Showing 18001 words to 21000 words out of 48110 words

Chapter 7 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf

, Kim na biye da bayanta ya na kiran
sunanta
amma ba ta tsaya sai da ta karaso one world trade center sannan ta sauke wata nanauyar
ajiyar zuciya kafin ta tsaya
a hankali ta juyo ta kalli Kim da ke tsaye bayan ta ta ce mishi " na tafi sai mun hadu an jima "

gyada mata kai kawai ya yi kafin ta juya ta shiga hall din
ta na shiga ko Motar Kevin ta yi parking bakin hall din ya fito sanye da wasu suit purple ma su
mugun kyau , ya na sanye da glass a idanun shi

kamar an kira sunan shi kawai ya juya ya kalli saitin da Kim ke tsaye
nan take su ka yi ido hudu , Kim na ganin hakan ya juya cikin nitsuwa ya bar wajen
da kallo Kevin ya raka shi har sai da ya kurewa ganin shi sannan ya juya ya shiga Building din



▪ADRIAN


sai da ya yi wajen good 30 minutes bayan fitar su Esra kafin ya jiyo Muryar Ayden ya na fadin "
har yanzu ba ka gama ba mu tafi ? "

wani dan karamin murmushi Adrian ya saki kafin ya dago kai ya kalli Ayden
ya na tsaye gaban table din , ya na sanye da wasu Tracksuit white color ma su mugun kyau ,
rigar na da hula
ya saka wasu sneakers green kalar gashin kan shi , amma ba ka iya ganin face din shi dan ya
saka Face mask , da wasu glass kamar medical glass , amma su na dan duhu kadan ba ka iya
ganin idanun shi

" tun dazu kai na ke jira , ya ? a kawo maka coffee ? " Adrian ya fada

girgiza mishi kai Ayden ya yi a hankali ya na fadin " No , idan ka gama tashi mu tafi kawai "

" okay mu tafi " ya fada ya na tattare papers dinshi , waje guda sannan ya mikawa Ayden laptop
din shi
ba musu Ayden ya karbi laptop din , su ka fara takawa a tare su ka bar wajen

har su karaso wajen Table din da su Esra su ka zauna kawai sai ya ji ya taka wata paper

cak ya tsaya ya na kallon paper din kassan kafar shi
a hankali ya sunkuya ya dauki paper din ya na kallon ta kafin ya kalli table din da su Esra su ka
zauna , har yanzu ba a gyara table din kawai sai ya yi tunanin ko na wanda ya zauna a wajen
ne

da sauri ya taro Ayden da ya nufi kofar fita ya na fadin " Ayden wait two minutes please "
a hankali Ayden ya juya , ya gyada mishi kai allamun okay

wani dan karamin murmushi Adrian ya yi kafin ya nufi reception ya na fadin " excuse me ,
wanda su ka zauna a cen sun manta wannan , da allamun kuma ya na da mahimanci "

wani cool murmushi Safna ta sakin mishi kafin ta ce " okay , na gode , za mu yi kiran su mu
mayar musu "

" okay " Adrian ta fada , ya na shirin dago paper din na hannun shi su ka kubce
da sauri ya sunkuyo ya dauki takardun shi kafin ya mikawa Safna paper din da ya tsinta kafin ya
juya ya bi bayan Ayden su ka bar wajen

kallon paper din da kyau Safna ta yi , cen kassa a geffen dama ta ga an rubuta ONE WORLD
TRADE CENTER , allamun da ga companyn su Esra paper din ha fito

a hankali ta juya ta kalli dayar receptionist , cikin sanyin murya ta ce mata " Please duba min
cikin register First client din mu na yau , minene sunan shi "

ba musu ta duba register din gaban ta kafin ta ce " Esra yahaya , around 7h20 su ka shigo
wajen nan "

" okay , na gode " Safna ta fada ta na murmushi kafin ta ninke paper din ta saka cikin bag din ta

bangaran Adrian kuwa ya na fitowa ya tardo Ayden zaune cikin wata dankareriar mota fara kal
ta ji da gani , irin motar da sai wane jikan wane ke iya shigar ta ba banza bare ba , dan tayoyin
ta ma sun isa daukar ido

kai tsaye wajen driver ya nufa ya shiga dan ya San halin abokin nashi , ba ya son tukin mota ,
idan kuma ya ce zai yi tukin to tabbas mutuwa zai tunkara dan ba karamin gudu ya ke ba kamar

zai tashi sama

tada motar Adrian ya yi ya na fadin " ina za mu je ? "
cikin nitsuwa Ayden ya ce mishi " One world trade center , ina son na yi wa kevin magana a kan
tafiyar da za mu yi Washington dan ganin sabon building din da mu ke shirin budewa a cen , ina
son mu ware Space din restaurant , at least ina son mu yi two type na restaurant a ciki "

wani dan karamin murmushin geffen fuska Adrian ya yi kafin ya ce " wai me ya sa harkar abinci
ke burge ka ? ka na fa cikin Top ten din billionaire din United State of America baki daya "

