Showing 45001 words to 48000 words out of 48110 words

Chapter 16 - TRUE LOVE Book Complete by Princess Meerah.pdf

mata " ko kusa , yadda na ke son ku haka na ke son shi har cikin
zuciyata "

wani dan karamin murmushi Emilie ta sakin mishi ba tare da ta ce komai ba
su na a haka Ayden ya fara sauko stair , ya na sanye da wasu Tracksuit purple , da sneakers
farare , ya saka wata face mask white ita ma , da wata coat black color sam ba na iya ganin
face din shi
bai bi ta kan su ba ya nufi kofar fita gidan ya fice abun shi
[28/02 à 10:12] :


TRUE LOVE
__________________

SOYAYYAR GASKIYA







( A HEART TOUCHING LOVE STORY )




STORY & WRITING BY : MEERAH

GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA
WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i




يبر حزأ ملألا يذلا رصتعي !يبلق ررح يناسل هصلخو نم لك ،ضومغ ىتح مهفي سانلا ام !لوقأ




BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM




{P A G E 31 & 32 �}




da kallo Emilie da Brian su ka raka shi har sai da ya fice sannan Brain ya yi wata yar karamar
dariya ya ce " ke dai wannan dan uwan naki ya na son face mask "
ita ma dariya ta yi ba tare da ta ce mishi komai ba


������������

▪ESRA ❤


zaune ta ke cikin parlourn apartment din su , ta yi zugum waje guda ta na tunanin yanzu ya za
ta yi tunda ba ta da aiki ta ya za ta ci gaba da zama a New York , ba za ta iya daurawa Safna
nauyin ta ba , in ba ta koma Nigeria ba , to dole ta nemi aiki ko da na server ne

ta na cikin duniyar tunaninta ta ji a na yi musu knocking
a hankali ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ta mike jiki a sanyaye ta nufi kofar
ko tambaya ba ta yi ba kawai ta bude kofar

ta na budewa idanunta su ka sauka saman Kim tsaye bakin kofar sanye da wani wandon jeans
dai'dai guyiwa white color da wata shirt white , gashin nan nashi a gyare yau ya yi wani smooth
a konce gefe guda

ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta na shirin magana ta jito wayar ta ta na ringing
a hankali ta juya ta na fadin " bismillah , come in "
ba musu ya shigo ya meda kofar ya rufe

Esra kuma ta nufi wayar ta ta dauka ta na kallon Screen din wayar ta ga sabuwar number ce
kuma ta New York ce

cikin rudu ta dago ta kalli Kim da ke tsaye ya na kallon ta kamar shi ne ya kira ta
a hankali ta dawo da kallon kan wayar kafin ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ba tare da ta ce
komai ba

kawai sai ya jiyo Muryar Adrian ya na fadin " please ina son magana da Miss Esra Yahaya "

" ita ce " ta fada a sanyaye murya cike da tsoro

cike da fara'a ta jiyo Muryar Adrian na ce mata " Good , Miss Esra my name is Adrian Manager
of Ayden Brian , PDG of ONE WORLD TRADE CENTER , na san dazu da safe sir Kevin ya je
ya ce miki ya sallame ki haka ne ? "

a hankali ta zauna saman sofar kamar za ta yi kuka ta ce " Eh haka ne , please sir ku yi hakuri ,
in sha Allah zan gyara ko ma minene matsa...... "

da sauri Adrian ya katse ta da cewa " I'm sorry Miss Esra Sir Kevin bai isar da sakon ba yadda
ya dace , ba sallamar ki a ka yi ba , Sir Ayden ne ya ba ki promotion na zama P.A din shi "

cikin rudu ta ce " P.A ? "

" Yeah P.A , hakan na nufin za ki samu karin Albashi , sannan kuma promotion din ta na tare da
gida da mota duk na P.A din shi , in har kin amince ki zo company karfe 7 da rabi dai'dai dan sa
hannu a cikin sabon contract din , da ga nan ki fara aikin ki , Hope za ki zo , Na gode "
ya na gama fadar haka ya katse kiran

slowly Esra ta sauko da wayar ta na kurawa gaban ta kallon ta kassa wani motsi
ganin ba ta ce komai ba ya sa Kim matsowa ya na fadin " Miss Chocolate , what happened ? "

ya na rufe bakin shi ya ji ta saki wata yar karamar kara ta tashi da sauri ta na tsale ta na kara
kamar wata yar karamar yarinya

dan zaro idanu Kim ya yi ya na kallon ta cike da rudu ya ke fadin " Miss Chocolate are you okay
? what happened ? "

ba ta ba shi amsar tambayar shi kawai ta nufe shi ta riko hannayanshi ta fara jujuwa da shi ta
na dariya
shi dai kawai ya biye mata sai tambayar ta ya ke amma ta ki amsa mishi kawai ya ja bakin shi
ya yi shiru

sai da ta gama juyin nata sannan ta shiga yi wa Allah godiya ta na karanto addu'a ta na
shafawa kafin ta kalli Kim ta ce " ka san wani abu ? "

