Showing 27001 words to 30000 words out of 60927 words
Chapter 10 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt
aranta tace duk yanda naso in yafewa Ali Abbas bazan iya ba, wato ni shekaruna hudu da kusan rabi da aurena akanshi amma sati uku kawai nayi ina moruwar aurenshi, moruwar auren ma mara amfani, be taba koda aikamun saqon sumba baki da baki ba, mena masa? Ni banida jinine? Kokuma ni itace bansan dadin auren ba? Bansan salon kwanciya da miji ba kokuma bansan amfanin 'ya'ya ba, nima inaso ingq jinina, inaso inji dadin mijina,inaso in ganni a qirjinsa kwanxe ina bacci,wannan wane irin shiga haqqi ne daze kawoni India sannan ya shige daki daga da matarshi taso ni kuma ko oho, ni er talakawa kenan, mara galihu,banida gata banida haqqi" kwafa tayi ta k'udurcewa ranta lallai indai har muddin Ali Abbas be kusancetaba har suka bar k'asar India bazata tab'a barinshi ya samu abinda yakeso aguntaba alokacin dayazo yana buqatar hakan, ranar dai a zaune ta kwana yayinda Ali da huddy suka kwana suna matuqar kulawa da juna musamman shi dai ya damu da ita sosai, motsi daya seya mata sannu tana maqale ajikinshi.....
Washe gari wuraren qarfe bakwai na safe tajiyo ana mata knocking, batare da wani tunani ba tazo ta bude kofar, kallon sosai suka tsaya yiwa juna yayinda ta mugun had'e rai batai masa magana ba kurun ta juya zuwa ciki, mazaunanta yabi da kallo ya had'iye wasu yawu masu d'aci ya qaraso ciki ya zauna kan gado, ita kuwa tana zaune kan kujerar dake cikin dakin ta had'e fuskar nan, sunfi minti biyar yana jiran yaji ta gaidashi amma sam ko gezau batai ba, jinjina kanshi domin yagano d'an Adam yanada wuyar gane hali sosai,be tsammanin cewar akwai sanda Manga zata sauya har haka ba, gyaran zamanshi yayi yace
"Duk kanin abinda ya shiga tsakanina dake baze zama hujjarki ta rainani har haba, wlhy zan matuqar sab'amiki idan ina miki magana kina qin amsawa,kokuma kina qin gaidani sabida niba sa'an kibane dazan zo induba lafiyarki ki budemun kofa ki juya batare dabgaisuwa ba, kina jina kam ko?" se a wannan lokacin taji matuqar kunyar halin data mai na rashin kunya kallonshi ta qarayi ido cikin ido
"Kayi hakuri, ina fatan ka tashi lafiya" amaimakon ya amsata seya miqe "Nizan tafi asibitin da za'a duba huddy na, dama zuwa nayi inga yanda kika kwana, dakuma me kikesan ci?" Dukar da kanta tayi tace
"Na qoshi, Allah ya kiyaye" juyawa kurun yae ya fita a dakin, hawayen datake tarewa ta ji ya silalo mata bata manta wani yammaci da gadanga ya fita ya dade sosai be dawo gida ba, lokacin tana Amarya data soma fushi taqicin abinci sosai ya damu ya dinga rarrashi tamkar ba gobe, dole seda ta sassauta fushin taci abinci amma ji wannan? Meke nan yake nufi yunwar ta kashe ta? Lallai ma, kukanta tasha me isarta seda ta qoshi sannan dan kanta tayi shiru....