" na sani , kawai restaurant din ne ke burge ni , yau Friday , ina fatan ka sa a shirya abincin da a
ke aikawa gidan marayu ? "

" yeah , ban manta ba , ai ko wace Friday abu na farko da ka ke fara tambaya shi ne Adrian ka
sa a shirya abincin da za a kai gidan Marayu ? Adrian ka sa an shirya kayan da za a kai gidan
marayu ? Adrian ka tura kudin da na ce ka tura gidan marayu ? wadanan tambayoyin kamar a
bakin ka a ka yi su , but ina jin dadin hakan gaskiya , kar ka damu na yi duk wani abun da ka ce
"

" okay " Ayden ya fada a takaice

da ga haka ba wanda ya sake ce ma wani ufan har su ka karaso wajen wani traffic light
a hankali Adrian ya yi parking din motar , ya na jiran a ba su izinin wucewa

a hankali ya juyo ya kalli Ayden , ya ga ya lumshe idanunshi ya tafi duniyar tunanin shi
wani cool murmushi Adrian ya saki kafin ya juya ya ce " me ka ke ji in ka na tare da ita ? "

kai tsaye Ayden ya ce mishi " peace " a takaice da allamun ba ya cikin hayacin shi
murmushi mai dan sauti Adrian ya yi kafin ya ce " ka yi a hankali , kar plan din ka ya juye maka "

shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba , da allamun ya lula duniyar tunanin shi bai ma san
abun da ya ke ba
a haka har traffic light din ya nuna green , Adrian ya ja motar su ka bar wajen
[17/02 à 14:02] : SOYAYYAR GASKIYA
__________________

TRUE LOVE

( A HEART TOUCHING LOVE STORY )




STORY & WRITING BY : MEERAH







GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY







TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i







يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ





BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM

{P A G E 13 & 14 ❤}








a haka har su ka karaso one world trade center , sai da Adrian ya yi parking din motar a parking
space sannan ya tabo Ayden cikin sanyin murya ya ce mishi " ta hanyar sirri yanzu ma za ka
shiga ko kuwa ? "

slowly Ayden ya ware idanunshi , ya sa hannu ya bude kofar motar ya na fadin " no , mu je
kawai , two minutes sun isa " ya kai karshen ya na sauka ya nufi hanyar shiga building din

cikin nitsuwa Adrian ya kashe motar ya sauko ya bi bayan Ayden



______________________________________



▪ESRA


da sauri² ta ke tafiya ko kallon gaban ta ba ta yi , idanun ta cike da ruwa , fuskar ta a marairaice
kamar za ta yi kuka , kamar za ta yi kuka ta ke fadin " shikenan ta kare min , in ban samo
takardar nan ba wlh mutuwa zan yi "

ta na gama fadar haka kawai ta ji ta bugi kirjin mutun da karfi ,
fuuuuu ta yi baya za ta fadi ta na sakin wata yar karamar kara ta datse idanunta da karfi
cikin zafin nama Ayden ya kai hannu ya damko kugun ta ya taro ta ba ta kai kassa ba
da sauri ta kai hannu ta riko damtsen shi da kyau ta

cak ya tsaya ya na kallon face din ta , ta wani lumshe idanunta ta na cije lips din ta na kassa
gwanin burgewa
lokaci guda ta tafi da imanin sa , dan ba karamar fadawa ya yi ba

su na a haka Adrian ya karaso wajen , ya na ganin yanayin da abokin shi ke ciki ya ida isowa da
sauri ya na fadin " Ayden , are you okay ? "

a dubu dari Esra ta ware idanunta jin an ce Ayden , idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin
nashi duk da ya na sanye da glass ba ta iya ganin su
lokaci guda idanun su su ka sarkafe cikin na juna ,
shi kuwa Adrian sai pic ya ke musu dan ba karamin kyau su ka yi ba kamar irin masoyan nan na
cikin film

haka ma duk wanda ke cikin hall din cak ya tsaya ya na kallon
su dai ba su ma san abun da ke faruwa a zagaye da su ba
wata boyayyar Ajiyar zuciya Ayden ya sauke kafin ya mike a hankali ya gyara tsayuwar shi ya
tallabo ta ta mike tsaye

su na mikewa tsaye ko Kebin ya iso wajen ya na fadin " Ayden , me ya faru ? " ya kai karshen
ya na tsayawa geffen Ayden

ya na ganin Esra ya saki wani dan karamin tsaki ya na fadin " Miss Esra , you again ? what are
you doing here ? "

