Showing 21001 words to 24000 words out of 48110 words
Chapter 8 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf
،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{P A G E 15 & 16 ❤}
______________________________________
▪ESRA
ido a rufe ta turo kofar office din ta ta shigo ta na kuka , hawaye na zubo mata bibiyu , kai tsaye
chair din ta ta nufa ta zauna , ta kontar da kanta saman desk din ta na kukan ta
a hankali ta fara rage sautin kukanta , lokaci guda abun da ya faru ya dawo mata a kai
a dubu dari ta dago kan ta ta na zaro idanu , ta bude baki a hankali ta furta sunan Ayden ,
sannan ta ce " wannan shi ne Ayden Brian ? "
da sauri ta mike tsaye za ta bar wajen kawai sai ta tsaya cak ta koma ta zauna ta ja wani dan
siririn tsaki kafin ta ci gaba da aikin ta
______________________________________
▪AFTER SOME HOURS
misalin karfe 6 ta sauka da ga aikin ta , kai tsaye hanyar gida ta nufa , ta na tafiya kamar wadda
a ka zarewa lakar jiki
ta na tsaka da tafiyar ta kawai ta jiyo Muryar Kim a bayan ta ya na fadin " Miss Chocolate ! Miss
Chocolate ! " ya fada da dan karfi da allamun ita ya ke kira
cak ta tsaya da tafiyar ta har wani dan sanyi ta ji cikin zuciyarta lokaci guda
a hankali ta juya , nan ta gan shi ya na tafiya ya tunkaro ta , bai sauya kayan jikin shi ba
haka ta tsaya ta kura mishi ido har ya karaso gabanta ya tsaya ya na fadin " Miss Chocolate ,
tun dazu na ke ta kiran ki amma kin share ni "
ba ta ce mishi komai ba ta sunkuyar da kai ta juya ta fara takawa a hankali
a hankali ya fara takawa ya karaso geffen ta su ka jera , ya dan sunkuyar da kai ya na lekon
face din ta
cikin sanyin murya ya ce mata " Miss Chocolate , lafiya na ga face din ki ta kunbura haka , ko
kuka ki ka yi ? "
kamar dama jira ta ke a yi mata tambayar kawai ta dago kai ta ce mishi " Eh , kuka na yi , ni wlh
gidan uwata ma zan koma , na gaji da wannan aikin , Wancen mara imanin mai fuskar shanun
ya takurawa rayuwa ta , komai na yi wajen shi ba dai'dai ba ne "
shi dai ya tsaya ya na kallon yadda ta ke magana cike da bacin rai idanunta cike da ruwa
sai da ta gama maganar ta sannan ya ce mata " calm down , me ya faru ne a wajen aikin naki ?
"
" wani file ne da za mu tatauna a kai yau na manta dayar paper a gida , shi ne kawai ya rufe ni
da fada gaban sauran ma'aikatan , sai da na ce ya bari na koma gida na dauko ta amma ya ki
sauraro na "
cikin ko in kula ya ce mata " ni wlh na dauka wani abu a ka yi , wai saboda paper ki ke kuka ,
paper din da na ke kunna taba da ita , mu je na saya miki wata "
wata yar karamar dariya Esra ta yi ta na fadin " rike abun ka ba na so " ta kai karshen ta na kara
saurin tafiyar ta ta yi gaba
ya na ganin haka ya sa hannayan shi cikin aljihu , ya rage tashi tafiyar ya na kallon ta
sai da ta yi mishi nisa sosai sannan ta juyo ta gan shi cen baya ya na tafiya jiki a mace
cak ta tsaya ta na kallon shi har karaso wajen ta ya tsaya su na fuskantar juna
a sanyaye ta ce mishi " lafiya ka ke tafiya a haka ? "
slowly ya bude baki ya ce mata " ba ki saya min sigarin da na ce miki ba "
ta na jin hakan kawai sai ta yi tunanin ko dan ya na son ya sha sigari ne ya ke wannan tafiyar
sanyin
tsuke fuska ta yi ta na fadin " ba zan saya ba , wuce mu tafi " ta fada ta na juyawa ta ci gaba da
takawa
tsayawa ya yi ya na kallon ta ta na tafiya , da ga ganin yanayin tafiyar ta ka san cikin fushi ta ke
slowly ya juya ya yi hanyar shi ya yi wata kwanar
Esra kuwa ba ta ma sani ba sai tafiyar ta ta ke , sai da ta fara hango building din su sannan ta
tsaya ta juyo ta na fadin " ni zan sh...... " kassa kai karshen maganar ta yi saboda ganin bayan
nata da ta yi fayam babu kowa
a hankali ta kalli hagu , ta kalli dama ta ga babu Kim babu mai kama da shi
" yanzu yaron nan dan na ki sayar mishi sigari shi ne ya gudu ? za mu hadu gobe ai " ta na
gama fadar haka ta juya ta shiga building din