Se bayan la'asar ya sake dawowa d'akin wanda Alokacin ita gaba daya taji ta qara tsanarsa, sabida sam batai tsammanin cewar ze iya barinta da yunwa har haka ba,gashi tanada judade a hannunta cox anbata amma batasan ko ina ba,ko kallon inda yake batai ba tace murya can laqe
"Ina wuni yaa Ali" kallonta yake harya zauna
"Lapia lau" yabata amsa a taqaice "Me zakici" ya buqata, wani irin takaishin shi taji ya tarnaqeta tace dashi
"Meko zanci aina qoshi a qoshe nake" kallonta yayi sosai yace " Kinyi ordering wani abinci ne daga reception?" kallonshi tamkar zatai kuka tace
"Sosai nayi harma na biyasu" murmushi yayi yace "To daga yanzu idan kinyi ki dena basu kudi nine zan biya komai idan na tashi" uhm kawai tace cikin takaici
"Ya jikin Aunty huddy?" ta buqata "Taji sauqi amma tana can asibitin bazasu barta a wurin muba, sunce ma cikinta 8 month ne bama qirga da kyau, ita dince da kafiya tun a can tayi ultrasnd taqi ashe cikin yayi nisa, yanzu sunce anan wurinsu zasu barta, dakamar aikin tare zasu yishi su cire babyn kuma suyi aikin breast din" jinjina kanta tayi
"lallai kam cikin yayi girma, Allahu ya bata lafiya me d'orewa" miqewa yayi yace
"Zanje d'akina akwai abinda kike buqata?" d'agowa tayi ta hadiye wasu yawun takaici tare da cura manyan idanuwanta cikin nashi tace
"Meko zan buqata ni Hafsatu Manga,bana buqatar komai se kad'aici" kallonta yayi yanaso ya gano ma'anar kalamanta amma san yanda fuskarta take a d'azu yanzun ma haka ne, be gane inda kalamanta suka dosa ba kad'aici kuma? Ma'anar ta bata buqatar takurawar dayake mata ne? Lallai ma batare dayayi magana ba ya juya kawai zuwa dakin shi yana mamakin sauyawar halin Manga sam ta zama wata kala kuma ta sauya kyawawan halayenta amma ya kula shi kadai take mawa........
Ammi tayi zaman dirshan wurin boka tana kora masa bayani akan taji shiru har anbar qasar tare da wannan yarinyar ihu bokan yayi yace
"Daga yaron har yarinyar babu wanda aljani ke iya zuwa wurin shi, sabida sunada tsari me girma ajikinsu shi mijin ma gabaki daya acikin ambaton Allah yake wuni ita kuwa bata rabo da azkar da adu'o in kariya na tsari ajikinta, sannan ko wannensu yana sanye da zobe har er taki da baya bari wani shaidani ya iya zuwa kusa dasu komai qarfinsa, sabida haka babu abinda zan iyayi akai kije ki sauya shawara da tunani kawai, ga hanyoyi nan idan ta dameki ki sanya a kasheta kawai, hanya dayace dana kula zata iya bulle mana itace basu taba saduwa da mijin ba, zan iya tura mata cikin iska shima dan aljanin ze hura ne daga nesa, idan anje gwajin asibitin ma ze nuna cewar akwai cikin, kuma zeyita girma,idan kin yarda sena tura mata cikin na iska, mu rikitar da komai a tsakanin su kinga daganan ba aure se mutuwar sa kenan,idan auren ya mutu semu b'atar da zancen cikin kowa ya huta, murna sosai ta shigayi ta zazzage mai jakarta tabar wurin cikeda d'oki da murnar abinda zeje ya dawo......
Haka suka zauna a india na tsawon watanni biyu tunda sukaje banda gaisuwa ko hira Manga da Ali basayi abinci kuwa sedai tace mai ta karba amma yoghurt ne taketa sha da snacks kullum,tama rame sosai, Anyi aiki kuwa an cirowa fine girl me kyau sosai, breast dinma an cire dayan an kashe wurin da wuta kar ciwon ya dirar wa dayan yanzu huddy ta samu lafiya sosai batada wata damuwa, shirye shiryen dawowa suke tayi ita kuwa Manga se a wannan lokacin ta soma ciwo, haka suka dawo gida kullum cikin Amai take da yawan kasala, bata samun wadataccen bacci, wani yammaci ta shirya zuwa sashen ummu, dama tunda suka dawo a bangaren huddy ta sauka lokacin kwanansu uku da dawowa daga India, tana zuwa ta sakawa ummu kuka akan batajin dadin jikinta, ita sam batawa ummu kallon suruka kallon uwa ta dauketa yanda itama ta dauketa 'ya,
