Showing 15001 words to 18000 words out of 60927 words
Chapter 6 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt
tsoron bani hannu musabu ladar musabaha, yayinda wasun su gabaki d'aya sun kasa miqo min hannun, ganin haka ya sanya me marta ya kira bayan na bar wurin yake mun fad'a akan bayi cewar nawuce na baiwa bayi hannuna mu gaisa sufa bayi nane, mamaki ya kamani sanida banga wani banbanci tsakanina dasu ba da har zan saki ladar dake cikin yin musabaha da musulmi dan uwana ba,amma dukda haka sena bashi hakuri akan zan kiyahe.
Ba'afi sati dayin wannan ba se kuma nazo zan shiga wurin dawaki na tarar wata yayata dabatayi aureba tana zagin wani bawa dake kulada sha'anin shuke shuken dake gidan tamkar zata cinyeshi, nayi mamakin ganin yanda yakeda qoqarin aiki amma kuskure daya an kasa yi masa uzuri, tausayinsa me tsanani ya shige ni,da wannan na sanyawa raina sanjin yaya sukeji idan aka ci zarafin su? Mesa ba'a musu adalci sumafa mutanene? Yaya rayuwarsu ke musu idan sukayi qoqari amma ba'a gani ba?...." nayi tunani iya tunani daga qarshe na yanke shawarar zuwa nima wani gidan nayi basaja nayi aiki ko wane irine inji yaya yake.......dana sanarwa abokina zuhair seya nuna rashin dacewar hakan amma inada wani hali daya na kafiya da kuma bana sauya zance idan nayi wannan ya sanya na kafe, muna nan haka mahaifina ya turani wannan aikin na Kd senaga na samu opportunity nayin hakan a garin daba nawa ba,da kuma naje America siyo wasu kaya kurin senayi sha'awar yin mask, na sanar musu a duba amun ta daidai skin color dina batare da bata lokaci ba kuwa akamun fuskar, koda na dawo na nunawa zuhair seya b'ata fuska akan karnayi bayaso, ni kuwa na kafe ban shiga tsoro ba seda naga neman aikin ma ashe baze yiyu ba, sabida wuya yakeyi aikin na qarfi ma wuya yakeyi duk inda naje babu......Harna watsar kuma seme martaba ya had'ani da mahaifin su huddy dama kuma tun ina qarami na sanshi aminin mahaifinane, bayan na gama zagayena ban samu aiki ba, wani yammaci muna tare da Daddyn huddy nake sanar masa,jiya na wani nazo nan neman aiki amma ban sanshiba ya sanar dani malamin addini ne amma nace dashi ni baqo ne bansan kowa ba, gobe da yamma nace yazo ya sameka ko ze samu,bansan ma sunan saba, yayi murna yace ze jarraba iliminshi idan yazo, dana tashi gobe sena masa wayan cewa bazan fito aiki ba, sena shirya kamar yanda kikaga inayi nazo wurin shi azuwan nine wancen, ya bincikeni na sanar masan qauyenmu soba da sauransu yace wurin kwana fa nace masa banida matsalar wannan, daga sannan nake masa zagaye duk sanda zan koma sakkwato sena baiwa wani bawa nawa danazo dashi nan aikin kula da flowers na gidanku......Bazan miki qaryaba Manga ban taba sanki ba, amma kwatsam se mahaifinki ya zomun da zancen kuma take a wurin ya sanya namai alqawarin aurekin ko bayan ranshi, babu yanda za'ayi na tsallake sharad'in alqawarin dana d'auka tsakanina da Allah, shine fa naje na samu mahaifina da zancenki amma tsakaninshi da Allah yace bazanmai haka nan ba, dole na haqura babu na biyunshi agarin nan dazan saka yamai magana, naje gun ummu amma kinsani bata saka komai nawa agaba, haka nayita yawo na rasa ya zanyi, hanyoyi kala kala nabi akan kaucewa aurenki amma na kasa, a haka zuhair yace na gudu kawai amma girman alqawari ya sanya nakasa daukar wannan matakin, wlhy manga babu yanda zanyi ne ya sanya na tsaya aka daura aurena dake da mutanen danake iqirarin dangi nane alhali kuma ko sanin su banyiba......bayan an daura aure na qara komawa mahaifina amma fir yaqi yadda dukda ban sanar masa an rigada an daura ba, a haka badan inasan huddy ba ya tilastani aurenta bazan iya yi masa musuba dole na aureta wanda halinta na gari da yawan girmamani ya sanyani na sota, abu dayane matsala da huddy shine rashin san talaka da rashin girmama shi komai yawan shekarunshi,da kaina nayi qoqari na magance wannan matsalar wanda kema shaidace alhamdulillah ta sauya..
