Showing 30001 words to 33000 words out of 60927 words

Chapter 11 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt

alokaci d'aya jini ya soma sakkowa daka cikin bakinta kuma ya zagaye mata ilahirin rabin idanta na hagu yana huci yace

"Bazan qara baki wata damar dazak8 rainawa tunanina hankali ba, jaka kawai me zina da auren wani akanta, jahila me bakar zuciya Allah ya isanni wlhy akanki,kin cutar da masarautar mu kin tozartar da zuri'armu kin kawo mana b'ara gurbi acikin mu, na tabbatar a India kikayi cikinnan,Allah yayi ikonshi ki haifo ba'indiye sak,kinga sena miqaki dashi baki daya awurin uban shi mayya kawai" kuka ta durqushe wurin tanayi kurun batare datayi yunqurin kare kanta ba a karo na barkatai......

*Bayan wata hud'u*

Banda duka zagi da cin zarafi babu abinda yake shiga tsakanin Manga da Ali dukta birkice yayinda cikinta ya zamto wani uban qato na ban mamaki ma dan bazaka yarda cewar wai watanni shida ne da cikin ba, yauma kamar kullum tana zaune ta rafka uban tagumi se kuka takeyi yana zabga mata zagi tamkar ba Ali Abbas me nutsuwa da hangen nesa ba

"Allah Manga duk sanda na kalleki naga wannan cikin se in riqa jin tamkar in shaqeki sekin sheqa lahira, sam bakida mutunci kuma kin citar dani, wato duk tsawon shekarun nan cutane kike se yanzu ne Allah tona asirinki jakar banza kuma jahila, kina haihuwa zan karbi dan dan Allah ki tallafi rayuwarshi dakika gurgunta ke kuma seki koma ki taya dattijon ki kwarewa masu gate, asararriya kawai" Ita wasu lokutan ma mamaki yake bata har dake sanyawa ta manta ilahirin duniyar datake ciki, kamar kuma an tsikareshi ya miqe yabar gidan, sabida ranshiyana b'ace ya sanya bema tsaya kallon qofar d'akin huddy ba ya wuce d'akin shi muryan daya jiyo ne ana waya daga ban d'akin ya katse masa tunaninshi

"Haba Ammy yaya zaki kunno wutar da Allah ne kadai ze iya kasheta, yanzu dani aka yiwa hakan zakiji dadi, mata da mijinta ki tashi hankulansu, ina namiji ze yadda da cikin daba nashi ba, kuma wannan aljanin da kika tura ki sani fa wlhy shima se Allah ya tambayeshi haqqin er mutane lahira,kuma wlhy bazan rufa asiri ba sena gayawa ummun Abbas kece kika turawa manga Aljani babu wani cikin datake dashi, tun lokacin da Ali yaji Manga nada ciki baya cikin nutsuwa yarinya duktabi ta fige ta lalace akan abinda bataji ba bata gani ba, dukda an haneta gayawa kowa amma wlhy sabida ta yarda dani seda ta sanar dani, amma ke Ammi kirana ma kike zancen waiko an saketa, Lallai wannan san kan naki ya tayar mun da hankali, bantaba ganin mutum me masifar sankai irin naki ba" shiru yajiyo alamun uwar ce ke zazzagawa er masifa ya sanya ya juya yabar dakin zuwa bangaren Ummu da sauri.....

Mom N'aiym ce

Kumun uzuri inata hidima shisa.
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS👑*

*Billy Galadanchi*

*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*


14

Wayanshi ne yayi qara ya zaro ta jin yanayin sautin dake tashi ya tabbatar wa kanshi cewar me martaba ne, Dagawa yayi sannan yayi sallama a hankali

"Kazo ina san ganin ka yanzu a fada" ya kashe kawai dama haka me martaba yakeyi idan ya gama fad'ar abinda ze fada seya kashe kawai, dafe kanshi yayi ya juya akalar shi zuwa fada yana mejin haushin wannan kiran ainun......

Huddy na kuka tace da mamanta "Ammy amma dai aikinsan cewar ba'a barin aikin Allah ayi na bawansa, ni nasan niyyan Alkhairi nake da sabida haka tsinuwarki bazata kamani da yardar Allah" tana gama fadar hakan ta kashe wayarta ma gabaki daya ta dauki hanyar b'angaren ummu zuciyarta na mata wani irin rad'ad'i shirkafa ai dole ta nemi zarewa ma gaba d'aya wlhy...

