Showing 12001 words to 15000 words out of 60927 words

Chapter 5 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt

qura masa ido sosai batama qaqqautawa wannan karon sosai take hango idon gadanganta cikin na Ali Abbas, sake qarewa qirar jikinshi kallo tayi har zuwa qafafuwanshi da en yatsunsa, ja tayi da baya tabbas wannan gangar jikin gadanga ce amma fuskar Ali Abbas, to amma mesa cikin qwayar idonshi take ta iri daya data gadanga sak??? Kumama mesa sautin amon muryarshi ke kamanceceniya data gadangan ta, dafe qirjinta tayi ta sunkuya da qasa da sauri, tsaye yake tamkar wani tsatue yana nazarin yanayinta, ga alama saqon dayake shirin aika mata ya samu karb'uwa acikin zuciyarta... Alamomi sun nuna cewar babu memory d'aya na gadanga data manta dashi a rayuwarta, matsawa yayi kusa da ita yace

"Hilwa so kike ki kashe kanki akan gadanga ne wai? Bazaki nutsu ba ki fuskanci duniyar ki ta yanzu" hannu ta sanya ta toshe kunnuwanta,gani takeyi tamkar gabaki d'aya bawai Ali Abbas bane Aljanaine suka soma bibiyarta, ganin ya rikitar da ita ya sanyashi juyawa kai tsaye zuwa cikin gidan, huddy ya had'u da ita a parlor ita kanta mamakin yanayin shigarshi takeyi

"Abbi Wannan shigarfa?" kallonta yayi yace cikin d'aure fuska

"me tayi?" murmushi tayi tace

"seka tunamun da Gadangan nan na manga, shiyake shiga irin haka kai mutuminnan akwai mugun girman kan tsiya" bece komai ba ya wuce ciki ta bishi da kallo tana mamakin yanayin data kula yake ciki kwana biyu, ta qudurta aranta seta gane menene damuwarshi, yaudai ita ke call asibiti zata kwana dana yammane ya sanya take neman Manga ta sanar mata girkin dazatayi musu, kai tsaye waje ta nufa sabida daga dakinta ta fito batanan, a garden ta sameta tanata uban kuka, yanzu kam tsaki ta saka

"Haba manga!!! Waike wace irin yarinyace me kafiyar tsiya? Wlhy ki sani yau d'innan zan kira daddy a rabaki da wannan jarababben aure a aura miki wani, tun anajin tausayinki har kin soma bada baushi, ni inaji ajikina wlhy wannan guduwa yayi ya barki, shekaru hudu aiba kwana hudu bane bare mukasa jin koda labarin mutuwarshi" matsowa tayi da sauri ta riqe kafan huddy

"A a Aunty huddy karki mun haka,rabani da auren Gadanga tamkar rabani da rayuwatane karki mun haka, ku hakura wlhy nasan gadanga ze dawo gareni,tunda yafara mun gizo nasani tabbas ze dawo gareni ne" wani takaici ta qara baiwa huddy

"Kinsan Allah Manga wannan ya zame miki na qarshe dazaki qara zuwa nan koma a inane ke kinawa mutane kukan rainin hankali senaci mutuncinki, kuma wlhy ki sani idan ina raye semun kashe wannan tsinannen auren,maza ki tashi kije ciki ki daura tuwon semo miyan kub'ewa d'anye kuma ki hada mana mojito,ni zanje office call nakeyi se safe kuma, by 8 a tabbatar an baiwa jekada ya kaimun abinci" tana kuka ta wuce ciki, itama zuwa tayi ta kifa daddy tanamai bayanin yanda take ganin ya dace ayi da auren Manga, koda ta kammala ta juyo ta kalli Ali

"yaa Ali daddy yace idan manga ta kammala exams na semester d'innan a turota gida zataje court araba auren,yaronnan ya cutar da ita da yawa shekaru hudu,koni nan ban yafe masa ba bare kuma ita karan kanta" zabura yayi a gigice

"To mesa bazaku jira dawowarshiba,inaji ajikina ze dawone ai ko,ke kin cika iyayi wlhy sekace arayuwa akanki take zaune ze dawo mana, kumama tsabar kin rainani seki kira daddy amaimakon ni ki fara tun tub'ana banida wani muhimmanci kenan ban isa ba" sororo tayi tana kallonshi zata iya rantsewa tunda takeda Ali yaune karonshi na farko daya mata masifa haka, mesa wai? Tafa kula komai indai na manga ne Ali baya barin kowa yayi, ko qyalle ya ganta dashi indai bashi ya siya ba ya dinga masifa kenan, anya babu wata a qasa kuwa? Akwai ranar data bata kudi ta sauya waya bata mantawa karbewa yayi yace haqqinshine kula da rayuwarta anya wayannan maganganun nashi ba abin dubawa bane? To Amma meye a qasa wai? Gaskia koma miye seta nemo shi...da qyar tace

