Showing 1 words to 3000 words out of 60927 words

Chapter 1 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt

Compiled By Umar Dalha Funtua.



*Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS 👑*

Billy galadanchi

Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*

  *Ina rokon duk wanda ya bud'e wannan shafin daya taimaka yawa er uwata fad'imatu zahrah adu'a samun rahamar Allah,Allah ya fadada yakuma yalwata mata qabarinta ita da dukkanin musulmin dasuka rigamu gidan gaskia Ameen*

*Ina rokon Allah ya bani ikon rubuta Alkhairi da kuma abinda ze amfani al'umma baki d'ayanta Ameen*

                            01
A hankali yake sakkowa daga matattakalar jirgin na sama wanda ya sauka a farfajiyar filin jirgin saman sultan Abubakar 111 dake birnin sokoto,sanye yake da jallabiya me asalin kyau da kuma tsada saman kanshi hulace wacce akafi sani da tab'ani kasha hadisi, kallon farko dazakai kasan cewar lallai hutu ya ratsa fatarshi tako ina, se bayan daya rage saura masa steps biyu ya qarasa sakkowa sannan ya d'ago kanshi ya baiwa idanunshi abinci, murmushi ne ya sub'uce masa ganin ilahirin danginshi suna tsatsaye suna sakar masa lallausan murmushin da kallo d'aya zaka musu ka tabbatar suna cikin d'inbin farin ciki wanda yake har cikin zukatan su, idanshi ne ya sauka masa akan me martaba,wanda lokaci d'aya ya qarasa sakkowa ya nufeshi cikeda fara'a.....

Har qasa ya duka ya soma gaidashi yayinda shi kuwa ya sunkuya ya d'agoshi ya rungumeshi gaba d'aya, yafi minti d'aya ajikinshi kan daga bisani ya d'agoshi ya mika masa hannu suyi musabiha sannan cikin isa da nuna cikar kamala ta mulkin fad'in Nigeria matsayinsa na sarkin musulmi ya furta

"Assalamu Alaikum *ALI ABBAS* muna maka barka da zuwa" murmushi ya sakarwa mahaifinshi sannan yace

"Ameen wa Alaikassalam *ABI* Ina matuqar godiya da wannan karamcin" har a lokacin hannayensu suna a had'e a haka mahaifinshi ya qara rungumeshi sannan ya sake hannunshi yamai alamu dayaje su gaisa da sauran mutane.....

  A hankali ya juya yaje ya gaggaisa da sauran sukazo tarbarshi tukunna yabjuyawa zuwaga Zuhair wanda shine babban Amininsa suka rungume juna, ganin me martaba ya juya gun mota ya sanya dukkaninsu suka juya suma zuwa shiga motoci bila adadin masu dauke da fad'awa da securities da akazo dasu domin tarar *ALI ABBAS*........

Yasha gaishe gaishe acikin babban gidan na sarkin musulmi Muhammad Lawal dake unguwar kan wuri a jihar sokoto,gidane me fadi da girman gaske, wanda yake dauke da manya manyan sassa daban daban wanda suke cikeda tarihi da kuma al'adunmu na hausa, kamar yanda koban fad'aba kowa ya sani sarkin musulmin Nigeria shine yake shugaban tar d'aukacin sarakunan dake fadin Nigeria, sam shi a tsarinsa ba girman kai ko wulakanta na qasa dashi, sedai kam lallai akwai cikar mulki da sarauta a masarautar ta sokoto......

Se bayanda yaci abinci ya huta sannan yayi wanka ya nufi b'angaren fulany Adama wacce ta kasance mahaifiya agareshi....Asaman kilisarta ya tadda ita zaune,tayi zama irinna mulki wanda tun tasowarshi hakan yasan tana nata zaman, qirjinsane ya mugun dokawa ganin yanda ta kawadda kanta tamkar batasan ganinshi yanda dai ta saba, gwiwa a sace ya qarasa ya zube domin kwasar gaisuwa, bata ansashiba ya sanya ya kalli bayin yace dasu

"Ku bamu wuri" sum sum suka wuce suka bar wurin ya tattare nutsuwarshi ya mayarda dubanshi zuwa gareta,har yanzu bashi take kallo ba,cikin qarfin hali ya furta

"Barka da yamma ummu,ina fatan mun sameku lafiya" batare data kalli inda yake ba tace

"Lapia lau Alhamdulillah yaro, ina fatan ka dawo lafiya" d'an sassauci yaji koda bata kalleshi ba, be zata zata ansashi haka ba

"Lapia lau na dawo ummu,ina matuqar godiya" shiru tayi shima haka sunfi 5 mnts a haka ba wanda ya qara cewa komai, gyaran murya tayi sega wata baiwa tazo da sauri aqasa

"Ran fulani ya dad'e me kike buqata a wadatar dashi yanzu" gyaran zaman alkyabbarta tayi wanda ya nuna cewar ciki zataje take tayi kiran sauran bayin suka raka fulani cikin d'akin ta, gwiwa a sace ALI ya mike zuwa sauran bangaroran matan gidan, ba laifi sun nuna murna da gganinsa tamkar sune suka haifeshi......