Tana zuwa akai mata iso, taje bayan sun gaisa da ummu se kuma wasu sababbin hawaye tace murya na rawa

"Ummu dan Allah karkiwa magana ta mummunar fassara wlhy banida masaniyar abinda mahaifiyata ke aikata se sati biyu dasu ka wuce, kuma nayi mata nasiha da wa'azin abinda take ba kyau amma batajiba wannan ya sanya nace ni agaskiaya zanzo da kaina na sanar dake halin da ake ciki, zancen cikin nan na Manga Ammy nane taje ta sanya akayi asirin da aka turo mata aljanin dake sanya ake ganin cikin koda a awon asibiti ne kuma yaketa hura cikin yake girma tamkar cikin gaske, wlhy ummu ba yanda banyi da itaba amma sam taqi ta gane taje ta sanya a karya asirin tunda ni nasani babu zaman lafiya tsakaninta da yaa Ali tunda gani yake shiba cikinsa bane ba, yanzun ma da ita na gama waya ta kasa ganewa ta tubarwa Allah ta raba er mutane da wannan takaicin datake ciki, yarinya duk tabi ta gama ramewa ta stuke ta lalace akan abinda bataji ba bata gani ba sam shine kurun nace nizan sanar dake, anemo malamai suyita adu'a ko Allah zesanya asirin ya karye kuma a tayani yiwa Abbin Ameer haquri wlhy ba laifi na bane banmasan da wannan abinba se daga baya" Nisawa Ummu tayi acikin zuciyarta tana godewa Allah daya karbi adu'arta gaskia ta bayyana

"Ki kwantar da hankalinki huddy nina sani wlhy ba hannunki aviki koda baki fada ba, sanida na yaba da nutsuwar da addininki tuni, so ban taba zarginki ba,kuma Har a wurin Allah bakida laifi danke akayi amma kika nunawa duniya kinfison waninki akan kanki lallai kin cika er halak kuma darajarki da qimarki ayau tafi ta duk wata mace da yaro ze auro agidannan dama wacce ke ciki,k8nyi abinda dubunki bazasu yiba Allah ya miki albarka ya sanyaki a aljannar sa mad'aukakiya, ni zan sanar da yaro dame martaba se asan matakin daza'a d'auka akai inshaa Allah, mahaifiyarki kuwa kina mata adu'a plss karki wani en damu zata gane gaskia ne inshaa Allah ta tuba kedai kiyi mata biyayya indai bata sab'a abubuwan Allah daya gindaya wa bayin saba" Yaudai ta kasa hakuri kwanciya tayi saman jikin ummu tayi ta kuka tana rarrashinta har Bacci ya kwasheta a wurin.....

Sosai me martaba ya tsorata da al'amarin mutane amma seya sanar wa Ali Abbas da Ummu kar wanda yayi wa Manga maganar ze kawo malamin daze yaqi abubuwan a hankali.

Yaudai banda sauri babu abinda Ali Abbas keyi so yake yaje yaga Manga koda kallontane ya dingayi, da sallamar shi ya shiga cikin d'akin nata kasancewar ya duba sosai parlor batanan, halin daya saba taddata aciki yauma aciki ya taddata, tana zaune saman sallaya ta rafka tagumi,jin sallamarsa besa dakoda motsa ba se bakinta datake motsawa a hankali wanda ya tabbatar masa cewar amsa sallamar takeyi, abakin gado ya zauna yana jiranta yau seya tsinci kansa da mugun tausayi dajin kunyarta fiyeda kullum, se yanzu ya gano tsananin damuwar datake ciki,se yanzu yake hango gaskiyar ta,yanayin ta kawai ya isa ya sanarwa me lura da hankali cewar lallai she's innocent, tajima a zauna kanta taso, nesa dashi ta zauna da wannan qaton cikin daze kai girman cikin en shida, gashi ajikinta shi kad'ai yake girma komai nata yana nan yanda yake lafiya lau kawar kanta tayi gefe d'aya tunda ya gama zazzaga mata wannan uban zagin takejin wani matsanancin tsanarsa na qara d'arsuwa a ranta da qyar ta furta

