Showing 24001 words to 27000 words out of 60927 words

Chapter 9 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt

tana zaune a qasa tayi tagumi, bazata iya tuna meya faruba tun bayan zuwan su station, ganin komai takeyi tamkar a mafarki, murmushi ta sakarwa ummu dake kallonta tana murmushi cikeda farin ciki sannan tace a hankali

"Ummu lafiya dai?" hannunta ta riqe "Karki tilastawa kanki yin magana Auta, bakida lafiya  ki saving strenth naki plss, ko akwai abinda kike buqata ne?" kallon Inno tayi tace

"Ummu yaushe mukazo kaduna?" murmushi fulany tayi

"Babu wata kaduna damu kazo, muna sokoto ai, kina asibitinr manga, raunin ya baki wahala dole tazo dubaki da kanta" murmushi tawa inno

"Inno ina Baban Manga?" kallonta ummu tayi

"Auta nace ki dena yawan magana sabida raunin dake kanki, ba a so kike baiwa kanki wahala koda ta magana ce" marairaice fuska tayi

"Ummu ninaji sauqi fa, Ina su Humaira?" shiru Ummu tayi tana kallonta sabida batasan ta daga mata hankali, seda ta gama nazari sannan tace "Duk sun komawa iyayen su, ko jiya ma sunzo duba ki" murmushi tayi tace

"Allah ya isarwa Humaira muguntar da aka aikata mata, Allah ya saka mata, Allah ka wulakanta masu irin wannan halin halin ya saka mana " se kuma ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi, ita kadai tasan me ta gani, ita kadai tasan kalar arzikin dasukayi,Allah kuma kad'ai ya sanya musu hannu suka kub'uta daga hannun wa'yannan azzalu man, tsorata takeyi kazalika takan samu kanta cikin mummunan fad'uwar gaba duk sanda ta tuna yanda ta karyawa wancen ogan nasu banana, tana roqon Allah ya sanya bawai mutuwa yayi ba, kuma kar Allah yasa wannan ma data harba a qafa shima ya mutu, sosai take cikin rudu mara misaltuwa ,bata fata ace wai ya mutun sabida bazataso ace tayi kisan kaiba har qarshen rayuwarta dukkuwa dayake ta aikatane bisa kare kanta datayi....... Rarrashinta ummu ta somayi harta koma baccin sannan ta nisa tace

"Ina roqon Allah ya cire miki wannan abin dakikeji a ranki Auta, Allah kuma ya sanya ki manta komai da kika gani" Ameen inno ta furta a hankali, tana tausayin rayuwar Manga sosai ba kadan ba.....

Kallon ta Ali Abbas keyi cikin tausayawa, wata irin azabtacciyar soyayyar ta yakeji har cikin ranshi, yaso ace sanda ta farka dinnan yana nan, yayi matuqar kewar ganin idanta a bude, yana mata wani irin so wanda baze taba faduwa ba, yana cikin shauqin santa ainun, hannunta ta soma matsowa sannan a hankali ta daura dayan hannunta saman kanta ta dafe shi tana yamutsa fuska alamun inda ta tab'a d'in yana mata ciwo ba kadan ba, kallonta kurin yakeyi ya kasa koda motsi bayaso ya wargaza mata jin dad'in ta, karya tasheta a bacci shine damuwarshi,wasu sirarran hawaye ne suka soma sauka a asaman kuncinta, zuwa yayi ya duka kusa da ita, yace cikin murya qasa qasa

"Hilwa sannu meyake miki ciwo?" hanninta ta sauke se a lokacin ta bude lumsassun idanuwanta ta diresu a kanshi tace

"Yaa Ali kainane fa yake saramun, ina baccina nasomajin tamkar ana kwad'amun sanda aka" hannunta ya riqe yace

"Barinwa huddy waya tazo ta sanya a dubamun meyene damuwarki, sannu kinji inshaa Allah ze dena" wayanshi ya zaro daga aljihu ya soma dannawa

"Baby kizo za'a duba Hilwa ta farka kanta yana ciwo sosai" a daya bangaren tace "Mashaa Allah ina kan hanyan d'akin dama" koda suka zo alluran bacci suka qara mata, sun tabbatar masa cewar zata riqa samun ciwon kai akai akai, sabidda tasha biguwa jini ya ratsa wasu sassa acikin kanta inda ba'aso yaje, amma a hankali da kanshi ze baje sabida kadanne abin....

