Showing 3001 words to 6000 words out of 60927 words

Chapter 2 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt

kyau ka tsaya inda Allah ya ajiyeka, niba inda zankai wannan kud'in nagode sosai, zan gayawa Baba idan ka qara zuwa ya bud'e maka gate da wuri kanada kirki kaida yaa D'an banki" dariya gabaki dayansu suka saka, huddy se yaqe takeyi azuciyarta kamar ta shaqe shegiyar mangar can kuwa, ahaka sukai sallama suka bar gidan har sukaje masauki basu dena labarin Manga ba.....Manga ikon Allahh....

A b'angaren Manga kuwa suna wucewa huddy ta hau dukanta tana ce mata mayya, shegiyar yarinya in qara ganinki kusa da su baqina, yarinya sekace aljana,na tsani buzayennan wlhy, kune kuke kilewa kuna qwace mana mazaje me iyayin Tsiya lilis tamata kanta juya cikin gidan rai a bace.....


Washe gari kuwa su ALI na dira a qofar gidan manga ta kwaso a guje tana shesheka adaidai lokacin kuwa huddy ta dannowa wurin kai ta fito tararsu, bataga huddynba tasoma rattabe

"Yauwa yaa Ali,yaa Dan banki sannu da zuwa,dama zuwa nai na gayama ka, karkaga ban qara gaidaka ba, jiya naci duka a wurin anty huddy tace ba ruwana daku, karna qara gaidaku, abinda yasa na fada banso kuce banda kirki ne, gobe kona ganku bazan gaidaku ba kam inasan lafiyata" tsayawa kallonta kurun sukayi sega huddy tana zuwa ta bata kyakkyawan mari

"Bance karki qara zuwa kiwa mutane shirme anan ba,banza jaka?" kuka ta saka ta juya da gudu yayinda haka kawai Ali yaji ranshi ya matuqar b'aci yasha mur, bema shiga ciki ba suka gaisa yace sauri suke suka juya......

Vote If u enjoy this page.....ur comments are important than anything....


Mom Nu'aiym ce

[7/6, 8:07 AM] ‪+234 706 571 7620‬: *Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS 👑*

Billy galadanchi

Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*

Wannan shafin nakine Bilqeess....Allahu ya saka miki da alkhairi keda dukkannin wanda suka yiwa yar uwata adu'a, ina roqon Allah ya baku me muku adu'a alokacin da kuke tsananin buqatar adu'ar, Allahu ya muku damu baki d'aya kyakyawan qarshe ya sanya kalmar shahada ta zamo kalma ta qarshe dazamu furta Ameennn....
                                   02
Huddy bataji dad'in yanayin ALI Abbas ba kanya tafi gashi ko digit nata be karba ba sanda ya tafi, duk ta d'aura wannan laifin akan Manga shegiyar yarinya mayya,acewarta......

    Gadanga kuwa seda yayi satinsa d'aya sannan ya dawowa gidan, Ya hadu da mahaifin huddy suka gaisa yake tambayarasa dalilin tafiyarsa cikin gaggawa ya shaida masa mahaifiyarsa ce batada lafiya,dama tun farko daukar sa aikin koyarwa da wankin motoci da baiwa fulawa ruwa ya sanar masa,yanada mara rafiya akai akai zena riqa zuwa gida zariya domin ya dubota......

   A bangaren Ali Abbas kuwa sam shi bayasan halayyar Huddy, ya kula tanada tsauri akan talaka shi kuwa yafi tsanar wannan fannnin fiyeda komai,mace komai kissarta ze rayu da ita muddin tanada san Allah da manzansa, amma yana kyamatar masu kyamatar na qasa dasu, ba yanda zeyi sa zab'in iyaye dolenshi ya aureta......duk yanda yaso ya yakice tunanin  Manga a ranshi gabaki d'aya abin ya faskara, gabaki d'aya wawtarta na bashi sha'awa beqi ya sanyata agaba ya dinga saurarar wawtar ta yana dariya ba, da zaran ya tuna sanda tace mai wai yaya me rawani se dariya ta taso masa, bare yanda tace dashi "Da lunch box nake zuwa skul" da zaran ya tuna girmanta da yanda zata rarumi kula zuwa skul seyayi murmushi, har mamakin kanshi yakeyi abune mawuyaci ka ganshi yana murmushi bawai yanada baqin rai bane  nooo yakan jima beyi magana bane bare yayi murmushin ma.....

