Showing 27001 words to 30000 words out of 48110 words

Chapter 10 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf

" Esra ta fada a sanyaye

cikin nitsuwa Arthur ya ce " kin ga face din shi ? ki na iya gane shi kenan ? "
a hankali Esra ta girgiza mishi kai ta na fadin " no , ban ga face din shi ba saboda ya na sanye
da face mask , amma ina iya gane saurayin da ke tare da shi na ji sir Kevin ya kira shi da Adrian
"

" ta baci , da a ce kin ga face din shi da za mu iya gano inda ya ke har mu yi mishi maganar
abun da ke faruwa " fadin Arthur

ya na gama rufe bakin shi Esra ta ce " no , yanzu ma ba ta baci ba , wannan paper din za ta yi
mana anfani dan kara karfafa hujjojin mu wajen shi , abu guda mu ke bukata kawai file din office
din sir Kevin "

Cherry : " to yanzu ya za mu yi mu samo file din , kin dai ji uban security din da ke office din Sir
Kevin "

Arthur : " idea din ku za mu bi , ta shiga ta System of climatisation "

Esra : " kai fa ka ce it's not a good idea , za mu iya bacewa ko zafi ya kashe mu "

wani dogon nunfashi ya ja kafin ya ce " That's why mu na bukatar ground plan din building din ,
cikin sa'a ko na samo daya da ga cikin architects din da su ka gina building din , but ya ce zai
dauki two or three days kafin ya samo mana ground plan din "

a tare Esra da Cherry su ka washe baki su na dan zaro idanu kafin su dago hannu su yi tapi ,
sannan Esra ta ce " Fine , yanzu plan din mu zai fara , sai mun kawo karshen wannan
azzalumin mai fuskar shanu " ta fada cikin bacin rai da allamun har yanzu ta na jin haushin
fadan da ya yi mata gaban mutane

a tare Cherry da Arthur su ka yi dariya dan sun gane abun da ke cikin zuciyar ta
har Cherry ta bude baki za ta yi magana Wayar Arthur ta fara ringing , a hankali ya kai hannu
cikin aljihun shi ya fiddo wayar ya na kallon screen din

a hankali ya mike tsaye ya na fadin " girls ina ga zan tafi , akwai in da a ke jira na "

" okay , see you next time " Esra da Cherry su ka fada a tare
bai ce musu komai ba ya fara takawa ya bar wajen ya fice restaurant din ya bar su nan
" ya kamata ni ma na tafi " Cherry ta fada

a hankali Esra ta kai hannu ta tattare kayan ta , ta dauki bag din ta ta na fadin " mu tafi " ta
qarashe maganar ta na mikewa tsaye
a hankali ita ma Cherry ta mike su ka baro restaurant din
su na fitowa su ka yi hannun riga , Esra ta yi dama , Cherry ta yi hagu

a hankali ta ke tafiyar ta cikin nitsuwa har ta karaso greenwich street
dan ta na mugun son ganin Kim , dan tun lokacin da ya baro apartments din su ta ke son ganin
shi ta ga in ya na cikin koshin lafiya

kai tsaye Dan kangon ban da ya ke zama ta nufa ta na sallama a hankali duk da ta san ba za a
amsa mata ba
cen ta hango shi zaune ya na sanye da wani crazy jeans blue , da t-shirt white color ya saka
wasu Thong farare a kafafun shi , yatsun kafar shi sun fito dogaye da su farare kal gwanin
burgewa

ya tirje wannan gashin kan nashi har ya rufe mishi idanu , ya na rike da sigari da hannu guda ,
gudan kuma ya na rike da gongwanin maltina ya na sha ya na busa sigarin shi

cikin nitsuwa Esra ta karaso gaban shi ta tsaya ta na fadin " Kim , please ba na ce ka daina
shan wannan abun ba " ta kai karshen ta na kai hannu ta buge tabar da maltinar

a dubu dari ya dago kai , ba karamar razana Esra ta yi ba har wani baya ta yi ta na dafe saitin
zuciyar ta bare ko idanun shi sun yi jazir
cikin bacin rai ya bude baki ya ce mata " why ? me ma ki ke yi a nan ? wai ba za ki iya ba ni
lafiya ba ? me na yi miki ki ke son takurawa rayuwa ta ? "

ita dai ta tsaya ta na kallon yadda ya ke yi mata magana cike da bacin rai da allamun a buge ya
ke
wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke ta matso a sanyaye ta ce mishi " Kim , please calm
down "

da sauri ya katse ta da cewa " stop ! ba na bukatar kyautatawar ki , please let me , let me , babu
abun da ke tsakani na da ke so let me " ya na gama fadar haka ya mike a zafafe zai bar wajen

da sauri ta riko hannunshi ta na fadin " please Kim wait , ka manta alkawari da ke tsakanin mu ?
"

da karfi ya kwace hannun shi ya tura ta baya ya na fadin " forget that , i don't need you in my life
, i'm happy without you " ya kai karshen ya na juyawa

da sauri Esra ta bi bayan shi ta na fadin " zan saya maka chocolate "
cak ya tsaya jin ta ce chocolate , abun da ya fi so fiye da komai a rayuwar shi