Washe gari ma koda ta farka Ali baya nan, amma yanzu da d'an sauqi kam ta samu ciwon kan ya lafa mata sosai.... Wuraren sha biyu na rana Ali na zaune ya tasa manga agaba akan lallai setaci abinci yayinda take ta turjiya harta baiwa Innoh dake d'akin mugun takaici wanda ya sanya tabar mata dakin ma gaba daya....suna nan ya hade rai, suka jiyo sallamar su Hannatu da sauri Manga ta miqe suka rungume juna hannatu na kuka tace

"Aunty Manga munyi arziki da ba'a mana fyad'e ba, Allah ne gatanmu kuma kece gatanmu kinga dai yanda rayuwar Humaira ta zamto tamkar ba'ayi ba, yanzu sedai tarihi Lil humaira Allah ya isan ta wlhy" dagowa tayi daga rungumar juna da sukayi tace

"Ban gane ba hannatu me kike shirin sanar dani" Ali se qiqiiiftawa Hannatu ido yakeyi amma bata lura ba taci gaba

"Ai humaira tun washe garin ranar damuka dawo ta rasu, tunkan ma a cafko sauran en fashin" kuka ta saka me tsuma zuciya gashi likitoci sunyi hani da bata damuwa, sabida yanayinta kukan nan takeyi tamkar ranta ze fita tama kasa furta komai kuma taqi zama, seda tayi kukan ya isheta har muryanta ya dashe

"Da naso kar ace na kashe wannan mutumin amma yanzu koda be mutuba ina mai fatana qarisawa lahira da gudun fanfalaqi, Allahu ya wulakanta rayuwarshi ya didita tunaninsa ya mawa humaira sakayya akan wannan abin na cutarwa da suka aiwatar agareta, Allahu ya saka mata sakamako mafi muni arayuwarshi,Allah kuma ya.....se kuma ta dafe kanta dake sara mata jiri ta soma gani se gashi ta sulale wurin a sume, gabaki daya Ali ya rude yasan an hanasu tashin hankalin mangar, wannan uban kuka datasha ai se Allah, huddy ya sanar wa meke faruwa ta waya segashi tazo dabgaggawa hannatu da mamanta dasukazo duksun rude ganin halin data shiga jin mutuwar humaira, kamar ma tafisu shiga matsala akan mutuwar, wataqil kodan taga yanda aka hayayyaqe mata ne, sabida daga hannatu har saliha yarane en 16 17, ita kadai keda 22 yrs a ciknsu, tafisu sanin ciwon kanta nesa ba kusa ba" Allaurar bacci aka danna mata ta kuwa koma baccin, sun jima kan su musu sallama su bar asibitin, baccin ta takeyi se washe gari ta farka wuraren 8 na safe, zuwa wannan lokacin tuni yaa Ali ya dira asibitin, tashi zaune tayi a hankali, se kallonta yake yana nazarin ta, tasowa yayi a hankali ya tashi yaje ya zauna kusa da ita ya riqe hannunta, kwantar da kanta tayi saman kafad'anshi wanda ya daukar masa hankali gaba daya se hawaye kuma

"Yaa Ali kaji wai Humaira ta rasu, Allah ya isanta Wlhy, bamu yafe ba" se kuma ta qara rungumeshi sosai ta sanya masa wani sabon kukan, d'ago kanta yayi yana share mata hawayenta yace

"Hilwa kinsan dai humaira tana aljanna ko?" kallonshi tayi ta dawo sekace qaramar yarinya

"Enhen bama zataji dad'i ba kina mata kuka, keda ya dace kina mata adu'a tunda kika fara kukan mutuwarta banji kince Allah jiqanta ba ko kince?" girgiza masa kai tayi alamar aa yace "Yauwa to u pray for her shi kadai take buqata a wurinki yanzu ki dena kuka my Hilwa, samun lafiyanki shine fatana" kwantar da kanta tayi saman qirjinsa tana sauke Numfashi a hankali a haka Huddy tayi slama ta samesu, ko Manga seda taji wani iri da sauri ta tashi, shida kanshi Ali Abbas seda yaji wani irin nauyinta, Huddy kuwa taji ba dadi kam sosai, bata zata haka kishi yake da mugun zafi ba se yanzu, da qyar ta saisaita nustuwarta tace