"Kayk hakuri yaa Ali bazan qaraba,yanda kakeso haka za'ayi" wata masifar ya soma

"Nine nakeda iko akan manga sabida a qarqashin kulawata take, ke din wa dazaki yanke mun hukunci a kanta, karki qara shiga zancen raba auren manga a kotu babu wanda ya isa ya raba wannan auren wlhy,aikin banza kawai" shiru tayi tana nazarin kalamanshi harya fita a daki, azatonta dakinshi yake wannan ya sanya tabi bayanshi, abinda ta gani akan gadon ne ya dauki hankalin ta, gashi baya nan, kai hannunta tayi ta dauki mask d'in ta kura mata ido tana tariyo wani abu, da sauri ta jefar ta dafe qirji ta furta da karfi

"GADANGA"!!!!!! Adaidai lokacin da Ali Abbas yashigo d'akin ya ga meke faruwa!!!!!!!

Billy Galadanchi( mom nu'aiym) idan lokaci ya yarda zan baku da dare inshaa Allah.
[7/6, 1:53 PM] ‪+234 706 571 7620‬: *Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS 👑*

Billy galadanchi

Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*

   *Ina baku hakuri barar adu'arku Allah ya biyamun buqatocina na alkhairi*

                      06

Wani kallo yabita dashi yazo kawai ya wuceta ya fad'a toilet, tsorace yake sabida tabbas indai har huddy ta ganeshi bawai shiba har Manga seta shiga wani sabon tashin hankalin, yasan huddy da kishin tsiya kuma yasanta da qyamar na qasa da ita wannan halinta ne babu me iya sauya mata shi, sedai tanada alkhairi sosai, dire jallabiyar jikinshi yayi ya sakar wa kanshi shaya, lumshe idanshi yana tunanin mafita yafi 10 mnts a haka kanya hakura ya fito ga mamakinsa,tana nan a inda yabarta a tsayen kuma wardrobe dinshi ya bud'e bayan ya kammala goge jikinshi ya dakko qananun kaya yazo ya dauki wani cream ya shafe jikinsa dashi....tana nan dai a tsayen tana mamakin ganin ko a fuskarsa bata hango wata alama data tabbatar da zargintaba, domin kuwa har qirarsa ta qarewa kallo yayinda take tariyo ta gadanga...gyaran murya tayi ta had'yi wani yawu me d'acin gaske tace

"Yaa Ali me wannan mask d'in yake nufi?" kallonta yayi fuska a d'aure yace "Keda kika kira daddy kika yanke naki hukuncin kin sanar dani ne? Ko kinyi shawara dani ne? Kije kiyi naki nima akan nawa hukuncin zanyi shawara ni kad'ai zanga zancen wa su daddy zasu d'auka" d'aure mata kai yai ta tako tazo kusa dashi a hankali tace

"Kayi hakuri yaa Ali ainace bazan qaraba, ya kamata kamun adalci iya tsawon zamana dakai komai nawa dakai nake shawara banda abokanan aikina banida qawa ko daya bare kace,dan dai yau kuskure d'aya seka dinga masifa inata ban hakuri kuma kaqi ka saurareni, dan Allah kayi hakuri yaa Ali" shiru yayi ganin tana sharar k'wallah ya sani yayi over reacting kam, wannan ne karanshi na farko daya taba yiwa huddy masifa haka, janyota yayi jikinshi

"Huddy ya isa haka bari kiji rainane ya baci dake ai, ni kinga danasa akai wannan mask din banyi taking wani action ba sedama na sanar dake naso, dama nasa anyishine sabida asamo namiji ya sanya ya gayawa Manga cewar shine gadanga kuma ya rabu da ita taje abinta kin gane dai, kinga da wannan bazamu wahala da itaba dole ta hakura, a hanjun ta na karbe hoton su naje na sanya akamun shi a london, nasan zakice bansan gadan ga ba, kuma ma a ina na samu hoton shisa nake gaya miki tiryan tiryan, naje miki ne dama da zuwan zan sanar dake nawa tsarin jiran zuwan mask din kawai nake dama" nisawa tayi wani sanyi taji ya ratsa ta jin yanda mask din take  sannan tace