Esra na ganin ya tsaya ta saki wani cool murmushi ta karaso geffen shi ta tsaya ta na fadin " ko
ba ka son chocolate din na tafi ? "
shiru ya yi bai ce mata komai ba har cikin zuciyar shi ya na son chocolate a yanzu

ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya ga ta yi gaba ta na fadin " shikenan tun da ba ka so na
tafi abu na "

cikin nitsuwa ya taro ta da cewa " ina so "
cak ta tsaya ta na sakin wani dan karamin murmushin geffen fuska , ta samu abun da ta ke so

slowly ta juyo ta mika mishi hannu ta na fadin " okay , let's go "
a hankali ya tako ya riko hannunta , kamar wani karamin yaro ta fara jan shi su ka bar wajen , ta
na sakin wani dan karamin murmushi shi kuma ya sunkuyar da kai ya na kallon kafafun shi

kun san yadda yanayin garin US ya ke kowa harkar gaban shi ya ke hakan ya sa ba wanda ya
damu su kowa na aikin shi

a haka har su ka iso wani market , sai da su ka shiga ta saki hannun shi sannan ta ce ya jira a
nan
ba musu ya tsaya waje guda ya na kallon ta ta nufi fridge din wajen , ta bude ta kwashi
chocolate har wajen goma sannan ta dawo ta nufi wajen biya ta , ta biya kudin
a ka saka mata chocolate din cikin leda , sannan ta dawo inda ta bar shi ko motsi bai ba

a hankali ta mika mishi hannu allamun su tafi
ba musu ya riko hannunta su ka bar wajen
sai da su ka dan yi nisa sannan ya ce mata " ban chocolate di ta "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " chocolate din ka ko tawa ? in ka na son chocolate din
nan ka bi ni a hankali "

shiru ya yi bai ce mata komai ba , ya na biye da ita dan ba ya jin zai iya tafiya ba tare da ya
karbi chocolate din nan ba

a haka har su ka iso wani kyawatencen garden cike da mutane musaman yara kowa na sha a

nin shi su na wassa su na dariya gwanin burgewa

sai da su ka karaso wajen wani banci sannan ta saki hannun shi ta zauna ta na fadin " Oya , Sit
down "
ba musu ya zauna geffen ta ba tare da ya ce komai ba

wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta kai hannu ta fiddo chocolate guda ta na fadin " zan
yi maka tambaya , duk lokacin da ka ba ni amsar da na ke so zan ba chocolate guda , ka yarda
? "

slowly ya gyada mata kai allamun Eh ya yarda

" okay , First question , minene cikaken assalin ka ? "
kai tsaye ya ce mata " ba ni da "
" no , impossible a ce ba ka da assali , minene sunan momyn ka , da Daddyn ka ? "
a takaice ya ce mata " gidan marayu na girma "
nan take yanayin face din ta ya sauya , kenan maraye ne ? ta tambayi kanta
slowly ta mika mishi chocolate din
a hankali ya kai hannu ya karba , kafin ya bude ta ya fara ci cikin nitsuwa

hannu ta kai ta fiddo ta biyun ta na fadin " tun da gidan marayu ka taso hakan na nufin ba ka da
yan uwa ko guda , right ? "

a hankali ya gyada mata kai allamun Eh
dan lumshe idanu ta yi a hankali kafin ta ajiye mishi chocolate din geffen shi , ta kai hannu ta
fiddo ta ukun ta na ce mishi " That's why ka ke shan wine saboda rage kadaicin da ka ke jin
kanka , right ? "

yanzu ma gyada mata kai ya yi a hankali Allamun Eh ya na ci gaba da cin chocolate din shi

a hankali ta ajiye mishi chocolate din sannan ta fiddo ta hudu ta ce mishi " yanzu me ka ke yi da
rayuwar ka ? a ina ka ke barci ? a ina ka cin abincin ? na san dai ba ka da aiki , ko kuwa ? "

ba tare da ya kalle ta ba ya ce " security a nightclub idan dare ya yi , ta haka na biya kudin
apartment din da na ke zama a ciki "

cikin sanyin ta katse shi da cewa " ka na da apartment ka ke zuwa ka kwana cikin wannan
kangon ? "

shiru ya yi bai ce mata komai ba
shiru ta yi ta na jiran amsar shi amma bai ce mata komai ba
sai da ya gama shan chocolate din ya kai hannu ya dauki guda cikin wadda ta ajiye mishi gefe
ya bude ya fara ci