"Alhamdulillah ashe en matan Ummu sun samu sauqi, shagwab'a ma kike yayan naki lallai ma" cikeda zolaya take maganar tana kokarin kawar da abinda ta gani takuma ji har cikin zuciyarta, Yanda suka saba haka yayi mata, koda Ummu kenan seya rumgume matarshi al'adar larabawa ta gama ratsashi, miqewa yayi ya rungume huddy gaba daya ya manna mata sumba a kunci sannan ya riqe fuskarta da tafikan hannayenshi yace

"Baby yadai, ya aikin?" wannan abin daya qara dashi bayan rungumarta ya tabbatar mata da cewar Ali baze taba wulakanta tataba har abada, kulawar dayake bata ko a gaban waye baze dena samu ba tunda gashi har a gaban manga ya nuna fiye da yanda ya saba

"Lafiya qalau Yaa Ali nadai gaji ne kawai" hannunta ya kamo ya zauna ya d'orata kan cinyar sa

"Na sanar miki ki huta da aikin nan haka Baby kece kin cika kafiya, ga Unborn na ma yanashan uwar wahala awurinki sena kawo miki kaykyawan ranqwashi idan kika haifomun yaro yazo ya gaji" murmushi tayi ita duk yau setaji nauyin Manga fiye da kullum, dukkuwa da yake ta saba sosai suke irin hakan agabanta, yauda ta tabbatar matarsace Manga har gashi ta ganta ajikinsa, ta tunano irin yanda taji sanda ta gansu a tare se kawai ta tsinci kanta da jin nauyin Manga dakuma ganin rashin dacewar hakan, kanta kai qarshen tunanin ta ta tsinkayi muryarshi yana fad'an

"Baby ina fatan Nonon baya miki zafi kamar yanda yake miki lokacin cikin Ameer,wlhy tausayi kike bani har wasu lokutan bana iya bacci, nidai da zaran kin haife wannan dake cikinki lafiya, London zamuje nasanya acire shi ki huta tunda still shi kadaine ke ciwon ba duka biyu ba karya sakarwa dayan in shiga uki ni Abbas" murmushi tayi ta sani ya damu na wannan cancer din nata na nono, tun farko itace bata bari a yanke nononba da tuni an wuce wurin, yanzu kam kalan wuyan datakesha gwara a yankeshi a qona wurin kawai......

"Inshaa Allah nima na yarda da hakan Abbi, so nake Allah ya saukeni lafiya se muje a yanke kawai na huta nima ina shan azaba" rungumeta yayi a yanda take zaune kan cinyoyinsa ya daura kansa saman bayanata yace

"Sannu Babyna khairi Inshaa Allah" d'an wayancewa tayi ta miqe daga saman kafarshi tace da Manga datayi sororo tana kallonsu

"Mangan Innoh how body?" murmushi Manga tayi

"Aunty Huddy naji sauki sosai yaudai matsala d'ayane mugun yunwa nakeji" dariya tayi tace

"Kice yauba shan masifa wurin yayan naki, da kanki kike neman abinci lallai yarinya kinji yunwa, bari na zubo miki aiga kayan abinci nan iri da iri ko?" da kanta ta zuba mata abinci taci sosai, sannan tasha tea, barin dakin tayi yayinda ta turo wata likita akazo za'a qara yiwa Manga allura ta koma bacci, kukan gaske ta saka akan batasan alluran kuma ita lallai gun Ummu zataje sabida ta gama gajiya da zaman wannan asibitin, da qyar da lallami aka mata alluran akan alqawarin tana farkowa se sallama.....


*Bayan sati Biyu*

seda manga ta share satuka biyu a asibiti sannan aka sallameta ta koma gidan,kai tsaye part din ummu aka kaita abisa umarnin ummun, raunin ya bushe harma an kwance daurin, se tabo daya bar mata shima bame yawa ba, Ali ya kasa zaune ya kasa tsaye akan lallai abashi Manga amma ko kallo be ishi ummu ba dole ya samawa kanshi lafiya.....

Tunda aka sallamo Manga asibiti sam bata sakewa Ali Abbas, ita kam ta dauki anniyar rama wulakancin daya mata aganinta wannan san mai ne amata,ya bata wahala na shekru hudu shikuwa dan gata za'amai horo na wata uku kacal lallai ma.....

