Showing 6001 words to 9000 words out of 60927 words
Chapter 3 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt
dazeje damu tasha kinji?" da sauri tayi ciki tana murna......
Sallama yawa Baban Manga ya wuce da sauri yabar unguwar akan babur...koda manga ta fito zatawa mahaifinta sallama seya sanar mata ai gadanga tuni ya wuce kuka kam tashashi, wayarta ta dauka tayi kiran wayar shi amma sam bata tafiya,tasha kuka kam a haka ta hakura tunda gadanga ya mata wayooo......
Ali Abbas yanata shirye shiryen zuwanshi kaduna gun huddy, ta isheshi da rigimar san zuwanshi akan tayi missing nashi sosai, duk yanda ya tuna huddynsa se yayi murmushi yarinyar tana burgeshi, banda halinta daya kula sam batasan talaka batada makusa a gunshi yana yabawa kyawawan d'abi'unta matuqa......kai tsaye gidansu ya wuce yana mamakin rashin samun wayarta dabayayi tunda ya taso, hakan ba d'abi arta bane indai yana hanya ta soma kiranshi kenan ba adadi...
Baban manga ya wangale mishi gate yana danna kanshi cikin gidan ya hangosu tsatsaye har huddynsu da maminsu,da amminsu su farouk dama Alhj tahir mahaifin su huddy....beyi qasa a gwiwa ba yaje ya gaidasu suka amsashi cikin sakin fuska, yanaso yayi shiru amma ganin Manga nata kuka ya sanya ya tsaya,yaga kuma kowa yayi cirko cirko ana kallonta bame magana har wacce yake tsammanin itace uwarta kasancewar suna matuqar d'iban kamanni....
"Hafsatu Manga lafiya dai kukan kuma na meye ne?" Alhj Tahir ne yace dashi
"Wlhy Ali mijintane ya b'ata yau sati uku, annemesa an sara, daga sunan zuwa gida gaida kawunsa da bashida lafiya yau sati uku,shine fa dukta tashi hankalinta haka" rike bakinshi yayi yace
"Manga tanada aurene dama?" murmushi yayi yace
"Dududu auren fa sati shida yanzu inaga, baka taba haduwa da mijin ba duk zuwanka,shine malamin dake koyar dasu karatun islama anan,yana kuma kula da shuke shuken gidan da wankin motoci" shiru ya d'anyi kanyace
"Naje gidansu kuwa?" cire hula daddyn huddy yayi yace "Nanfa d'aya mundai san dan Zaria ne a qauyen soba,amma babu wanda yasan gidansu, kawunsa ma da qanin mahaifinsa dasukazo daurin aure ni bazan shaidasu ba idan na gansu, Anan muka hadu yazo neman aikin koyarda yara islamiyyya kuma banan yake kwanaba, mundai yaba da halayyarshi ne muka baiwa manga shi a matsayin miji" nisawa yayi yace
"Hakane amma daddy mezai hana aje soban a bincika aji ai yafi ko kuwa?"
"Munje tashar motar dake kai mutum soba ma, babu zancen wai suna daukan record, yanzu zancenka zamubi muje soban tunda ba wani nisa zuwa zariya, akira idi direba" sosa kanshi yai yace
"Manga ai er gidanace, gwara nazo na biku daddy, na nemo mata mijinta kalli yanda take kuka hadda majina ko kunya" ya qarasa maganar cikin sigar tsokana, murmushi tayi kurin sabida tana cikin damuwa.....koda sukaje soba cewa aka musu babu wani suna me kamada wannan bare kawunnan shi ba wannan sunan a soba, kansu ya matuqar d'aurr suka juyo amma daddy ya hana a gayawa iyayenta kurin yace dasu dai basu gane iyayenshi ba a soba......
Haka dai Manga tayita hakuri tun ana jiran tsammanin dawowar gadanga har aka cire rai, kowa har daddy suka alaqanta b'atanshi da mutuwa, bazasu ce sun zagaye garin sobaba kuma a yanda malam gadanga yakeda sanin Allah baze tab'a yiyuwa ya aikata hakan ba, tunda da suka binciki yarinyar ba ba abinda ya tab'a shiga tsakaninsu idan ma mugunta ze mata aima shine ya nemi aurenta ba kumama ai daya ajiye takardar sakinta ya gudu, suna dai sakaran hatsari yayi bame kawo labarinshi, matsalar kuma har wanda yake kawowa ya wakilceshi idan baya nan ya sanar musu cewar baida labarin gadanga......