" ta ya zan sani bayan tun dazu ina tambayar ki kin kyale ki ne " ya kai karshen ya na kauda kai

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " i'm sorry , farin ciki ne ya hana na ji ka , yanzu
Manager din shugaban companyn mu ya kira ni , ya ce an ba ni promotion din zama P.A din
Shugaban mu , hakan na nufin za su min karin Albashi "

dan zaro idanu Kim ya yi ya na kallon ta baki sake ya ce mata " P.A fa ? "
da sauri ta gyada mishi kai ta na murmushi ta ce " hakan na nufin za mu samu kudin sayan
Chocolate ko yaushe , kuma har gida su ka ba ni da Mota "

shiru ya yi bai ce mata komai ba , ya ma rasa me zai ce mata
ganin bai ce komai ba kawai sai ta daina murmushin , a sanyaye ta ce mishi " Kim , da allamun
ba ka ji dadin abun da na fada maka "

wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yi wani dan karamin murmushin geffen fuska ya
ce " Ta ya za ki ban ji dadi ba ? ni da za a dinga saya ma chocolate kullum , congratulations I'm
really happy for you " ya qarashe maganar ya na mika mata hannu

ba musu ta riko hannunshi su ka gaisa ta na sakin wani kyawatencen murmushi

da ga haka ta ce mishi " okay , yau me za mu girka kuma ? "

dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " ina ga kamata ya yi mu fita mu yi celebrated wannan news , ko
ya ki ka gani ? " ya kai karshen ya na daga mata gera guda

da sauri ta nufi Corridor ta na fadin " give me ten minutes yanzu na dawo "
da kallo ya rakata har sai da ta shiga sannan ya nufi sofa ya zauna ya na jiran ta

sai da ya yi ten minutes cib ko zaune a haka kafin ya jiyo wani dadaden qamshi ya fara tashi
cikin parlourn
har wani dan lumshe idanu ya yi dan bai taba jin qamshi mai dadi irin wannan ba

slowly ya juyo da kallon shi saitin corridor
nan ya gan ta ta na tafiya a hankali cike da nitsuwa , ta na sanye da wata Abaya navy blue mai
mugun kyau , ta sha ruwan stone launin gold ma su mugun kyau , ta gyara gashin ta , ya zubo
mata har saman shoulder ta yafa veil din abayar white color
ta na rike da wata yar karamar bag a hannunta , fuskar ta cike da annashuwa

tun da ta fito ya tsare ta da ido babu ko kiftawa , wannan shi ne first time da ya gan ta cikin
Abaya kuma gaskiya ta yi mugun kamata

a haka har ta karaso gaban shi ta na yi mishi magana amma sam bai ji ta ba tuni ya tafi duniyar
shi

murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta kai hannun ta saitin face din shi ta kyasta mishi yatsu
a dan razane ya dawo cikin hayacinsa ya na fadin " me ya faru ? "

cikin zolaya ta ce mishi " irin wannan kallon haka ai sai ka saka min evil eye "
bai ce mata komai ba ya mike tsaye ya na fadin " i'm sorry , ban taba ganin ki ba ne cikin irin
wannan kayan "

daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " sun yi min kyau ? "
slowly ya gyada mata kai allamun Eh
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta yi mishi godiya ta na fadin " yanzu ina za mu je ? "

a takaice ya ce mata " shan ice cream , amma ke a ki biya "
ba ta ce mishi komai ba ta kai hannu ta dauki wayar ta , ta bude bag din ta ta saka kafin ta juya
ta fara takawa ta na fadin " let's go ! "

ba musu ya bi bayanta su ka fito , kai tsaye building din su ka baro , su na tafe ta na zuba mishi
hira , shi dai kawai ya na kallon ta ya na jin abun da ta ke fada mishi , yau bakin nata ya ki
rufuwa kamar parrot

a haka har su ka karaso chop din , su ka sayi ice cream din , ta sayowa Safna ita ma , amma

dan jaraba shi Kim biyu ya ce ya na so daya ta chocolate daya kuma vanilla
babu yadda Esra ta iya haka ta saya mishi biyun , ta biya kudin kafin su juya su nufi hanyar gida

tafiyar su ke yi su na shan ice cream din su har su ka iso greenwich street ba tare da ta lura ba ,
shi kuma a ganin shi ta nan zai fi sauri su koma gida ne shi ya sa ya biyo ta nan

hanyar babu kowa , ko lamps ma daya daya ne ke kunne , kamar an yi busa a wajen
su na tsaka da tafiyar su kawai su ka ga wasu samari uku sun sha gaban su , da ga ganin su ka
San ba mutanan kirki ba ne , har wani warin taba su ke yi

dum Esra ta ji zuciyarta ta buga har ta saki bowl din ice cream din ta ba shiri , da sauri ta yi
bayan Kim ta buya