"Toni Auta niba likita ba ba komai, bansan meke damunki ba ko asibiti zamu je?" shagwab'e fuska tayi tace barinje in gayawa Aunty huddy ta dubani to kobe yiba?" murmushi ummun tayi
"Ki zauna anan barin wa huddyn waya, ai bakya riqa yawo ba bayan kince har jiri kike gani" kwantar da kanta tayi zaman jikin ummu, ta lumshe ido tanajin qaunar ummu har cikin ranta da ruhinta, mata me karamci da qaunarta..........Kallon ta sosai huddy tayi cikin dokawar qirji na kishi irin na mata bayan kwajin fitsarin daya mata ya fito kuma bincika yanayin al'adarta ta gano tayi tsallaken sati biyu be zoba ta kalli ummu tace
"Ummu juna biyu ne da ita na tsawon wata d'aya da satuka biyu" Washe baki ummu tayi aranta tace ashe an angwance a India" ta kalli huddy tace tana fad'ad'a murmushinta
"Lallai ma auta an gama girma, kije zanga en jikokina ta wurin auta, toki sani bana san kishiya,bazaku taru keda hudaisa kuna jeremun kishiyoyi ba muji zaki kawo, kinga yanzu me martaba bashida magana seta Ahasan yaga yarinya ze qyale tsohuwa" mayarda dubanta tayi zuwa ga huddy taci gaba "A rubuta mata magun gunan dazatasha tasamu sauqin wannan wahalan, tunda juna biyu beje ko ina ya kawo ba yasoma baiwa auta wahala, keni wannan koda mijine banayi,ze daddage yake baiwa Autan ummu wahala,ko Auta" sadda kanta tayi qasa qirjinta na wani irin mugun dokawa, harta ji jirin datakeji yana qaruwa, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un itace kalmar data furta a hankali, huddy senyaqe takeyi tace aranta wato ni inacan ina fama da kaina duk ciwon danake shi kuwa honey moon yaje da matarshi dukda yake nice na kafe akan sena tafi da ita.......
"Zanje na rubuta sena baiwa abbin su Ahasan ya siyo mata, seta zauna anan kawai tunda ni bana zama" murmushi tayi tace
"Dama bazan bada autana ba, tana nan kusa dani inshaa Allah" murmushi tayi ta juya sabida basa wasa da ummu" a parlor ta sami Ali Abbas ta zauna kusa dashi ya kalleta
"Kin jima da yawa wani abinne?" murmushi tayi tace
"Kasan halin ummu indai akan sha'anin Manga ne, dukta tashi hankalinta amma nisam bazan gaya maka komai ba seka bani goro" murmushi yayi yace yana kallonta
"Zan bayar mana sanar dani menene? Wani abin farin cikinne ya samemu?" murmushi tayi itama tace
"Manga ce da ciki wata d'aya da sati biyu, kaga har strip dinma na pt nazo maka dashi,kace angwancewa akayi daga India?" wani kallo ya wurga mata wanda ta kasa fassara ma'anarsa,yace cikin mamakin
"Ciki kuma Manga kamar yaya?" murmushi tayi tace
"Kamar yanda kamata ciki mana Haba Abbin Ahasan sekace wani mugun labari kalli sauyawar fuskarka kodai kaso seka gama shan angwanci ciki yashiga,to wane angwanci kuma bayan wannan anje honey moon an dawo da goro" da qyar ya saisaita nutsuwar shi ya qaqaro murmushi cikin hikima ya wayance mata yasa dariya yace "Mamaki nake ciki da wuri haka" ita kuwa kasan zuciyarta ma takaicin sa takeji tace
"Kaine kayi shigar wuri baka jira ta tare ba, dole kaga ciki da sauri haka" murmushi yayi abinda be taba yiba fita da irin wannan jallabiyar dayake zaman gida da ita shi yayi, ya miqe kurun yayi ban garen fulani.....batanan da saurinta taje kaiwa sarki albishir shi kuwa ya shiga d'akin kai tsaye, kuka ya tarar tana yi ya cizgota ta miqe tsaye tana ganin yanayinshi ta shiga rudu murya na rawa ta furta
"Na rantse da girman wanda rayuwa ta take hannunsa ban taba sanin wani d'a namijiba, bansan inda aka samo wannan cikin ba" Wani mahaukacin mari Ali ya dire mata seda taga taurari ba adadi, yace