"Ina wuni" tausayinta me tsananin gaske ya mugun kamashi muryarshi na rawa yace

"Lapia lau, na ganki wani kala yau, menene yake damunki?" kallon mamaki ta mishi dama kuma tanada damuwar setace dashi

"Kasan ance idan yaro ya mutu acikkn uwa mahaifa rub'ewa takeyi uwar ma ta mutu idan ba'a gane da sauri ba, naji ance ciki yana motsi na bantab'a jin motsin dan Allah ka kaini gun Aunty huddy ta dubani" Wani uban tausayinta yaji ya kamashi daya sanya ba shiri yaje gareta ya rungume kasa daurewa yayi yau kad'ai tausayinta ya sanya ya soma yi mata kuka tamkar wani jinjiri

"Bansa dayaya zan kalleki ba Manga bansan mezan ce dake ba, bansan ta ina zan fara ba, a bakina babu wasu ragowar kalmomi masu amfani dazan fad'a miki, tuni na b'atanci sun gama rinjayar su an sun kore su gaba d'aya sam banida hankali ni wawa ne jaki ne ni, kuma butulu wanda besan halacci ba, lallai na cutar dake matuqa kuma nasan dab guntun bayanin dake bakina be isa ya gamsar dake abinda zan aika miki ba, dan Allah badan mugun hali naba Manga ki gafarceni, tun tasowarki da bakin cikina kiike kwana dashi kike tashi, sanina da wanzuwana a rayuwarki be haifar miki komai ba se baqin ciki, Zuwana arayuwarki na kawar da hafsatu Manga yarinya me ban dariya da walwala da fara'a ga barkwanci mara qarewa, zuwana a rayuwarki na sauya ki daga mesan zama cikin mutane zuwa wacce batasan kowa a kusa dake, kasantuwa ta acikin rayuwarki ya sauya kika tashi daga me yawan magana zuwa kurma,bebiya kuma wacce batasan koda ganin mutane, Bayyanata arayuwarki ya sanya kika zama makauniya wacce bata gani sam, yanzu kuma gashi zamtowata jgo arayuwarki ya sanya kika zama abokiyar gabar wasu har suke bink8 da sharri,dan Allah kimun aikin gafara Manga" ita sam bata fahimce shiba gani take tamkar bayan ya zagi iyayenta ne yake bata hakuri bayan ya bar gidan yaga rashin dacewar hakan, besan da tanada encin kanta data shaqeshi ya sheqa lahira ba a yanda dai takejin mugun takaicinsa matuqa......


Koda malamai susu uku sukazo gidan mamaki manga tayi, cikin ikon Allah sega aljanin yayi bayanin komai gameda sharrin da aka aikoshi dashi, kuma yana bacewa cikin ma ya zama ba komai ajikinta, lallai Manga ta shiga tsoron daya sanyata firgici, bata tab'a zaton hakan ba, gashi anbarta a duhu da qyar aka samu nutsuwarta cokin hikima Ummu ta mata bayanin komai, kuka ta saka seda tabi ummu wanda sam Ali beso hakan ba ko kadan, awurin ummun taci gaba da zama har tsawon wata d'aya a wannan lokacin ne kuma aka turasu bautar qasa wanda ita kuma a kaduna aka kaita, dole aka soma shirin tafiya kd, har wannan lokacin kuwa bata nunawa kowa komai ba, abu d'aya ne dai ta qudurce a ranta ita da sokoto har abada inshaa Allah, kamar yanda tabar sokoto haka tabar Ali Abbas da rayuwarshi har abada......

