Showing 39001 words to 42000 words out of 48110 words
Chapter 14 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf
sai ta daura mishi takardun ta na fadin " i'm sorry "
bai ce mata komai ba ya meda takardun dayan hannun kafin ya sake mika mata hannu
kallon hannun ta yi da kyau sai a lokacin ta tuno ashe a kassa ta ke
slowly ta dago ta daura hannunta saman nashi , sannan ya taimaka mata ta mike tsaye ta na
yi mishi godiya
da murmushi a face din shi ya ce mata " Miss Esra , ya kamata ki dinga kallon gaban ki , sau
biyu yanzu ki na yin karo da shi , please kar a yi na ukun "
dan sunkuyar da kai ta yi ta na fadin " i'm so sorry , in sha Allah zan kiyaye , i'm sorry "
" okay , sannan a rage wannan late , gobe akwai meeting din da mu ka shirya tare da duk
ma'aikatan One world trade center , a cikin amphitheater ina fatan za ki kasance a lokaci "
" in sha Allah Sir , zan kiyaye " ta fada a sanyaye
wani dan karamin murmushi Adrian ya yi kafin ya raba ta geffen ta ya wuce ya bi bayan
Ayden
ya na jin ya fara takawa ta dago kai ta na sauke wata nanauyar ajiyar har da kai hannu saitin
zuciyar ta ta dafe kafin ta ci gaba da tafiyar ta amma wannan karan cikin nitsuwa har ta isa
office din ta
duk abun nan da ha faru a kan idon Kevin dan ya na tsaye ya jiyo bayan Ayden amma kawai
sai ya ga Esra ta kai mishi karo har ya taho zai yi mata magana Adrian ya tare shi bai san dalilin
ba , amma ya yanke shawarar kawo karshen wannan shirmen na Esra tun ba ta shiga hanyar
shi ba dan in ta shiga hanyar shi zai samu matsala babba
[28/02 à 08:18] : TRUE LOVE
__________________
SOYAYYAR GASKIYA
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : MEERAH
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb
يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{P A G E 27 & 28 ❤}
bangaran Esra kuwa kai tsaye Office din ta ta nufa , ta na shiga ta ajiye bag din ta ta fara aikin
ta
ko ten minutes ba ta yi ba da zama Cherry ta turo kofar office din ta shigo ta na sanye da wani
mini skert pink color da shirt white color mai dogayen hannu
da murmushi a face din ta ta karaso cikin office din ta na fadin " you're late Miss Esra "
wani dan karamin murmushi Esra ta yi kafin ta ce " wlh , akwai in da na biya ne , but i'm here
now "
" okay , amma kin yi late sosai fa dan yau na fada miki abu guda ya hana mu haduwa da Ayden
Brian "
slowly Esra ta dago kai ta kalle ta ta ce mata " ban gane ? "
" Ya dawo bakin aikin shi , but yanzu ya koma gida wai kan shi ke ciwo , amma an shirya
Meeting gobe duk ma'aikatan wajen sai sun hallata , si kar ki zo late gobe "
shiru dai Esra ta yi ba ta ce mata komai ba kamar mai tunanin wani abu
ta na a haka kawai ta ga Cherry ta mike
cikin sanyin murya Esra ta ce mata " ina kuma za ki je ? "
" zan koma aiki na mana , tun da mai wajen ya zo dole mu kama jiki , see you later " ta qarashe
maganar ta na nufar kofar fita ta fice
da kallo Esra ta raka ta har sai da ta fita sannan ta saki wani cool murmushi ta sunkuyar da kai
ta ci gaba da aikin ta
ta share wajen good one hour a haka kafin ta ji an turo kofar office din ta
wani dan karamin murmushi ta saki a tunanin ta Cherry ce ta dawo kawai sai ta ce " Ba kin ce
za ki kama jiki ba ? me ya...... "
ba ta kai karshen maganar ta ba sakamakon dago kan ta da ta yi ta ga Kevin tsaye bakin kofar
office din ta
Dum ta ji Zuciyar ta ta buga dan Kevin kamar tarmamuwa mai wutsiya ya ke , ganin shi a office
din ta ta san ba al'heri ba ne
a razane ta mike tsaye ta na dan zaro idanu ta ce " Good morning Sir , ku na..... "
ba ta qarashe maganar ta ba ya daga mata hannu ya katse ta ya na fadin " ina jiran letter din
barin ki aiki gobe a office di na , Miss Esra you're fired " ko amsar ta bai jira ba ya juya ya na
taku cike da nitsuwa ya fice office din
ko motsin kirki Esra ta kassa ta yi kawai ta tsaya ta kurawa kofar ido hawaye na zubo mata
bibiyu ,
a hankali ta yi kassa ta zauna saman chair din ta na sakin kuka kamar wata karamar yarinya
ta na fadin " yanzu tsakani da Allah ya zan yi ? ya sallame ni da ga aiki ? me na yi mishi zai
sallame ni ? " ta ke fada ta na kukan ta
ta na a haka kawai ta ga wani security ya turo kofar office din ya shigo fuska a daure tamau
a hankali ya karaso tsakiyar office din ya riko hannayanshi a baya ya ce mata " Sir Kevin ya ce
na raka ki waje , please don't waste my time let's go ! " ya fada ya na nuna mata kofar office din
ba musu ta tashi ta rufe laptop din ta ta saka cikin jakar ta sannan ta dauki handkerchief ta goge
face din ta sannan ta fara takawa jiki a mace ta nufi kofar office din
amma kafin ta fice sai da ta juyo ta kalli office din nata kallo na karshe sannan ta fita ta na
hawaye Security din nan na biye da bayan ta
kai tsaye Lift ta nufa ta shiga ta baro building din baki daya , sai da security din nan ya rakata
wajen building din sannan ya koma cikin building
a hankali ta ke tafiya idanun ta cike da hawaye ta na kuka kassa kassa , yanzu ya za ta yi ?