"Aruwa kika sha? Nace dan ubanki a ruwa kikasha cikin? Zaki kawomun hauka anan banza shegiya mara imani, dama duk shekarun nan maza kike bi ko? Se yanzu Allahu ya tona miki asiri, wlhy ki sani bazan tab'a lamuntar wannan jakancin ba, idan na karb'i cikin nan shege nake wlhy se duniya tasan abinda kika aikata, aini bawai wawa bane jahilar yarinya mara dangana kawai" kuka kawai tana bashi hakuri amma se fada yakeyi kallonshi ttayi
"Dan Allah ka dena daga murya yaa Ali kar bayi su jiyo mu, se maganan ya zam tsegumi acikin gidannan, wlhy ka yadda dani ban taba aikata wani abu ba da igiyar aurenka" wani marin ya kuma dire mata ya cafki wuyanta, seda taga mutuwa kusa sannan ya turata ta fad'i akasa ya juya, yana kawowa qofa ummu dataje me martaba na fada ta dawo ya gani a tsaye ta qura masa ido cikin tukuma, ze iya cewa wannan ne karonta na farko data tsoma idanuwan ta acikin nasa,murya a qasa tace
"Idan ka fitar da wannan maganar Allah ya isa ban yafe maka ba, ko zuhair ka sanarwa da zancen cikinnam cewar banaka bane ban yafe na, kuma bazan lamunci kace ba danka bane, da nakane kona waye kaji na gaya maka, wawa kawai dabesan ciwon kanshi ba" sadda kanshi yayi a qasa yawuce kawai batare da yayi magana ba sam......shiga cikin d'akin tayi ta zauna saman gado ta qurawa Manga ido tanaso ta gano gaskiyar ta, kallonta manga tayi tace tana kuka
"Wlhy Ummu bansan komai ba, ba abinda na sani ban tabayiba wlhy sharri ne kawai dan Allah ki taimakamun ki nuna masa gaskiaya ummuna dan Allah" Rungumeta kawai ummu tayi tana bubbuga bayanta a hankali.
Mom Nu'aiym
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa ta gari Fulany saddy*
13
D'agota tayi ta kalleta sosai tace "Auta kalleni nan dena kukan haka" d'agowa tayi ta kalleta sosai tace da ita
"Auta ki kwantar da hankalinki ki dena kukannan, ki nutsu ki gaya mun gaskia abinda nake san sani" gyad'a mata kanta tayi amar to taci gaba
"Sanar dani gaskia alokacin da yan fashi suka d'aukeku sun miki fyad'e?" tana kuka tace
"Wlhy Ummu basu samu nasara ba ko kad'an akaina, Humaira ce kawai suka samu sa'arta amma banda ita bakowa harni" jinjina kanta tayi tace
"Shirya tashi mu fita" ba musu suka fito a tare zuwa asibitin qwararru ta jiha, binciken dai ya nuna cikin watanshi d'aya da sati biyu kuka sosai Manga keyi harsuka dawo, wato dai ta tabbata cewar lallai cikinne da ita, to amma ta ina? Garin yaya hakan ta faru? Har suka isa bangaren su kuka takeyi, zama ummu ta qarayi ta fuskance ta tace
"Autan Ummu sanar dani gaskia tsakaninki da Allah, na miki alqawarin zan yadda da komai zaki fad'a ke kuma kiji tsoron Allah ki sanar dani iya gaskiyan ki,Waye mahaifin wannan cikin?" da sauri ta d'ago ta kalleta tace
"Wallahil Azeem ummu ban tab'a tarawa da wani namiji ba, ciki kuwa harda mijina *ALI ABBAS* bazan miki qaryaba ummu bansan mafarin wannan cikin ba, ban kuma san ubanshi ba" jinjina kai ummu cikeda al'ajabin wannan lamarin, indai har Manga ta haihu yaro ze bayyanar da ubanshi, amma tafi zargin Ali Abbas ne keson ya rabu da Manga yanzu kuma, qwafa tayi tace
"Maza jeki ki kwanta ki huta, domin kuwa bacci nakeso kiyi, kar inji kin sanarwa kowa wannan maganar domin Ali Abbas shine ze karbi wannan yaron......."
Batace komai ba se kurun ta kwanta badan tayi bacci ba sedan batasan mema zatayi ba. A b'angaren Ali Abbas kuwa yana zuwa d'aki wani baqin ciki datakaici ya tarnaqe shi, wato daga zuwansu india har wani ya hurewa Manga kunne harya la hanta mata rayuwa, shidai wlhy yaji gabaki daya ta sire masa arai, amma baze iya jayayya da hukuncin ummu ba....."