cikin nitsuwa Kim ya ce musu " Guys , what are you doing here ? "

wanda ke tsakiya ne ya ce mishi " ni ke tambaya a nan , where is my money ? ka ce min two
weeks , yau har one month shi ne ka sauya wajen zama dan kar na kama ka , yau sai ka ban
kudi na "

cikin sigar rarrashi Kim ya ce mishi " I'm sorry Pablo , i don't have money now , ka ba ni one
week wlh zan kai maka kudin ka har gida "

ko sannu Pablo bai ce mishi ba ya juya ya kalli saurayin da ke daman shi , da kai ya yi mishi
allamun ya caje shi
ba musu ya karaso ya kai hannu ya fara caje Kim
da sauri Esra ta dan ja da baya ta na sakin kara

da sauri Kim ya juya ce mata " please calm down " kafin ya juya ya kalli Pablo ya ce mishi "
please , ka ba ni one week zan ba ka kudin ka "

ya na gama fadar haka kawai ya ji saurayin nan ya kai hannu saman dick din shi
a dubu dari Kim ya sa hannu ya ture shi ya na dan zaro idanu

kallon Pablo saurayin nan ya yi ya na fadin " Boss , babu ko sisin kwabo a tare da shi "
cike da bacin Pablo ya kai dunkule hannu ya kai wa Kim bugu a face har sai da Kim ya dan
rinsina kamar zai fadi
amma ya dago ya na dan ja da baya ya ce " please Pablo , i promise zan biya ka kudin ka , ka
ban one week , in na wuce ka kashe ni in ka na so "

ko sannu Pablo bai ce mishi ba ya kai hannu ya damko kwalar rigar shi , ya daga hannu a
dunkule zai sake kai mishi wani bugun

da sauri Esra ta shiga tsakiyar su ta datse idanun ta da karfi ta na jiran saukar naushin a face

din ta
Pablo na ganin ta ya tsaya Cak , wani makirin murmushi ya saki ya na kallon ta

Kim na ganin irin kallon da ya ke yi wa Esra ya san ba al'heri ba ne , da sauri ya sa hannu ya
buge hannun da ya rike kwalar shi da shi , ya riko hannun Esra ya meda ta bayan shi ya na
kallon Pablo cikin ido

Wani dan karamin murmushi Pablo ya saki kafin ya ce " ai ga kudina nan a bayan ka , ka ban ita
kawai mu tafi "

Dum Esra ta ji gaban ta ya fadi , nan take idanunta su ka ciko da ruwa , kawai sai kara kankame
Kim ta yi ta baya ta na girgiza kanta a hankali

a sanyaye Kim ya ce mishi " No Pablo , please and please na ce zan biya ka kudin ka "
murya kassa kassa Esra ta ce mishi " nawa ne kudin zan biya shi "
murya kassa kassa shi ma ya ce " ki na ji ? zan kirga zuwa uku , ki juya ki bar wajen nan da
gudu "

da sauri ta ce mishi " No , ba zan iya tafiya na barka ba , ka fada m....... "

ba ta kai karshen maganar ta ba Pablo ya katse ta da cewa " kai , wai maganar me ku ke yi
kassa kassa haka ? "

Kim bai amsa mishi tambayar shi ba kawai ya shiga girkawa da ga uku , a rube su Pablo su ka
tsaya su na kallon shi
sai da ya ida girkon shi kawai ya ji Esra ba ta motsa ba , cikin rada ya ce mata " ki bar wajen
nan na ce miki ! "

ya na gama rufe bakinshi ta sake shi ta juya ta kwassa da gudu
Pablo na ganin ta fara gudu ya dan zaro idanu kafin ya kwassa da gudu shi ma ya yi bayan ta
da sauri Kim ya bi bayan shi ya na fadin " No Pablo , please ka kyale ta ! " ya na haka kawai ya
ji an riko hannayanshi ta baya an tsayar da shi
dai'dai lokacin da Pablo ya cin ma Esra ya damko ta ta kugu
wata razananiyar kara ta saki ta na neman kwatar kan ta har sai da ta saki bag din hannun ta
[28/02 à 10:22] :







Assalamu alaykum Barkanmu da warhaka yakk Allah ya sadamu da alkhairin dake cikin

wannan ranar Ta Juma'a yamana kariya daga dukkan sharri In sha Allah gobe za mu
shiga watan Azumi mai Albarka zan so na nemi gafarar baki daya , wanda na batawa ba
tare da sani na ba ku yahe min

yau dai kun gani har pages 3 na yi posting na bankwana ne , da ga yau zan tsayar da
posting sai bayan sallat , da ga nan kuma sai dai na ce mu hadu a paid group d'ina ,
da farko na saka kudin littafin a kan 500 ne , so saboda abun da ke faruwa kwana
biyun nan na ce zan sauko da shi kan 400 ko kuma 300 har yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login