     Part d'inshi ya koma yana jinsa wani daban, rayuwar madina akwai dad'in gaske komai ana yinsa ne cikeda musulunci da addini me tsafta, yasani shida madina yanzu kam sedai ziyara amma yana matuqar kewar garin, yanayin da fulani madina ke nuna masa na b'ata ranshi, ace kaida mahaifiyarka amma ko kallonka batayi wai kaine d'an fari, harse yaushe zata soma zaunawa dashi ta saurari matsalolinsa ne? Dafe kanshi yayi ya runtse ido kawai......

  *KADUNA NIGERIA*

Wani uban horn Huddy keyi ba qaqqautawa kai kace wani abin tsoro ne ya biyota, yayinda Gadangaa ke zaune abinsa yana sauraren rediyo ko gezau beyi ba, takaicin wancen mutumin takeji da girman kanshi, idan baba me gadi bayanan ya bud'e mata gate shine ze wani tsatsare ta da idanshi sekace wani maye,mutum ba kowa ba galadinman tsumma se d'aukar kai wata tsiya, da sauri Baba me gadi ya sauke butar dake hannunshi bayan ya fito daga toilet ya ruga da gudu ya wangale mata tangamemen gate d'in yana me bata hakurin cewar yana ban d'aki ne....

"Amma ya kamata ka ajiye duk wani uzuri naka iro, seka sallami wanda suka ajiyeka kokuma ni kakeso in riqa budewa kaina gate ne?" bece komai ba sabida yasan halin huddy se hakuri dayaci gaba da bayarwa,ta figi mota tamkar zata gurje masa en yatsun kafa tayi gaba dasu....girgiza kansa yayi kurin ya juya zuwa b'angarenshi yana mamakin halayyah irinna huddy da uwarta sam su basusan girman mutane ba, mahaifinsu sam beyi dacen mata da yara ba.....

  Wayarshi qirar tecno ya kalla yaga k'arfe d'aya da mintun sha biyar, haramar alwala yayi yaje ya gabatar da kiran sallah kamar yanda ya sabayi kullum, se bayan sun idar da sallah sannan ya qara komawa kan wannan bencin ya zauna, yana me daddana wayarshi, Manga ce tazo da sallamar ta ta duqa kusa dashi ta dire masa kwanon abinci sannan tace

"Yaa Gadanga gashi inji inno, tace a kawo ma abinci" murmushi yayi ya gyara zamanshi sannan yace

"Ina godiya sosai Manga, Allah ya saka da Alkhairi ki qaramun godiya wurin inno" batace komai ba se murmushi se kuma ta tsugunna anan tana wasa da 'yan yatsunta, kallonta yayi sosai yace

"Mutuniyata daganin wannan kallon nasan akwai magana ko, sanar dani menene inji?" murmushi ta sakar masa sannan tace

"Yaa Gadanga Babane wai baze barni inje boko ba kuma, kuma ni inasan in kammala ko secondry ne, yanzu fa ss 2 nake, idan yayi hakuri ai saura mini shekara daya da watanni ko?" murmushi yayi yace

"Ba komai mangan Inno kije ni zan masa magana inshaa Allah zaki koma ne kinji?" murmushi ta sakar masa sannan ta kwasa a guje kaikace wata qaramar yarinya zuwa cikin gidan, girgiza kanshi yayi sannan ya bude kwanon yaga tuwon shinkafane miyan kuka tasha man shanu, hannunshi ya wanke ya cinye abinshi tatas sannan ya dire kwanon yayi hamdala.....