ta na ganin ta tuno ashe ba ta ajiye mishi chocolate din ba
da sauri ta ajiye chocolate din hannun ta , ta dauko wata ta na fadin " ba ka ban amsar tambaya
ta ba "

sai da ya hadiye chocolate din bakin shi sannan ya ce mata " saboda na fi jin dadin zama ni
kadai , babu wanda zai takura min , amma ga shi yanzu ki na son ki takura min "

wani cool murmushi ta saki kafin ta ajiye mishi chocolate din ta dauki wata ta na fadin " ban
takura maka ba , kawai ina son na gyara maka rayuwa ne , ba dan ka na maraye ba za ka
meda kanka mara gata , tabbas ban san ka ba kuma ba ka san ni ba amma zuciya ta ba za ta
lamince ganin ka cikin wannan halin da ka ke jefa kanka , wine da taba babbar illa ce ga
rayuwar ka "

" akwai ma su shan taba da wine dayawa a garin nan , why sai ni za ki taimakawa ? "

murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " ai kai ma ka taba taimaka min lokacin da samarin nan
su ka sace min bag di ta , ka ga ko dan hakan zan iya taimaka maka , yanzu fada min minene
favorite habit din ka , wanda in ka na yin shi ka na jin duk damuwar ka tafi gushe har ka daina
tunanin shan wine ? "
sai da ya dauki wajen two minutes bai ce mata komai ba kafin ya bude baki ya ce mata "
cooking "

wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ajiye mishi chocolate din ta kai hannu ta dauki
guda ta ce mishi " Fine , da ga yau duk wajen karfe 8 na dare ka tardo apartment di na , za mu
yi girki a tare dan ni ma na iya girki sosai "

a hankali ya dago kai ya kalle ta ya ce " specially with chocolate ? "

gyada mishi kai ta yi ta na fadin " yeah , with chocolate , za ka dinga zuwa ? "
slowly ya gyada mata kai allamun Eh
" Fine , ka ga in ka daina tunanin wine , za ka daina shan ta , in kuma ka daina za ka ga komai
na rayuwar ka ya sauya "

" why ki ka damu da ni haka bayan ba mu hada komai da ke ba ? "

wani dan karamin murmushin geffen fuska ta yi mishi kafin ta ce " ni ma ban sani ba , kawai
zuciya ta ce ta ke ce min na taimaka maka , kuma ni ina bin duk abun da zuciya ta ke fada min "

" a ka je duk abun da na fada miki yanzu karya ne , a ka je yadda ki ke tunani ba haka na ke ba
, wannan rayuwar tawa duk basaja ce "

a sanyaye ta ce mishi " Idan har duk abun da ka fada min karya ne , ba zan ji komai ba saboda
kai abokina ne , kuma tsakanin abokai sai dai wassa da dariya ba fada ba "

" abokai ? we are friends ? "

gyada mishi kai ta yi ta na fadin " yeah we are friends , ko ba ka son zama abokina ? "
" ina so , ko dan ki dinga saya min chocolate " ya kai karshen ya na kai chocolate din shi a baki

wata yar karamar dariya Esra ta yi dan maganar shi gaskiya ta ba ta dariya wai zai zama abokin
ta ko dan ta dinga saya mishi chocolate
[24/02 à 09:13] : SOYAYYAR GASKIYA
__________________

TRUE LOVE




( A HEART TOUCHING LOVE STORY )




STORY & WRITING BY : MEERAH






GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ




BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM




{P A G E 21 & 22 ❤}




sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta ce mishi " kenan saboda chocolate din ne za ka zama
friend din na ? "

cikin ko in kula ya ce mata " yeah , rayuwar yanzu babu wanda ke zaune da kai da zuciya guda
sai in ya na son wani abu wajen ka , kowa abun da zai gyara shi ya ke dubawa , ni ban san me
ya sa ki ke son zama friend's di ta dan ba ni da komai kuma ba za ki samu komai ba sai
problems , amma ni zan zama friend's din ki dan ki dinga saya min chocolate , kin ga advantage
di na na ke dubawa "

wani dan karamin murmushi geffen fuska Esra ta saki kafin ta ce mishi " abun da ke fada
gaskiya , kowa advantage din kan shi ya ke dubawa , but ba zan ga laifin ka ba ko da a ce ka yi
anfani da ni dan samun abun da ke so , asali ma zan ji dadin ta sanadiya ta ka samu abun da
ka ke har ka yi farinciki , na san ko ba komai wata rana in ka tuno da abun nan za ka tuno da ni
"

shiru ya yi bai ce mata komai ba ya na shan chocolate din shi cikin konciyar hankali
ya na a haka kawai ya ga wata ball ta buge shi a kafa
slowly ya dago kai ya ga wani dan yaro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login