Showing 33001 words to 36000 words out of 60927 words

Chapter 12 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt

masa yawa ainun.....

  Manga yau ta rasa nutsuwarta gaba d'aya ta qanjame ta bushe ta gama ramewa, abu mafi ban tsoro data kula dashi shine wayanda ta tarar a wurin wasunsu basa magana wasu kuma sunayi, kuma wanda suke maganar anrubuta musu one yr a goshi acikinsu ne ta kula mutum uku sun mutu, da zaran sun fara amai kudi na fita babu qaqqautawa se kuma su dawo suna kashi yana dawowa kudi harsu soma zawo daga nan se zawon jini, kan kace meye jini ta baki hanci da kasan su, se shure shure se kuma mutuwa, ba mutuwar bace abin firgita fiyeda yanda za'azo agabansu a cire ma gawarwakin wasu sassa a jikinsu ana wani ihu da wasu surutai kuma se gawar tasoma ci da wuta harta zama toka, sesuzo suna raye raye suna kwashe tokar, hankalinta ne ya kaita ga cewar da zaran kayi shekara daya kaima haka za'ama kenan amfaninka ya qare? In kuwa hakane ita yanzu watanninta shida a wurin......kuma saura mata shida,kenan musulmai bazasu sallace taba? Kenan baza'a mata wankaba a mata sutura  yanda akewa en uwa musulmai? Kenan dai ita da samun gatan mahaifinta ko mijinta ya sanya a qabari har abada? Kenan dai ita yanzu amaimakon amata salla matsafane zasu zo suna mata hauka akai? Sune zasuzo suna yayyab'eta suna yaga yaga da naman jikinta? Lallai tazo ta soma istigfari wataqila ta kuskurewa rabbu samawati wal ard ta wani b'agaren, ba kashin datakeyi ne na kudi ke damunta ba ko rashin abinci aa, wannan qasqantacciyar mutuwar dasuke yi....se a sannan ta soma tunawa da adu'o in daya dace ace ta somayI, se yanzu ta tunasu, aikam ta hau yi acikin zuciyarta sabida sam tunda tazo sedai zancen zuci bata magana gashi batama iya kuka, adu'o in ma data somayi yaune ta soma yinsu azuci dan duk ta manta da komai na addininta se yanzu.....

   "Haba Halima, tayaya zan zauna ina faman miki magana bakyaji, idan kinje yamai wlhy abakin aurenki, ban yarje miki zuwa yamai ba da wannan abin kunyar damukayi, ace kuma seda ermu ta b'ata zamu koma musu, ke bakida hankali ne, ki nutsu nasa ana mata adu'a kuma zata bayyana inshaa Allahu, ki kwantar da hankali wlhy na kiki alqawarin daga zaran ta bayyana zanje dake agadez inda en uwanki sannan daganan muje yamai a tare muma koma can gaba d'aya idan hakan kike so kinji?" ya qarashe maganar cikin sigar rarrashi, tana kuka ta gyad'a masa kai yayinda ya rungumota jikinsa gaba d'aya yana shafa bayanta a hankali......

   Yau Manga suna zaune aka kawo abincin su, kallon mamaki tawa abincin sabida bata taba kula cewar haka yake ba, tamkar dai an dafa tsutsa da wasu ruwa dabazata rabashi da majina ba, en uwanta se tutturawa suke yayinda ita kuma ta tasashi agaba amma ta kasa kai koda loma d'aya ne a bakinta, jikinta se wani qyarma yakeyi da alama adu'an da ake mata daga gida ya soma shiga jikinta ta soma gane cewar tana cikin hatsari tunda har take iya adu'a..... Dama wuri mafi wulaqanci aka ajiyesu qasa ce baki siminti, hannunta ta saka da taimakon fuck da aka sako saman abincin tayi gida ta zuba aciki ta rufa wurin ta zauna ta daddale da qafar ta ruwan ma koda ta kalleshi bada san rantaba da bismillah a zuci ta shanye, yunwa ce sun saba se bayan kwana uku ake basu abinci shima wani dan mitsitsi a wurin..... Tofa segashi kowa yana amai da kashi banda Manga, sam tunda bataci wannan abincin ba bata yi aman kudin ba ko kashin su, dataga haka kuwa tafi wata bataci sukuwa basu gane ba, tunda basa zuwa ebe kudin sedai su manga suga kudin suna bacewa da d'aya d'aya, acan b'angaren su kuwa sun kasa ganewa kan matsalar acewarsu sabida wanda suka mutu ne,dolene akawo sababbin d'auka.......