lokaci guda Kuka ya kubce mata , ta bude baki har wata yar kerma ta ke
ta na shirin magana Ayden ya daga mata hannu allamun ta yi shiru
ba musu ta yi shiru ta na sunkuyar da kai hawaye na zubo mata bibiyu

cikin sanyin murya Kevin ya ce " Ayden , Adrian , ku tafi office di na ina zuwa , Miss Esra , koma
office din ki "

tun bai rufe bakin shi ba Esra ta raba ta geffen Ayden ta bar wajen da gudu ta na kuka

sai da ta bar wajen sannan Ayden ya juyo ya kalli Kevin ya ce " me ya faru ne ? "
wank dan karamin tsaki Kevin ya yi ya na fadin " nothing , kawai ba ta meda hankali kan aikin ta
, shi ne na yi mata magana , mu tafi "

" no , in mun je gida mun yin maganar , akwai inda zan je yanzu , Adrian mu tafi " ya kai
karshen ya na fara takawa ya fice wajen Adrian na biye da bayan shi

shi ma Kevin bayan su ya bi ya bar wajen dama fito ya ke son yi
bangaran su Ayden kuwa , ya na isa wajen motar su ya shiga wajen driver , tun kafin Adrian ya
iso ya tada motar

da sauri Adrian ya nufe shi ya na fadin " Ayden please sauko zan yi driving , ban shirya mutuwa
ba please "

" za ka shiga ko na tafi ? " ya fada cikin wani yanayi kamar ran shi a bace ya ke
da sauri Adrian ya zagayo geffen me zaman banza ya shiga ya zauna

ya na zama Ayden ya tada motar ya bar wajen a 360 kamar zai tashi sama , ga shi kuma ya
danne horn , ya ki saki
da sauri motoci ke rabewa gefe su na ba su waje har police din da ke kula da traffic su ka yi
kokarin tsayar da shi amma ya ki tsayawa

sai da ya yi ten minutes ya na irin wannan tukin kafin ya ja wani mugun burki sai da kan shi ya
bugi steering motar , shi ma Adrian kan shi ya bugu a gaban motar

slowly su ka dago kawunan su a tare , sannan Adrian ya ce " you're mad ? kashe ni ka ke son yi
ko kuwa ? "

a sanyaye Ayden ya ce mishi " i'm sorry , idanu na ne su ka rufe "
wani dan karamin tsaki Adrian ya ja kafin ya ce " sauko na mayar da mu gida , ni yunwa ma na
ke ji "

cikin nitsuwa Ayden ya ce mishi " mu fara biyawa gidan marayu , kuma gidan ka za mu tafi ba
zan koma ya yanzu ba "

" okay , yadda ka ke so haka za a yi " Adrian ya fada ya na bude kofar geffen shi ya sauko
Ayden kuma maimakon ya sauko kawai sai ya matsa ya koma wajen mai zaman banza dan ba
ya da ra'ayin saukowa ya shiga yin wani zagaye

shi dai Adrian ba abun da ya ce ya shiga wajen driver ya tada motar ya reversing din ta , ya
kama hanyar gidan marayu
cikin abun da bai fi five minutes ba su ka iso
kar ku so ku ga yadda yaran ke farin ciki ganin Ayden da Adrian , sun samu kyakyawan tarba ,
ga yaran turawa ko da mugun shiga rai ji na yi kamar na sace guda na gudu

haka zalika Ayden ya ji wani mugun sanyi a ranshi ganin yaran nan , duk ya na sanye da face
mask amma sai da ya yaran nan su ka gane shi , kenan sun san me kula da su
Ayden kuma bai yi mamakin yadda a ka yi yaran su ka gane shi ba , sai da ya yi musu wassa
kamar wani familyn su sannan ya yi musu albishir zai mayar da su makaranta baki daya kuma
shi zai dauki nauyin karatun su

ba yaran ba har mai kula da gidan marayu sai da ta yi farin ciki kamar ta yi kuka , ta na yi wa
Ayden godiya duk da ba ta san ko wanene ba , ita dai kawai ta san kowace Friday ya na
kawowa yaran abincin da kaya wani lokaci har kudi ya ke turawa a kai su shopping , amma ba
ta taba sanin wanene Ayden ba

sai da su ka yi wajen one hour a gidan marayu kafin su baro shi , su ka nufi gidan Adrian
na san kuma ku na son ki san dalilin shi na kula da yaran nan kamar yan uwan shi , nan gaba
kadan za ku sani amma ba yanzu wajen ba
ku dai ku ci gaba da bibiyar labarin dan yanzu a ka fara

kamar kullum ku na tare da alkalamin MEERAH ✌


[18/02 à 11:55] : TRUE LOVE






( A HEART TOUCHING LOVE STORY )




STORY & WRITING BY : MEERAH






GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login