Showing 3001 words to 6000 words out of 48110 words
Chapter 2 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf
lift kai tsaye hawa na 97 ta nufa dan ta na cikin manya manyan ma su
aiki a wajen Sai da ta dauki wajen 2 minutes kafin lift din ya bude ta fito
Wajen cike da ya ke da mutane sai zirga zirga su ke yi , kowane rike da file a hannun shi sai
sauri su ke yi
Da sauri ta nufi wani dan madaidaicin office na glass
Ta na isa ta daura hannun ta saman finger print nan take door din ta bude kan ta
Har ta daga kafa za ta shiga , ta jiyo Muryar wata yan mata a bayan ta ta na kiran sunan ta
Slowly ta juya ta na ganin yarinyar ta saki wani cool murmushi sannan ta shiga cikin office din ,
ta na shiga ita ma yarinyar nan ta shigo
Yarinyar cikakiyar baturiya ce a shekaru za ta kai 24 haka , ta na sanye cikin wata gown dai'dai
guyiwa navy blue , ba laifi ta hadu
Sai da Esra ta nufi desk din ta , ta zauna saman chair sannan ta ce " Hi ! "
ajiye bag din ta ta yi saman desk sannan ta juyo ta kali baturiyar nan ta ce " Good morning
Cherry "
Gyada kan ta Cherry ta yi sannan ta ce " lafiya ki ka yi late haka , ko dai har yanzu ba su gyara
Lift din building din ku ba , ya kamata ki sauya apartments gaskiya Esra "
Dan karamin murmushi Esra ta yi ta na zama saman chair din ta , ta ce mata " Cherry in na
sauya na tafi ina , kar ki manta ba ni daya ba na ke zaune ciki ba , Sun gyara lift din tun
shekaran jiya , Wlh tsotsayi ne ya kai bin GREENWICH STREET a tunani zan fi sauri , kawai na
hadu da wasu yan iska su ka kwace min Bag di ta da waya ta "
" No , har yanzu a na yaayin wannan abun ? To ya a ka yi ki ka karbo su ? "
Dan karamin tsaki Esra ta yi kafin ta ce " Wani dan iskan kamar su ya amso min su , shi ma da
kyair ya ban wayar cewa ya yi sai na ba shi wani abu , ni kuma babu cash a jiki na "
Yar karamar dariya Cherry ta yi sannan ta ce " Esra akwai ki da abun da dariya , wai wani dan
iskan kamar su , inda dan iskan ne ba zai medo miki kayan ki ba sai dai ya yi gaba da su , kin
san dama raba sata ga barawo........ "
Ba ta karasa maganar ta ba wani bature ya turo kofar office din Esra ya shigo ya na sanye cikin
Suit Bakake
Ya na shigowa ya nufi wata yar sofa da ke fuskantar Desk din Esra
Wani cool murmushi ya saki kafin ya ce " Miss Esra yau ma late , hope dai ba ki hadu da
wannan mai fuskar shanu ba , dan fa yau a sama ya ke "
Yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " ni ko na hadu da shi , har mu ka buge juna , ai shi
dama kullum sama ya ke "
Wannan karan a tare duka su ka yi dariya sannan baturen ban ya daura da cewa " Amma kin yi
sa'a fa , yanzu haka abun da na ji ya sallami ma'aika ta har biyu ba su ji ba , ba su gani ba "
Dan zaro idanu Cherry ta yi ta na komawa geffen shi ta zauna ta ce " please da gaske ka ke
Arthur ? "
Gyada mata kai ya yi ya na fadin " da gaske na ke , yanzu haka ma sun bar building din "
" Toooo , lafiya ya sallame su haka kawai " Esra ta fada cike da tsoro cikin zuciyar ta
Mikewa tsaye Arthur ya yi , ya dawo bakin kofar office din ya dan soko kai , ya leka ya ga ba
kowa sannan ya koma ya rufe kofar , ya rage sautin Muryar shi ya ce " ni ma ban sani ba amma
na ji an ce wai , ana fitar da kudi da ga cikin account din companyn , last relieve ma babu one
Milliard , kuma ba yanzu ba a ka fara , in dai wannan satar ta ci gaba ina ga Dukan mu sai dai
mu nemi wani wajen aikin daban "
" Arthur , one milliard fa ka ce ? " Cherry ta fada
a hankali ya gyada mata kai ya na fadin " Abun da ya fi Hakan ma , kin san fa PDG din
companyn nan sam bai damu da abun da ke faruwa cikin ta ba , karewar zancen , big bro din
shi ke kula da gidan nan , da sauran companyn shi "
" Wait , ka na Nufin Sir Kevin ba shi ne mamallakin Companyn nan ba " Esra ta fada cike da
rudu har da dan zaro idanu
TRUE LOVE
__________________
SOYAYYAR GASKIYA
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : Princess Meerah
