Showing 42001 words to 45000 words out of 48110 words
Chapter 15 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf
ya juyo ya riko hannunta da kyau cikin nashi ya saki wani cool murmushi ya ce mata " ni
ma na gode , rabon da na saka mutum cikin farin ciki har na manta , na san ni da ke ba mu
dace ba , kuma na san babu wata alaka tsakanin mu amma duk lokacin da na ke tare da ke ina
rage kewa sosai , na gode ko ba komai kin saka ni cikin farincikin da na jima ban ji kaina a ciki
ba "
wani kyawatencen murmushi ta saki ta na fadin " it means we're friend's now ? "
murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " kin yi kokari , amma har yanzu ba ki ci makin zama
friend's di ta ba , amma ki ci gaba kin kusa yin nassara " ya na gama fadar haka ya juya ya fara
takawa ya na rike da hannunta
ba musu ta bi bayan shi ta na murmushi cikin zuciyar ta ta na fadin " za ka gani , in sha Allah sai
ka bude baki ka roke ni na zama abokiyar ka "
a hankali su ke tafiyar su cikin park din kamar wasu masoya
a haka su ka fara hango wasu samari guda uku zaune saman wani bancin , biyu na rike guitar
dayan kuma ya na rike da saxophone su na kidan su cikin konciyar hankali , kuma gaskiya sun
iya
[28/02 à 08:19] : TRUE LOVE
__________________
SOYAYYAR GASKIYA
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : MEERAH
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb
يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{P A G E 29 & 30 }
a hankali ya juya ya ce mata " mu tafi ko gani "
ba musu ta bi bayan shi su ka iso wajen musician din nan , su ka tsaya kawai su na kallon su
haka su ma samarin ba su daina kidin nasu ba , har sai da su ka kammala
su na kammala wa ko Kim ya shiga yi musu tapi ,
da sauri ita ma Esra ta shiga yi musu tapi ta na wata yar karamar dariya
da ga haka Kim ya ba su hannu daya bayan daya su ka gaisa sannan Kim ya ce musu " gaskiya
, song don nan ya yi min dadi sosai "
a tare su uku su ka yi dariya kafin su yi mishi godiya
" please , ko za ka ara min guitar din ka ? ina so na gwada ni ma "
" why not " wanda ke rike da guitar guda ya fada ya na mika mishi guitar din hannun shi
wani kyawatencen murmushi ya saki kafin ya kai hannu ya karbi guitar din , sannan ya zauna
geffen shi
da sauri Esra ta ce mishi " Kim , ka ga ka ba shi abun shi , yaushe ka iya wassan guitar ? "
bai ce mata komai ba ya fara buga guitar din
sai da ta dan zaro idanu jin yadda ya ke buga ta cike da kwarewa , har su kan su musician din
sai da kidin ya burge su
shi kuma sai ya dan yi nisa da kidin sannan ya bude baki cike da nitsuwa ya fara rera waka ya
na fadin "
LOOKING ME LIKE I'M CRAZY , WHEN I SHOT MY FEELINGS OUT
LOOKING ME LIKE I'M DIFFERENT , STILL YOU STAY CAUSE YOU FEEL SOMETHING
REAL
IT'S SO LOST IN MY MOMENT , DOESN'T MEAN I DON'T NEED YOU , I , I........
FELL IN LOVE WITH THE COLORS , THEY KINDA TELL ME WHAT I'M THINKING
FELL IN LOVE WITH THE WAY WE ARE , AND THE WAY WE LOSE IT
SOMETHING DIFFERENT ABOUT US , AND THE REASON WHY WE STAY , STAY......
WE FLY AROUND LIKE PAPER PLANES THEY NEVER KNOW WHERE WE WILL FALL
NOBODY CAN SEE US STILL THEY WANNA TEAR US APART , THERE'S SOMETHING
DIFFERENT ABOUT THE WAY WE ARE , ARE , ARE.........
OOHHHHHH , OOH , OOH.........
THERE'S SOMETHING DIFFERENT ABOUT US
OOHHHH , OOH , OOHHH........
THERE'S SOMETHING DIFFERENT ABOUT US "
Ita dai Esra ta tsaya cak ta na kallon shi , ta na sauraron zazzakar Muryar shi ya na wakar shi
cike da nitsuwa
ba ita ba har su musician din sai da ya burge su
slowly ya daina kidan bayan ya gama rera wakar shi , har ya daina kafin ya dago kai slowly ,
idanun shi ba su sauka ko ina ba sai cikin na Esra
ta na ganin ya tsaya ta saki wani cool murmushi ta na yi mishi tapi
a tare su ma samarin nan uku su ka shiga yi mishi tapi kafin wanda ya ba shi guitar din ya ce "
guy , wakar nan ta hadu gaskiya "
wani dan karamin murmushi Kim ya yi kafin ya mika mishi guitar din shi ya na fadin " na gode "
a hankali ya kai hannu ya karba , mikewa tsaye Kim ya yi kafin ya koma geffen Esra ya tsaya ya
riko hannunta , ya na kallon musician din nan ya ce musu " mun gode sosai "
wanda ke rike da Saxophone din ne ya amsa mishi da cewa " ba komai , we are HAPPY to see
mun saka couple din ku farin ciki "
dan zaro idanu Kim ya yi ya na kallon shi jin ya ce wai couple
har ya bude baki zai yi magana Esra ta riga shi cewa " Thanks a lot "
ta na gama fadar haka ta juya ta kalli Kim ta ce mishi " let's go now "
ba musu ya bi bayan ta su ka bar wajen ya na tunanin abun da saurayin nan ya ce wai couple ,
yanzu a haka sun yi kama da couple ?