Manga gaba d'aya tayi sanyi tazama shiru shiru, dukta rame gwanin tausayi ba qaramin so takewa gadanga ba, bataji zata rayu idan har wai yanda ake zargi ya mutu ya mutu din, dukda yake ta gagara yadda da mutuwar tana gani ko yaushene ze dawo gareta inshaa Allah.....
Saura sati biyu bikin huddy da Ali Abbas yazo kd, sanyawa yayi aka masa kiran Manga yace huddy ta basu wuri, ita bata kawo komai arantaba sabida tasani Manga tanada auren wani akanta, takuma sani tausayi sosai manga ke baiwa Ali Abbas, acewarsa yarinya me san wasa da raha duk ta zama wata iri daban, zama tayi bayan ta shigo parlor din tace cikin sanyin dake qoqarin zame mata d'abi'a
"Barka da yamma yaa Ali,anzo lafiya?" kallonta yayi sannan ya nisa ya sanya hannu ya shafi sajensa sannan yace
"Manga inaso kiyi hakuri da abubuwan dasuka faru a arayuwarki tunkan ki qarasa mallakar hankalinki, ki sani shi Allah haka yake al'amuranshi, kowace rayuwa tana had'uwa da jarabawa iri iri,hadisi ya inganta akan yadda da qaddara ta alkhairi data sharri, nasan bazaki rasa karanta hadisi na biyu ba acikin arbawuna hadith inda ake bayani gameda imani, anan aka bayyanar mana yin imani da kadddara ko wace irice, "wa tu'uminu bil qadari hairihi wa sharrihi" kinga anan zaki zama me imani me kyau akan yanda da kika dauki kaddararki dazamu iya kira mara kyau, dukkuwa dayake bakida masaniya gameda tanadin da mahalicci ya miki, nasani Manga baze yiyu inganki kamar da ba amma ki sani bazanso ganinki haka ba, ki nustsu dan Allah ki fauwalawa Allah lamuranki, ga waya nan nazo miki da ita, akwai number na aciki, dukkanin buqatunki kina sanar dani karkiyi shakkar komai ni yayankine, nayi magana da mahaifinki da daddy sun amince dana kula dake ba laifi bane, kuma banasan gaddama karnaji kin tambayi wani komai ni nan nine zaki kira zan miki komai,kuma idan har mijinki be dawo ba, aka soma daukar dalibai a jami'ar sokoto zaki koma gun huddy kici gaba da karatunki har Allah ya bayyanar da mijinki,kindai ga ai kece babba awurin iyayeni, kiyi karatu ki zama wani abu sabida ki taimaka musu, idan kuma ya dawo Alhamdulillah dama fatanmu kenan, idan yayi ra'ayi zan roqeshi ya barki idan bayaso ki hakura shine mafi aala.....godiya sosai ta masa sannan takoma b'angarensu domin tuni wuri su inno take kwana.....
To masu karatu,ko ina Gadanga ya shiga?? Nifa tunani na ya tsaya cak!!!! Alqalamina se rawa yake ina kyautata zaton yanzu aka soma wasan.........
Vote and comments plssssss
[7/6, 8:07 AM] +234 706 571 7620: *Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS 👑*
Billy galadanchi
Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*
Zeeyy qaseem,wannan shafin kuma nakine,Allah bar qauna....
03
Shagalin ya soma kankama,yayinda sam Manga bata wani d'okin bikin, mosti biyu da uku duk gani take tamkar zataga Gadanga agabanta, duk tayi rama tayi fayau da ita, yayin biki babu wanda daddy be mataba, gani yake tamkar komai shine sila na lalacewar rayuwarta mugun tausayinta yakeji, duk yanda sukaso ta sake jikinta abin yaci tura, zuwa yanzu yawan shirun datake ya sanya hatta Ummin su huddy tausayinta takeji, a wurinta ma take zama ba wurin Innoh ba, Allah ya d'aura mata tsananin qaunar gadangan ta ba iyakaa......