THE WRITER'S OF
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE
HASKE BIYU ( YAR JARIDA )
TAURIN ZUCIYA ( RETURN )
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN
NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb
يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
PAGE 3 & 4
Har hada baki Arthur da Cherry su ka yi su na ce mata " wai ke dama a tunanin ki shi ne mai
wajen ? "
a hankali ta gyada musu kai ta na fadin " Ni na zata shi ne mai wajen , saboda shi ke kula da
komai tun lokacin da na fara aiki a wajen nan , kuma ban taba jin wani ya ce akwai wanda ke
sama da sir Kevin "
dan tabe baki Cherry ta yi kafin ta ce " tabb ki na cikin Duhu ko "
Arthur ne ya katse ta da cewa " Wannan companyn da ki ke gani , ni da kai na ban taba ganin
mai ita ba , Abu guda na sani , sir Kevin big brother din shi ne , Da farko Companyn ta
mahaifinsu ce , amma ya kamu da ciwon zuciya a tunanin shi mutuwa zai shi ya sa ya
mallakawa yaron shi na biyu duk wata company da ya mallaka , shi kuma ya ba wa Sir Kevin
ragamar kula da su baki daya "
" me ya sa ba zai kula da kayan shi ba , tunda mahaifin nasu bai mutu ba , ya meda mishi
companyn shi in ba zai kula da su ba "
" Ni ma haka na gani , yanzu ga shi bai ma san abun da ke faruwa cikin companyn shi ba "
Cherry ta fada ta na komawa geffen Arthur ta zauna
ta na zama ya ce mata " ba mamaki sir Kevin da kan shi ke satar kudin , ko ni na ji an ce
mahaifin mu ya ba wa little brother di na duk abun da ya mallaka , ba zan hakura da sauki ba "
hararrar wassa Esra ta yi mishi kafin ta ce " kai dai Arthur , a dinga fadin gaskia , Sir Kevin ta ya
zai iya satar kudin dan uwan shi "
mikewa tsaye Arthur ya yi ya na fadin " Humm a na ki tunanin ko , amma ai mu na tare da ke ,
za ki gani " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya fice Office din
da kallo su ka raka shi har sai da ya fita sannan ita ma Cherry ta mike ta na fadin " ya ne yau za
mu je shan coffee ne ? "
" No gaskiya yau ba zan samu dama ba , may be tomorrow " Esra ta fada ta na dan marairaice
fuska
wani cool murmushi Cherry ta saki kafin ta gyada mata kai a hankali ta sa kafa ita ma ta fice
office din , su ka bar Esra ita daya cikin office din
su na fita ta fido laptop din ta da ga cikin bag din ta , ta fara aikin ta
a haka ta ci gaba da aikin ta ita daya cikin nitsuwa har wajen karfe 6 na yamma sannan ta baro
building din
a hankali ta ke Tafiyar ta saman Titi , ta na taku cike da nitsuwa ta na kallon gaban ta
kamar da ga sama kawai ta ji an kwace mata bag din ta ta baya
dum ta ji gaban ta ya fadi , a razane ta juya ta na shirin ta saki kara
ta na ganin shi ta rufe bakin ta , ta na dan lumshe idanun ta , ta sake bude su
ko sannu bai ce mata ba ya bude bag din ta ya na leko ya ce " where is my chocolate ? "
" ka ga malam ka ban jaka ta , ni ba wani chocolate da gare ni " ta fada ta na mika mishi hannun
ta allamun ya bata jakar ta
a hankali ya juya ya fara takawa ya na rike da bag din ta ta
da sauri ta bi bayan shi ta sha gaban shi ta marairaice fuska ta ce " please ka ban jaka ta , mu
tafi zan saya ma "
tsaya wa ya yi ya na kallon ta na dan lokaci kafin ya ce " Mu tafi yanzu "
" shikenan ban jaka ta , sai mu tafi "
ba musu ya mika mata jakar ta ,
da sauri ta sa hannu ta karba ta na sauke ajiyar zuciya sannan ta ce " yanzu idan na saya maka
chocolate din shikenan mun rabu ? "
a hankali ya gyada mata kai allamun eh
wani dogon nunfashi ta ja kafin ta ce " shikenan mu tafi " ta fada ta na fara takawa ta bi ta
geffen shi ta wuce
a hankali ya juya shi ma ya bi bayan ta
a tare su ka yi tafiyar su ba wanda ke ce ma wani ufan har su ka iso cikin wani dan market ya
na biye da bayan ta
su na shiga ta nufi kai tsaye wajen Fridge , ta bude ta dauko Chocolate har biyar sannan ta rufe
ta dawo ta nufi reception ta biya kudin su ka fito market din
su na fitowa ta mika mishi chocolate Hudu ta rige gudar