Yanda Manga taga rana haka garin Allah ya waye mata, koda aka kawo breakfast ma ko kallonshi batayi ba, tayi mamakin dalilin Ummu na qin zuwa ta dubata, tasani koda batazoba kullum takan aiko azo aduba ta, sabida main dakinta ba'a shiga da wuri wuri se ta fito....tana tsakiya da tunanin tajiyo sallamar wata hadima, d'agawa tayi ta kalleta ita kuwa ta zube a wurin
"Ranki ya dad'e Inji Fulany wai kifito zaku fita" Ba musu ta miqe ta sanya hijab d'inta ta fito tabi bayan hadimar har suka isa gun mota ganin Ali Abbas a mota ya mugun qara tayar mata da hankali, kallon Ummu tayi tace kanta aqasa
"Barka da kwana ummu" janyota ajiki ummu tayi dayake tana baya tace
"Lafiya qalau Autan Ummu Hafsatu Manga, Allah ya miki Albarka,yaya jikin kuma?" qwallah ne ya taru a idonta ta kasa magana, seda suka hau hanya tace
"Yaa Ali barka da kwana" A daqile ya amsa da "Lafiya" a tak'aice Ummu bataji dad'in yanda ya mata ba sam, gabaki d'aya tausayin Manga takeji sannan kuma batasan tonuwar asirin yarinyar, ta kasa gane kan wannan al'amarin amma sam batawa Manga tunanin bin maza, am mata shaidar halaye na gari sedai ko wani abin dabaze wuce qaddara ba, a yanda tayi lissafi ma da yan fashin sukai mata fyade da tuni cikin yakai wata biyar ai koma fi tunda aiba yau bane amma wannan daga ina, girgiza kanta tayi tana jinjina tunanin da me martaba yayi kai tsaye na kawar da wasu en Gulmace Gulmace daka iya tasowa acikin masarautar lallai wannan shikadaine mafita agaresu baki d'aya...... kai tsaye gidan Ali Abbas dake Arqillah gandu suka wuce, a babban parlor suka sauka dama babu wani na buqata a gidan sannan akwai hadimai, bayan sun zauna ummu ta kalleshi da kyau tace
"Agaban idanka me martaba ya gama zartar da wannan hukuncin lallai ka kula da matarka sosai da sosai, Banasan wannan maganar da qara tashi harseta haihu tukunna, alwai abinda muke zargi akan wannan cikin kuma ta hakanne kurin zamu kai ga gano me ake ciki menene ma'anar wannan cikin,tunda yake tanada hadimai kwanaki biyu zaka musu anan sekayi biyu acan d'inma kayi biyu kana dai jina ko?" gyad'a mata kanshi yayi cikeda takaici ta miqe kawai tace
"Autan ummu zan kiraki anjima, ayita zaman haquri kayan ki suna hanya, yanzukam kiyi zaman gidan mijinki shine mafi aa la agaremu baki daya, ban yarda da rashin kunya ba ko wani abin qi" Itama gyad'a mata kai kurun tayi batai magana ba daga nan ta fice, haka suka zauna shiru ita a tsorace shikuwa tamkar ya hallakata yakeji har wasu daqiqu da mintuna suka shud'e ba wani mewa waninsa magana, seda ya gaji dan kanshi sannan ya tashi ya shaqo wuyanta yace cikin fusata
"Tun farkon had'uwa ta dake tausayine ya rinjayi hangen muyagun halayenki a wurina, daga bisani kuma narasa da wane mugun tsafin naku na buzayen daji kika yi sa'ar sacemun zuciyata na soma sanki, na tabbatar da zancen huddy na baya a yanzu cewar ku d'innan mayune, banda haka tayaya iyayena da kansu zan rantse musu cewar ni d'innan bani na miki ciki ba, bansan da wannan qazantar cikin ba amma su nuna sunfi yadda da qarairayinki akan gaskiyar dana sanar musu, wlhy ku baqaen mayu ne masu muguwar zuciya, kuma ni bazan koreki ba amma baqar wuya ce zata sanya ki gudu daga gidannan da qafafunki, matsafa kawai masu bin mutane da baqar yadiya azzalumai masheranta" kuka manga ta fashe dashi iya qarfinta
"Haba Yaa Ali, banyi tunanin duk mutanen duniyar idan sun kasa yadda dani ba kai bazaka yadda dani ba, yaya kake qoqarin toshe idanka da kunnuwanka daga ganin zahiri wlhy ni bantaba aikata zina ba, kuma nida iyayena ba matsafa bane bakuma mayu bane" Tassss taji saukar wani gigitaccen marin da