    Ali Abbas durqushe agaban me martaba yana kwasar gaisuwa, bayan ya natsa sannan sarki ya sallami fadawanshi ya kalli Ali yace cikin nutsuwa

"Ali Abbas yaya hanya kuma, ya wurin aikin naku" murmushi yayi yace

"Hanya Alhamdulillah Abi, wurin aikin kuma komai Alhamdulillah yana tafiya a yanda kake so ba wata mishkila" girgiza kanshi yayi cikeda gamsuwa da bayanin d'an nashi sannan yace

"Inaa magana dakaine a halin yanzu matsayin uba ba sarki ba, wane shiri ne dakai game da aure kasan fa shekaru 34 bawai wasa bane" sosa kanshi yayi sannan yaja siririn hancinsa wanda hakan ya zame masa al'ada ya furta a hankali

"Abi,ban nutsu bane ai, zan kawo matar ba jimawa inshaa Allah" murmushi me martaba yayi yace

"Wacece matar to inji tun yanzu mana" sake yin qasa da kanshi yayi yace kuma cewa

"Abi ai tunda na dawo kasar ban zauna bane, zan dubota ne inshaa Allah" shiru me martaba yayi yace tsawon watanni takwas bega matar aure ba aikam da jira ko yanzu, a zuciyar shi yayi wannan maganar a fili kuma seyace

"Idan ka cika shekara d'aya da dawowa kasar nan, baka gama lalubo ta ba, ni zan lalubo maka a inda ya dace dakai" murmushi yayi yace

"Khair inshaa Allah Abi" daganan suka danyi hira kan yawa me martaba sallama ya koma part dinsa......

Seda ta tako a yangace tamkar batasan taka qasa haka take tafiyar, yana koyarda su hujaima da farouk karatu ta qaraso tsatsaye da ita ta wani yarfa mai kallon raini sannan tace

"Gadangaa na kula sam agidannan baka cika ayyukan ka, narasa dalilin daddy na rashin ganin laifinka a komai idan ka aikata" d'anjan fasali tayi had'eda wurga masa key na motarta saman jikinsa

"Zan fita bayan magrib so motana yazama clean b4 then" d'agowa yayi ya kalleta a karo na farko tunda ta fara maganar ganin irin wulaqancin data masa dan kawai ta ganshi a qarqashin ta ya sanya yace

"Idan na gama da yara zan wanke inshaa Allah" tsaki taja

"Banzaa kawai, se anyi magana ya soma kirawa mutane sekace Allahn ya sani, mutumin dabaya kula da aikinsa tsakani da Allah ai besan Allah ba, tunda biyanka ake bawai kyauta kake mana ba mugu kawai" ta mayarda dubanta zuwa ga Manga dake ta sakin tsaki a kaikaice jin irin cin zarafin da ake malamin su na addini tace a fusace

"Ke kuma dan uwarki wa kike kallo? Mayya kawai" manga dai batace da ita ci kanki ba, haka ta kwasa tabar wurin tanata faman banbamin dabashida maraba da rashin abinyi domin kuwa gadanga inzata shekara tanayi bawai damuwa zeyiba hasalima wasu lokutan abinda ke qara qular da ita befi yawan murmushin datake ganin yanayi ba aduk sanda take taqamar fad'anta.....

"kayi hakuri yaa mu'allim gadangaa" shine abinda Manga ta furta cikin qunan rai, dariya ta bashi ya kuwa yi dariyar har haqwaranshi suka bayyana

"karki damu Manga su dama masu kud'i haka suke ai, indai kana qarqashin su tokai bawane" murmushi tayi itama tace

"Amma ni idan ana maka ko anawa babana koma Inno na haushi nakeji, inshaa Allah idan na gama makaranta nayi kudi na zama lauya sena rama muku" dariyar ta qara bashi kan wani yae magana kuwa farouk yac


"Amma dai yaa mu'allim aiba kowane masu kud'in bane suke haka, Aunty huddy da maminta ne haka mu ai Ammin mu batawa talakawa wulaqanci kuma haka take gaya mata wulakanci ba kyau, meyi ma se an masa.... Murmushi ya sakarwa farouk yace

"Dama mana ai hakane farouk, ba kyau wulaqanta bayin Allah, kuma tunda kuke daraja d'an adam me kudi da talaka Aljannah zaku shiga inshaa Allah" narai narai hujaima tayi da ido tace

"To yaa mu'allim mu mamin mu fa? Wuta zataje itada da Aunty huddy sabida suna wulaqanci ko?" hannunta ya kamo duka biyu sannan yace

"Ba haka bane hujaima,Allah shine kad'ai yasan suwaye en wuta, sedai fa ana kyautata masu aikata kyawawan halaye samun rahamar ubangiji yayinda ake wa masu muna nan ayyuka zato mara kyau, yanada kyau d'an dama yasan meyakeyi, yakuma san yanda yake mu'amala da mutanen dake kewaye dashi, se kiga ana zatar masa shiga aljanna mad'aukakiya" shekarun hujaima sha uku amma tsaf ta gane me Gadanga ke nufii wannan ya sanya ta jinjina kanta ta furta a hankali

"Allah ka shiryar da mamina da Aunty hudaisa,ko zasu samu kyakyawan zato a wurin mutane" Ameen suka amsa gaba dayansu sannan sunaci gaba da karatun da sukeyi......

