Showing 6001 words to 9000 words out of 48110 words
Chapter 3 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf
ta
kuma kitchen ce , har da fridge
geffen Hagu kuma wani corridor ne na hango , akwai wasu door din bedroom biyu a ciki su na
fuskantar juna sai guda a tsakiyar su wadda ina kyautata zaton toilet ce
a hankali ta karaso cikin parlourn ta na sallama , sannan ta ajiye Bag din ta saman table din
tsakiya ta nufi corridor
ta shiga bedroom din da ke saman damar ta , ta tura kofar ta shiga ta na sallama
bedroom din ya na da dan girma
saman damar ta wani Desk ne da chair kamar dan office , da wasu takardu a sama
gaban shi kadan akwai wani dressing mirror , dauke da lotion perfume da sauran su
a geffen hagu kuma Wani closet ne White color na kayan ta me door hudu
a cen cikin dakin geffen hagu akwai bed din ta game da bango , shi ma white color har
bedsheet din shi white color ce , da bedside drawer din ta , ta daura wata bedside lamp da
alarm clock
ta na shigowa ta warware veil din kan ta , ta yi baya da kan ta , ta girgiza shi a hankali
nan take jelar gashin kan ta , ta zubo mata , ta na da gashi gaskia , smooth da shi brown color
kamar na turawa
ajiye veil din ta ta yi saman bed din ta , sannan ta nufi closet din kayan ta , ta bude na karshe
underwear ne cike a wajen , da pant da bra har da wasu towel white , pink , green colors
hannu ta kai ta dauki Towel Fari sannan ta juya ta fice dakin
kofar toilet ta nufa ta bude ta shiga sannan ta turo kofar ta rufe
After some minutes ta fito Daure da Towel a kirjin ta , kai tsaye bedroom din ta ta nufa ta shiga
ta na shiga ta nufi closet din ta , ta bude door ta uku , ta fido Wasu kayan barcin ta wando da
T-shirt pink color
ta saka kayan ta , sannan ta dauki Hijabin ta pink color shi ma , ta dauki Daddumar ta
ta nufi dan carpet din da ke gaban gadon ta ta shinfida sannan ta saka hijabin ta , ta tada sallar
ta
bayan ta Kamala ta tashi ta fida Hijabin ta , ta nufi Dressing mirror din ta , ta dauki lotion din ta
ta fara shafawa , sannan ta feshe jikin ta da perfume
sannan ta nufi kofar fita dakin ta fito parlour
ta na fitowa ta nufi doguwar Sofa ta zauna sannan ta janyo table din tsakiya gaban ta , ta dauki
Jakar ta , ta fara fido abun da ke ciki daya bayan daya
ta na a haka wata kyakyawar budurwa ta bude kofar gidan ta shigo ta na Sallama
Budurwar kyakyawa ce gaskia , a shekaru za ta kai 22 to 23 years , Skin din ta chocolate ce
mai mugun kyau , da ga kan ta ka ga jinin Hausa fulani
ta na sanye da Wando palazzo black color da t-shirt Orange , da wani Veil shi ma orange ta yi
Rowling din shi a kai , ta na rataye da wata yar karamar bag a bayan ta , ta karaso cikin
parlourn ta na kokarin cire bag din
dago kai Esra ta yi ta na kallon ta , ta amsa mata sallamar ta sannan ta daura da cewa " Safna ,
yau kuma sai yanzu ki ka dawo "
ajiye bag din ta Safna ta yi saman sofa geffen Esra sannan ta zauna ta na fadin " Kin dai gani
wlh duk na gaji jiki na har ciwo ya ke min "
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta juya kan ta , ta ci gaba da fido abun da ke cikin Bag din ta
mikewa tsaye Safna ta yi ta dauki bag din ta , ta na fadin " na shiga wanka " ta fada ta na fara
takawa ta nufi corridor
da to kawai Esra ta amsa mata ba tare da ta dago kai ba
ta na tsaka da fido kayan bag din ta , ta fido wani dan karamin abu baki kamar USB stick haka
dago USB din ta yi ta kawo ta saitin fuskar ta , ta na bin ta da kallo
" wannan kuma da ga ina ? " ta fada dan ita a sanin ta ba ta da USB key
sai da ta dan dauki lokaci ta na kallon USB din nan kafin ta janye ta da ga gaban face din ta , ta
dauki bag din ta ta fara meda duk kayan da fido ban da wayar ta , da laptop
sai da ta Kamala meda wa sannan ta dauko laptop din ta , ta daura saman cinyoyin ta , ta
kunna ta , sannan ta saka USB key din a ciki ta fara latsawa