Anyi biki na gani na fad'a wanda har mamakin yanda ake dirzar naira Manga keyi, ranar da aka daura aure ranar akaje dinner, Ango gabaki d'aya ya gama rikicewa yaudai yasha qudurin nunawa duniya yanasan huddynsa.... Bayan sun ciyar da juna da weeding cake nasu da juice, sekuma suka juya wurin rawa rungume abarsa yayi ya riqe hannunta d'aya suka soma juywa a hankali abinsu....Runtse ido Manga tayi tana tariyo ranar da zasu rabu da gadanga rungumar daya mata, abin ya matuqar tsaya mata a wuya,wannan rawar dasuke bazata iya kalla ba, sulalewa tayi daga hall d'in taje can waje ta sadda kanta a qasa ta soma uban kuka ba qaqqautawa...har aka tashi wurin dinner tana kuka ranar kam fuskar nan ta haye tayi sukutum da ita.....
Koda za'aje kai Amarya sokoto Manga zazzab'i takeyi sosai, dole aka barta gun Ammin su hussy dayake daddy yace itada ummi base sunje ba, kullum cikin kuka take har Ammy ta fahimci bata samun bacci, ba qaramun tashin hankali ta shiga ba taje ta sanarwa daddy, Aka sake bazama neman gadanga aka koma har soba amma ba labarin ko wanda ya sanshi.....
Tunda Amarya tazo gidanta dake cikin masarautar sokoto takejin tsoro, fad'uwar gaba me tsanani yake shigarta,Allah sarki huddy dukda yawan shekarunta ta kame kanta sosai, kuma dukda tasan meye aure tana cike da tsoro tunda bawai sabawa tayi ba....haka dai Ango Ali Abbas yarima ya shigo part d'in cikin shiga ta alfarma a wannan yanayin na faduwar gaba ya sameta, zama kusa da ita yayi yace
"Amarsu ta ango, hudaisa ta Ali Abbas, wannan lullub'in fa?" qara sunne kanta tayi a qasa tana murza zoben hannunta da yan yatsunta da kunshinta daya ebe mai hankali yayi matukar kyau dukda yake fatarta baqa ce amma hakan be hanawa lallen samun kyakyawan matsugunni me kyau a jikintaba, hannunshi yakai ya riqo hannun nata a hankali ya shafi lallin yakai bakinshi kuma ya sumbaci lallin nata sannan ya furta
"Huddy lallin nan yayi kyau matuqa,inasan kunshi sosai musamman a jikinki matana" bata d'agoba still se murmushi da takeyi, wanda yake sauka lokaci d'aya tare da hawayenta, hannunshi ya sanya ya yaye mata mayafin
"Subhanallah huddyyy naaa, badai kuka bako? Na menene ko kadunan zaki koma?" kukan tane ya qaru ta duqar dakanta tashiga rerawa a hankali, janyota yayi sosai jikinshi ya sanya hannu ya goge mata hawayen nata sannan cikin sigar rarrashi ya futa
"Huddyy keba yarinya bace, dukda yake na sani rabuwa da gida ba dadi, koda a kadunan aka kaiki kuwa bare a skt ma, amma haka aure ya gada sekinyi hakuri kinji?" gyad'a msa kanta tayi yace
"Tashi muje zan miki wanka ne,nasan kin gaji" zaro ido waje tayi gaba daya,labbanta na motsi amma kalmomin datakeso ta fad'a harshenta ya gagara sarrafa haruffan dazasu aiko da kalmomin, kasa haquri yayi ya had'e bakinshi da nata, kasa hanashi tayi sabida tajima tana kwad'ayin wannan yanayin datakeji, yafi 2 mnts yana murzar bakin daya jima yana bashi sha'awa kanya saketa yace cikin isa
"Banasan gaddama, wanka zan miki, na tabbatar kinsan cewar ke d'innan matata ce bawai haka kawai zan miki abu ba" batace komai ba amma bata motsa ba....da kanshi ya miqar da ita tsaye sannan ya sanya hannu ya zare mata zip na doguwar rigar datake sanye da ita, atake ta fadi a qasa ,ta dawo daga ita se skirt,pnt da bra,take jikinta ya soma rawa ma, towel ya dakko ya sanya a kafadarshi sannan ya had'e jikinshi da nata ya soma b'alle mata bra d'inta yayinda yake amfani da gargasan gemun sa yana shafa mata bayan wuyanta dashi...... Wani iri Huddy keji tama rasa abinyi se hawaye kawaii cire ta yayi sannan ya cillar a qasa ya dawo da dubanshi zuwa gareta, da sauri ta runtse idanta ,murmushi yayi,kunyarta na burgeshi sannan ya ya sanya hannunshi ya lalubi waist dinta yasoma zare mata under skirt har qasa ya kaishi tana nan tsaye kaman statue ba laifi ya fada a zuci tanada qira me kyau, hannu yakai domin zare pants dinta da sauri ta daura nata hannun akan nashi, murya na rawa tace
"Ba gaddama nake maka ba yaa Ali,taimakona zakayi ka ragemun wannan kayan nauyin dake kaina, ka barni da wannan karna saka maka ihu" murmushi yayi ya daura mata towel daga qirjinta sannan yace