Manga bayan da kikaga na tafi ban dawo ba mahaifinane ya tilasta akan lallai indawo kusa da gida sabida shi mahaifinshi be rasu ba da ranshi kinsan me martaba takawa ai, shine yace sena dawo sokoto da zana na baro kaduna sabida ban tashi nan ba bansan komai gameda mulki waye waye, dole akamun na dawo sokoto,manga bansan yanda zanyi dake ba yasa ban sake waiwayarki ba, amma senayi yunqurin ganin kin dawo kusa dani ina kula dake sosai,yanzu kuma banida abar so kamarki kuma zuciyata ta kasa daurewa rashinki da kuma ganinki cikin damuwa danake kullum, ki tallafawa rayuwata ki yafemun abinda na miki, ki agazamun mu nunawa duniya mun aminta da juna mata da mijine mu qaddara ce sanya mukai wa juna nisa, kuma a shirye nake dana nunawa duniya ke matatace kuma ina sanki" kallonshi takeyi ba qaqqautawa tunda ya soma wannan maganar, ita gani take komai tamkar a mafarki, miqewa tayi da zummar barin dakin ya rungumota gaba d'aya yana ban baki,tureshi tai da qarfi tasoma masifa kukan ma ya gagareta
"Bance qarya kake ba, ban kuma ce bakai bane Aliyu Gadanga amma dankaine na gane sai me?? Bakada imani wlhy kuma nayi dana sanin saninka arayuwa, nayi dana sanin san danake maka, nayi dana sanin aurenka arayuwa, nayi danasani zuwana duniya gaba d'aya, abu d'aya zan sanar maka kuma wlhy summa tallahi karka saka a ranka wasa nake, ni Hafsatu Manga na gama aurenka daga yau, wannan fuskar ta zalinci dacin amana daka sako ta karya, zan dauketa ta karya kamar yanda zan mayarda soyayyar ka ta qaryar gaske azuciyata, ni ba wannan Aliyu gadangan na aura ba, Aliyun dana sani shine me fadar Allah yace Annabi yace yake kuma aiki da cewar su, ban auri wannan fuskar takaba, sabida bazan taba zama da kaiba, inaso kayiwa kanka adalci karka daga wannan maganar daganan sabida wlhy bazan saurara maka ba, zanje kaduna dana kallama exams kuma zanje court araba aurena dakai kai tsaye malam,mugu kawai azzalumi macuci" matsawa yayi ya riqe mata hannu, tsabar mamaki ma takasa k'wace hannunta
"Haba Hilwa ki tausayamun mana wlhy zan iya rasa raina idan baki"
"Kai kasan tausayi kuwa Yaa Ali!!! Kasan yanda nasha wuyar rashinka a kusa dani? Kasan azabar dana d'and'an akan rashin ka? Bari kaji wlhy wa ennan hujjojin daka kawomun wai kake iqirarin sune dalilinka na takurani ka cutar dani ka tauyemun haqqina basu gamsar dani ba, sam basukai matsayin dazan karbe su matsayin uzuriba,kaidai kayi amfani da rashin karfin mahaifina ka wulaqantar dani, daka barni da igiyar aure aida sakina kayi ka tafiyanka, kana cewa Aunty huddy batasan talaka aita fika wlhy kaine babban mugun dabesan haqqin dan adam ba, kuma ka rubuta ka ajiye an raba aurena dakai an gama, gwarama kaja bakinka azuwan bakasan komai ba innuna nina gaji inba haka ba tonuwar asirinka ka janyo, karkayi duba da irin qarfin san danakewa gadanga ka dauka wai zan sassauta maka, gadanga naso ba Ali Abbas ba kuma bazan taba san Ali Abbas ba, dama gadangan naso kuma babushi, fuskar gadanga qaryace, zuciyar gadanga qaryane, soyayyar danakewa gadanga ma karya ne, zan maka hauka idan baka buden kofar nan na fita ba wlhy, dole ya bude nata da qafa tabar gidan, shi kuwa kwantawa yayi ya runtse idanshi, be taba zata abubuwan zasu cabe masa haka ba sam!!!!!!