"Yaa Ali inaga wannan da muke shirin yi ha'incine da zalunci, yanzu qaddara munyi nasarar yin hakan, se kawai bayan tayi wani auren tsohon mijinta ya dawo, kokuma misali ace tun wancen lokacin ma ya mutu se yanzu mukaji labari,me kake ganin zamu sanarda iyayenta da ita kanta? Kasani ko kotu aka raba auren tayi wani auren idan ya dawo sedai a bata zab'i ta zaba koshi ko sabon mijin, zancen gaskia Abbi ba haka ya dace muyi ba, anawa ganin kenan" nisawa yayi yace

"Kuma kema kinyi tunani me kyau, ba damuwa a ajiye wannan zanyi magana da ita" shiru tayi batace masa komai ba.

   Dare lokacin ba kowa a b'angaren se Ameer da yalwa se kuwa Manga, dama d'akin yalwa daban yake Ameer kuwa dama  wurin Manga yake kwana, baccine ya dauki manga batare da shirin yin shiba ko adu'a batayiba saboda gajiya, se wuraren sha d'aya ta farka, wanka taje tayi ta dauro alwala sannan tazo ta tanawa  Ameer adu'a jin an murd'o k'ofar d'akin ya sanya ta mayarda dubanta zuwa ga k'ofar zubara tayi sabifa kayan bacci ne kawai ajikinta, tasoma janyo hijab d'inta dake kan gado,sanyawa tayi sannan ta qura masa ido yaudai ta kasa ce masa komai

"Hilwa bakiyi bacci ba?" tsoratar da ita yake qarayi idan yana ambatar mata wannan sunan, murya na rawa tace dashi

"Yaa gadanga ya sanarmun cewa kalmar hilwa alarabce ma'anarshi kyakyawa mesa kake kirana da wannan sunan?" murmushi ya sakar mata me sanyi sannan yace

"Gobe kinada muhimmin abinda zakiyi?" kallonshibta sakeyi "Ba abinda zanyi" tabashi ansa a taqaice cikeda kasala

Takowa yayi ya masto inda take sosai, ya kamo hannayenta duka biyu ya riqe, jikintane ya soma rawa ta d'an zame hannunta daya,ya qara kamowa ya matso daf da ita har suna jiwo bugun da zuciyoyinsu keyi

"Gobe ki shirya da safe k'arfe 9 zamu fita, akwai maganar danakeso muyi wacce take buqatar sirri"  zuwa yanzu harta soma hawaye

"Wace magana yaa Ali daba zamuyita cikin gida ba kokuma tare da Aunty huddy" hannunshi ya sanya ya soma share mata qwallan da suka zubo mata sannan yace "Banasan kukannan kamar yanda banasan gaddama kinji hilwa" tsiratar da ita yake duk sanda yake murya ko d'abi'u irinna gadanga ,gyad'a masa kanta kurun yayi ya sake hannayenta

"kiyi adu'a kafin ki kwanta kinji" nanma gyad'a ma kanta kurun ta kumayi,be damuba ya juya kawai ya bar d'akin, zaman dirshan tayi saman tile tana tunanin wannan abin, waishi yaa Ali besan tanada aure bane? Ko kuma shibesan darajar aureba, koshi d'an iskane dai? Banda haka mesa yake taba ta? Koda batada aure ai wannan haramunnne bare kuma da auren a ka? Gaskia da sake.....

Duk yayinda gadanga ya runtse idanshi Manga yake gani, wannan ganin daya mata cikin kayan bacci ya firgitar da tunaninsa, babu abu mafi daukar hankalinsa irin lallausan gashin manga, yana tsananin buqatar yaji yakai hannunshi yana shafar kanta, runtse idan shi yayi yayinda qirjinshi ke tsananin doka masa sabida abinda yake shirin yi besan yaya ma za'ayi manga ta karb'eshi ba.....

