Showing 33001 words to 36000 words out of 48110 words

Chapter 12 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf

16 Sep 2025

2045

ta ji an bubuga musu kofa a sanyaye
slowly Esra ta dago kai ta kalli saitin kofar , kafin ta rufe laptop din ta , ta ajiye saman table ta
mike a hankali ta nufi kofar ,l
ko tsoro babu ta bude kofar
ta na budewa idanun ta su ka sauka saman Kim tsaye bakin kofar fuska a marairaice , ya na
sanye da kayan shi na safe

idanun shi na sauka saman ta ya ji zuciyar shi ta yi wata muguwar bugawa ya rasa dalili , har
wani dan zaro idanu ya yi kadan ya na kallon ta kamar bai san ta ba

ita kuma ta na ganin shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta na fadin " na zata ba za ka zo
ba "
shiru ya yi bai ce mata komai ba ya na kallon ta babu ko kiftawa

ta na ganin haka ta juya ta na fadin " tun da ba za ka ce komai ba shigo , na shirya maka duk

abun da za ka bukata a kitchen "

ba musu ya biyo bayan ta ya shigo gidan kafin ya tura kofar ya rufe
ya na ida shigowa ya gan ta zaune saman sofa ta na rike da laptop din ta
kawai sai ya yi tsaye ya tsare ta da ido babu ko kiftawa

ita kuwa duk hankalin ta na kan aikin ta , ta ma manta da shi
lokaci guda kawai ta ji duk ta tsargu kamar a na kallon ta
wani cool murmushi ta saki kafin ta dago kai ta kalle shi , cikin zolaya ta ce " Ba ni za ka girka
ba , ga kitchen din cen , akwai aikin da na ke yanzu idan na ida zan zo na taya ka "

a hankali ya gyada mata kai kafin ya juya ya nufi Kitchen
da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta juya ta ci gaba da aikin ta
Kim kuwa ya na shiga kitchen din ya tsaya ya na kallon ingredients din da ta jera mishi
saman counter
a hankali ya juya ya nufi fridge ya bude ya fara bin abun da ke ciki da kallo
cen ya hango fish , Potato , carrot , peas , cikin irin ledodin nan na deep freeze
bai tsaya bata lokaci ba ya kai hannu ya dauki Fish , potato da carrot , ya dawo ya ajiye
saman counter , sannan ya juya ya dauki green pepper , da chilli pepper sannan ya rufe fridge
din

a hankali ya nufi Oven ya bude ya fiddo tray din ciki ya ajiye saman counter , kafin ya juya ya
fara bude closet na sama daya bayan daya da allamun ya na neman wani abu
sai da ya bude closet na biyu sannan ya ga wasu kwalaben spices , hannu ya kai ya dauki
thyme , rosemary , garlic powder , onion powder ya juyo ya ajiye geffen tray din oven

sannan juya ya bude closet na gaba ya fiddo Aluminum, ya juya ya ciro ya shinfida saman
tray din oven
bayan ya shinfida ya juya ya nufi mixer din da ya hango dayan geffen , ya bude ya fiddo bowl
din , ya zuba green pepper , chilli pepper Thyme, rosemary garlic da onion , ya zuba salt da
black pepper , ya zuba oil ya koma ya yi mixing din su ya yi marinade

sannan ya fiddo bowl din ya dawo ya wajen counter din ya ajiye
ya kai hannu ya dauki fish da potato da carrot ya Zube su saman tray din oven ya dauki
marinade din na ya zuba a sama ya juya ta shiga cikin kowane , sannan ya dauki tray din ya
juya ya saka cikin oven din ya riga ya kunna ya yi zafi sannan ya rufe

ya dawo ya tattare ledodin ya zubar a trash ya wanke bowl din mixer din ya mayar
ya na juyowa ya ga Esra tsaye bayan shi ta na sakin wani kyawatencen murmushi

ba karamar razana ya yi ba dan har wani dan baya ya yi
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " me za mu yi yanzu ? "
a hankali ya karaso gaban counter din ya tsaya ya na fadin " oven nawa gare ku ? "