aikin nan shi kadai ne ya zaunar da ita US , in har a cen gidan su su ka ji labarin ta rasa aikin ta
, da kan shi mahaifin ta zai zo US ya meda ta Nigeria
yanzu ya za ta yi , ita kuma gaskiya ba ta jin za ta iya komawa Nigeria bayan ta sama sosai US
tsawan shekaru biyar yanzu , dan a nan ta yi karatun ta har a ka dauke ta aiki a one world trade
Center
gaskiya Kevin bai kyauta mata ba ba ta ji ba ba ta gani ba ya raba ta da aikin ta kawai saboda
son zuciya irin nashi
ta yi nisa cikin tafiyar ta kawai ta jiyo Muryar Kim a bayan ta ya na fadin " Miss chocolate , Miss
Chocolate "
ta na jin shi amma ba ta tsaya ba dan yanzu zuciyarta sam ba ta yi mata dadi
ta na a haka kawai ta ji ya kwace mata bag din ta ta baya
yanzu ma ba ta ce mishi komai ba ta ci gaba da tafiyar ta a sanyaye
a hankali ya matso geffen ta su ka jera ya na fara duba abun da ke cikin bag din ta ya na fadin "
Miss Chocolate , yau kuma da wuri ki ka sauko ? yau ba monday ba ? "
shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba amma ta na jin shi
sai da ya gama lalube bag din ta sannan ya dago kai ya kalle ta
nan ya ga ruwan hawayen da ta ke yi
a dan razane ya ce " la , Miss Chocolate , lafiya ki ke kuka ? ko dan na karbi jakar ki ne ? ki yi
hakuri ba dauka kin sayo min chocolate ne , I'm sorry ki daina kukan nan ni ba na son ganin
mutum na kuka , ni ma kuka ya ke saka ni "
ya na gama rufe bakin shi ko ta saki kukan kassa kassa ta datse idanunta
cak ya tsaya ya riko hannunta ya juyo ta su na fuskantar juna ya na kallon yadda ta ke kuka ido
a rufe hawaye na zubo mata bibiyu
duk da babu wani abu a tsakanin su amma gaskiya ba ya jin dadin ganin ta ta na wannan kukan
, ko dan chocolate din da ta ke saya mishi ya kamata ya yi wani abu
cikin sanyin murya ya ce mata " Miss chocolate , please stop crying , ki fada min kukan me ki ke
? wani ya ci zarafin ki ? ki fada min zan je na rama miki "
a hankali ta girgiza mishi kai ba tare da ta bude idanun ta ba
" to minene ki na kuka ? ko ciwo ki ke ? "
a hankali ta girgiza mishi kai ba tare da ta bude idanunta ba ta ce " sun sallame ni da ga wajen
aikina , ban yi mishi komai ba kawai ya ce gobe na kai mishi letter din barin aiki na wai ya kore
ni " ta kai karshen ta na kara sautin kukan ta
cikin ko in kula Kim ya ce mata " to sai me , ki kai mishi letter din , ya je ya rike aikin shi in ya na
so ya cinye shi ba "
a dubu dari ta ware idanunta ta na kallon shi ta ce " ka na jin abun da ka ke fada kuwa ? tun da
ba ni da aiki hakan na nufin babu kudin da dinga saya maka chocolate , in kuma gidan mu su ka
ji labarin na rasa aiki na ce min za su yi na koma ni kuma gaskiya ba na jin zan iya komawa
gida " ta kai karshen ta na sakin kuka
shiru ya yi ya na kallon ta , jin ta ce babu kudin sayan chocolate , a hankali shi ma ya fara kuka
kassa kassa kamar wani karamin yaro
ai ba shiri Esra ta yi shiru jin sautin kukan shi sai da ta nemi kukan nata ta rasa
a rude ta ce mishi " Kim , lafiya ka ke kuka ? "
" yanzu wa zai saya min Chocolate ? ni gaskiya ban yarda ba " ya fada ya na kuka
Wata yar karamar dariya ta yi ta na kallon shi yadda ya ke kuka kamar wani karamin yaro har
da lumshe idanunshi
ya na jin ta yi dariya ya bude idon shi guda ya ga Eh da gaske dariyar ta ke
a hankali ya bude idanun shi ya yi shiru ya na fadin " tun da kin yi shiru yanzu mu je park "