kallon chocolate din ya yi kafin ya ce " Dayar fa ? "
hararrar shi ta yi ta na fadin " tawa ce , ka karba mana "
a hankali ya girgiza mata kai ya na fadin " no , ni wacen na ke so " ya fada ya na nuna dayar da
ke cikin hannun ta guda
kallon shi ta yi baki sake cikin zuciyar ta ta ce " amma wlh ya raina min hankali "
ba ta gama fadar haka ba kawai ta ji ya kwace mata chocolate din
a razane ta dawo cikin hayacin ta na shirin yi mishi magana ta ga ya fara takawa ya yi gaba
dan karamin tsaki ta ja kafin ta fara takawa ita ma a hankali har ta kamo shi
har ya bude Chocolate din ya fara ci
cikin konciyar hankali ya ke cin chocolate din nan , har wani lumshe idanu ya ke yi , da allamun
ya na son chocolate sosai
kawai sai ji ta yi ta tsargu da kallon shi , ba karamin burge ta ya yi ba har sai da ta saki wani
cool murmushi ba ta sani ba
ta na a haka kawai ta jiyo Muryar shi ya na fadin " daina kallo na haka kar ki cinye ni "
da sauri ta kauda kan ta gefe ta na fadin " ni ba kai na ke kallo ba "
" uhm uhm to me ki ke kallo ? " ya tambaye ta dai'dai ya kai chocolate din shi a baki
" ni chocolate di na na ke kallo , wannan na ke so amma ka kwace min ita " ta fada ta na dan
turo baki , ita wai ta ba kallo ba
a hankali ya tsaya da ya tafiyar shi , cak ta tsaya ita ma kamar ya riko ta
slowly ya juyo ya kale ta ya ce " shikenan karbi kayan ki " ya fada ya na mika mata ledar
chocolate din dan ya cinye
kallon ledar ta yi kafin ta saki wani dan karamin murmushi mai sauti ta ce " amma ka raina min
hankali ko ? bayan ka cinye , rike ba na so " ta kai karshen ta na fara takawa
da sauri ya ce mata " ji mana yan mata "
cak ta tsaya da tafiyar ta , ta juyo a hankali ta na matse gera
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " please ko za ki kara min wata , ba ta ishe ni ba " ya kai
karshen ya na dan marairaice muryar shi
yanayin da ya yi mata maganar ba karamin tada mata gashin jikin ta ya yi ba , nan take ta ji
zuciyar ta ta fara duka uku uku kawai ta tsare shi da ido , su ka yi ido hudu babu ko kiftawa
a hankali ya daga mata gera allamun minene
da sauri ta janye idanun ta , ta na girgiza mishi kai kafin ta mike mishi sauran chocolate din
hannun ta
wani cool murmushi ya saki kafin ya tako a hankali ya tsaya gaban ta , ya kai hannu ya karbi
chocolate din ya na fadin " Thanks " da ga haka ya juya ya fara takawa
tsaya wa ta yi ta na bin shi da kallo , sam bai yi kama da wadanan bata garin ba , da ga yanayin
da ya ke maganar shi ma , cike ta ke da nitsuwa ga kaifin harshe duk yadda a ka yi wannan ba
bata gari ba ne akwai dai wata a kassa
sai da ta dan dauki lokaci ta na kallon shi kafin ta juya ita ma ta fara takawa ta nufi apartments
din ta , ba ta dauki five minutes ta iso
building din ya na da girma sosai , a killa zai kai hawa 40 , a kowane hawa kuma part 5 a
dakwai , duk da Parlour guda , Bedrooms biyu , toilet guda sai kitchen kuma dukkan su design
guda gare su kuma piece of furnitures din iri daya ne har colors din
ta na shigowa building din kai tsaye lift ta nufa , ta shiga ta Haye Floor na 10
ko da ta fito lift din wani dogon corridor ne da ga dama zuwa hagu , mai dauke da doors har
biyar
kofar lift din kuma ta na fuskantar kofar wani daki , an rubuta ROOM 52 da manyan harufa mai
launin White
hannun damar ta ta yi ta nufi Door ta Biyu an Rubuta ROOM 51 a sama ita ma
ta na isa ta kai hannu cikin bag din ta ta ciro key , ta saka kofar ta bude sannan ta zame key din
ta tura kofar ta shiga ta na sallama , sai da ta shiga sannan ta juya ta rufe kofar
sannan ta juya ta karaso cikin parlourn
ba laifi wajen a gyare ya ke masha Allah , duk furnitures din white and green color ne , da wata
yar karamar Tv plasma din ta
parlourn gaskia ba shi da laifi ya na da dan girma komai na ciki White and green colors ne a
geffen dama akwai wata yar karamar table allamun dining table ce mai chair biyu bayan