*Bayan wata biyu*

"Amma Ali Abbas zancen aure haka ze ci gaba dashan dukan ruwan sama bame rama masa, ayi haka kuwa, nidai na yanke shawarar had'aka da yarinyar gidan Aminina Alhj Mubarak hasan,dake garin kaduna sunanta Hudaisa kuma harna nema maka aurenta an kuma baka, seka shirya zuwa kaduna wani satin domin ku gaisa da kyau" lokaci d'aya Ali Abbas yaji ranshi ya baci, gashi sam baze taba iya yiwa Abin shi musu ba, murmushi ya qaqalo yace

"Mashaa Allah Abi,Allahu ya sanya Alkhairi ina matuqar godiya da karamci,Allah ya kara girma" sosai me martaba yaji dad'in wannan na'am da zabin shi da Ali yayi, ya dinga zuqaqa masa albarka ba iyaka......

Sosai gadanga kejin dad'in mu'amalar sa da Manga yarinya ta matuqar shiga ransa, yana matuqar ji da ita,tamkar wata qanwar sa haka ya dauketa, iyayenta ma suna girmamashi yana ganin qimarsu susan darajar d'an adam, kimanin watanninshi shida kenan agidan yana koyarda yara yana kuma baiwa fulawowin gidan ruwa, lokaci zuwa lokaci yakan tafi ganin gidan kuma baya tafiya seya kawo wakilinshi, duk kuwa sanda zeyi tafiyar to kuwa Manga da kuka suke rabuwa, da kyar take barin ya tafi wasu lokutan har qwalla take sakashi, ganin ita macece kuma gidan wani zata,wannan shine karonshi na 4 da zeyi tafiya tun bayan zuwan shi gidan, bazece ga ranar dazeyi tafiya batare datasha kuka ba harda majina, gashi dai ajinta 6 secondry amma wawta kamar me indai Manga ce.....

Yauma dai rigimar tafiyar akeyi, gabaki d'aya ta gama birkita masa lissafi, mahaifinta yazo yanata mata fad"a yayinda Inno se haquri take bashi, shi kamma ji yakeyi tamkar ya rufe ta da duka,yarinya tana girma tana cin qasa sekace wata er sha biyu kinada shekaru harsha bakwai amma bakisan inda ke miki ciwo ba,duk iya banbamin da Baba yayi dai manga seda gadanga ya mata dabara akn yafa kwana bakwai kwana biyu kacal zeyi sannan ta haqura ya tafi...

Kallon Innoh Baba yai yace "Indai Har wannan yaron gadanga ya dawo auren Manga zan bashi, bata yanda za'ayi ace ba soyayya a tsakanin su wannan lakuwar" kallon shi inno tayi sannan tace

"Banqi ta taka ba malam, amma fa bazeyu kabashi 'ya baka san dangin shiba ko d'aya"

"Amma ai inno kema kin shedi halin gadanga na qwarai, ke bakya ganin en manyan gidajennan ma se aiko masa suke da abin alkhairi suna saka yaransu yana koya musu karatun islama? Yaro me tsananin addini ina Manga zata samu irinshi?" shiru tayi sabida tasan halin Baban Manga indai ya tasarwa abu bame hanashi, tunda gashi ko zancen zuwa gidansu yaqi tunda ya samu matsala da en uwansa yau shekaru sha biyar kenan, ko Manga da sauran qannenta a nan aka haifesu,ko sunan Niger baya sanji........

Yaudai shirye shiryen tarar baqon Huddy akeyi, wanda zezo daga sokoto, d'an gidan sarkin musulmi, huddy se rawar kai akeyi, ana yadawa Ammin su faruk habaici a kaikaice,ita dai iya kacinta dariya kurun sabida tasan wannan tsarin Allah ne, kuma da Allah ya qaddari hussyn tace za'a aura ba makawa se anyi, da yardar Allah kuwa zata samu miji na gari ita d'inma subawai kwadayin su mulki ba......

Iya kwalliya da ado ansha su huddy, ba karya wani rantsatsen less ne a jikinta ruwan madara,an masa d'inkin gown play qasanta ya bude sosai,a saman wuyan anyi adon d'uwatsu pink colors da flowers masu kyau pink colors, dazeita tazo har gida tamata makeup, aka maka mata tauban aka mata lullub'i da mayafi pink color,tayi kyau matuqa......

