Showing 30001 words to 33000 words out of 48110 words

Chapter 11 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf

ya nufo shi ya na dariya allamun tashi ce

sai da ya karaso gaban Kim ya tsaya ya na fadin " please Sir ko za ka iya ban ball di ta ? "

ba musu Kim ya kai hannu a hankali ya dauki ball din kafin ya ce mishi " zan iya yin wassa da
kai ? "
wani kyawatencen murmushi yaron nan ya saki kafin ya gyada mishi kai da sauri ya kai hannu
ya karbi ball din ya na fadin " Oya , let's go and play "

ba musu Kim ya tashi ya bi bayan yaron nan , kafin ya iso wajen yaron ya ida chocolate din
hannun shi ya tilla leda , ya kai hannu ya meda gashin gaban goshin shi baya

ita dai Esra ba ta ce komai ba ta na kallon shi har su ka fara wassa da yaron nan gwanin
burgewa kamar uba da yaron shi , ga shi ko yaron sai dariya ya ke ya na biyewa Kim , lokaci
guda su ka yi mugun burge ta

wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta kai hannu cikin bag din ta , ta fiddo wayar ta , ta yi
musu wata yar karamar video ta yi musu pics har uku kafin ta meda wayar cikin bag din ta

ta dauki chocolate din da ta ajiye wa Kim ta meda su cikin ledar sannan ta ajiye
ta mike a hankali ba tare da ta ce komai ba ta fara takawa ta nufi hanyar fita garden din ta na
sakin murmushi

Kim kuwa bai ma san abun da ke faruwa ba ya na wassan shi kamar wani karamin yaro
sai da iyayen yaron su ka kira shi za su bar wajen sannan su ka daina , Ya na juyawa ya ga
babu kowa saman bancin su sai ledar chocolate din da ta ajiye mishi

a hankali ya tako ya dauki ledar kafin ya fice Garden din shi ma


_________________________________________________________


▪BROOKLYN


▪DISTRICT OF WILLIAMSBURG



wani kyawatencen parlour ne mai mugun girma , ya kyawatu iya kyawatuwa komai na cikin shi
White and black colors ne , duk walls din wajen na zallar glass ne , ka na iya hangen garin , da
allamun samun building ne dan ka na ganin garin da wasu buildings ta ko ina

a bangaran dama , parlourn kyawace ya ke da wata doguwar sofa White color irin wannan ma
su disign din L , sai wasu kananan pillow a saman ta white colors suma
a dayan geffen ta akwai wasu Sofas one seater biyu duk black color
da ga tsakiya kuma an shinfida wani kyawatencen carpet round , Black color mai ratsin white ,
an daura wata kyakyawar table ta zallar glass white color da ga sama
da ga saman ta kuma akwai wasu magazine wajen uku ko hudu haka ajiye , geffen su kuma
remote ne biyu sai dan decoration na flowers ma su kyau

wall din da ke fuskantar Sofar ya na rufe da wasu curtains farare kal , an rufe wall din da su
da ga gaban wall din akwai wata yar table an daura wata makekiyar Tv plasma a sama

wall din da ke fuskantar wadanan sofas one seaters guda biyu kuma , da ga gaban shi kadan
akwai wata doguwar dining table ta zallar glass black color zagaye da wasu slipcover chair
guda goma sha biyu su ma duk black colors ne ,
saman table din gaban ko wace chair akwai wani dan karamin tablecloth white color kamar
handkerchief haka
da ga saman shi akwai wani plate white color a juye , sai spoon da fork da eating knife a geffen
dama
geffen hagu kuma glass ne guda biyu kamar irin na shan wine haka , guda babban guda karami

dan nesa da dining table din na hango wata kyawatenciyar kitchen cike da kayan girki na
zamani , kuma duk abun da ke ciki white color ne a nan ba a saka black ba

a bangaran hagu kuma na hango wani dan madaidaicin office , da wani closet cike de books
kamar library
da ga gaban Closet din akwai wani carpet white color mai dan girma , ya fi na parlour girma da
ga saman shi an daura wasu Armchair guda biyu white color su na fuskantar junan su da ga
tsakiya kuma wata yar table kamar ta ice haka

bayan wannan closet din kuma na hango wani Stair na zallar glass , sai abun ya yi kamar
saman closet din nan stair din ya ke
takaitaciyar description din wajen kenan amma a zahari abun ya fi haka dan in na ce na ci gaba
da description din sai mun kammala book din ma ba page din nan ba , abun dai Masha Allah
kawai za a ce dan ka na ganin wajen nan ka san ba na kananan mutane ba ne , amma bari mu
koma cikin labarin mu
a zaune na hango Kevin saman chair a dining table da allamun diner ya ke yi ya na sanye da
wasu pajama farare kal fuskar nan tashi a daure kamar hadari
a geffen daman shi na hango wani kyakyawan bature fari kal da shi , ya na kama da Kevin , sai
dai ya tsufa sosai dan zai kai 55 years , kun san yadda farar fata ta ke ba ka da resistance , da
ka fara Tsufa ta ke jemewa ,
ga shi kuma duk gashin kan shi fari ne , amma ba shi da gemu ko kadan ya na sanye da wasu
Suit navy blue ma su kyau tsadadu da ga gani da allamun wannan shi ne mahaifin su Ayden
wato Brian