"Tunda kinji tsoro jeki kiyi wankanki, inyaso ki dauro alwala dagacan.....wani sanyin dadi taji a ranta ta juya da sauri zuwa toilet, koda ta dawo baya dakin, da sauri ta shirya cikin wata lallausan rigar bacci pink color....Tare suka sallaci sallar nafila sannan.. Suka kwanta, gabaki daya juya masa bata tayi ta nemi nutsuwarta ta rasa, birkito ta yayi ta fuskanceshi gaba d'aya, ya sanya d'an yatsa yana zagaye lips d'inata da suka dad'e suna d'aukar masa hankali, ya matsu ya kasance tare da matarshi kasancewar sa bame neman mata ba dacan, cikin wata murya dabata tab'a ji yayi magana da itaba ya kira sunanta
"Huddy?" bata d'ago ta kalleshi ba, cikin nauyin baki tace "Na'am yaa Ali"
"Inaso ki zamto mace ta gari,uwar 'ya'ya ta gari, Amintacciya wacce zata qaunaci mijinta dan Allah, kiyi supporting d'ina akan dukkan komai ki soni kuma ki qaunace ni, Nasan a tunaninki bana sanki sabida auren had'i mukayi, sam ba haka bane, ina sanki tun ganin farko huddy, dan Allah ki riqe amanar aure" murmushi tayi tanaso tayi magana amma sam ta kasa furta komai sabida tanajin yanda yake magana yana mata wasa da en yatsunshi akan cikinta, gano yayi gaba d'aya saqon daya ke kokarin isar mata ya gama saukar mata da kasala gaba d'aya, bakinsa ya cura a nata ya soma sarrafa harshen ta a hankali, kasa hanashi tayi gaba daya ta sake masa ragamar ta, ranar kuwa yaa Ali ya mayarda Huddy cikakkiyar 'ya mace, yaji matuqar dad'i daya sami matarsa a tsare kamar yanda ya kame kanshi haka ya samu matar data kare masa mutuncin ta har gidan aurensa.....
*Bayan wata shida*
Har wannan lokacin ba gadanga ba labarin sa, gabaki d'aya iyayen ta sun tashi hankalinsu, sabida yanda taketa rama,yaudai Baban Manga da Inno ne zau e a tsakar gida suna tattaunawa
"Innoh gaskia ni al'amarin yaron nan gadanga ya gama tsoratar dani,yanzu ace ko waiwaye, idan da mutuwace wlhy munji labarinta yanzu, amma ba wannan, ni ina ganin kawai Allah a abki fir'auna a zuci ya mana" kan Innoh tai magana har manga ta qaraso wurin aguje
"Haba Baban Manga dan Allah ka kyautatawa Mijina zato, wlhy na tabbatar gadanga baze tab'a aikatamun hakan da gangan ba, iya tsawon zamanmu dashi sati uku zallar soyayya ce a tsakanin mu da kulawa, ko sanda yace zeje dani ya tafi wlhy sabida rigima na yamun wayo, kamai Adu'a idan yana raye Allah ya bayyanar dashi idan kuma ya mutu Allahu ya bamu ilimin sanin hakan, na tabbatar gadanga ze dawo gareni" nisawa Baban manga yayi
"Mangan Inno ki sani koni nan wayannan kalaman iya bakina kawai suka tsaya amma sam zuciyata bata aminta dasu ba, sabida nasan halin Gadanga halinshi ba haka yake ba, bana fatan mutuwa yayi, ammafa ki sani a qa'idar aure idan namiji ya tafi abinshi da gangan harna tsawon watanni 4 tofa babu aure,idan kuwa fad'a yayi toko shekaru hud'u be wa'adin indai muddin be dawo ba dole a raba auren ki auri wani, wannan tsarin ba nawa bane manga na musulunci ne"
Tana kuka tace "Niko shekaru dari gadanga zeyi zan jirashi na tabbatar ze dawo gareni, dan Allah Baban Manga ka dena fadar zancen raba auren nan,wlhy inasan mijina" tausayinta ya kamashi yace
"Allah ya zab'a miki mafi alkhairi Manga, aalhj ya sanar dani ki shirya kayanki jibi zakije sokoto hurin hudaisa, dukda yake nasani cewar bakwa shiri amma haka zakiyi hakuri, a yanda naji batada lafiya ne, kuma ma acewarsa bazakine wurinta matsayin er aiki bane zakijene a matsayin er uwarta ya sanar da ita hakan, zance na gama kije da komai naki na karatu zaki soma makarantar gaba da sakandire acan kan Allah ya bayyanar mana mijinki ko labarinshi, banso hakan ba Amma bazan iya masa gaddama akan lamuranki ba, sabida Alhj yayi duk yanda akeyi ya d'auke ki matsayin 'ya, ki kame kanki ki sani fa danigiyar auren wani a kanki bawai sagaga zakina yin wannan haukan nakiba.... Kuka kawai take, batason zuwa sokoto itakam tafiso ta zauna gida tayita jiran gadangan ta amma yata iya batada zabin daya wuce bin umarnin iyayenta......