   Zaune gadanga yake akan tebur dake tacikin harabar ajiye motocin gidan sanda Manga ta rugo da gudu tazo ta tsuguna kusa dashi tace

"Yaa mu'allim gadanga barga da safiya" kallonta yayi yana murmushi dayake jimawa yanayi idan ya soma sannan yace

"Manga ni wannan sunan yanamun tsawo, ki zab"a ko yaa mu'allim ko kuma yaa Gadanga" murmushi tayi

"Tunda baban Manga yace ze baka aurena gwara kawai ince yaa gadanga Ango" kallon mamaki ya mata sannan da qyar labb'ansa suka iya furta

"Aure kuma Mangan Innoh?" murmutayi

"Ea mana, haka yace da Innoh a gabana,wai soyayyya muke kuma kai malamine, dan haka kuwa ze bakani ka aura, yaa Gadanga ni qawayena sunada saurayi suna bani labarinsu amma ni banida saurayi, ance da saurayi ake soyayya tonikam kaine saurayina tunda Baban Manga da kanshi yace muna soyayya" kallonta ya tsayayi harta idar sannan ya kawadda kanshi gefe d'aya ya soma magana a hankali

"Manga banasan shirmen kinnan, kije ki nutsu kiyi karatu, bakince lauya zaki zamaba? Karna qarajin zancen soyayya a bakinki ko wani aure a yanzu, komai kikaji an fad'a sekinzo kina fad'a kokuma shi Baban Manga shine yace kizo ki sanar dani zancen da sukayi da Innoh?" narai narai tayi da ido sannan tace

"Baya so na fad'a ya gaya a gabana, aiba komai bane kai kad'ai na gayawa se qawata Nana khadeejah, kuma tace mun dace da juna tunda kai kyakyawane,nikam indai zamu aure ka dena tafiya kana barina tonama dena zuwa makarantar daga yau, bakaji yanda nake san in ganmu a tare ba" shiru yayi sabida ya fahimci yarinyar sanshi take batare datasan da hakan ba, sam batada wayo ko kad'an,shi tausayi take bashi sosai sabida ya kula duk inda zama ya had'a da mutane zatasha wahala kasancewar tanada surutu harna wawta,batasan meye sirri ba sam!!.....bece da ita komai ba harta bar wurin jin Innoh na qwala mata kira.....

Kwana bakwai kenan ta tafiyar Ali Abbas wani yammaci su gadanga sun idar da sallah a masallacin kofar gidan da isha,Ali Abbas ya qara dira a gidan, yau kam ajikin shigar qananun kaya yake dasukayi matuqar karb'ar fatar jikinshi....yayi kyau ainun yakuma qara haske da jiki ba laifi, Manga ce ta wangale masa gate d'in kasancewar Baban Manga yana masallaci har lokacin be fito ba, ita bata ganeshi ba shine ya ganeta yana parking ita kuwa harta qarasa rufe gate d'in zatai cikin gidansu tajiyo muryan shi

"Hafsatu Manga, zo mana" juyowa tayi babu wani duhu kamar yanda ba wadataccen hasken dazata ganeshi kai tsaye beside ranar cikin rawani yake,sedai muryan ya mata kamar ta wanda ta sani, takowa tayi tazo tace "Waye gani?" murmushi yayi yace

"Yayan kine Ali Abbas" washe baki tayi "Laa yaa me rawani yau kai kad'aine ina d'an banki to?" murmushi yayi yace

"Zance nazo gun Huddy ki kiramun ita" kallonshi ta d'anyi tana murmushi

"Nima nayi sabon saurayi sunanshi Gadanga yana masallaci, amma baya zuwar mun zance, zaku gaisa idan ka fito ko?"murmushin dai ya qarayi yace

"Lallai ma yarinya ke yanzu har wani saurayine dake, naji to idan na gama zanzo mu gaisa,yanzu maza kimun kiran huddy, ki sanar mata ina sauri ne" batace komai ba ta kwasa aguje zuwa cikin gidan, kowa yasan halinta dan haka ba wanda ya damu da yanda ta shigo aguje, ta daiyi sallama kanta isa parlor d'in, ba wanda ya ansa sallamar tata se Ummi datace

"Ke Mangan Inno me kikazoyi anan yanzu kuma,neman tsokana ko" kallonta tayi dama ita bawai ishashiyar nutsuwa ce da itaba tace

"Nikam dama mezan zo na muku yanzu, Wannan me rawaninne yace azo akira masa Aunty Hudaisa, kuma yace a sanara mata yana sauri ne karta dade" da sauri huddy ta miqe tsaye zuwa cikin dakin domin gyara kanta, ba wanda ya kuma bi ta kanta se kallon hujaima tayi tace
"Su hujaima musulman loko, ana nan ana karatun Allah badonshi ba sedon gudun bulalar yaa mu'allim" takaici hujaima taji tace