kai tsaye Part din su ta nufa
ko da ta shiga ta ajiye bag din ta saman table , ta wuce bedroom din ta , ta cire kayan jikinta , ta
saka bathrobe sannan ta fito ta shiga toilet
wanka ta yi sannan ta dauro da Alwalla kafin ta fito , ta shirya cikin wata gown mata nauyi irin ta
zama gida haka
ta saka hijab din ta , ta shinfida sallayar ta ta tada sallat
ko da ta kammala ba ta tashi ba sai da ta zauna ta yi karatun kur'ani , har lokacin sallar isha ya
zagayo , ta tashi ta gabatar da ita
bayan ta kammala ta cire hijabin ta ajiye saman bed din ta sannan ta fito
ta dawo parlour ta zauna saman sofa , ta kai hannu ta dauki bag din ta
ta fiddo wasu takardu da laptop din ta dai² lokacin da Safna ta shigo gidan ta na sallama
a sanyaye Esra ta amsa mata sallamar ta , ta na kokarin bude laptop din ta
cikin nitsuwa Safna ta karaso cikin parlourn ta , ta zauna saman sofa ta na murmushi ta ce " ya
? Allah ya sa yau ma kin shirya mana Diner ? "
" hmmm , ba abun da na shirya , ni bar ni da kayan takaici ma " Esra ta fada ta na latsa laptop
din ta
" takaici kuma , me ya faru ne ? " Safna ta fada ta na ajiye bag din ta saman table
ba tare da ta dago kai ba Esra ta ce mata " yau akwai wani meeting da Sir Kevin ya shirya
mana , wlh akasi a ka samu na yarda daya da ga cikin paper din file di na , mara mutuncin nan
kawai ya same ni ya rufe ni da fada wai ba na aiki na yadda ya dace , sa'a ta guda ina da copy
din file din a laptop di na , shi ne zan kammala yanzu na tura mishi ta Email "
murmushi mai dan sauti Safna ta yi kafin ta kai hannu ta dauki bag din ta , ta bude ta fiddo
paper din nan da Adrian ya ba ta ta mikawa Esra ta na fadin " sa'ar ki guda ki na da friend's din
da ke aiki cikin restaurant din da ki ka je cin abinci har ki ka yarda paper din ki "
slowly Esra ta dago kai ta kalli paper din , hakan na nufin a restaurant din da su ka ci abinci ta
baro paper din ? ya a ka yi ta fito bayan ita ta san ba ta fiddo paper din ba ? ko dai wani ya
fiddo ta ba ta sani ba ?
wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta kai hannu ta karbi paper din ta na fadin " shi ya sa na
ke mutuwar son ki , ki na ji tashi ki je ki shirya yau a restaurant za mu yi diner kuma ni zan biya "
dan zaro idanu Safna ta yi ta na fadin " la , da gaske ? duk wannan farin ciki saboda paper ?
wannan paper ? "
" hmmm , Safna ba za ki gane ba wlh , ba ki san pression din da Sir Kevin ke daura min ba ,
kamar ni kadai ce ke aiki a wajen " ta kai karshen ta na tattare takardun ta , ta meda cikin bag
din ta da laptop din ta
ita kuwa Safna ta tashi ta shiga corridor ta wuce bedroom din ta
da ga nan ta shiga toilet ta yi wanka ta fito ta shirya cikin wata gown red color mai kyau , ta yi
Rowling veil din ta white color a kai
ta na fitowa parlour ta tardo Esra zaune saman sofa ta na sanye da kaya tak tak irin nata
wata yar karamar dariya Safna ta yi ta na karasowa cikin parlourn ta na fadin " hmm , my twins
ya a ka yi wannan hadin haka ? "
" ke dai zan tambaya " Esra ta fada ta na mikewa tsaye ta dauki yar karamar bag din ta
murmushi kawai Safna ta yi mata ba tare da ta ce komai ba su ka nufi kofar fita su ka fice a tare
su ka rufe part din nasu
______________________________________
▪KIM ❤
a hankali ya ke tafiya saman wani kyakyawan titi , ya na rike da wani gwongwanin kamar na
maltina amma ba maltina ba ce
kayan nan dai na safe su ne a jikin shi , amma gashin kan shi a tirje ya ke , ya zubo mishi har
gaban goshi ya rufe mishi idanu , ya sunkuyar da kai ya tafiya jiki a mace
a haka har ya karaso wani kyawatencen garden cike da ciyayi , babu kowa a ciki sai tsintsaye
a hankali ya nufi wata fountain fara kal , ya tsaya gaban ta ya na kallon kan shi ta cikin ruwan
a hankali ya sa hannu ya janye gashin da ke gaban goshin shi , nan na ga idanun shi sun yi
jazir , sun kunbura da allamun kuka ya yi