" biyu ne " ta fada ta na karasowa geffen shi ta tsaya
" okay , ki na da puff pastry ? Apple , cinnamon , cane sugar , lemon "
cikin rudu ta ce mishi " me kuma za ka yi da su ? "

sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " Apple pie , ko ba ki so ? "
dan zaro idanu ta yi ta na fadin " no , da gaske , shi ne favorite dessert di na "
slowly ya juyo ya kalle ta sai sakin murmushi ta ke , shi kan shi bai san lokacin da ya saki
wani dan karamin murmushin geffen fuska ya na ce mata " ni ma haka "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta juya ta nufi fridge ta fiddo mishi duk abubuwan da ya
zano mata ta dawo ta ajiye gaban shi ta na fadin " amma fa ban da mold din yi pie "

" no wonder , wadda za mu yi ba ta bukatar mold , it's simple and delicious , cikin 30 minutes
za ki iya yin ta "

gyada mishi kai ta yi a hankali kafin ta ce " okay prof , bismillah ina kallon ka "
wani dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " yawwa student , yanzu kawo min tray din
gudan oven din , sannan ki kunna shi saman 180° "

" Yes Chef " ta fada cikin zolaya kafin ta juya ta nufi dayan oven din
maganar ta gaskiya ta ba ta shi dariya har wani murmushi ya ke saki shi kadai
fiddo tray din ta yi ta kunna oven din kafin ta juya ta ajiye mishi gaban shi

ta na ajiye wa ya juya ya nufi gas cooker dama pan din na ajiye a sama , kawai sai ya kunna ,
ya dawo ya dauki Apples din ya yanka su kana kana sannan ya zuba cikin pan din da ta riga ta
yi zafi , ya zuba cane Sugar din da cinnamon da juice din lemon kadan , ya jujuya su , su ka
shiga cikin juna har apples din su ka fara yin laushi
ya na ganin hakan ya kashe ya dauko pan din ya juyo da ita ya ajiye saman counter
sannan ya juyo ya kalli Esra ya ce " ina fatan ki na ganin abun da na ke ? "
" ni fa kaina 10000GB ne , duk na yi recording abun da ka ke yi "

wani dan karamin murmushi ya yi kafin ya juya ya dauki puff pastry din nan , ya shinfida
saman tray din oven , sannan ya dauki knife ya raba shi gida 8
da ga haka ya dauki spoon ya fara debo apples din ya zuba saman parts 4 , sannan ya
dauko wadancen da bai zuba ba a kai ya rufe su da su , ya dauki fork ya danne bakunan su
daya bayan daya dan kar su bude

ya na gamawa ya matsa gefe ya kalli Esra ya ce " za ki iya sakawa a oven "
dan zaro idanu ta yi ta na fadin " ban gane ba , har mun ida ? "
gyada mata kai ya yi a hankali ba tare da ya ce komai ba
" mun yi sauri fa " ta fada ta na daukar tray din ta saka a oven ta rufe kafin ta dawo geffen shi
ta tsaya ta na fadin " minti nawa zai yi a ciki ? "

" juste 20 minutes " ya fada ya na kai hannu ya dauki spoon ya debo apples ya kawo saitin
bakin Esra allamun ta ci

wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta bude baki a hankali ta karba ta na kallon shi
gaskiya ba karamin dadi abun ya yi mata ba har wani dan lumshe idanu ta ke yi
sai da ta gama cinyewa sannan ta kalle shi ta ce " gaskiya ya yi dadi , har na matsu ya gama
"

wani cool murmushi ya sakin mata kafin ya ce " ke ce mutum ta farko da ta ci abun da na
girka kuma ya ce ya yi dadi "

" hmmmm , yanzu mintina nawa za mu jira ? "
" just 20 minutes " ya fada a takaice

wani dogon nunfashi ta ja ta na saukewa a hankali kafin ta ce " Yanzu me za mu yi ? "
sai da ya dan jinkirta kafin ya ce mata " Watch cartoon "
dan zaro idanu ta yi a hankali ta na fadin " cartoon ? da wannan shekarun naka ? "
" yeah , har yanzu ni baby ne "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kai hannu ta ja mishi kumatun shi na dama ta na fadin "
yeah , you are a big baby "

shi kan shi maganar ta sai da ta ba shi dariya , har sai da wadanan fararen hakwaren nashi
su ka fito
a hankali ta janye hannunta ta na kallon face din shi gwanin burgewa tun da ta ke ba ta taba
ganin murmushi mai kyau irin nashi ba