dama ba kukan ne ya ke ba kawai dan ya sa ta dariya ne ya yi hakan
" park kuma ? " ta fada ta na kai hannu ta goge hawayenta
gyada mata kai ya yi kafin ya fara takawa ya yi gaba , a hankali ta juya ta bi bayan shi su ka
fara takawa a tare
▪PROSPECT PARK
park din cike ya ke da mutane specially couples kowane ya na sha-anin gaban shi , sai wassa
su ke su na dariya ,
ga wajen da mugun girma cike da ciyayi da itace , ga kukan tsintsaye da ke tashi , abun dai
gwanin burgewa
tun da su ka shigo wajen Esra ke jin zuciyarta ta yi mata sauki , saboda yanayin wajen ,
Kim na ganin ta fara sakin face din ta , ya sauke wata yar karamar ajiyar zuciya
a hankali ya riko hannunta ya ja ta da gudu
a razane ta saki wata yar karamar kara ta bi bayan shi su na gudun ta na fadin " Lafiya ? me ya
faru ka ke gudu ? "
ba tare da ya tsaya ba ya ce mata " wani abu zan gwada miki "
ba ta ce mishi komai ba ta bi bayan shi su na gudun ta na wata yar karamar dariya ,
a haka har su ka karaso tsakiyar park din wajen katuwar fountain ta na zubar da ruwa gwanin
burgewa
su na isowa wajen ya saki hannunta ya tsaya ya na kallon fountain din
a hankali ita ma ta tsaya ta na haki , ta na kallon fountain din ta ce mishi " Kim , wai me mu ke yi
a nan ? "
bai ce mata komai ya ajiye bag din ta bakin fountain din , ya kai hannu ya tattare kafafun
wandon shi har zuwa guyiwa
nan ta ga farare kafafun shi cike da gashi baki kirin ya konta mishi luf gwanin burgewa
ya cire sneakers din shi sannan ya shiga cikin fountain din kamar wani karamin yaro ya fara
watsa ruwan da kafafun shi
wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta fidda flat shoes din ta , ta shiga cikin fountain din ita
ma
ta sa sannu ta watsa mishi ruwa
da sauri shi ma ya sa kafa ya watsa mata ruwan a fuska
wata yar karamar dariya ta yi kawai ta biye mishi su ka shiga wassa kamar wasu kananan yara
su cikin wannan yanayin mai dadi su ka jiyo Muryar wani security ya na fadin " kai , ba a shiga
cikin ruwan nan , maza ku fita ! " ya fada da dan karfi
a tare Esra da Kim da su ka zaro idanu su na kallon juna kafin su juya a hankali su ka kalli saitin
da su ka jiyo Muryar security din
nan su ka ga ya na takowa ya nufo su fuska a daure
kawai sai ganin ta Yi Security din ya tsaya ya na kallon Kim , ya na dan zaro idanu
da sauri Kim ya riko hannunta ya na fadin " Run , Run , Run ! " ya fada su na fitowa da ga cikin
fountain din
da sauri ya dauki sneakers din shi da takalmin ta da bag din ta da hannu guda dukka ya na rike
nata hannun da gudan
su ka fara gud da sauri su ka bar wajen Esra kuwa sai dariya ta ke
Security na ganin sun bar wajen da gudu ya juya a hankali ya koma bakin aikin shi
sai da su ka yi nisa sosai da Fountain din sannan Ya tsaya ya saki hannunta ya zube a kassa ya
na haki ya saki kayan hannun shi
ita ma zaunawa ta yi a kassa ta na sauke nunfashi sama sama ta na dariya ta na kallon shi
sai da nunfashin shi ya dawo dai'dai sannan ya dauki sneakers din shi ya saka sannan ya mika
mata shoes din ta ya na fadin " tashi mu bar wajen nan tun kafin ya kamo mu "
ba musu ta karbi takalmin ta ta saka sannan ta mike tsaye
a hankali shi ma ya mike tsaye ya na rike da bag din ta ya fara takawa
cak ya ji an riko hannun shi
a hankali ya juya ya na kallon ta sai sakin murmushi ta ke
cikin sanyin murya ta ce mishi " na gode , bayan kai babu wanda ya taba saka ni annashuwa
haka "
slowly