Kwananta biyu a kaduna suka soma shirin shiga camp, tunda tazo Ali Abbas ke kiranta amma sam bata d'aga wayarshi, yau tana shiga b'angaren su Ammy ta gaidasu Ammyn tace da ita tazo da sauri taje bayan layinsu ta karbo mata saqo gun haj Azumi, bazatai musu ba haka ta juya bayan ta shaida mata karta tsaya gunsu Innoh zata sanar dasu tunda ba nisa da layin nasu, haka ta dauki hanya ita kadai gashi after 8 amma dukda haka bata kawo komai a ranta ba game da aiken.......tabar harabar gida da nisa ta kula wasu samari na binta anaya ga kuma wata mota dake tafiyar dirar hawaniya cikin yanga tamkar itama motar su take bi, cikin sassarfa ta qara mai amma ina ata nayanta kurun taji an rufe mata hanci da wani qyalle...........farkawa kurun tayi ta ganta acikin wani parlor me girman gaske kwance saman kujera, zare ido ta somayi a tsorace tana tariyo abinda ya faru, a bayanta tajiyo ana waya

"Mun samota hajiya amma dai gaskia kudin yayi kadan, Idan kina bamu dama semu miqawa su b'auna ita, kema zaki samu kud'i aiba kasheta zasuyi ba, zadai su ajiyeta ne ta dinga musu amai da kashin kudi mu kuma zasu bamu miliyan dari, kinga mu mudauki hamsin kema haka can musu kisan dabakeso ayi bakiyi ba kenan" dariya taji ya sheqe da ita meban tsoro sannan yace

"Se hajjaju tamu sekinji ni" tana zaune se zare ido takeyi taji yana wayar da wasu

"Ta aminta kasan hajiya ai ba wasa da naira, kuzo kawai irinta kukeso, e wacce kace dai" daganan ya dire call din ya zago ta gabanta ya tsuguna yana mana wani kallo, kan yace wani abu wasu sun shigo parlor din, kallo shi suka tsayayi kan wani yace

"Ka tabbatar budurwace batasan namiji ba?" kwashewa yayi da dariya yace

"Idan kunje ai zaku gani na rantse ma batasan Namiji ba karka damu kawai ayi sha'ani" dariya sukayi suka tafa daganan suka dauketa suka ajiye musu tsabar kud'i a jaka, giri riri aka jata zuwa waje, se kuka takeyi tana ambaton Allah......

Tunda akaji manga ta bata a zaune aka kwana bataje inda aka aiketa ba bakuma ta dawo gida ba, Ammy duktafi kowa rud'ewa sabida ba haka taso ba sam, ita yaran ma data tura sam sunce basu had'u da Mangar ba to yaya akayi hakan ta faru?" Tasani ita za'a tuhuma me take dashi na fad? Haka zata jajirce ta hakura dole ai tace ba ita bace tunda kam ba itan bace ba......

Manga naji tana gani aka yi tafiya me nisan gaske da ita bayan an rufe mata ido, mamaki ne ya damqeta ganin am mata saki tatas, an sanya mata jajayen kaya, abinda yafi daure kanta shine duk wani abu na addini mantashi tunda aka kawota cikin wannan gidan, gashi komai seda aka cire mata, ita gabaki daya ma ta dena kukan ta kangare kafff ta gama yadda cewar mutuwa zatayi, satinta d'aya ana tsafe tsafe akanta kandaga bisani a sanyata awani qaton rami batasan ko ina bane, sedai taga tana aman kud'i idan ma kashi zatayi dazaran ta gama setaga ya dawo tsabar kudi sababbi fill, kuma sunkai su biyar a wurin duk mata, sannan kuma sam ba mewa wani magana, gashi abinci se bayan kwana bakwai ake kawo musu kuma sannan ruwan so daya jal a rana......acikin sati biyu Manga ta gama lalacewa, kudin yana fitane tamkar da tsokar jikinta da jinin jikonta yake fita.....


Ali Abbas kuwa abubuwa sun tab'arb'are masa gaba d'aya ya gama haukacewa, rashin Manga ya zamto tamkar wani babban rashi na mutuwa atare dashi, gashi me martaba ya hana kowa tuhumar Ammy sabida mutunci na huddy sedai amata adu'a kawai......