    Washe gari kuwa da sassafe Manga ta shirya Ameer yaje wurin yalwa, itama tayi wankanta ta sanya abaya baqa da mayafinta tayi kyau ainun.....kai tsaye part d'insu taje tamasa knocking lokacin ma huddy ta dawo tun 7:am, itace ta bud'e mata k'ofar seta kasa ce mata Ali take nema kurun tace

"Zan wuce school ne" kallonta huddy tayi

"Ina kince yau bakuda lecture's?" wayancewa tayi

"Da akwai wanda ze koyamun karatu ne,kuma yau ammana fixing lecture har biyu ma" jinjina kanta tayi "To kudin kashewa fa akwai?" ta kuma tambayar manga

"Ea wannan karon 40k yaa Ali ya sakan a acc nawa"  murmushi tayi tace "Lallai er gata duk ina zakine dashi, nagano yayankinnan yana shagwab'aki da yawa" murmushi tayi har haqwaranta suka bayyana gefen kumatunta d'aya kawai ya lob'a sosai, ta juya kawai tana cewa ta tafi, gogan kuwa ya rogata waje tana zuwa wurin motoccin ta ganshi tsaye jikin motar data kula yafiya amfani da ita, da hannu yamata alama data zago ta shiga motar ba musu ta shiga suka bar harabar gidan, be zame da ita ko inaba se gues house d'inshi dake sama road.....
 
   Kallonshi tae bayan yayi parking tace dashi "yaa Ali nanfa?" murtuqe fuska yae tamau

"Kizo muje kinji,banson yawan tambayoyi tunda ba cinyeki zanyi ba" murmushi kurun tamasa tagano beji dadin tambayar ba ta sakkoo.....

A parlor bayan tasha ruwan daya sanya wata dattijuwa ta kawo mata ya umarceta data shiga bed room dake hade da parlor din wanda ta kula se an shiga wani lubby haka ake tadda kofar dakin, ba musu ta shiga shima ya rufa mata baya, mamakin ganin ya baiwa wannan dattijuwar umarnin kar wanda yashigo gidan yake sannan ya kawota dakin ya kuma qulle, batace masa komai ba ta dai sunne kanta qasa, wata jaka ya dakko ya zauna kusa da ita sosai har jikinsu na gogar na juna,bata daice masa komai ba harya zuge jakar, ya zaro wani zobe ya miqa mata

"Hilwa kin gane wannan?" karb'a tayi ta qurawa zoben ido se kuma ta mayarda dubanta zuwaga na hannunta, zare natan tayi ta had'a da wannan kai tsaye heart d'in dake half ta had'e,murmushi tayi ta kalleshi

"Kalar zoben da yaa Gadanga ya banine a ranar dazeyi tafiyan dabe dawo ba, yace dani in riqe yabani ajiyar rabin zuciyarsa yayinda yace nima rabin tawa na hannunshi harya dawo gareni,bangane dalilinshi namun wayo ya gudu ba bayan yace na shirya mutafi tare, wlhy danasan yaa gadanga ze mun nisa har haka dabazanje dauko kayan nanba sedai nabishi a yanda nake..." murmushi yayi yasake kallonta ya miqa mata pictures dake hannun shi yace "wa'ennan hotunan fa" da sauri tasoma kalla tana zare ido, kallon shi tayi murya na rawa ta soma magana

"Yaa Ali dama ka had'u da yaa gadanga shine baka sanar dani ba, nasan a hannunshi kawai za'a samu wannan zoben da wa'en nan hotunan, ranar daze tafi ya ebe su ya sanar dani ze nunawa en uwansa, ko d'aya bebar munba, dan Allah yaa Ali sanar dani wane halin yake ciki yanzu?" shiru yana yana jin matuqar tausayinta lokaci d'aya bugun zuciyarsa yayi mugun qaruwa, da qyar ya iya furta "ki kwantar da hankalinki muyi magana Hilwa zakiji komai" riqo hannunshi tayi harta soma hawaye

"To yaa Ali amma karka sanar dani cewar wai gadanga mutuwa yayi, nasan be mutuba wlhy yana raye ko yaa Ali?" shi kamma qara rud'ar dashi takeyi riqe hannunta ya qarayi shima yakula bata cikin yanayin hankali ma, mask d'in ya ciro agabanta ya daura akan fuskarsa dama yanayin sanya irin na gadanga yayi, miqewa tayi da sauri taja baya cikeda tsoro se sannan ta kula da yanayin shigarsa

"Idan tunani kake zaka iya siye zuciyata ka lalata mun rayuwa wlhy kayi kad'an kuma Allah yafika, kasani wannan hanyar daka d'akko bame dorewa bace kuma ka cutar da Aunty huddy kama da wane ai bata wane Yaa Ali, shiya sanya ka kawoni nan har kana rufe d'aki sabida kai lalata dani ko?" beyi tsammanin zuciyarta zataje mata canba, cire mask d'in yayi yaje kusa da ita ya riqo hannunta da sauri ta warce hannun, d'an had'e fuska yayi