Ammin huddy ce zaune asaman wata matacciyar tabarma tana zayyanewa bokanta yanda takeso ayi da Manga

"Boka nifa so nakeyi duk yanda za'ayi a murgunawa wannan yarinyar a sanya mata qiyayyar Ali ta sosai, akuma aika aljanu baqaqe su riqa sanyata rashin kunya tana zagin har sarkin uban Ali, kaga dole a raba auren kota qarfin tuwo" wata shegiyar dariya bokan ya saka yace

"Zan jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya ita kanta Mahaifiyarshi zan sanya kwata kwata taji ta tsani Manga,kuma tunda en fashi sun sacesu zanyi kkkarin cura musu ra'ayin an rigada anyi amfani da ita a zukatansu.... Dariya ta kwashe da ita itama tace

"Shifa Alin bazamu saka masa qiyayyar taba?" kallonta yayi yace

"Qiyayyarta bazata darsu a zuciyarsaba se an samu had'uwar maniyyin Ali da hudaisa na da nawa sun had'u, ma'ana zan kwanta da ita kafin awa ashirin da hudu ta tabbatar sun sadu da ita, se na aika aljani ya debo duka ukun da suka gauraya a mahaifarta se a hada aje a zuba babban teku, yanda yawan ruwan ze wanke wa ennan maniyyan haka soyayyar ta zata wanke tas a zuciyarsa, kuma yanda yawan ruwan ya rinjayin maniyin haka ze mamaye qoyayyarta a zuciyarsa idan zata iya tazo ko yau ne" nisawa tayi tace

"Ai boka hudaisanne da kafiya taqu ta saka mun hannu wlhy" zare ido yayi yace

"Kanta tayiwa, ita ma ta dagewa adu'a da azkhar dasena juyo miki da hankalinta, amma ba komai zanyi iya qoqarina...godiya ta masa bayan ta jibga mai kudade sannan ta wuce.....

Mom Nu'aiym

*Bazan fasa neman adu'arku ba er uwata hafsat Elham bata da lafiya, gashi bana samun wayanta, babban abin tashin hankalin ma tana saudia banida wani dazan wa waya ya sanar mun halin da take ciki, Allahu ya bata lafiya*
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS👑*

*Sadaukarwa gareki qawa ta gari Fulany saddy*

                                       12

Sallah isha ta idar tana zaune tajiyo sallamar Ali Abbas har cikin d'akin, tun da taga yanda wani nanuqewa Huddy agabanta setake jin mugun takaicinsa ya qara kame zuciyarta, bata juya ba aciki kamar bata san magana ta ansa shi, qarasawa yayi har cikin d'akin yau ya samu dama Fulani taje turakar me martaba, kusa da ita ya zauna ya sanya hannu ya d'ago hab'arta sannan ya soma duba raunin dake kanta, ko kad'an batayi yunkurin hanashi ba kallonshi kawai takeyi ido cikin ido tana mamakin qarfin hali da rashin imani irin nashi, kullum kwanan duniya idan ta tuna lokacinta data bata tana tunanin akan rashin wanda kullum seta ganshi sedai idan baya gari ko tayi busy da yawa skul setaji ta tsaneshi tsana mai tarin yawa kuwa, bata shiryawa zuwan tsakin daya sub'uce mata tajiyo sautin zuwan shi sauke k'wayar idanta tayi a qasa a karo na farko tun bayan data kusa masa manya manya idanuwanta, mamakin wanda takewa tsaki ko dalilin daya sanya take tsaki yake, habarta ya qara d'agowa tana kallon shi ya d'age mata girarshi d'aya ta kula wannan d'abi arsace kasancewar ko Ko Gadanganta haka yakeyi bata fahimci hakan a wurin AlI Abbas ba se yau

"Meyake damunki yanzu akwai inda yake miki ciwo ne Hilwa?" tsuke bakinta tayi batai magana ba ta kawar da kanta gefe d'aya" mamakinta yake tsawon satinta uku kenan da dawowa baya samun magana da ita se idan fulani taje turaka amma duk yanda yaso ta masa magana bata yarda sam, sedai ta  bishi da ido da wani kallonta me rikitar dashi, sam batada tsoro ko kunya kanta tsaye take saka idanta anashi cikin nuna tsananin jin takaici da tsanarsa" kawai da nashi idan yayi daga dubanta ya tabbatar ita bazata janye nata ba sannan yace