*Sokoto*
Koda Manga tazo gari mamaki tayi ganin cewar har cikin jikin huddy ya fito, sedai fa tayi baqi sosai ta rame har tsoro ta baiwa Manga, tunda tazo gidan bataga Ali ba, kodai dan bata fita ko ina bane ohoooo....
Satinta biyu da zuwa wani yammaci tana zaune sega Ali Abbas yazo parlor d'in, tashi tayi ta sunkuya ta gaidashi, ga mamakin ta wannan wasan dayake mata sam beyiba, fuskarnan a hade alamun ba wasa yace da ita
"Ke Manga kikace da huddy bakyason course da aka baki? Me kikeso a miki to? Late admn fa na sanya aka baki, karatun dole sekinyo zab'i a kanshi? Idan kikace dole se kinyi Law idan kuma ba alkhairi bane a gunki fa? Med lab aka baki kuma shi zakiyi, idan kinje ki bari inga sakamako mara kyau kiga yanda zamuyi dake, akwai driver daze kaiki jami'ar gobe ki fara registration" lokaci d'aya taji qirjinta ya doma kuma ta soma wani tsoron shi, muryarta na rawa tace
"Kayi hakuri yaa Ali inshaa Allah zanyi" miqo mata kudi yayi yace
"Ungo wannan keba indigen din nanne dake ba, na kd ne, zaki biya registration sannan kuma ku biya ta bank dashi, na sanar masa ya kaiki gt ki bude acc goben" godiya ta masa sannan batare daya saki fuskar ba ya wuce abinshi.....
Tun daga ranar da ya bata kudin bata sake ganin shiba gashi dai takan jiyo muryarshi sabida part dinsu take zama amma sedai ta jiyo suna raha abinsu shida matarshi, yaune ranar farko dazata soma zuwa lecture koda ta fito wuraren 7 ta ganshi zaune Huddy tayi matashin kai da cinyarshi yana shafa sumar kanta a hankali, kawar da kanta tayi gefe sannan tace
"Yaa Ali ina kwana, Aunty huddy ya jikinki" be amsa gaisuwar tba huddy tace "Naji sauqi Manga,skul din zaki tafi?" kan tabata amsa ta tsinkayo babbar muryarshi yana cewa
"Zonan Manga" zagawa tayi a kunyace tace "Gani" seda ya danja fasali sannan ya saki muryarshi dake da fad'i yace
"Manga ki sani kinada aure akanki, sannan dukkanin abinda kika aikata na batanci Allah yanaji kuma yana gani, kada kiyi amfani da damarki ta ya mace ki cuci igiyar auren dake kanki, inshaa Allah mijinki ze dawo gareki ko yaushe ne, duk abinda kikayi me kyau masarautar nan kikayiwa, idan kinyi mara kyau ma haka, motar da zakije skul da ita ki dawo da ita duk tanada tambarin nan gidan, driver daze kaiki ma na nan gidan ne kowa ya sanshi, dan Allah ki rufa mana asiri ki kare mutuncin aurenki" shiru kawai tayi masa yaci gaba
"Nine nake kula da komai da komai na karatunki, idan kina buqatar wani abu ni zaki tambaya, seki sanar wa huddy buqatunki ni kuma nasan zata sanar mun" godiya ta masa sannan ta tashi ta miqe zuwa skul din....
Allah sarki rayuwa haka Manga ke rayuwa agidan batare data samu wata walwala ba, gabaki d'aya tayi sanyi sedai ba laifi tana karatunta, bata