanin ta
ba ta fi ten minutes ba ta iso hall din ONE WORLD TRADE CENTER
sai a lokacin ta dawo cikin hayacin ta , ta na shirin shiga ko ta ga Kevin ya fito da ga cikin
building din , ya na sanye da Suit sky blue ma su mugun kyau , ya na sanye da bakaken glass a
idanun shi , ya na takawa cike da kwarjini

a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ci gaba da takawar ta kai a sunkuye yau duk jikin ta a
mace ya ke

har ta kai bakin kofar ta jiyo Muryar Kevin ya na kiran ta

dum ta ji Gaban ta ya fadi har sai da ta karanto kalmar shahada
a haka ta juya ta nufe shi ya na tsaye bakin motar shi , driver ya bude mishi kofar

kai a sunkuye ta ce mishi " Good morning Sir "

a hankali ya sa hannu ya sauke glass din shi ya zuba mata idanu babu ko kiftawa
nan take ta ji duk ta tsargu , slowly ta dago da kan ta , idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin
nashi

da sauri ta meda kan ta ta sunkuyar
ta na sunkuyar da shi , shi kuma ya meda glass din shi ya ce mata " lafiya yau ki ka zo da wuri ?
"

ba tare da ta dago kai ba ta ce " nothing Sir "
gyada kan shi ya yi a hankali kafin ya ce " no wonder , Hope za a ci gaba da zuwa a cikin lokaci
" ya na gama fadar haka ya juya ya shiga cikin motar shi

ya na shiga ita ma ta juya ta nufi building din ta shiga dai'dai lokacin da motar su ta bar wajen
da mugun gudu
kai tsaye lift ta shiga ta nufi floor na 97




TRUE LOVE

__________________

SOYAYYAR GASKIYA







( A HEART TOUCHING LOVE STORY )

STORY & WRITING BY : Meerah



THE WRITER'S OF

TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE
HASKE BIYU ( YAR JARIDA )
TAURIN ZUCIYA ( RETURN )



GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN
NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY







TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION



https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb

يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ










BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM





P A G E 7 & 8




kofar Lift na budewa ta daga kafa ta fara takawa ta nufi office din ta , ta na isa ta kai hannu
saman finger print , nan take kofar ta yi wata yar kara ta bude kan ta , a hankali Esra ta shiga ta
na sallama cen kassan makoshi ,

office din ta ta nufa , ta ajiye bah din ta a saman desk din , sannan ta zagaya ta zauna saman
chair din ta

ta na zama ko Cherry ta turo kofar ta shigo office din
da murmushi a fuskar ta ta ce " Hi Esra , How are you ? "

murmushi kadan ita ma Esra ta yi mata kafin ta ce " Fine Cherry "
karasowa cikin office din Cherry ta yi ta nufi daya da ga cikin chair din da ke gaban desk din ta
janyo ta zauna ta na kallon Esra ta ce " ya a ka yi ki ka riga ni zuwa yau ? "

murmushi mai dan sauti Esra ta yi kafin ta ce " ai dama kullum sai na riga ki zuwa "

wata yar karamar dariya Cherry ta yi ta na shirin magana Arthur ya shigo office din ya na fadin "
wai da gaske Esra ce a karfe 8 dai'dai ? "

hararrar wassa Esra ta yi mishi ta na fadin " wai kowa cikin companyn nan ido ya saka min "

karasowa ya yi cikin office din ya ja chair din da ke geffen ta Cherry ya zauna ya na fadin " Ni
ban sani ba , amma ni da Cherry dai mun sa miki ido "

ya na gama fadar haka Cherry ta mika mishi hannu ta na fadin " ka gani ai , karfe 8 saura
mintina biyu , ban kudi na "

cikin rudu Esra ta ce mata " Wane kudi kuma ? "

