Showing 18001 words to 21000 words out of 60927 words
Chapter 7 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt
tashigayi yanda duk kuka zauna da ummu seta maka zancen marigayiya hafsa amma ace wai Ali be sani ba, lallai ma akwai rashin adalci
"yanzu ummu ko in kulan dakike nunawa Ali harya kai nan, qanwar shi ahaifeta be sani ba tayi shekaru uku a duniya kuma harta mutu be sani ba, gaskia yaya fulani ki sauya wannan kunyar kema shaidace iyayenmu ba haka suka miki ba koda kike ta fari kuwa" bata daice komai ba sabida itama mamaki take ace wai be sani ba, tama kula har qwalla yayi dayaji maganar ita kuwa harga Allah dalilinta na qara shareshi harda rashin gaisuwar dabe mata ba sanda Hafsat ta rasu, bata daice qalaba har mariya ta gama mai bayani ya tashi abubuwa biyu suka masa tsaye, na farko zantukan manga da ummu, na biyu zancen qanwarsa dabe masan da ita ba arayuwa.........
*Kaduna Nigeria*
Tunda Manga ta dawo take shirye shiryen zuwa court araba auren batare da Ali ya sani ba, ana i gobe zaman court d'in Huddy ta sanar masa, ai haukace mata yasoyi, kuma da qyar 4 na asuba nayi yace mata zashi kaduna, bata tsaidashi ba se adu'a data mishi taji komai tun a ranar daya bi manga dakinta sanda batada lafiya, daganan ta soma bibiyars u harta gano shine mijin Manga na zahiri kuma tabibiyi diary d'inshi daya rubuta komai koda ya mutu, tasha kuka kam amma yazatayi ita lafiyarta ma take nema gata da ciki wata uku, tasan arina tadaice bazata nuna masa ta sani ba tunda shima yamata biriss ........
A kotu kuwa alqali yagamjin zancen iyayen manga na buqatarsu ta raba auren ta huta tunda ga yanda abin ya zama kuma babu labarin shi har yanzu, katsam sega gadanga a court hall d'in, mamaki daddy yaji wanda kan ya isa garesu har Ali ya soma daukar excuse a wurin alqalin, batare da b'ata lokaci ba ya zayyane musu komai har kayan da mask duk yazo dasu bayan ya gama bada labarin daya kashewa ilahirin mutanen jiki ya basu mamaki ya qara da cewar
"Yanzu na gane kuskurena kuma na mata bayani tun a sokoto amma taqi ta saurareni, ina san matana yame shari'a dan Allah wannan kotu me adalci tayimun sassauci abani matana mu tafi da ita" kan alqalin yayi magana Manga ta soma bori
"Wlhy bazan tab'a zama da macuci irin ka matsayin mijiba, ko gawana aka kai maka senayi wa wanda yakai Allah ya isa koda kuwa iyayena ne, kasani wlhy babu wata shari'a a doron duniya dazata tilastani zama dakai mugu kawai, bakai bane gadangan dana aura fuskace, fuskar kuma qaryace kamar yanda fuskar take qarya, haka na dauki auren matsayin qarya, soyayyar danawa gadangan ma qaryace, kayi wasa da rayuwata sabida ina talaka, bazan qara dama ta biyu ta jefani cikin qunci ba wlhy, kasani wlhy zan nemo koma a inane na biyaka duk abinda ka kashe amma bazan lamunci zaman aure dakai ba" tsawa alqali ya daka musu suka nutsu a tare.....
Mom Nu'aiym...