shi ko bai san tun lokacin da su ka shigo park din kowa kallon couple ya ke yi musu musaman
hannun ta da ya ke rike da
sai da su ka yi dan nisa sannan ta ce mishi " Kim , babu toilet a cikin park din nan ? "
ba tare da ya juyo ba ya ce mata " akwai , ki na son shiga ne ? "
" Eh " ta fada a takaice
bai ce mata komai ba su ka ci gaba da takawa har su ka karaso wajen toilet
sai da su ka iso sannan ya saki hannunta ya na nuna mata kofar wata toilet ya ce " cen ne toilet
din Mata "
okay kawai ta fada mishi kafin ta taka ta shiga toilet din
ya na ganin ta shiga ya juya ya nufi wata katuwar bishiya da ya hango ta na fuskantar toilets din
, ya jingina bayan shi jikin bishiyar ya lumshe idanunshi , ya tafi duniyar tunanin shi
ya na a haka ya jiyo Muryar Esra ta na fadin " Kim , na ga jakata please "
slowly ya bude idanun shi kafin ya juyo ya kalle ta ya mika mata bag din
hannu ta kai ta karba ta na yi mishi godiya , bai ce mata komai ya juya ya lumshe idanunshi
hannu ta kai cikin bag din ta fiddo wata yar karamar leda , sannan ta ajiye bag din gaban ta
bude ledar ta yi ta fiddo wata ledar amma kamar sallaya ta ke
a hankali ta daga kai ta kalli sama , kafin ta juya ta shinfida Sallayar , ta na fuskantar gabas , ta
haye sama ta juyawa Kim baya
sannan ta kai hannu ta warware veil din ta , nan take jelar gashin ta , ta warware ta zubo mata
har tsakiyar baya
slowly Kim ya bude idanun shi wai ya ga me ta ke yi , nan idanun shi su ka sauko saman gadon
bayan ta da jelar gashin ta
ita kuma bude veil din ta ta yi nan ga ashe babba ne sosai kawai ta na ninke shi ne
meda ta yi ta yi Rowling din shi a kai , ya zubo mata har wajen guiwa
cikin nitsuwa ta tada sallar ta
shi dai Kim ya tsaya ya tsare ta da ido ya na kallon yadda ta ke sallar
sai da ta yi sujada ta farko sannan ya ce mata " minene ki ke yi haka ? "
kawai sai ya ga ko juyowa ba ta yi bare ta amsa mishi , hakan ya sa ya ja bakin shi ya yi shiru ,
ya zauna a kassan bishiyar ya na kallon ta
kawai sai ya ji wani bakon yanayi cikin zuciyarshi , ya ji wata nitsuwa ta shigo lokaci guda
ita kuma cikin nitsuwa ta yi sallar ta , bayan ta gama ta zauna ta na addu'o'in ta ta shafa kafin ta
juyo a hankali ta shafa mishi shi ma
ya na ganin haka ya ce mata " wai me ki ke yi tun dazu na miki magana kin kyale ni "
wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " Sallat ce na yi "
cikin rudu ya ce " Sallat ? minene sallat ? "
" ta na daya da ga cikin kinshigin addini na , sallat ita ce abu me mahimanci ciki addinina , ta ita
ce kawai a ke iya gane musulmi "
" kamar dai irin sallar da a ke yi church ? "
girgiza mishi kai ta yi a hankali ta na fadin " a'a , ka na dai gani yadda na yi yanzu , haka nan su
ke yi a church ? "
slowly ya girgiza mata kai allamun a'a
sai da ta saki murmushi sannan ta ce " to ka gani , ka ga ko na fada maka ba ganewa za ka yi
ba dan haka tashi mu tafi "
cikin nitsuwa ya ce mata " wata rana za ki fada min ? dan ina son na san yadda addininki ya ke
"
wani kyawatencen murmushi ta saki abun da ta ke so ya samu , cikin sanyin murya ta ce mishi "
yau daddare idan ka je , zan yi maka bayani "
okay kawai ya fada mata kafin ya mike tsaye , ya na fadin su tashi su koma gida
ba musu ta tashi ta nade sallayar ta , su ka bar wajen
a tare su ka baro park din sai da ya raka ta har building din su , sannan su ka yi sallama , shi ya
juya ya bar wajen ita kuma ta shiga ciki , da allamun ta mance da sallamar ta da kevin ya yi
ko da ta koma apartment din su bayan ta ajiye bag din ta , kai tsaye toilet ta wuce ta yi wanka ,
ta fito ta shirya cikin kananan kaya kawai ta haye gado ko two minutes ba ta yi ba barci ya yi