Mom Nu'aiym
[7/6, 3:06 PM] +234 706 571 7620: *Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS 👑*
Billy galadanchi
Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*
07
Tafiya kawai takeyi amma batasan inda take sanya qafanta ba, wani irin tashin hankali take ciki mara misaltuwa ta dade sosai tana ganin yanayin gadanga akomai na Ali Abbas hatta tafiyarshi da muryarshi tasha ayyana aranta dama shine takeso ba gadanga ba sekuma ta tuna yafi qarfinta, tasha jin tanasi tayita kallon qwayar idanshi sabida yanda yake mata kama da gadanga amma bata taba kawo wa ranta cewar wai Ali Abbas shine gadanga ba, tayaya ma hakan zata faru a rayuwa? Mesa ya zab'i cutar da ita? Sabida tana talaka? Mara galihu ko sabida ita d'in ba mace bace? Kai tsaye gidansu wata friend dinta ta wuce dake lowcost wacce dama tana cikin qawayenta na sokoto tana yawan mata qorafi akan bata zuwar mata, koda tashige dakin Bilkisu bata qara fitowa ba, yau dai ta kasa daurewa rayuwarta zama tayi ta gayawa Bilkisu komai daya shafeta tana kuka sosai tamkar ranta ze fita, Bilkisu ma kukan tayi na tausayin qawarta sannan tace
"Nasani abinda ya aikata agareki cutarwa ne ammafa ki sani mijinki mijinki ne, bance ki sake masa fuskaba kokuma kici zarafinsa noo ina daiso ki gasashi cikin ruwan sanyi, ki sani wllh hafsat yanzu maza wuya sukeyi,idan kika kashe aurenki wuya zakisha, karki dubi wai wata huddy to saime dan mijinta ne, kibi komai a hankali sannan karki kuskura ki gayawa wani wannan maganar da kika gayamun, kiyi tamkar baki sani ba shi yaje ya fada da kanshi, ki nuna masa lallai abinda yayi bame yafiya bane, kuma lallai bazaki zauna dashi ba amma karki tsaurara kin ganni nan miji nake nema ido rufe, so ki kula ki kuma kame kanki, karki bari ya fahimci kin razana ki daure kiyi komai yanda kika saba a gaban mutane ma ku gaisa yanda kuka saba kinji?" murmushi tayi taiwa qawarta godiya, tayi zamanta anan suka ci gaba dashan hirarsu.....
Ali Abbas be koma gidan ba se wuraren karfe 7 na dare, yana shiga ya had'u da yalwa, zubewa tayi ta soma wurga masa gaisuwa
"Hudaisa fa?" ya buqaci sani sadda kanta qasa tayi tace "Tana d'akinta batada lafiya ne tun bayan fitanka" kai tsaye d'akinta ya wuce ya tarar tana bacci alamun ta samu sauqi, be tashe taba yabar dakin zuwa dakinshi, se wuraren 9 ya qara zuwa ya tarar ta tashi tayi salloli ma tana cin abinci murmurshi ya sakar mata
"Huddy na akace bakida lafiya ya jikinki,nashigo d'azu kina bacci, nace bazan tasheki ba" murmushi tayi tace
"Laa ai naji sauqi kuwa Abbi, karka damu damafa kainane yake mun ciwo nasan stress ne na aiki" jinjina kanshi yayi
"Ki huta plss baby, get well soon" murmushi tamasa sannan tace
"Ance kunfita tare da Manga tun safe amma ko yanzu na tambayi yalwa tace dani bata dawo ba ita while kai kuma tun magrib ka dawo,ban nemeta bane nasan kuna tare, wani irin tashin hankali yashiga lokaci d'aya hakan ya nuna a fuskarsa
"Haba hudaisa,wannan wane irin rashin hankaline?? Ina zanje da ita tun safe har yanzu ni city campus na ajiyeta tun safennan, yarinyar nan zataci qaniyarta a hannuna, wato yawo ta tsira ko,ke kuma tsabar sakarci bazaki nemeta quater after 9 fa yanzu" shiru tayi tana saurarenshi harya kai aya sannan tace
"Too Abbi ya zanyi nikam? Kana ganin fa banida lafiya, kumama nasan bata sabyin hakan ba,and tunkan magrib nake bacci tashina kenan na tashi da yunwa sosai" tsaki yaja
"Maza kiramun ita a waya" janyo wayarta tayi tana mamakin wannan masifan da yake ita a en kwanakinnan tana mamakin abinda ke damunshi abu qalilan ya saka jaraba, sallama tajiyo tunkan tayi dialing number d'in, Manga ce ta shigo yalwa ta sanar mata huddy batada lafiya....yanayin sa kad'ai ya tabbatar mata ba wasa a lamuransa haka kurun ta tsinci kanta da tsoronsa da faduwar gaba me tsanani, sunkuyawa tace