[7/6, 8:08 AM] +234 706 571 7620: *Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS 👑*
Billy galadanchi
Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*
*Zainab S Abdul* wannan shafin nakine kyauta Allah ya bar mun ke*
08
"Kai Aliyu bakajin kunyan abinda ka aikata kana yaro dan gidan masu mulki, kake sakin wannan wawtar har haka, yanzu me zaka sanar da mahaifinka? Kasan inda wannan labarin zekai kuwa? Baka da labarin zubewar girman sa kake kira da hannunka?" sadda kanshi qasa yayi duk yanda yaso ya had'iye seda yayi qwallah, da qyar ya iya furta
"A gafarceni yame girma me shari'a" gyaran zaman tabaraun shi yayi sannan yace
"Zan baku dama kuje gida ku sassanta kanku, idan hakan be yiyu ba kuma seku dawo nanda sati biyu* ba haka Manga tasoba ba kazalika Baban Manga ma ya shaqa sosai ranshi ya b'aci ainun, haka suka kwasa zuwa gida rann daddy ma a b'ace a parlor suka zquna dukansu har manga da Ali, daddy ne ya soma magana
"Amma Aliyu tabbas yau ka shayar dani mamaki mara misaltuwa.... Ban tab'a tsammanin haka daga wurin kaba ka aikata aiki irin na marasa ilimin addini, kayi wasa da igiyar aure matuqa dakasan haka dabaka bari an d'aura muku aure da itaba, kaiba yaro bane tunda ai ita huddy ka bata haqqinta har tanada yaro da wani cikin yanzu, kasan cewar koda mazan tabi batada laifi sabida tanada jiki ajiki, ka kuma yi yaudara wannan ma ha'inci ne babba da zalinci had'ida cin amanar zaman tare, banji dadi ba kuma wai harni ka mayar gaula ka kwasheni mukaje har soba yawon neman ka bayan gaka tare dani, gaskiya kazo da salon raini kuma babu abu da zan b'oyewa me martaba, ku shirya gobe har Baban Manga zamuje wurin me martaba shida kanshi shine zeyi shari'ar nan" d'agowa Ali yayi da sauri
"Dan Allah daddy karka mun haka ka rufa asirina wlhy me martaba ze iya tsinemun ka taimakamun ka rufa asirina mubar wannan maganar anan" kallonshi daddy yayi cikin takaici
"Idan kai bakasan haqqin d'an adam toni na sani, kaciwa yarinyar mutane zarafi itada iyayenta wlhy seka sani, nima akwai hukuncin dana tanadar maka me qwari semunje wurin me martaba" matsawa yayi kusada Baban Manga
"Baba dan Allah ka ceci rayuwata, bawai zuwa wurin me martaba din ba ne matsalar, wlhy nasan zab'in manga zebi cewa zeyi sena rabu da ita, ni kuwa wlhy bazan iya rayuwa babu manga ba, itace farin cikina tun a baya dan Allah ku taimakeni karku je da maganar nan wurin me martaba" Baban Manga ya kalleshi
"Lallai ka dade sosai kana bani akan yawan hidimarmu da kakeyi, nazata duk kanayine sabida tausayin manga, ashe kai munafiki ne kaine kasanya yarinya me juzari irin manga ta kasa sukuni ka siyar mata da nutsuwarta, ka sani bazan hanaka matarka ba indai tace ta zabi zama dakai, amma wlhy dazaran tace batayi seka saketa tunda babu wani adalci atattare dakai" Yaudai sega sarki me jiran gode yana rarrafe yana roqon gafara, Manga dai koci kanka batace masa ba yau shiru tamai harya ida magiyarsa, ta tashi ta wuce wurin Innoh dabatasan me ake ciki ba itada matan alhaji, sundai san anje kotu amma basusan labarin dake gudana ba, Baban manga mane daya shigo yake zayyane mata komai itadai matsayin ta na uwa nunawa baban manga tayi lallai abar manga ta komawa aurenta yafiye mata yawon zawarci anata ganin kedai......
Bayan isha kai tsaye Aliyu gidan baban manga ya wuce, suka gaisa tamkar ba komai yace dashi manga yakeso yae magana da ita Baban Manga yace
"Ali ai bazan hanaka ganin manga ba tana ciki ka shiga, d'akinta a tsakiya" godiya yayi ya shige ciki da sallamar shi, Innoh ya fara cin karo da ita ya sunkuya har qasa ya gaidata, mamakin sake masa fuskar datayi yake harya miqe ta dakatar dashi, ya koma ya sunkuya gyaran zamanta tayi saman kukerar tsuguno da take kai sannan tace
"Nasani Abinda kayi sam bame kyau bane kuma matsayin na mahaifiyar manga lallai banji dad'iba sam, amma abu d'aya nake roqon ka shine, naji ance ka dage akan zaka zauna da ita, to dan Allah idan kasan baso aranka na Manga ka sauwaqe mata tayi aurenta da wani, amma indai kasan zaka zauna lafiya da ita kakuma riqeta amana kaci gaba da rarrashinta nima zan tayaka" sunne kanshi yayi qasa
"Inshaa Allah innoh zan riqe Manga amana wlhy ina santa tsakani da Allah, wannan ma rashin tunani ne nayi kuma inshaa Allah hakan bazata qara faruwa ba" jinjina kanta tayi