ta dauki wajen good Five minutes a haka kafin ta mike tsaye a dubu dari ta na rike da laptop din
ta , ta na zaro idanu ta ce " oh my God , ya Allah me na ke shirin gani haka "
ni dai ban san me ta ke kallo ba , wasu rubutu ga su nan irin statistics haka , ita kadai ta san
abun da ta ke gani
slowly ta koma ta zauna ta rufe laptop din ta ta zame USB din ta meda cikin bag din ta , sannan
ta dauke ta , ta koma bedroom din ta , ta ajiye saman table din office din ta , sannan ta juya ta
fito dai'dai lokacin da Safna ta fito da ga cikin toilet ita ma ta na sanye da bathrobe white color
ko sannu ba ta ce mata ta sa kai ta fito corridor din ta koma parlour
Safna kuma ta shiga bedroom din ta
jim kadan ta fito Sanye da kayan barcin ta ita ma amma nata navy blue ne kuma wandon ta iya
cinya ne kawai
ta na fitowa ta nufi parlour ita ma ta zauna geffen Esra ta ce mata " wai ba ki gyara komai ba
yunwa na ke ji "
dan karamin murmushi Esra ta yi kafin ta ce " kin gan ni nan , ko kitchen din ma ban shiga ba ,
bare na yi tunanin gyara wani abu , ni na zata za ki biyo mata da take away da ga Restaurant
din ku "
dan karamin tsaki Safna ta yi kafin ta kauda kan ta , ta ce " wane restaurant , yau bayan wuya
ba abun da na sha , dan jaraba ni su ka bari serving yau , Wlh ba zan yarda ba , ni fa a
matsayin Chef na nemi aiki cikin restaurant din , amma wai su ka ba ni receptionist"
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " To tashi mu koma Nigeria mana "
dan zaro idanu Safna ta yi ta na fadin " wa ? ni ? ai ni da Nigeria sai dai Ziyara , Ziyarar ma , sai
da babban dalili "
TRUE LOVE
__________________
SOYAYYAR GASKIYA
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
PAGE 5 & 6
Dariya sosai Esra ta yi , wai Ziyarar ma sai da babban dalili kenan sai in parents din ta sun mutu
ko kuwa ?
hararrar wassa Safna ta yi mata ta na fadin " matsala ta da ke kenan ba a iya hira da ke "
tsagaita dariyar ta Esra ta yi kafin ta ce " Oya shikenan na daina "
" ko ke fa , amma ba ki tambaye ni abun da ya faru restaurant ba yau "
daga mata gera guda Esra ta yi ta na fadin " Oya fadi ina jin ki ! "
gyara zaman ta Safna ta yi , ta juyo su na fuskantar juna ta ce " Shugaba ku na ONE WORLD
TRADE CENTER , ya je sun yi wani meeting da wasu mutane a restaurant din mu , ni da kaina
na yi serving din su , sai wajen karfe 4 na yamma su ka tashi "
dan tabe baki Esra ta yi ta na fadin " no really , kenan Saurin da na ga ya na yi da safe cen za
shi ? "
daga kafadun ta Safna ta yi ta na cewa " na san ba , amma kin san abun da ya fi ba ni mamaki
? "
girgiza mata kai Esra ta yi allamun a'a
" wani hadaden saurayi ne na gani a tare da su , Esra ina fada miki , duk zaman da na yi a New
York , ban taba gani Saurayi hadade irin shi "
katse Esra ta yi ta na tsaki sannan ta ce " Shi ne abun mamakin ? " ta kai karshen ta na kauda
kai
cike da zumudi Safna ta ce mata " Ki tsaya ki saurare ni mana "
juyo da kan ta Esra ta yi kafin ta ce " to shikenan ina jin ki "
" yawwa ! ni fa ba haduwar saurayin nan na ke fada miki ba , idan ki ka gan shi ba zai wuce 30
years ba , amma duk mutanan da su ka halarci Meeting din da Boss su ke kiran shi , har shi kan
shi shugaban ku , a sani na Kevin Brian shi ne Boss din ku , ko kuma akwai na sama da shi ? "
" haka na ji su na cewa amma wlh ban sani , Fada min ya kamanin shi su ke ? "
yar karamar dariya Safna ta yi kafin ta ce " Gaskia a jiki dai ya hadu ga tsayi ga fafadan kirji
kamar mai dambe , sai dai ya na sanye da face mask ban samu na ga fuskar shi ba , idanun shi
kadai na gani , ya na da dara daren sexy eyes , Sai dai kwayar cikin su ban sani ba in blue ce
ko green dan da ga nesa na gan shi kuma ya sunkuyar da kan shi , amma dai between Blue or
green ce gaskia , ni sai da na ji Muryar shi ma na kara tabbatar wa da shi ne boss din su , kar ki
so ki ji Muryar shi kamar a na busa sarewa dan dadi , kuma cikin nitsuwa ya ke magana kamar