   *Bayan kwana biyu*

Manga na zaune zuwa yanzu abin duniya ya soma damunta, sabida zaman shirun yamata yawa, gashi yanzzu ta fahimci zata iya yin magana sab'anin da dasedai zancem suci, bazata mantaba tunda wayancan da suka mutu suka soma magana komai ya cab'e musu se mutuwa kuma, kuma ta kula an dena basu abincin kansu mutu kodai itama mutuwar zatayi ne? Ta tambayi kanta aikam rana ta farko se gashi tana hawaye, yaudai ta quduri niyyar sedai su kasheta seta hallaka su, a yanda ta lura mutane biyu ne kurun suke kawo musu abinci da ruwa sannan kowannensu bindiga ce saqale a aljihunsa, banda ita babu komai, Akwai wasu ruwa, data kula kullum suna wurin saman wata wutar dake waje da d'akin dasuke ciki, ta kula ba'a taba qara ruwan amma kullum akan sanyawa wutar garwasu kusan so biyar koma fiye, su kuwa ruwan sun dinga tafasa kenan batare dasun qone ba, qwafa tayi kurun, tayi sa'a mutum d'aya jal yazo kawo musu abinci, duqawa yake yana dire wa kowa abincin sa, a hankali cikin dabara ta kwanto key na kwad'on da ake rufe buglary din dasuke ciki dashi ta gama observing shine, ta b'oye a bayan ta d'aya daga cikin su ta ganta amma batace mata komai ba, haka ta nutsu a wurin zaman ta, gashi ko uwar manga ta ganta bazata gane taba yanda tayi wani mugun baqi ta koma wata qwarangwal sekace skeleton, haka ya gama basu abincin ya miqe ya rufe su ta waje suna kallonshi kasancewar bugler ne ya juya ya fita ya koma jan qofar ya rufe daga waje tan jin shiru ta kallesu tace

"Nasan duk kuna jina magana ne wasunku basa iyayi ku sani bazamu zauna muna musu kashin kud'i haka kawai ba, kuma amaimakon ma su barmu se su dinga kashemu daga qarshe su qwaqule mana kayan jiki su qona mu, ku bani hadin kai mu gudu, kunga key abu daya nakeso kuna bin umarnina a wannan tafiyar kawai kunaji na?" wasu daga cikinsu suka gyada mata kai yayinda wasun su suka qura mata ido ganin haka ya sanya tayi da turanci take suka washe baki anan ta kula wasun su qabi lune, bude kofar sukayi a hankali suka fito se suka rufe ta batare dasun saka key ba, dama wurin akwai yalwar duhu kam, can ba jimawa se gasunan sun shigo d'akin atare kwashe plates da cups dama haka sukeyi sannan sesu basu wani maganin da wani ruwa susha daganan se suyi bacci gaba d'aya....mamakin ganin wurin ba kwad'o suka soma yi, sannan kuma ya duba bega key ba sun kuma san ba window gashi basu d'aga daga bakin qofar ba sam konan da can, atare suka shiga inda su kuma suka fito da shirin su, suka rufesu da sauri da kwado dama b'oyewa sukayi a bayan durom da suke tsammanin na kero ne sunkai bakwai sebida dashi sukaga ake hura wutar, ruwan nan dake ta tafasa manga ta dakko ta d'agashi daga waje ta kwararawa shegu wata na tayata, sannan suka watsa garwasun daketa ruruwa suka sanya kwanon da ake dafa ruwan zafin dashi su tsiyoyo wannan man suka wasmtsa musu take wuta ta kama se ihu suke sukuwa sukayo hanyar waje da gudun su, amma sun kasa gane kan gidan ga wutar ta kai saman Roof seci takeyi, ta bangarensu suke jiyo ana yare iri iri ana kusanto inda suke, adu'o i manga ta soma yi iya qarfinta, sannan tace kowa ta riqe itace daya daga cikin wayanda suke wurin tace dasu idan sunzo ku riqa cewa Bismillahirahmanir raheem ku qwala musu,duk mutuwa zasuyi da yardar Allah, tanayi tana adu'a sega wasu mutane nan da jajayen kaya sunkai su goma suka nufatosu aikuwa Manga se adu'a take se kawai sukaga daya daga ciki yaje ya bude wata kofa yana cewa da harshen turanci su gudu kawai suna adu'a manga tace subi hanyar kawai Allah na tare dasu, gashi duk basa magana se ita kadai sedai zancen zuci, haka suka samu cikin ikon Allah suka fito daga gidan, sedai fa ga dukkan alamu acikin qungurmun daji suke, wanda baida iyaka, gashi lokacin sanyi ne kuma dukkanin su bamai riga ko wando basuda shi, wataqil wannan ne dalilin daya sanya ake kunna wannan ruwan,kuka kawai manga ta saka tace suzo su yanki daji kurun shine mafita gashi ita yunwa se addabanta yakeyi, bilhaq a haka suka darkaki dajin batare da sunsan inda suka nufa ba, a hanya mutum biyu suka mutu suna ji suna gani suka bar gawar anan, haka sukayi ta cin hanya seda suka kwashe kwana biyu suna cin dajin kansu kai ga titi, 35klmtrs to JEGA shine abinda suka gani a rubuce kan hanya,in hakane babu nisa da sokoto kenan,gashi lokacin a qiyasin su sha biyu na rana tayi, ga yunwa, haka suka isa wani qauye abin duk inda suka bi se ana gudun su waiga mahaukata ga mahaukata, wasu masu jin hausa sun fahimci kalmar yayinda wasu basu gane ba, manga se kuka take,kuma zuwa wannan lokacin duk suna magana, uku daga ciki yarbawa ne amma dukkansu kirista yayinda biyun ciki suke inyamurai suma kiristane....yayinda sauran suke musulmai kuma hausawa tantagarya, susu bakwai ne,biyun da suka rasu ne basu san qabilar su ba ko addinin su......