Tunda yafito daga mota sanye da rawaninshi na saurata ya sungume imanin ilahirin mutanen dasuka fito waje tarbarsa ciki kuwa hadda uwar gayyar huddy, dukda yake acikin shiga ta saurata yake hadda rawani hakan baze hanaka ganin cikar hakittar saba da haiba, ga wani uban qwarjini daya ke dashi.. ...

Iso akai masa har cikin gidan bangaren masaukin baqi, aka wadatashi da kayan ciye ciye shida malam zuhair abokinshi, kallon ta yakeyi yyanda takeyin komai cikin nutsuwa a hankalo ta zauna a daya daga cikin kujerun dake parlor din,sannan cikin rausayar da kai tace dasu

"Muna muku barka da zuwa, muna kuma fatan hanya Alhamdulillah" kallonta yake yanaso ya hango inda takeda makusa har zuhair ya amsa mata gaisuwarta be ankare ba seda ya tabashi a hankali sannan ya saisaita nutsuwarshi yace

"Hudaisa mun sameku lapiya?" lumshe idanta tayi setaji tamkar fad'in duniyar nan babu wanda ya kaishi iya fadar sunanta

"Lapiya qalau Yaa Ali, yaya hanya da mutanen gida?" be ansataba se kallonta dayakeyi cikin nutsuwa yana nazartar halayenta, shiru ya ratsa parlor na kusan mintuna goma kan daga bisani yace da ita

"Mu zamu koma masauki se kuma gobe idan Allah ya kaimu, yanzu muna tattare da gajiyane, muna godiya da shimfid'ar fuska" murmushi tayi sannan tace

"Muke godiya da wannan ziyarar,Allah ya hutar da gajiya,ya kaiku masaukin ku lapiya" besan dalili ba seya tsinci kanshi da sakar mataurmushi har cikin ranshi yaji dad'in adu'arta agareshi, cikin qasaita ya miqe shima zuhair ya miqe, waje suka fito tayi musu rakiya har wurin motarsu, sunayin sallam sega Manga tazo ta tsaya tana kallonsu cikin quluwa Huddy tace

"ke mayyah wa kike kallo?" da sauri Manga ta shiga taitayinta shi kuma ALi seya ce akira masa ita, zuwa tayi ta duka tace dashi "Ina wuni yaa me rawani gani?" wani takaicine ya tarnaqe huddy jin wannan rainin hankalin datazo dashi wai yaa me rawani, yayinda shikam Yarima Ali da abokinshi zuhair dariya sosai ta basu suka kuwa dara abinsu, ya sake kallonta yace

"Sunana Ali amma mesa kika ce dani me rawani?" d'an d'ago kanta tayi ta kalleshi sannan tace

"Bansan sunanka yaa Ali ba ai, kuma naga rawanine akanka, shikamma wannan yaa d'an banki nake shirin ce dashi na ganshi sanye da suit" mamakin surutun ta zuhair keyi ba ruwanta da komai ita kam,da alama tanada quruciya,gyaran tsayuwarshi yayi yace

"Tokefa ya sunanki?" murmushi tayi sannan tace

"Hafsatu Manga sunana, amma kowa banda makarantar boko Manga yake kirana,kaima idan ka ganni kana kirana Manga kawai, sabida yaa Mu'allim gadanga kawai ke cemun Hafsat se en school kuma" dariya yayi yanzu kam har hakwaranshi suka bayyana gabaki daya yace

"To shi yaa m'uallim gadanga mesa bakice yadena ce miki hafsa ba?" wani far tai da idanta tace

"Shi d'in na dabanne ai, kowama yace Manga banda yaa gadanga yafi kowa iya fad'ar sunan" nanma dariya sukayi ta wawtarta huddy kawai ce taji wani bakin ciki, kasancewar ita se wani sha mata qamshi yake amma ji yanda yake biyewa Manga sakaryar yarinya yake biyewa haka....tsagaita dariyarsa yayi sannan yace

"To ni Hafsatu Manga zab riqa had'awa duka, ungo zoki karb'i na breakfast idan kinje skul" kallonshi tayi yana miqa mata kud'i sannan batare data karb'a ba tace

"Ni kullum Baba yana baiwa Innoh kud'in break ta bani, wani zubin ma da abincina nake zuwa, qawayena sutamun dariya waina girmi lunch boxx,niko ko'a jikina wlhy, kuma yaa gadanga ma yace kwad'ayi ba kyau, yana da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login