an yi mishi dole , kai gayen nan duniya ne kawai wannan ina ga shi ne Mister US baki daya ma
"
Dariya sosai Esra ta yi har da lumshe idanun ta , ta na fadin " Ni dai na san akwai Miss US ,
amma ban taba jin Mister US ba sai yau "
hararrar ta da kyau Safna ta yi kafin ta ce " ke wlh dan ba ki gan shi ba ne , amma Allah ya sa
su dawo restaurant din sai na dauki pics din shi dan ki gani "
tsagaita dariyar ta Esra ta yi ta na fadin " hum na ji dai malama , yanzu tashi gyara mana wani
abu mu Ci yunwa na ke ji "
hararrar wassa Safna ta yi mata kafin ta ce " kin yi sa'a ni ma ina jin yunwa ba dan haka ba sai
dai ki sha ruwa " ta kai karshen dai'dai lokacin da ta shiga kitchen din
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta dauki wayar ta saman table
ta na daukar wayar ba abun da ya fado mata a rai sai Kim , kawai sai ta saki wani cool
murmushi cikin zuciyar ta ta ce " ko ba komai ya Hadu gaskiya " ta na tuno yadda ta gan shi ya
na shan chocolate din shi cikin konciyar hankali , duk yadda a ka yi wannan akwai wani
boyayen Al'amari a tare da shi
ta yi nisa cikin duniyar tunanin ta , ta jiyo Muryar Safna ta na cewa " ke malama tun dazu a na
kiran ki a waya ba ki jine ? "
a dan razane ta dawo cikin hayacin ta dago wayar ta ta na kallon screen din
wani cool murmushi ta saki kafin ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na fadin " Amarsu ta
ango , lfy a ka kira ni warhaka ? "
wata yar karamar dariya na fara jiyowa kafin na jiyo Muryar wata macen da ga jin ta ta budurwa
Ce ta na fadin " Za ki fara ko ? ni yanzu fada min yaushe za ki zo kin san fa jiya a ka kawo lefe
amma ko kira na ba ki yi ba " a kai karshen cikin shagwaba
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " Sorry sister na , ya ki ke ya su momy duk da ma mun
yi waya da ita da safe "
" Fine ! kowa ya na nan lafya , yanzu fada min yaushe za ki zo ne ? "
" kawai dan ki tambaye ni yaushe zan zo , auren da ko rana ba saka ba " Esra ta fada ta na
mikewa tsaye ta fara takawa ta nufi corridor
a daya bangaran kuma a ka ce mata " Hum wa ya fada miki , ai jiya a ka saka rana , Farko ga
watan March "
" wow ki ce nan da two months " ta fada dai'dai lokacin da ta ke shiga cikin dakin ta
" eh , nan da kwana 52 bai kai two months ba "
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " to sannu malama har kin kirga ko kwana nawa ne "
" eh mana dole na kirga kwana nawa su ka yi mana saura ni da Habibi kafin mu zama Mr & Mrs
Raouf " ta kai karshen ta na yar karamar dariya
dan karamin tsaki Esra ta yi kafin ta ce " ke ki ka san wani Habibi , kin ga sai an jima ni Sallat
zan yi , sai da Safe " ta na gama fadar haka ta sauko wayar ta katse kiran
ta nufi closet din ta , ta bude ta dauki wani Hijab White color
ta saka , har kassa sannan ta dauki Sallayar ta shinfida , ta Haye ta tada sallar ta cikin konciyar
hankali
___________________________________________
WASHE GARI
▪GREENWICH STREET
a hankali ta ke tafiya saman titin , ta na sanye wando palazzo pink color da Shirt White color , ta
yi Rowling veil din ta a kai shi ma White color , ta na rike da bag din ta , ta na tafe ta na juyawa
kar a je yau ma akwai baratin nan da su ka tare ta
a haka har ta karaso wannan kwangon da ta ga Kim ya shiga a jiya
ta na shiga ta hango shi cen zaune saman wasu case , ya hada bayan shi da bango ya lumshe
idanun shi , ya na sanye cikin wando Crazy jeans black color , da wata T-shirt white color
gaskia wannan bai min kama da dan shaye² ba , dubi yadda ya ke a wanke tsab tsab Masha
Allah akwai dai wata a kassa
a hankali ta karaso gaban shi ta na Sallama duk da ta san abu me wuya ne a ce zai amsa mata
ko motsi ma bai yi ba , amma ya san da ita dan tun lokacin da ta yo kwanar ya jiyo qamshin
turaren ta
Murya cen kassan makoshi ta ce mishi " Kim ? " ta fada ta na dan lekon Face din shi
ba tare