a haka na hango wata kyakyawar budurwa ta na fuskantar Kevin , fara kal da ita kamar ka taba
jini ya fito , cikakiyar baturiya a shekaru ba za ta wuce 20 to 21 years ba

ta na kama tak tak da Kevin kamar an tsaga kara sai dai color din idanun ta Hazel ne mai
mugun kyau

ta na da gashi sosai har tsakiyar bayan ta kuma mai laushi russet color da shi mai daukar
hankali

ta na sanye da wani mini skert pink ko ida rufe mata guyiwa bai yi ba , da wata yar karamar
T-shirt dai'dai cibi Red color , amma gaskiya ba ta da shape kun san turawan ban ba wani
shape ne da su ba , dama dama breast din ta ya dan tasso kuma ba ramamiya ba ce sosai

kowane ya na cin abincin shi cikin konciyar hankali babu me cewa ufan

a hankali Kevin ya kai hannu ya dauki glass din ruwan da ke geffen shi na hagu ya kai a baki ya
surbi kadan kafin ya ajiye
ya juyo ya kalli Brian ya ce " Daddy , gaskiya ya kamata ka yi wa Ayden magana , na daina
wannan shiriritar da ya ke , ya dawo mu kula da companyn mu , mu na samun matsala kwana
biyun nan , a na yi mana satar makudan kudade Daddy , ba zan iya kula da komai ba ni kadai "

a hankali shi ma Brian ya kai hannu ya dauki glass din ruwa ya kai bakin shi ya surbi kadan
kafin ya ajiye ya kalli Kevin ya ce mishi " kai ma ka sani , bayan restaurant din shi ba abun da
ke cikin zuciyar shi , ko ya dawo ba zai maida hankali ya kula da companyn kamar yadda ya ke
kula da restaurant din shi ba "
" but Daddy , i've my own life , ba iya ci gaba da kula da companyn nan ba , ni ma ina dreams ,
ina da aikin da na ke so na yi , please ku yi mishi magana mana , duk abun da ya ke ku/ku ke
goya mishi baya ya na yi , da tun farko kun bar shi ya kula da companyn da ba za mu fuskanci
wannan matsalar ba , ni ban ma san abun da ya sa momy ta bar mishi companyn ta ba "
ba tare da ta dago kai ba budurwar nan ta ce " Saboda ya fi ka kaifin basira , ya fi ka ilimi , ya fi
ka tunani , ya fi ka sanin ya kamata , ya fi ka sanin harkar kasuwanci , ya fi ka zuciya , ya fi ka
kula da tattali , na ci gaba ko ya isa haka ? "

gaskiya maganar ta ba karamin batawa Kevin rai ta yi , cikin bacin rai ya dago hannu zai wanka
mata mari
cak Brian ya taro hannun ya na fadin " Kevin , are you mad ? marin ta za ka yi ? "

da karfi Kevin ya kauce hannun shi kafin ya koma ya zauna
ita ko ko a jikin ta dan ko dago kai ba ta yi da allamun ta san Brian ba zai bari ya mare ta ba

cike da bacin rai Kevin ya ce " Daddy ka na fa jin abun da ta ke fada "

dawo da kallon shi Brian ya yi kan budurwar nan ya ce " Emilie , why za ki fada mishi hakan ? "
" ai gaskiya ce na fada " ta fada ta na kai abincin ta a baki

" da ke da wancen sakaren zan yi maganin ku , sannan Daddy ka ce mishi ya shirya ya koma
companyn in ya wuce one week gaskiya ni bari zan yi , i'm tired " Fadin Kevin

slowly Emilie ta dago kai ta kalle shi
a sanyaye ta ce mishi " don't worry , na ji ya ce monday zai koma "

a tare Kevin da Brian da su ka zaro idanu har su na hada baki su na cewa " da gaske ki ke ? "

a hankali ta gyada musu kai ta na fadin " i'm serious , na ji shi ya na waya da Adrian ya ce wai
ya sa a gyara office din shi , monday zai kama aikin shi "

wani kyawatencen murmushi Brian ya saki ya na fadin " to ka gani , ka na nan ka cika mu da
surutu , ka ji monday zai karbi companyn shi , idan ka so za ka iya tafiyar ka "