"Ummi kinji manga waiba dan Allah nake bitar karatu ba" kallonta ummi tayi zatai magana manga ta rigata

"kaji wawiya yo koni ai gudun bulala yake sanyawa nake bitar, ko babba kikaga yana zuwa makaranta yana bita idan dai beyi dan gudun duka ba dole zeyine dan gudun kar amar dariya" dariya ta baiwa ilahirin mutan parlor din ciki kuwa hadd hussy da farouk, suna shiri da hussy sosai kusan sa'anin junane, suna nan har huddy tafito ta wuce su....seda ta gama tsokana da sakasu dariya tukunna sannan ta fito a tsaye ta taddasu matsawa tayi kusa dasu tace

"yaa Ali kaga sarkin zagwad'i ta riga er aiken zuwa ko? Kan na gama fad'a ma ta miqe, kayi sa'an mace kyakyawa kam" mamakin surutunta yake sekace wacce aka aiko ji wani shirme,ya sani kuma huddy taji kunya danyama kula da hakan, se yace cikin siqar wasa

"Dama mana ina zagwad'i nazo ita me kikeso tayi ne? Nafita ai nida nazo" tab'e baki tayi

"To Allah shibar qauna,yaa Ali ni nayi nan" takama hanyar gidansu be tsaidata ba ya kalli huddy yace

"Huddy?" kallonshi tayi batai magana ba

"ki dena damuwa da maganganun manga idan kin kula batada nutsuwa kuma tanada tarin quruciya akanta, abu d'aya zan sanar miki shine ki dena dukanta,iyayenta bazasuji dad'i ba ina horonki daki girmama talaka, da wannan halin kadai zaki samu karbuwa a masarautar mu, da kuma birnin zuciyata" murmushi tayi har hushiryarta ta bayyana tace

"Zan kiyaye inshaa Allah" Mota ya bude ya dakko wata leda ya miqa mata, hannu biyu ta sanya ta karba sannan yace

" Akwai waya da sabon sim aciki, tawace ni kadai, koda wane lokaci ki kasance riqe da wayar banasan tarin msd calls ba'a daga ba, bana san ganin call waiting kuma gwara nini kadai, sauran kayan kuma duk nakine,kiyi hakuri ranar ina uzuri ban tsaya mun gaisa da ke ba" fara'arta ta fad'ad'a sannan tace

"yaa Ali nagode Allah ya qara girma da d'aukaka,Kariyar mahalicci tabika a duk inda kake, Allah ya sanya Alkhairi acikin tarayyarmu dakai, nagode sosai ba adadi Allah ya qara bud'i" murmushi yayi har cikin ranshi yanajin dad'in adu'ar huddy, yasani bezo da shiri. Santa ba, be kuma zo da shirin qiyayyarta ba sedai fa ya kula sosai soyayyar ta naso ta rinjaye shi,kyaunta yana burgeshi, kalamanta masu hikima na masa dad'i,tanada girmama mutane wannan ma ya masa...... A haka sukai sallama ya juya ya tafi......


Shiru gadanga yayi bayan ya gama jin bayanin Baban manga, tabbas baze iya yiwa baban manga musuba akan auren manga, kazalika sam baze iya cewa tsakanin santa da rashin santa wanne ne yakejiba, shidai abu daya ya sani bayasan rawar kan yarinyar,da uban surutun datake dashi, anso mutum ya auri mace me sirri yaya zeyi da auren Manga????? Da qyar ya iya tattaro nutsuwarshi yace

"Ba laifi Baban Manga, ina godiya sosai da karamci Amma ina roqon alfarma abani lokaci kasancewar takamammen wurin dazan ajiyeta banida shi gashi kuma se anyi suturu da sauransu, zanso kuma ta kammala karatunta tukunna" murmushi Baban manga yayi

"Babu komai gadanga, Allah yashige mana gaba,ya hore abin lalura, nidai alqawari d'aya zakamun shine ko bayan raina zaka auri manga, kadaiga manga batada wadatacciyar nutsuwa nayi mata sha'awarka ne sabida na kula duk abinda ka lurar da ita to tanabi, kaga kuwa zaka saisaita nutsuwarta inshaa Allahu" gadanga yaji tamkar an daura mai wani dutse aka, nauyin ya masa yawa matuqa,ina zeje da girman alqawari,kalmar aminta da qudurin baban manga tamasa nauyin fad'a a harshe wanda harya sanya yai shiru....