wani cool murmushi ya sakin wa kan shi kafin ya bude baki a hankali ya ce " shikenan , haka
rayuwar ka za ta kare ? , ka ta so a maraye cikin gidan marayu babu uwa ba babu uba , kuma
ka mutu a haka ? ko friend babu sai wine da taba ? why Kim ? why za ka lalata rayuwar ka haka
? , na san da ki na nan haka za ki ce min , but now i'm alone , you're not here with me "
ya na gama fadar haka ya saki kuka a hankali ya na fadin " why ? why za ki tafi ki bar ni bayan
kin san ke kadai gare ni a duniyar nan , ya ki ke so na yi yanzu ? " ya na gama fadar ya zube
saman guyiwowinshi ya na kuka kamar wani karamin yaro
a hankali ya dago drink din shi ya kai a baki ya sha kadan ka fin ya sauko
ya na kallon kan shi cikin ruwan foutain din ya bude baki a hankali ya fara rera waka ya na fadin
" SUNDAY MORNINGS WERE YOUR FAVORITE
I USED TO MEET YOU DOWN ONE WOODS CREEK ROAD
YOU DID YOUR HAIR UP , LIKE YOU WERE FAMOUS
EVEN THOUGH IT'S ONLY CHURCH WHERE WE WERE GOING , OHHHHH
NOW SUNDAY MORNINGS I JUST SLEEP IN
IT'S LIKE I'VE BURIED MY FAITH WITH YOU
I'M SCREAMING AT A GOD I DON'T KNOW IF I BELIEVE IN
CAUSE I DON'T KNOW WHAT ELSE I CAN DO , YEAHHHHHH
AND I'M STEEL HOLDING ON TO EVERYTHING THAT'S DEAD AND GONE
NO I DON'T WANNA SAY GOODBYE CAUSE THIS ONE MEANS FOREVER
NOW YOU'RE IN THE STARS AND SIX-FEET'S NEVER FELT SO FAR
AND HERE I AM ALONE BETWEEN THE HEAVENS AND THE EMBERS
OHH IT HURTS SO HARD FOR A MILLION DIFFERENT REASONS
YOU TOOK THE BEST OF MY HEART , AND LEFT THE REST IN PIECES "
sai da kammala sannan ya kai hannu a hankali ya fara goge hawayen da su ka zubo mishi , ya
dago drink din shi ya kai baki ya daga kai sama ya shanye ta lokaci guda kafin ya sauko ya tilla
gongwanin cen gefe
murya a disashe ya ce " I really missed you " ya na gama fadar haka ya lumshe idanunshi a
hankali ya ida sulalewa a wajen ya konta , ya kankame kan shi waje guda ya na ci gaba da
kukan shi kassa
( WLH HAR YA BAN TAUSAYI )
[19/02 à 10:53] : *PAID BOOK*
SOYAYYAR GASKIYA
__________________
TRUE LOVE
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : MEERAH
GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ZAI IYA TABO WANNAN
NUMBER +22795577612 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{F R E E P A G E 17 & 18 ❤}
________________________________________
▪ESRA ❤
a hankali su ke tafiya ita da Safna saman titi , su na tafe su na dariya da allamun sun ji dadin
fitar da su ka yi
sai da su ka karaso wajen wani traffic light sannan Esra ta tsaya ta na fadin " tsaya mu tsayar
da taxi ya meda mu ni gaskiya na gaji "
a hankali Safna ta dawo ta riko hannun ta ta na fadin " please mu tafi , mun ma kusa isowa "
marairaice fuska Esra ta yi kafin ta bi bayan ta su bar wajen ta na fadin " Uhm , Uhm ni kawai ki
na son ki gajiyar da ni , to wlh in mu ka koma sai kai yi min tausa "
wata yar karamar dariya Safna ta yi kafin ta zagayo da hannun ta a wuyan Esra ta na fadin "
duk abun da ki ke so , yanzu dai mu tafi , Sarauniyar kyau ba " ta kai karshen ta na bushewa da
dariya
wani dan karamin tsaki Esra ta yi ta na fadin " ni wlh ba dan kin tare ni ba da na koma na yi
mishi rashin mutuncin da ya dace shege dan iska kawai "
sake bushewa da dariya Safna ta yi ta na fadin " haba Sarauniyar kyau , ke da fan din ki , ai ya
ga abun d aya burge shi ne , amma bai san Esra ta fi karfin shi ba , sai dan sarki jikan sarki , ko
ba haka ba Sarauniya " ta kai karshen cike da zolaya
wani dan karamin tsaki Esra ta yi ta na kauda kai gefe
Dum ta ji zuciyarta ta buga da mugun karfi , cak ta tsaya waje guda ta kura mishi ido
a rude ita ma Safna ta tsaya ta na fadin " lafiya ki ka tsaya ? "
hannu Esra ta kai ta janye hannun Safna da ke saman wuyan ta ta fara takawa da sauri ta
tsallaka titi ta shiga garden din
kai tsaye Kim ta nufa ta na kiran sunan shi
ta na isa ta zube saman guyiwowinta ta talabo kan shi ta na fadin " Kim , wake up , me ka ke yi