" oh bet mu ka yi , na ce mata yau ma sai kin late , ita kuma ta ce ba za ki yi ba " Fadin Arthur
ya na fidda 100 Dollar ya ajiye saman hannun Cherry

wani dan karamin murmushi Esra ta yi ta na kallon su ta ce " yanzu tsakani da Allah bet ku ke yi
a kai na ? "

" may be ba mu kadai ba ne , ko kuwa Arthur ? " Cherry ta fada ta na dawo da kallon ta kan
Arthur

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " shikenan yanzu Esra minene ki ke son gwada mana
, yi sauri kar Sir Kevin ya dawo ya tardo mu nan "

gyada mishi kai ta yi kafin ta kai hannu ta janyo jakar ta , ta bude ta ciro laptop din ta , da
wannan USB key din ,
bude laptop din ta ta yi , ta kunna ta , sannan ta saka wannan USB key din ta shiga latsawa na
dan lokaci kafin ta juyawa su Arthur laptop din

a hankali Arthur ya kai hannu ya janyo laptop din gaban su shi da Cherry su na kallon screen
din

can kuma sai Cherry ta daura hannun saman bakin ta , ta na zaro idanu ta ce " Oh My God ,
Esra ina ki ka samo wannan abun ? "

" yadda ku ka gan ta haka na gan ta ni ma , abun ya yi matukar ban mamaki " Fadin Esra

ta na gama rufe bakin ta Arthur ya ce " Esra , ba fa karamin abu ba ne a nan " ya fada ya na
latsa laptop din

wata ajiyar zuciya Esra ta fada kafin ta ce " ni kai na na yi mamakin ina na gamo da wannan
abun wlh "

katse ta Cherry ta yi da cewa " Duk wasu kudi da a ke fitarwa da ga account din company , duk
relieve din shekarar nan su na a ciki , Idan har da gaske ne hakan na nufi abun da a ka sata
cikin companyn nan sun kai wajan one Hundred Milliards of American dollars kuma duk da
sunnan Sir Kevin " ta kai karshen ta na dawo da kallon ta kan Arthur
" kenan Sir Kevin shi ke satar kudin companyn nan ? " Arthur ta fada ya na dago kai ya kali Esra

kada mishi kafadu ta yi allamun ita ma ba ta sani ba
da sauri Cherry ta ce " Tabass shi ne , a na satar irin wadanan makudan kudaden kuma ya yi
shiru bai sa an fara investigation a kai ba , ku ma kun san da wata a kassa "

gyada mata kai Arthur ya yi ya na cewa " ni ma abun nan ya tsaya min , ya san satar da a ke yi
kuma bai sa an fara investigation a gano waye ke satar ba , shi ya ke aikata satar shi , shi ya sa
ya ja baki ya yi shiru , sai dai ya yi ta sallamar ma'aikatan da ba su ji ba , ba su gani ba " ya kai
karshen ya na dan tsaki
" yanzu Esra ya ki ke so mu yi , dan gaskiya ba zan iya yin shiru ba , Idan ya ci gaba mu ma za
mu rasa hanyar cin abincin mu , duk gidan mu fa da aikin ga nawa su ka dogara , idan ya kore
ni akwai matsala fa ! " fadin Cherry cikin nuna damuwa

Dan jinkirtawa Esra ta yi kafin ta ce " ni ma abun da ya sa na kawo muku ky gani kenan ,
saboda abun da ha ke ba dai'dai ba ne , Arthur ka ce ai companyn ba tashi ba ce ? " ta fada ta
na kallon Arthur

gyada mata kai ya yi kafin ya ce " eh ba tashi ba , ta little brother din shi ce "