"Dake nake magana fa Hilwa" miqewa tayi ta bashi wuri batare data amsa shiba, hannunta ya janyo bayan ya moqe ya bata kyakyawar rungumar data gigitar dashi dukda acikin hijabin ta na salla take, bata yi yunkurin kwatar kanta ba tadai masa sororo tayi tsaye tamkar wat statue tana kallon bayan shi kasancewar fuskarsa na bayanta, a hankali ya rad'a mata a kunne

"Hilwa dan Allah kimun Managa, bakiji yanda zuciyata ke d'aci ba akan rashin jin muryanki kina mun magana, ki taimakeni ki sassauta mun wannan hukuncin yamun tsauri,ga mamakinshi harya qaraci surutun sa batace masa ci kanka ba, sakinta yayi zuciyarsa namasa zafi yaje ya zauna saman kujera yace a kasale

"Hilwa ki zauna a kusa dani plss"  Hanyar waje ta nufa batare data koda kalleshi bane, bata dawowa dakin ba harya qaraci xamanshi yabar wurin. ....

  Yaudai Huddy ta shirya zuwa gun fulany domin ta dawo Manga b'angarenta kafin tariyarta zuwa yanzu cikinta ya soma mata girma ga nononta dake dauke da cutar sanqarar mama harya soma wasu ruwa masu warin gaske kullum take dreasing abinta da knat, ciwon dayake mata ya soma wuce tunaninta yana neman zautar da ita, yasoma kaita fagen da bata iya koda aiki idan taje office har dan kansu sun bata hutu tare da bata shawarar zuwa wajen datace kafin ta haihu domin a ceto rayuwar ta..... Da sallama ta dira part din akai mata iso kai tsaye wurin fulani, bayan ta gama kwasar gaisuwa ta soma magana

"Ummu dama nazone ina roqon Alfarma abani manga mutafi da ita wurina, sosai banida lafiya har wurin aikima sun dakatar da zuwana akan sena samu sauqi, zuwa yanzi ciwon jikina harya soma wari yana fitar da wasu bakuna masu bani tsoro ummu, bansaniba ko zan rayu amma ina cike da tsoron bari harna haihu duba da cewar har yanzu akwai sauran wata biyu haihuwar, kuma idan na haihu dole na jira babyn yayi qwari kafin ayi tafiyar yin aikin, wannan azabar danakeji banaji zan iya daurewa kaina ita har zuwa lokacin, da zan samu Manga tazo tana kamamun wasu ayyukan" jinjina kanta tayi sabida tana ganin wannan ne jaronta na farko da huddy tayi mata irin wannan bayanin me tsawo gashi wani uban tausayinta ya kama ta

"Muje daga ciki Hudaisa" ba musu ta miqe suka shiga dakinta a tare ta kalleta tace

"Huddyn ummu budemun ciwon naki in gani, banasan kice kunya inaso inga yanda ya dawo sabida insan abinyi" Ba musu ta cire rigarta har rigan mamanta, koda ta janye dressing datayiwa wurin Ummu kasa daurewa tayi ta saka kuka, gani take duk laifintane da ace tana janta ajiki da tuni tasan cewar ciwon ya mata nisa toshi kuwa Ali yana me basu shirya zuwa aikin ba har ciwo yakai haka? lallai sunyi babban sake akan lamarin, zaunar da ita tayi ta mayarda kayanta, kai tsaye ta sanarwa me martaba halin da ake ciki ta waya, shi kuwa dama baya kula Ali yama hanashi zuwar masa se bayan 1 yr, yace agayawa Ali lallai ya tabbatar nanda sati daya sun bar kasar zuwa india anfi samun qwararrun likitoci acan din, hakan kuwa akayi......

Visa din Manga ne ya sanya sukayi 2 weeks basu tafiba sabida ita bata tab'a fita waje ba, kuma huddy ta dage se tare da ita zata tafi.....

*India*

     Yamma likis suka isa birnin india, ko a jirgi Ali Abbas beyi yunqurin yiwa Manga magana ba sabida a yanda ya kula ma batasan tafiyar sam, koda suka isa masauki shida huddy ya kamawa d'aki d'aya yayin da Manga kuwa ya kama mata d'aki daban...Kasancewar sun gaji ya sanya kowa nacin abinci ya nemi wurin kwanciya, Manga kuka ta zauna tana dirza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login