Haka suka taka har garin Jega kebbi state, Garine babba bazakace local govt bane ma sam, amma abin takaicin duk inda suka dosa guduwa akeyi, da qarfin tuwo sunzo wani shagon hijabai aka ka watse aiko manga ta janyo wa kowa daya manya har qasa tace su saka hakan kuwa akayi hijabai masu hannu dogwaye har qasa, sannan ta nufi wani shago tana zuwa gashi tayi wani zuru da ita tace

"Assalamu Alaikum" amsawa me wurin yana mamakin me jigi haka a tsaye harda baki radau

"Taimaka mana zakayi ka kaimu gun hukuma ko sarkin garinnan, wlhy yan shan jini suka kamamu, se bayan kwana uku abinci se yanzu Allah ya tserar damu muka yanko daji muka iso nan,gashi sabida muna tsirara kowa se gudun mu yakeyi, wannan hijaban ma wancen shagon dasuka gudu na kwaso mana su da kokai ka ganmu dole ka gudu anata mana kallon mahaukata" sosai ya gamsu da bayanin ta yace yana zuwa, yaje ya gayawa abokan kasuwan cinsa take aka rakasu gun sarkin Jega mutum adili me karamci, ba jimawa kuwa ya saurari komai da manga tazo mai dashi aka shigar dasu cikin gida aka basu abinci sukayi wanka sannan ya sake kiran Manga ya kula itace shugabar taron, haka yagama jin inda tafito cewar surukar sarkin musulmi ce yace ilai kuwa aranar zasu sokoto.........


Koda sarki yagan su sam be wayi Manga ba amma ya gane muryar kamar yasanta, haka ta bayyana komai se a sannan ya kula sosai manga ce, media da cops ya kira aka taru akazo jin zancen manga beko kira su ummu sunsan me ake ciki ba, kuka kuma agaban media yayishi sosai akan rashin kulawar gwamnati na tura sojoji yawon dazuka domin ceto rayuwar bil adama da ake sacewa ana cutar dasu, kowa yaga Manga baya shaidata seya qura mata ido, farin ma babu shi ko kadan ga kan qwam ba komai a ciki, a wannan lokacin kuwa Ali Abbas na bangaren su ba lafiya ko tashi da qyar yakeyi duk akan rashin Manga....