"Ke a tunanin ki ko mata zan nema sena rasa wacce zan nema saike, shekaru nawa ina ganinki bansan zan neme kiba se yanzu, me kika d'aukeni? Cewa na miki zamuyi magana kuma maza ki zauna ki nutsu magana zamuyi ki kuma bude kunnuwanki ki saurareni da kyau" zama tayi tanata faman kuka yace cikin nutsuwa


"Kamar yanda kika sani Sunana*ALI ABBAS* muhammad Auwal, haifaffen garin sokoto ne kuma mune mukeda masarautar sokoto gabaki dayanta, Na taso ne gidanmu naga mahaifiyata itace Babba acikin matan sarki, ya dad'e bayan ya aureta be qara aure ba, kasancewar yana matuqar santa amma sedai Allah be basu haihuwa ba da wannan Allah ya bashi ikon qaro mata har biyu, Umma hasana da mama iya nasan duk kin sansu da 'ya'ya yensu, bayan yayi auren se matan suka dinga haifa masa yara amma duk mata to kuma kinsan duk wani sarki da bashida magaji hankalinshi baze kwantaba sabida mata basa sarauta sun shiga damuwa sosai katsam Fulani Adama ta samu ciki, cikin ikon Allah data tashi haihuwa seta haifeni!!! A wannan lokacin anga murna kasancewar sarki ya d'oki san duniya ya d'ora akaina, baya ganin kowa se ni kawai, sekuma na taso cikin tsananin tsana agidan wurin en uba, bayanni akwai qanina shamsudden da haris fulany ce ta haifemu mumu uku batada mace ko d'aya,yayinda sauran mata basuda maza a yaransu duk matane duk yawan haife haifen su kuwa, aduk yanayin tsanar danake gani daga gun en uwana babu wacce take damuna irin yanda fulani adama kemun, ba ruwanta dani ba'a dukana tai magana ko aci zalina itadai kurin kawai, bata bari na rab'e ta sam, duk azuwan dan fari nake, ko sunana bata kira!

Wannan abin datake mun yana cikin abubuwan dasuka janyo cabewar wasu al'a mura nawa gaba d'aya, ganin haka ya sanya ina gama primary school mahaifina ya daukeni zuwa saudiyya, a can nayi secondry school nakuma je jami'atul madeenah inda na karanci mechanical enginrng, har master's d'ina acan nayishi da phd da komai, kuma ina karatun addini sosai wannan ra'ayin mahaifinane, nikanyi shekaru banzo ba, dama sabida mahaifiyata nake zuwa to bata kulani gaisuwa kawai take ansamun shikenan, wannan ya qular da mahaifina sabida yashayi mata fada amma bata dena ba, wai a dole nine d'an fari, da wannan ya hanani zuwa gabaki daya nafi shekaru 14 banzo Niger ba sam seda na kammala duk abinda ya dace a saudi sannan na dawo Nigeria, Tun a airport na samu yanayin nutsuwa na dirata gida, kowa ya tarbeni cikin karamci en uwana ma da basa sona sena tarar dayawa daga cikinsu sun sauya hali sosai, amma abin haushi koda naje gun fulani Adama banda gaisuwa babu abinda ya kuma shiga tsakanina da ita, kece tafi shiri dake a gidannan nasha zuwa sashen ta kinacan kema shaidata ce akan yanda takemun tamkar wani d'an tsuntuwa. Shiru ya d'anyi kanyaci gaba

"Bayan na nutsu se mahaifina ya turani wani kamfaninshi dake kaduna na sarrafa qarafa ganin nafi qwarewa acan,tunda na dawo gidannan naga yanda bayi kemun tamkar sumun sujjada se abun ya d'aure kaina matuqa sekace ba mutane ba ko kuma rayuwarsu a hannunmu take? Wata rana naje wurin me martaba lokacin ban dade da dawowa ba sena tarar bayi sun zagayeshi anata fadanci ina zuwa se dukkansu suka miqe seda na zauna sannan suka fad'i suna zuba gaisuea yarima me jiran gado waye waye, mamaki nake ya sanya na miqa musu hannu muka fara musabiha nasan haka akeyi abinda na kula dashi shine wasun su suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login