"Malam Gadanga kayi shiru, ina fatan baka tunanin inaso na maka dole ne?" murmushi gadanga yayi yaji kunya matuqa tamkar me koyon magana haka ya furta

"Ba haka bane Baban Manga, nayi alqawarin Inshaa Allahu zan auri Manga ko bayan ranka" dad'i yaji matuqa yashi masa albarka sannan suka shiga masallaci domin gabatar da sallah isha.....

Ko kad'an Gadanga be shirya aure ba yanzu, badan bayason manga ba sedan kawai yana ganin lokacin aurenshi beeyiba, mema ze cewa iyayenshi? Kodai kawai ya bari se an daura ya sanar dasu? Haka gadanga ya zauna cikin rashin sanin abinyi,tunaninshinya tsaya cak, yana matuqar dana sanin abubuwa da yawa, ya zanyi da manga???" wannan itace tambayar dayakewa kanshi ba qaqqautawa.......


*Bayan wata hudu*

Su manga sunyi candy amma har yanzu ba hankali kam,se du'ayi kawai, Dama skul d'aya take zuwa dasu hussy, kuma tunda ga ranar da Baban manga yayiwa Gadanga maganar Manga be qarayiba shisa ma hankalinsa ya kwanta ya dena neman solution gaba daya.....yau yana zaune asaman bencin daya saba zama Baban Manga yamai sallama, suka gaisa cikeda girmama yace

"Gadanga dama zancen aurenka da Manga ne, kuma narigada na sanar da Alhj tuni, na sanar masa kaine ka zab'i seta kammala karatu gaba d'aya,tunda ta gama shine yamun zancen jiya akan na tuntub'eka aji ta bakinka" gabaki d'aya seda gadanga yaji tamkar ba'a duniya yake ba, sam be zata Baban Manga zewani gayawa me gidan su ba, yama rasa me zece seda yakuma cewa

"Gadanga kayi shiru" nisawa yayi yace

"Baban Manga ad'an qaramun lokaci, har yanzu ban gama had'awa manga kayan lefe ba, ban shirya wurin zamanmu a garinnan ba,tunda kaga ai nan nake aiki,bazeyiyu nakai Manga soba ba" nisawa yayi yace

"Gadanga na fahimci damuwarka amma Alhj yace anan bayan gidan zaku zauna tunda kaga ba samari ne dashiba se faruk kad'ai,kaga kanaci gaba da aikinka, yakuma ce bayasan ka mata komai shine ze muku har kai, A sanshima jibi juma'a daurin aure,sekayi haramar sanarwa iyayenka" qirjin gadangane yayi mugun dokawa yasani sarai iyayenshi bazasu tab'a amince masa auren manga ba, tayaya ma ze tunkaresu da wannan maganar tunda yanada zabinsu ajiye? Ina zekai girman alqawarin daya d'aukar wa Baban Manga? Ta ina ze soma juyawa kanshi? Gyaran zamanshi yayi yace

"Baban Manga, na sanar maka ni mutumin zaria ne a qauyen soba nake, banida kowa uwa ko uba duksun mutu, qanin mahaifinane zan masa waya yazo da kawuna, amma juma'a batai kadan ba, kuma ita Manga bata ra'ayin yin wani shagali ne? Zancen sadaqi dai zan biyawa kaina inada halin yin hakan" murmushi Baban Manga yayi yace

"Ka rabu da manga ba hankaline ya isheta ba,kuma ba wani bidi'a da za'ayi, iyayenka kuma ai badamuwa ko basu zoba dama nine waliyinka Alhj kuma shine waliyin Manga shine da kanshi ya fad'i hakan" murmushi Gadanga yayi ya masa godiya sannan ya wuce


Gadanga nasan Manga indan so,amma sam yasan aurenta babbar matsalane shida danginshi,juma'ar nan fa jibi ne? Saura kwana biyar aurenshi kenan yaya zeyi? Haka yayita saqawa da warwara harya daure dai ya sanarwa wanda ya dace suzo din.....

ALi Abbas ma da Huddy aurensu nanda 4 months masu zuwa, shirye shirye tsakanin sokoto da kaduna ba'a magana an shiryawa bukin auren ba kad'an ba komai yaji a yanayin shirye shirye lokaci kawai ake jira,dama huddy ba yarinya bace,itace 'ya babba acikin 'ya'yayen Alhj Tahir Maude,bashida manyan yara maza farouk ne kawai yaronshi namiji kuma qaramine sosai, yanzu haka huddy shekarunta 32 a duniya,mijin aurene bata samuba se yanzu........