"Yaa Ali ina wuni?" be ansaba se kallonta da yake cikeda masifa, dubanta ta mayar ga huddy
"Auntu huddy ya jikin, ashe bakida lafiya wlhy ban saniba yanzu yelwa ke sanar dani" murmushi tayi
"Naji sauqi hafsat sosai fa, ciwon kaine kawai yelwa ke d'aga muku hankali karki damu" miqewa tayi ganin Ali na cikin d'akin
"Allah ya baki lafiya Aunty zan dawo anjima" tana kaiwa qofa yace cikin tsawa
"Ke manga zonan" da qyar ta had'iyi yawu sannan ta juyo ta tsaya kawai
"Daga ina kike tun safe dakika fita school se yanzu karfe taravya gota kike dawowa?" d'agowa tayi sukayi ido biyu tamasa banza, ga mamakin ta saukar mari taji a kuncinta
"Da wani shegen nake magana anan badake ba ehe,nace gidan uban wa kikaje tun safe?" dafe wurin tayi sabida ba shakka taji azaba, sannan tace cikin kuka
"Lowcost na tafi gidansu bilkisu" qara yamutse fuska yae "Wakika tambaya izini kanki tafi, kuma wayema ya gayamiki ana kaiwa dare idan an fita, wani sabon iskanci kikeji ko eye?" duqawa tayi "Kayi hakuri yaa Ali inshaa Allah bazan qara ba, yayanta ne ya tsayar dani akan ze dawo dani gida kuma se be dawoba se yanzu" wani tashin hankali ya kuma shiga jin an ambaci Namiji
"Wato tsbar kin rainani namiji ya kawoki gida kuma kike gayamun kanki tsaye ko, an gaya miki cewar haka matan aure sukeyi ko kin manta cewar da aure a kanki" cikin sanyi huddy tace
"Abbin Ameer manga fa batada yawo, tunda yaune karanta na farko nama laifi kayi zan mata magana bazata qaraba in Allah ya yarda" tsaki yaja fuuuu yabar d'akin, mamakin Huddy kullum qaruwa yakeyi akan lamarin Ali Abbas sekace wanda akaiwa turaren masifa dama ta sani batace dashi bata dawo ba duk ita ta janyo mata mari, lallashin manga dake kuka tahau yi, sannan ta mata fad'a akan fita ba'asan inda tajeba ba kuma neman izini kazalika takai har dare irin wannan, hakiri dai ta bayar sannan ta tashi zuwa d'akin ta, kuka kam tashashi ko Ameer bata d'akko ba lallai ma wannan mutumin yazo da salon raini, amma zata magance matsalar ne dole......K'ofar da aka bude ne ya mayarda hankalonta wurin shine ya shigo mata d'akinta bayama tsoron muna funcin gidan sarauta, zabura tayi zata saka hijab yayi azamar riqota gabaki daya ya mannata jikinshi
"Kinyi kadan ki hanani ganin matana a duk yanda naso, wazaki sakawa hijab" kwatar kanta takeso tayi amma ta kasa sabida yanayin riqon daya mata kuka tasomayi
"Bazan taba zama dakai matsayin miji ba wlhy, mugu kawai" sassauta riqon daya mata yayi
"Haba Manga, mesa bazaki rungumi qaddarar datazo miki ba?, ki taimakamun mu rufawa juna asiri mu gayawa su daddy halin damuke ciki,idan kunyar huddy kikeji nina miki alqawarin zanma raba muku gida zan kaiki gidana na arqillah" dariya ma yabata ta kalleshi sheqeqe
"Yaa Ali bazaka gane bane wai kai? Wlhy na tsaneka tsana mafi muni, mutumin daze wulakantar da iyalanshi ba abin so bane, bana burin ma zauna dakai na haifi d'a me irin mugun halinka, bana kuma san ganin koda fuskarka ne, gidan nan ma dan ba yyanda zanyi ne dabazan zauna aciki ba wlhy, na gode Allah sauramun sati biyu na soma exams ina kammalawa na barka da gidanka da komai naka har abada, abu na gaba dazan fada maka shine, wlhy ko kanaso ko bakaso seka sakeni, kota ruwa kota tsaki, kota masifa kai koma ta meye sabida bana sanka bana san me sanka na tsaneka, Allah a baki fir'auna azuci kawai" shiru yana mamakin Manga ko sanda yasan batada nustuwa batada rashin kunya lallai wannan abin ya girmi tunaninsa gaba d'aya be zata haka zata masa ba, qwace jikinta tayi
"kafitarmun daga d'aki koni na fita" ta fad'a a qufule idanta ya qanqance yayi jajir tsabar masifa, haka ya fice gwiwa a sace yabar d'akin lallai Ali yaga Ali kenan....