gaba da ita
_________________________________________________________
▪BROOKLYN
▪DISTRICT OF WILLIAMSBURG
A zaune duk mutanan gidan su ke a saman dining table su na cin abincin su cikin konciyar
hankali , amma Ayden ya na zaune ya na rike da wata jarida ya na karantawa , ya rufe fuskar
shi da ita ba na iya ganin komai sai hannayan shi da ke rike da jaridar
cen sai Brian ya ce mishi " Ayden , ka ajiye jaridar nan ka ci abincinka tun bai yi sanyi ba " ya
fada cike da kula
ba tare da ya ajiye jaridar ba Ayden ya ce mishi " i'm full Dad , mun biya restaurant ni da Adrian
kafin ya sauke ni "
" okay , " Brian ta fada a takaice kafin ya juya ya ci gaba da cin abincin shi
su na a haka su ka jiyo Muryar Ayden ya na fadin " Kevin , na ji an ce ka sallami wata da ga
cikin ma-aikatan mu na one world trade center "
ba tare da ya kalle shi ba Kevin ya ce mishi " Yes , haka ne "
" zan iya sannin dalilin ka na sallamar ta ? ko wani laifi ta yi maka ? "
cikin ko in kula Kevin ya ce mishi " no , kawai na gaji da aikin ta ne , kullum late ta ke zuwa shi
ya sa na sauwake mata aikin "
dan jinkirtawa Ayden ya yi kafin ya ce " dan ta na zuwa late kawai sai ka sallame ta , ba ka san
abun da ke tsayar da ita ba , kuma ai ni ban ba ka izinin sallamar ta ba "
shiru Kevin ya yi bai ce mishi komai ba ko dago kai ma bai yi ba ya na cin abincin shi
a hankali Ayden ya mike tsaye ya na rike da jaridar ya ce " next time idan za ka sallami wani
ma-aikacin ka fara ba ni hujjojin sallamar tashi kafin ka sallame shi , ba zan lamunci ka na
sallamar ma-aikatana ba haka kawai babu dalili , kar ka manta kai ma zan iya sallamar ka idan
har na ga dama " ya na gama fadar haka ya juya ya nufi stair ya haye
gaskiya maganar shi ta yi matukar sosawa Kevin rai , sai da ya ji ya fara takawa sannan ya
dago kai a hankali ya bi shi da kallo har sai da ya haye stair sannan ya kai hannu ya dauki glass
din ruwan geffen shi ya juya ya tilla shi a glass din bayan shi ya na huci kamar zaki
cikin sanyin murya Brian ya ce mishi " Kevin , ai ba karya ya yi ba , why za ka dinga sallamar
ma su yi mishi aiki ? at least ka fara sanar mishi , ka yanzu ya karbi kayan shi , zan so ka
hakura ka bar mishi ya kula da abu ne "
Cikin bacin rai Kevin ya juyo ya wurga ma Brian wani mugun kallo kamar ba shi ne mahaifin shi
ba
" dama na sani ka fi son shi fiye da mu , mu ne fa yaran ka ba shi " Kevin ya fadawa Brian
da sauri Emilie ta ce mishi " Kevin , wannan zancen bai tasso ba na Daddy ya fi son shi fiye da
mu , na sani tun ya na karami ka ke mugun kishin shi har zuwa yanzu , please ka danne
zuciyarka , tsawan shekaru 20 ya na tare da mu amma har yanzu ka kassa kabar shi a
matsayin dan uwanka " ta karashe maganar cikin dan rauni
wata boyayyar ajiyar zuciya Kevin ya sauke kafin ya ce mata " ranar da ya bar duniyar nan a
ranar zan karbe shi a matsayin dan uwana " ya na gama fadar haka ya mike ya nufi stair ya
haye
da kallo Brian da Emilie su ka raka shi har sai da ya Haye sannan Emilie ta kalli Brian , ta na
marairaice fuska ta ce " Daddy , why Kevin ba ya son Ayden ? brother din mu ne fa , amma duk
duniya shi ya tsana "
" na sani Emilie , Ba ba ya son shi ba ne kawai hanyar da ya shigo ahalin mu ne ba ya so ,
tabbas na san abun da momyn ki ta yi bai dace ba , kuma har yanzu ina jin zafin hakan , amma
ba laifin Ayden ba ne abun da ta yi , shi kan shi na san ba zai so ya shigo duniya ta hanyar cin
amana , amma babu yadda mu ka iya "
" yanzu kennan Daddy kai ma ba ka son Ayden ? " ta fada idanun ta na cikowa da ruwa
wani dan karamin murmushin geffen fuska ya sakin mata kafin ya kai hannun saman face din ,
murya a sanyaye ya ce