*Rana Bata qarya*

Ranar juma'a kuwa kawun Gadanga da kuma qanin mahaifinshi sukazo daga soba aka d'aura auren Manga da gadanga, akan sadaki Naira dubu 30, duk yanda kike tunanin manga tashiga farin ciki abin ya wuce nan, sosai takeji da gadanga zama mu iya cewa tama fishi d'okin auren, anyi wuni ranar asabar batare da d'an uwan Baban Manga ko daya yazo ba kona Innoh kasancewar tunda ya baro gida be waiwaye su ba, Amarya tayi kyau ba laifi dama gata kyakyawa er jan buzu....a ranar aka miqa ta a BQ dake bayan gidan,wurin sahibinta gadanga.....

*Yazo mata da kaji na ban mamaki har guda uku gasassu da yoghurt,yakuma kawo mata sababbin kaya akwatuna guda uku wanda ta tsorata da gani, acewarshi shine yafi cancanta yawa matarshi suturu.....ranar dai duk surutu irinna manga batai masa shiba har tsokanarta yake yau ina bakin amma takasa koda kallonshi ne......

Duk yanda Gadanga yaso ya had'a jikinshi da Manga ya kasa, zancen gaskia yana mugun qyamar yanayin warin buzaye,kuma harya zamewa Manga halitta,duk kuwa dayake cewar sunada tsafta sosai wannan ne ya sanya yakecin abincin su,amma dai yana yin qmashin nasu be masa ba sam.....da wannan ya sanya bayama kwanciya wuri daya da ita....so kawai yakeyi ya zauna ya natsu seya riqa koyar da ita yanda zatayi amfani sa turarukan da yake so da kuma yanda zata riqa kwalliya kalar wacce yakeso ya shirya wayar da manga dan dai yana santa matuqa......haka suka rayu da juna cikin kulawa daso da qauna, zuwa yanzu gadanga ya gama sakankancewa yana qaunar mangan shi.....

*Bayan sati uku*

Waya akawa gadanga akan qanin mahaifinshi baida lafiya sosai, a haka ya shirya tafiya zuwa duboshi

Kallon shi Manga ta tsayayi tana kokarin tare hawayenta sabisa Inno ta sanar mata yanzu ta girma ta rage quruciya, amma sam ta kasa karo na farko daya rungumeta a jikinshi sosai yana bubbuga bayanta a hankali

"Kiyi hakuri Hilwa (sunan dayake kiranta dashi kenan tun bayan aurensu, kalmar Hilwa yana nufin kyakyawa kenan da Larabci) gobe zan dawo inshaa Allah" d'ago da kanta tayi tana hawaye tace

"Yaa Gadanga zan bika dan Allah,banaso ne ko kwana d'ayan kayi, ko masallaci kaje Allah Allah nake ka dawo, kuma idan ma kaje makarantar koyarwa har kuka nake,yaa gadanga kwana fa zakayi, dan Allah kaje dani" tausayinta yaji ba yanda za'ai ya tafi da ita duk yanda yaso,rungumeta ya qarayi

"Hilwa kiyi hakuri, daga zaran naje yau ni kad'ai duk inda zamu na miki alqawarin tare zamuje,bakya ganin nima zanyi kewarki sosai.... Girgiza masa kanta tayi

"yaa gadanga dan Allah kamun rai ka tafi dani, wlhy kewarka zata hallakani,bazan iya kwana gidan ni ka daibama" zuwa yanzu shima seda yayi kwallah, yace

"Haba Hilwa,kingafa abinda yasanya bazanje dake ba,banida kudin motan dazamuje mu biyu mu dawo shisa" d'ago kanta tayi "Zanje na karb'o kud'ad'ena dana baiwa Inno ajiya semu tafi tare" Hannayenshi duka biyu ya saka ya tallafi fuskarta yace

"Hilwa kinaso nayi fushi dake?" da sauri ta girgiza kai alamar aa, yace "Yauwa to idan bakyaso nayi,karna tab'aji kin dauki sirrinmu kin gayawa wani, idan inadashi sirrin mune, idan banidashi sirrin mune, idan muka samu sab'ani sirrin mune base kowa yajiba, idan muka tattauna matsalolin mu ma sirrin mune, ina fatar kin fahimceni sosai, banso koda su innoh kike gayawa sirrin mu,Zancen tafiya kuma kiyi hakuri namiki alqawarin wata rana tare zamuje" shiru tayi amma se kukan take haka ya saketa ya dauki jakarshi ya juya haryakai kofa taje ta rike mai kafa tana roqonshi

"yaa gadanga kewarka zata kasheni dan Allah kamun rai, kaje dani wlhy zanyi kewarka kuka bazemun magani ba" yaji tausayinta matuqa jiki a sanyaye yace

"Jeki dauki kayanki qwaya biyu kanna taro mana a daidaita sahun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login