Sanda aka kaisu dukkansu gun Ummu ba qaramin kuka tayi ba,kuma karo na farko kenan dataje da kanta b'angaren su huddy tun bayan aurensu, ta sanar wa Ali Abbas yanda ake ciki cewar matarshi ta dawo ga bayanin labarin ta, sega mara lafiya a tsaye lolxxxx ba shiri ya bazama bangaren ummu, yaudai har Manganshi da kanta ta rungumeshi agaban ummu tana tsananin mamakin ramar dayayi da baqi sosai.....

Mom Nu'aiym.......

Vote plssss
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS👑*

*Billy Galadanchi*

*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*

*Ina godiya sosai pheey da alkhairin ki, Allah ya saka miki da alkhairi ya bar qauna,wannan shafin nakine ke kadai kiyi yanda kikeso dashi*

16
Koda Ali Abbas ya d'ago ya kalli Manga yaga yanda ta dawo se kawai ya sanya wani kuka me ban tausayi, wai Manganshi ce ta dawo qwarangwal tamkar ka busa ta fad'i, manga fara ta dawo baqa, Manga gajeruwa ce sedai ba cancan ba amma fa yanzu gabaki d'aya tayi wani tsawo sabida a bushe take, juyawa yayi ga ummu yana kukan yace

"Ummu kalli abinda aurena ya janyowa Manga? Kalli dalilin aurena abinda Manga ta zama, sam wlhy ban cancanci zama mijin Manga ba, tun ranar dana tsoma rayuwata acikin tata take fad'awa iftila'i iri iri, dana riqe igiyar aure da muhimmanci dabata shiga cikin wannan masifar ba,yanzu mezance wa iyayenta irin wa ennan musibun haka" hannunshi ummu ta kama

"Ka nutsu babana ka sani sarai bakajin dad'i godiya ya dacewa kawa Allah daya dawo mana da ita da rai dan bazamuce da lafiya ba sedai adu'a kawai, yanzu me martaba yace a dauketa a je da ita asibiti su mata qarin ruwa da sauran gwaje gwaje, sannan ta kwanta ta huta acan kuma dole amata adu'o i sabida sharrin matsafannan dabazamu san me suka mata ba ajiki, idan kana haka ita kuma fa ya zataji? Ka nutsu kawai kamata adu'a" shiru yayi yana me tsananin tausayawa Mangan shi.....

*Bayan kwana bakwai*

     Inno kam tasha kukan ganin yanda Manga ta dawo qata abar tausayi, tamkar ba ita ba, gabaki d'aya halittarta ta sauya dukuwa da yake sunzo ne bayanda komai ya lafa awurin manga sabida a kwana biyunnan harta wartsake ta soma cikowa, Kallonta tayi bayan kowa ya wuce adakin asibitin daga Manga se Inno tace da ita