shiru Kevin ya yi bai ce mishi komai ba sai ma hannu da ya kai ya dauki ruwan shi ya kai a baki
ya sha kadan kafin ya sauko ya ci gaba da cin abincin shi da allamun ya yi sumar zaune ko
kuma wani makamancin hakan

su na zaune a haka Ayden ya fara sauko stair
a tare duk su ka kai kallon su wajen stair din
sanye ya ke cikin wasu Tracksuit farare kal kamar madara , ya saka wasu sneakers farare kal
su ma a kafafun shi
ba na iya ganin face din shi saboda ya saka hular rigar ya kuma saka face mask baki , ya na
takowa Hannayanshi cikin aljihun rigar shi , kai a sunkuye

a haka ya gama sauko stair din ya nufi hanyar fita gidan

da sauri Brian ya taro shi da cewa " Ayden ba za ka yi diner ba ? "
a hankali ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " No , ni da Adrian za mu fita may be idan na
dawo zan yi "

bai gama rufe bakinshi ba Kevin ya ce " kullum ka fita , kullum ka fita , wai ina ka ke tafiya ? , a
sani na ba kai ke dahuwa cikin Restaurant din ka ba , ba kuma company ka ke zuwa ba , kawai
ku na cikin gari kai da wancen sakaran ku na yawo "

maganar shi ta so ta sosawa Ayden rai gaskiya , duk duniya ba abun da ya tsana kamar a ci
mutuncin wani na kusa da shi , wannan abun ya na bata mishi sosai

wani dogon nunfashi ya ja kafin ya daga kafa a hankali ya taka ya fice gidan

ya na fita Brian ya ce ma Kevin " kai dai ba ka iya fadin al'heri da bakin nan naka , ga shi yanzu
ka bata mishi rai "

" ai gaskiya ce na fada , tun baya kai ne da ba ka tsawatar mishi , ni ban ma san abun da ya ke
cikin familyn mu ba "

da sauri Emilie ta dago kai ta ce mishi " no , our family , shi ma ya na cikin familyn mu , ka daina
mayar da shi bare , little brother din ka ne "

cike da bacin rai Kevin ya ce " no , ni ba brother di na ne ba , kawai yaron da momy ne ta samu
wajen cin amanar Daddy da ta yi "

" Kevin ! " Brian ya fada da dan karfi ya na zaro idanu dan maganar Kevin ta bata mishi rai

shi kuwa Kevin ko a jikin sa sai ma cewa ya yi " why za ka daga min murya ? ai ba karya na yi
ba , ba banza ta mallaka mishi duk companyn ta ba saboda na uban shi ne , da a ce ba ta ci
amanar ka ba da ba zai zo duniyar nan ba "

a hankali Brian ya kai hannu ya dafe saitin zuciya shi ya na yamutse fuska ya na kallon Kevin
cike da takaici

Emilie na ganin haka ta zaro idanu ta na fadin " Daddy , are you okay ? "
murya a disashe ya ce mata " ban ruwa "
ba musu ta dauki ruwa ta mike ta kai mishi a baki ya sha sannan ta sauko shi ta koma ta zauna

wani dan karamin tsaki Kevin ya yi kafin ya ce " I'm sorry maganar ce ta fito haka kawai , amma
ba haka na ke tunani ba , i'm so sorry "




MY BOOK IS ₦500
VIA

8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank




SOYAYYAR GASKIYA
__________________

TRUE LOVE

( A HEART TOUCHING LOVE STORY )




STORY & WRITING BY : MEERAH






GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i





يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ




BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM





{P A G E 23 & 24 ❤}

Da Brian da Emilie duk babu wanda ya ce mishi ufan , amma har cikin zuciyoyinsu sun ji zafin
maganar shi
duk abun nan da Kevin ya fada a kunnen Ayden , dan ya na tsaye bakin kofar da ga baya ,
bai tafi ba , abun da Kevin ya fada ya kara tabbatar mishi da abun zuciyar shi ke fada mishi na
Kevin ya tsane shi , kawai ya na nuna mishi soyayya ne a fili ,
abun nan ba karamin zafi ya yi mishi ba dan har hawaye sai da ya zubar amma da ido guda

a hankali ya kai hannu ya goge sannan ya bar wajen ya yi tafiya shi





▪MISALIN KARFE 8 NA DARE


▪ESRA ❤


Zaune ta ke cikin parlourn apartment din su ta na sanye da wasu kananan kaya blue ma su
mugun kyau , sun yi mugun kama ta ko kamar a jikin ta a ka yi su

ta na zaune ta na latsa laptop din ta cikin konciyar hankali , Safna kuma ta na cikin bedroom
din ta ta na barci dan tun safe ta ke jin jikin ta ba dadi
ta na a haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login