" Fine , shi ya kamata mu kai wa wannan abun ya gani "

cikin nitsuwa Arthur ya katse ta da cewa " ki bar ma wannan tunanin , it's not sure ya yarda da
mu , kuma wannan ba zai isa ba , dole mu samo File din in har ta cikin laptop ne zai iya cewa
karya mu ke yi wa dan uwan shi "

cikin rudu Cherry ta ce " wai wanene mai companyn nan , ni fa shekara uku yanzu ina aiki a ciki
, ba dan jiya ka ce min ba sir Kevin ne ba PDG da ba zan taba sani ba "

wata yar karamar ajiyar zuciya Arthur ya sauke , Kafin ya jingina bayan shi a jikin chair din ya ce
" Ayden Brian , shi ne PDG din wannan company , asalin wannan companyn ta mahaifiyar su ce
, ya na da shekara 20 ta rasu , duk wani abu da ta mallaka ta saka shi a sunnan Ayden Brian
har da companyn nan , a lokacin ya na cikin kuruciyar shi ne ya sa mahaifin su yanke shawarar
ba wa Kevin companyn dan ya kula da su , dan Ayden ya samu damar kamala karatun shi ,
bayan ya Kamala karatun shi ne ya shiga harkar restoration , yanzu haka maganar da na ke
miki ya na da restaurant a ko ina cikin New York , Washington , New jersey da canada , ya fi

meda hankali a kan Restoration din , da a ce ya meda hankali a kan Companyn nan , da zai
gano irin satar da dan uwan shi ke yi mishi , ni dai ko so guda ban taba ganin shi cikin
companyn da sunnan ya zo aiki , shi ya sa kowa ke ganin cewa Kevin shi ne PDG " ya kai
karshen ya na jan nunfashi
" kenan Restaurant din , da Safna ke aiki a ciki nashi ne ? " Esra ta tambayi kan ta cikin zuciyar
ta

ta na a haka kawai ta ji Muryar Cherry ta na fadin " Yanzu ya za mu yi mu samu file din , ya
kuma za mu yi mu samo Ayden Brian yadda za mu gwada mishi tun kafin lokaci ya kure mana "

" File din na san ba zai wuce cikin Office din Kevin ba , maganar Ayden kuma gaskiya abu me
wuya ne samo shi " Arthur ya fada

ya na gama rufe bakin shi ya jiyo Muryar Esra ta na cewa " ni zan Samo muku Ayden , ku yi
kokarin samo mana File din nan t ........ "

ba ta kai karshen maganar ta ba Arthur ta katse ta da cewa " ke malama shiga office din Sir
Kevin ba karamin abu ba ne , A floor na 101 ya ke , kuma Security system din shi ya fi na
kowane office , musaman scanner din na kwayar idon shi ce ba na hannun ba , sannan akwai
wani password wanda Kevin ne kadai ya san shi , Idan ka yi kokarin saka password din da ba
shi ba har sai uku , nan take machine din will send an electric shock before you even move, you
will be electrocuted to death, on top of that, when Kevin closes his office with his magnetic card,
there is a laser beam system which is triggered, the only way to deactivate it is with this
magnetic card , so forget even the idea it's dead "

" kun gani ko , dan ba shi da gaskiya ne ya sa wannan uban security , da a ce ya na da gaskiya
password din ma kadai zai isa " Cherry ta fada cike da bacin rai

a hankali Esra ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " yanzu babu wata hanya da za a shiga office
din nashi ? "

da sauri Cherry ta ce " System of climatisation "

cikin rudu Arthur da Esra su ka maimaita abun da ta ce

da sauri Cherry ta mike ta nufi bayan desk din Esra , ta na nuna mata wani air conditionner ta
ce musu " duk yadda a ka yi akwai ac a office din shi , why ba za mu yi anfani da hakan ba
wajen shiga office din nashi ? "

" ki na da hankali kuwa ? dubi girman building din nan , kafin ma mu samo na office din shi zafi
ya kashe mu , ko kuma mu bace " Fadin Arthur

cikin nitsuwa Esra ta ce musu " ku na ji ko , ku bari idan mun sauka mu tafi apartments di na ,
ko kuma mu tafi shan coffee a cen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login