*Bayan wata daya da sati biyu*
Har wannan lokacin kullum masifa dayace, Manga san bata sake ma gadanga ta tsaneshi sosai bata kosan ganin shi arayuwa, gashi wannan ne last semester dinta harta gama project dinta da komai, gashi ta kammala exams tana shirin tafiya kd ...........
A zaune ta sameshi gaban fulani yayi shiru ya sadda kai ita d'inma ba magana take ba, dama ta saba ganinsu a haka so bata wani damuba, kai tsaye wurin fulani ta wuce ta matsa jikinta sosai ta kwanta ta daura kanta saman cinyar fulany, dariya tayi tace
"Wai Auta mesa bakyajin kunyane, yanzu sabida Allah idan kika qara sani fa iehn" dariya tayi
"Kai Haba ummu, ni yanzu bakiyi missing dinaba dan Allah, tunda fa na fara exams ban hau cinyaba haka ake auta?" dariya tayi sosai tace "To Auta kwanta abinki aike 'yace daga Allah bata biyunki" murmushi tayi tace
"Ummu yanzu a misali Gadanga ya dawo,kuma ku gane yanada rai da lafiya haka kawai ya gujeni, amma yana dawowa yace ze tafi dani ni matarsace zaki yadda ki bada autanki?" mumurshi tayi
" Hmm Auta kenan ai bari kiji, indai hakan tafaru wlhy kotu zata rabani dashi, cutarwa kenanfa, ai da ranshi da lafiyarshi indai yanada hankali baze soma aikata hakan ba, kedai kawai ki riqa adu'a kinji, lokaci kuma yayi dazaki dena zancen wannan mutumin ki fuskanci rayuwarki araba auren kawai nina qosa inga en jikokina" dariya tayi tace
"Ai inshaa Allah ummu idan naje kaduna zanje dasu daddy araba auren, ni kaina yanzu bana ma sanshi ina dai masa fatan alkhairi in kuma ya mutu Allah jikanshi" shafa kanta fulani tayi "Ameen Auta Allah ya miki zab'i mafi alkhairi Ameen" kan wani yayi magana sega qanwar Ummu nan hajiya mariya tashigo da sallamarta, matsawa tayi kusa dasu ta d'akawa Manga duka a cinya, ja'irar yarinya maza ki tashi karki qarasa mana ita, kai yanzu Ali kana kallo zaka bar wannan gandamemiyar saman cinya" murmushi yayi yace
"Ni Umma banmasan yanda akai wannan tazama autaba" kallonshi tayi tace
"To ai Ali tunda Hafsat ta rasu Yaya fulani take cikin damuwa, duk inda taga hafsa kuwa zakaga ta liqewa santa, wannan autar kuwa tace ta maye mata gurbin hafsan ta" da rashin fahimta ya kalleta
"Wace hafsat ce ta rasu wai Umma?" murmushi tayi tace
"Ali akwai mantuwa shiyasa akace uwa uwace, 'ya macen da Allah ya baiwa Yaya fulani qwaya d'aya akeji da ita tamkar qurjin gwiwa Allah ya mata rasuwa tunda tayi baqon dauro shine fa kaga dukta damu tanasan mace, kai harka manta hafsa kenan, koda yake bakazowa qasarba harta rasu wataqil a hoto kawai ka ganta" gabaki d'aya mamaki ya bayyana a fuskarsa yace
"Wlhy umma ban tab'a sanin Ummu ta haifi 'ya mace ba wai har ta rasu, babu wanda ya sanar dani wannan maganr har ita" itama tayi mamakin jin maganar amma seta kawai da kanta gefe d'aya kurun ita kuwa umma mamaki