"Kaje Allah yamaka Albarka tana d'akin tsakiya nanne nata" Ameen ya furta cikin jin dadin furu cinta ,sannan ya wuce ciki kai tsaye, yayi sallama a qofar d'akin daga ciki aka amsashi,batare datasan ko waye ba tace "Shigo" zabura tayi sanda ya qaraso cikin dakin, dukda yake doguwar rigar atamface ajikinta amma ba d'ankwali akanta, tsaye yayi yana kallonta harta rarumo hijab ta saka
"Mekazo yimun a d'aki?" matsowa yayi kusa da ita
"Hilwa dan Allah ki saurareni" kallonshi tayi sosai amma batayi magana ba
"Dan Allah Hilwa idan munje gun me martaba ki tallafi rayuwata kice kina sona kinaso ki zauna dani, Manga wlhy bazan rayu ba idan baki dan Allah kiji qaina" kallon sheqeqe ta masa
"Kasan Allah Aliyu, wlhy babu wani abu me kamada rayuwar aure dazanyi dakai har abada, bana sanka na tsaneka, na tsani ganinka, wlhy abisa umarnin daddy ma zan tsaya har wani aje sokoto, kasani wlhy qiri qiri zance dashi basonka araina aure kuma indai muddin ina numfashi an rabashi an gama, gwaramun inga gawata da inganni a d'akinka wlhy Aliyu, macuci irinka a mutanen dana tsana duniya banda shed'an bana biyunka a zuciyata, macuci kawai" matsawa yayi kusa da ita sosai ya riqe hannunta "Haba Hilwa anason mutum me yafiya dan Allah ki tallafi raina kinji" harara ta wurga masa
"Wlhy Abbas kayi kadan ka sake wasa da tunanina, kayi yanda kaso da rayuwata sanda banda enci amma yanzu kam wlhy nafi karfin ka kaji na gaya maka, ka sake mun hannu wlhy karnama rashin mutuncin daze sanyaka mamakin gaske" Jiki a mace ya saketa yace
"Hilwa ki tausayamun karki cutar dani" tsaki tayi ta shige ban dakin dake cikin bedroom din ta barshi tsaye, jiki ba qwari ya fito ya jua zuwa masaukinsa gaba daya ji yake tamkar ya zunduma ihu tsabar tashin hankali.......
Manga na zaune tana danna wayanta kiranshibya shigo rejecting tayi haka ya dinga kira tana rejecting har kusan so biyar, messega ya sending mata
"Dan girman Allah ki dauki wayana Hilwa" tsaki taja ta kashe wayan gaba daya, ana haka sega mamanta ta shigo d'akin zaune ta tashi tace
"Sannu innoh" tafada yayinda maman tasha mur
"Manga wato ke kinfi so ki kasance cikin tsinuwar Allah da mala'ikun sa ko? Ki sani wlhy nida kene labarin kince mijinki ya sakakeki ya qara zuwarmun, ke mahaukaciyar inace, ke mijinki tafiya yayi ya barki nu kuwa yanzu shekarunki ishirin da biyu a duniya ni kuwa shekaruna sunfi 30 banga iyayena ba, akan laifin dabasu sukayiba bakuma ni nayiba, tunda na aureshi akan bani yakeso ba wata er uwarshi yakeso ya kwasoni mukazo nan hukuncin kenan dayake mana nida iyayena da nashi iyayen, akwai baqin cikin dayafi ka zauna ka tara 'ya'ya tare da mutum amma ace ba sonka aranshi, har akan qiyayyar dayake maka dan an masa dole yabaro gidansu kaima ya sanya ka rabu da naka gidan, bansan halin da kowa nawa yake cikiba, ko iyayena suna raye ko suna mace, ki sani wlhy bazan yadda ki kashe aurenki ba dolene ki zauna da Ali Abbas koda bakyaso, kece nake saka ran zaki sadani da mahaifana, ke bakya ma kallon rayuwarmu bamuda dangi akusa damu sekace wasu mayu, maganar ta karshe da zan gaya miki itace, idan har kikace bakysasn mijinki kinaso araba auren to bani bake har abada kuma ban yafe miki ba" da sauri ta kalli Innoh, ita kuwa ta miqe ma tabar dakin, kukan kam ranar Manga tasha shi ba iyaka seka wacce akace gobe zaki mutu.......
Qurawa Ali Abbas ido me martaba yayi bayan gama jin bayanin daddy, sannan ya nisa ya d'aga wayarshi,fulani ya kira ba jimawa segata ta qaraso a fadar, zayyane mata komai yayi sannan yace
"Dukkkanin abinda yaron nan ya aikata arayuwa laifin nake gani, tarbiyar yara kacokam an d'aura ta akan iyayene mukuwa maza maza sabida nauyin ayyukan dake kanmu muka baku ragamar komai, haqiqanin gaskia kinyi mun sakaci da tarbiyar yaro kuma ni yanzu dagake harshi kun janyomin tozarci mafi muni na tabbatar wannan abin seya tabamun mutuncina a idon duniya, dakinja shi ajiki dole ne ya sanar dake damuwarshi koya nemi shawararki yanzu wannan haukan dayayi wa gari ya waya??" duqar da kanta tayi cikin b'acin rai lallai seta koyawa Ali Abbas hankali
"Me martaba dan Allah a gafarcemu,inshaa Allahu hakan bazata qara faruwa ba" murmushi yayi sannan yace
"Ke hafsatu sanar dani kanki tsaye zaki iya zaman auren dashi ko kuwa?" sadda kanta tayi qasa batace komai ba" daddy ne yace
"me martaba ni inaga abar Ali da matarsa tunda ya buqaci hakan, ita manga dama tanaso sanda akai auren ai" shiru me martaba yayi can kuma yace Baban Manga
"Malam Iro menene ra'ayinka game da auren erka da Ali?"