"Mangan Innoh yau dai zan sanar miki tarihin rayuwata data mahaifinki abinda kika dad'e kinaso kiji, da farko dai mahaifinki sunanshi Ibrahimou Ahamadou mousa, sanin kowane har yanzu Ahamadou mousa shine sarkin garin yamai dake qasar Niger wanda tun shekaru arba'in dasuka wuce shine akan karagar mulkin, mahaifinki mutum ne da yake da kyakyawan usuli kasan cewar sa d'a d'aya tilo a wurin me martaba sarkin yamai Alhj Ahamadou mousa, yasanya ya taso a sangarce kuma cikin gata mara iyaka, tun a wancen lokacin a wajensa yayi karatu acan france, bayan ya kammala karatunsa ya dawo ya had'u da wata yarinyar er bawan gidansu,soyayyar gaskia ta haqiqa yake yiwa Aicha  kazalika itama tana tsananin sansa, sun gama shirya cewar zasuyi aure yaje ya gabatar da ita awurin me martaba, amma qememe me martaba yaqi amincewa da buqatarsa, babu yanda beyiba,ba wurin wanda be jeba amma me martaba yace baze taba zubar da martabar masarautar saba ta hanyar  aurawa sarki me jiran gado yar bawa ba, daga qarshe dai ina zaman zamana, mahaifina wanda ya kasance sarki a jihar agadez dake Niger ya umarceni akan auren d'an sarkin yamai,ni a wannan lokacin banida wani tsayayye kasancewar bama inda nake zuwa, dayake ni nafito a cikin dangi gaskia ba kamar mahaifinki ba dayake shi d'aya tilo ba wa ba qani awurin mahaifinshi da babarshi, Ranar daya soma kawomun ziyara yamun gargadi akan nace bana sanshi, ya sanar mun lallai zanyi bankwana da farin ciki kamar yanda zanyi bankwana da en uwana duk na sake aka daura aure na dashi, ban baiwa maganarshi muhimmanci ba haka kuwa aka daura aurena dashi bayan ansha biki na tare da kwanaki tara ranara ya tasheni da dare  a haka ya sakoni a kotarsa muka bar gidan su, washe gari kuwa da kanshi ya tuqomu har Nigeria muna iskwa yaje ya sayarda motarshi munsha wuya sabida bamajin hausa sosai... Haka inaji ina gani mahaifinki yace tunda yake sarakuna basa san yaransu suna rayuwa da talakawa,kuma suke tauyewa talakawa haqqinsu suna nuna cewar lallai talaka qasqastaccene to kuwa se yaransu sunyi rayuwa irinta bayi ya da sukeji idan an wulakansu seya saka suma an musu koda iyayen basu sani ba dai yasan ammusu, da wannan ya nemi gadi sabida baya sona ya sanya duk sanda nayi ciki ya asa masifa kenan akan sena zubar kafin ya zubar se kiga cikin yafadi da kanshi, haka dai inata hakuri sabida yace idan nayi yunqurin komawa garinmu abakacin aurena nidashi, harna samu cikin ki, cikin ikon Allah daga ni harshi bamusan da cikin ba sabida ina al'ada ta har tsawon watanni sannan na soma jin motsi naki gaya masa, har seda cikin ya bayyana kanshi lokacin yakai watanni 6 abin mamaki senaga yana murna tun lokacin daya san da cikinki sena soma ganin sauyi tarayraya ta yake yana kuma nunamun kulawa matuqa, ban damu ba dai haka naita daurewa da halayenshi, dama ni gaskia inasan iro wannan ma yasa sam ban ganin laifin sa ko kadan a irin azabar dayake ganamun,a haka harna sauka lafiya, zan iya cewa soyayyarki ce ta haifeni wacce harta sanya komai na yanayin qiyayyar da mahaifinki yakemun ta sauya zuwa soyaya me ban mamaki, a haka a haka dai har kika zama abinda kika zama yanzu, babu yanda bana roqarshi akan komawar mu gida amma sam yaqi, se wannan lokacin ya yarda da zuwan mu gun en uwansa, a yanzu haka daga zaran kin murmure tare dake zamu tafi" mamamakin jin asalain su ya kama manga ta jinjina kai kurin tana me al'ajabin halayen mahaifinta na kafiya.....babu kalan gatan da Manga bata samu har aka sallameta ta koma gida, babu wanda ya qara zancen tafiyar su Niger seda tayi good 2 month ta dawowa jikinta tayi kyau sabida hutu gashi ana yawan mata adu'a se ta dawo tamafi da yin kyau da komai, a wannan lokacin kuma baban Manga yayi bayanin komai wa me martaba dan gane da asalinsa da dalilin barowarsa gida dakuma dalilinsa nasan komawa sabida ya nemi gafarar iyayenshi musamman mahaifiyarshi da mahaifinsa, ya kuma roqi alfarma abashi manga domin ya gabatar da ita wurin mahaifansa, ba gaddama Ali Abbas ya amince da zancen tafiyar yaso ya tafi tare dasu amma se me martaba yace tunda sunce wata daya zasuyi ya bari in zasu dawo seyaje su dawo tare.....

   Sun jima a tsaye suna kallon kallo tsakanin Ali Abbas da Hafsatu Manga, lallausan murmushi ta sakar masa, ta gama sakewa Ali Abbas ragamar zuciyar ta, ta gama yadda yanzu wahalar da kanta kurun takeyi Ali Abbas shine masoyinta,bazata rayu bashi ba, huddy da kanta ta sanar mata kalar azabar  dayasha akan rashin ta har ciwon hawan jini ya kamashi, tace cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login