*Lokacin zubarwa Manga da k'wallah yayi abin tausayi ce manga, yanzu story ya fara yanzu abubuwa zasu sauya salo, yanzu muka fara race din*

Mom Nu'aiym....
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
$
*👑ALI ABBAS👑*

*Billy Galadanchi*

*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*

                                        15
Ko shakka banayi aakwai saka hannunn Ammy a wannan abin da aka aikatawa Manga, yaya zakace nayi shiru? Kana sane fa da irin abubuwan da suke gudana agidannan,kakuma sani ina haquri, karfa ka manta inada gata nima, nima bawai wulaqantacciya bace,ba kuma er bayi bace a masarautar mu ka daukoni, a gidan sarkin agadez, kafi kowa sanin inada gata sabida ni dinnan haifaffiyar 'yace a wurin sarkin agadez, bazan lamunci cin kashi ba daga yanzu, 'yar tawa d'aya tilo zan qura ido a mun izgili akanta, na kwashe shekaru ina maka biyayya, na dade sosai ina maka kawaici, na rayu dakai acikin qunci da wulakancin iyayen gidanka, yaya Za'ayi Ibrahim kana dan masu gari guda d'aya a qasar Niger ka dawo nan sabida kawai baka sona da qaunata, daka gujewa gidan iyayenka da dangi duk akan qiyayyar dakakemun ka sauya sunan mahaifine har yanzu ibrahim? Zan shirya wlhy zanje yamai (Niami) da kaina na sanar wa me martaba yanda ka wulaqanta rayuwarmu dukda kasantuwarmu masu tsananin gata a duniya, kawai ka kawo mu nan an sace mun 'yata wlhy yanzu kam bazan yarda ba" nisawa Baban Manga yayi zuwa yanzu ya gano ya gama qure hakurin Innoh, dukda yasan Halima sam batada rashin kunya amma beji dadin wannan abin datake shirin yi ba na zuwa Yamai, sannan kuma ya sani tafishi gaskia dukda yake ya tauye mata haqqi ya sani yaune rana ta farko data tab'a daga muryarta sama da tasa, sanin kansa ne kuma cewa duk yanda bayasan halima yayi qarya yace bata burgeshi ta bangaren kawar dakai da haqurin ta

"Kibi komai a sannu Halima" kallonshi tayi bayan yayi furucin a sanyaye tace

"Idan kullum ka fada nayi shiru wlhy banda yau, bazan bi komai a sannu sabida badakai nayi naqudar Manga ba, haka kawai wlhy hakurin sati zanyi idan ba wani labari Yamai zanje, kai wlhy koma an samota wannan karan sena nunawa duniya Manga yarinyace me gata ta uwa ta uba, ina dalilin wannam cin kashin" yaudai Baban Manga ya kula sam Innoh bazata saurareshi ba wannan ya sanya ya juya kurun ya bar mata gidan zuciyar sa tana masa matuqar zafi ga rashin Manga da kuma jarabawowin data shiga yana ganin tamkar sabida abinda ya aikatawa iyayensa ne wanda yake ganin ada tamkar shine maganin su baki d'aya, amma yanzu ya hango tsananin wawtar daya tafka arayuwa, da ace be bijirewa iyayensa ba da ace be gudu daga gida ba, toda yanzu manga tana can ita ma ta auri dan gidan sarauta me nagarta wanda ze kula da ita, a ainahin qasar ta ta haihuwa....

   Ali Abbas kam ganin an share fiye da sati hud'u babu Manga ba labarinta gaba d'aya seya soma ciwo, wasa wasa fa haryakai kwance, ankuma kasa gane menene ciwon nashi, likitoci sesuce kurun damuwa ce ta masa yawa, daga qarshe dai aka gama gano cewar hawan jini ya kamashi sosai, kwance yake amma yakasa dena damuwa akan Manga,dukkuwa dayake damuwa ta mugun masa yawa arayuwarsa, besan ta ina ze faraba ta b'angaren neman Manga likitoci sunyi umarni akan ya dena damuwa amma ta yaya? Ina ze soma mantawa da hafsatun sa? Mangarsa  kuma masoyiyarsa gaba d'aya, besan kalan azabar da Manga tajiba sanda ya guje mata se yanzu, ada dakaje da ita yola koda besan inda takeba yadai tabbatar tana lafiya lau be damu da yawa haka ba, yanzu kuwa daya tabbatar wa kanshi babu Manga kazalika babu labarin Manga se duk inda hankali nashi yake ya tashi tsaye qiqam, baida nutsuwa kullum tunaninshi an kasheta wannan tunanin yafi komai tayar da hankalin gadanga a b'angaren rashin Manga, shisa kullum hawan jinin amaimakon ya sauka qara hawa yake koda an sallamo shi daga asibiti kwana biyu ko uku an koma a rikice kuma, abubuwan sun masifar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login