wani cool murmushi ta saki kafin ta juya ta na fadin " mu je na saka maka , Big baby kawai "

ba musu ya bi bayanta su ka koma parlourn , su ka zauna sannan ta kunna mishi Tv , ta ba
shi remote din sannan ta dauki laptop din ta ta ci gaba da aikin ta

cikin nitsuwa Kim ya fara sauya chanel din har ya samu chanel din da su ka saka cartoon
kamar wani karamin yaro ya tsaya ya na kallo amma ta wutsiyar ido Esra ya ke kallo
ya na a haka kawai ya fara jiyo Muryar ta sama sama kamar ta rero waka

shi ko karatun Qur'ani ne ta , ta na karanto suratul Mariam cike da nitsuwa ga Muryar a
sanyaye mai dadin sauraro

duk da bai san abun da ta ke fada ba amma ya ji wani sanyi cikin zuciyar shi , irin sanyin da
bai taba ji ba
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juyo ya kalle ta da kyau ya ce mata " wace waka ce

wannan ki ke ? "

wani cool murmushi ta saki kafin ta dasa Aya ta dago kai ta kalle shi ta ce " ba waka ba ce "
" to minene ? ni ban taba jin wannan abun ba "

" dama ta ya za a yi ka ji shi , kai da ba musulmi ba kuma babu musulmai a kusa da kai , ka
san minene religion ko ? "

" Eh na sani , amma ban taba yarda da su ba saboda duk makaryata ne , sai su yi ta
maganar abubuwa da ba gaskiya ba su na karbar kudaden mutane "

" wannan church ne su ke yin hakan , akwai mosque a garin nan zan so ka je ko so guda ne ,
za ka gane abun da ya ke gaskiya da abun da ya ke karya , amma zan so ka san addini na ba
karya ba ne , sai wanda Allah ya so ke samun damar kasancewa musulmi "

cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " wanene wannan Allah , kenan in bai so mutun ba ba zai
iya zama musulmi ba ? , kenan ni ba ya so na ? "

" Allah shi ne ubangijin da mu ke bautawa , shi shi kadai ya ke , babu wani abun bautawa
bayan shi , shi ya hallice samai da kassai sannan ya hallice mu dan mu bauta mishi , cikin
addini na shan wine haramun ne , shi ya sa na ke son ka daina , bayan hakan babbar illa ce ga
rayuwar ka ma "
bai ce mata komai ba ya mike a hankali ya nufi kitchen
Esra kuwa tambayar shi ba karamin dadi su ka yi mata ba tun da har zai iya tambaya wanene
Allah hakan na nufin ta fara jan hankalin shi zuwa ga musulumci , in har Kim ya koma musulmi
to tabbas abun alfahari ne wajen ta

ta na kallon shi har ya shiga kitchen din ya bude oven kai tsaye kawai ya kai hannu zai dauki
tray din
a dubu dari ya janye hannun ya na ja da baya shi duk ya mance da zafi abun gare shi

da sauri Esra ta ajiye laptop din ta ta tasso ta nufe shi ta na fadin " Oh my God , Kim kai ma
ina hankalinka za ka sa hannu kai tsaye babu mitten "

" mantawa na yi " ya fada ya na matsowa wajen washbasin ya kunna fanfon ya zuba ma
hannun shi ruwan sanyi kafin ya janye

cike da kula Esra ta ce mishi " mu je na shafawa maka pommade kar wajen ya ja ruwa ya
zame maka matsala "
potholder ya dauka ba tare da ya ce mata komai ba ya saka , sannan ya fiddo tray din ya
ajiye saman counter
ya na ajiye wa wani qamshi mai dadi ya fara tashi a wajen ko ni sai da na hadiye yawu

a hankali ya juya ya nufi gudan oven din ya bude ya fiddo tray din ya ajiye geffen dayan
sannan ya fidda gloves din ya ajiye gefe
ita dai Esra ta zama yar kallo a nan ta na hadiyar yawu

shi kuma plates biyu ya dauko , dan madaidaita , ya dauki spoon da fork ya fara dauke Apple
pie din nan daya bayan daya ya jera saman dayan plate
sannan ya fara kwassar fish din nan da potato da carrot ya Zube duk saman dayan plate

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login