"Ranka ya dade inaga abar musu aurensu Allah shi kadai yasan ma'anar yin hakan" godiya sarki ya masa ita kuwa fulani tace
"Ranka ya dade ina roqon alfarma abani dama na hukunta Ali Abbas daidai da laifinsa,sabida ya cancanci hukunci gaskia" Murmushi me martaba yayi yayinda qirjin Ali Abbas yayi mugun domawa sabida yanda takira sunansa kanta tsaye yaune karonta na farko data furta kalmar ita kanta ta sani tun bayan da aka sanar mata sunansa, ya tsorata ainun da yanayinta ba kad'an ba, kasa daurewa yayi ya duqar dakai sosai
"Ummu dan Allah ayimun sassauci" banza ta masa,me martaba yace
"Kije kimai hukuncin daya dace dashi kowane irine injini, kuma hukuncina na gaba shine karka kuma zuqarmun nan koda gaisuwane she bayan shekara daya idan ka nutsu ka tariyo cewar addinIn Allah na tura saudia ka koyo ba wofintar da aure ba" kuka Ali Abbas ya soma yayinda kowa ya watse har me martaba aka bar shi shishi kadai a fada.....
*Bayan sati Biyu*
Har yanzu huddy babu wanda ya mata zancennan domin daddy yasan halin Amminta bata barwa Allah lamuranta, ko Ali Abbas be mata zancen ba ita kuwa bata nemi sanin komai ba........
Ali kuwa tunda aka gama wannan zaman rabon dayaga Manga koya samu wayarta, gabaki daya hankalinshi ya gama tashi, gashi baze iya tambayar fulany ba waneshi ma tunda bata amsa gaisuwarsa, idan yaje bangarenta ma bata fitowa,yakuma bincima an tavbatar masa Manga bata gidan......
A adamawa Manga nacan cikin dangin mahaifiyar Ali Abbas tana samun gata da kula na musamman, ba laifi tanajin dadin zamanta dasu........
Mom Nu'aiym
Kuyi hakuri da wannan se kuma gobe inshaa Allah..
[7/6, 8:24 AM] +234 813 124 3554: *HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Sadaukarwa gareki qawa ta gari Fulany saddy*
*Ina baran adu'arku mamana batada lafiya*
09
Zirga zirga Ammin huddy keyi tamkar me yunqurin naquda, gabaki d'aya hankalinta ya tashi jin wannan xancen da daddy ya gaya mata, tayaya ma d'iyar wulaqantacci irin su Baban Manga zata auri d'an sarki even so ma ace wai kishiyar erta, ina Manga tayi matsayin dazatayi kishi da Hudaisan ta? Ina ita ina matsayin likita? Wacece ita dazata yi wannan haukan? Wato ma cutar ta Manga keyi duk zaman da wannan munafukin mijn na huddy yakai Manga gidansa tanayi ashe zaman aure suke, Allah ne ma be bata haihuba kenan da yanzu ta haihu..."Wlhy indai ina numfashi baze tab'a yiyuwa inbar auren nan na su ya d'ore ba, sena ga bayan wannan mangar sena wulakanta rayuwarta sena sanya ta gudu da qafafuwanta daga Nigeria gaba d'aya, dangin ubanta da uwarta zata koma koma ta shiga duniya, da wanne huddy zataji a rayuwa?" kwafa tayi bayan data gama sambatunta tabar cikin dakin ta dauki wayarta ta dannawa huddy kira.....
" Amma ke dama huddy kinsan da wannan kika qura ido kika yi shiru? Sekace wata sokuwa mara hankali da wayo? Sekace bani na haife kiba, yarinya sakarya kawai mara wayau"
"To Ammi niya zanyi? Wannan qaddararmu kenan nida ita, tun anan na qara gane Allah shi karimun rahimun ne, saboda bantaba zata inda na sanya qafa Manga zataje ba,segashi wai itace uwargida yayinda nake binta abayan baya ma, Dan Allah Ammi nasan halinki karki soma shiga hurumin Allah wlhy niba ruwana, tunda har gobe mijina yana matuqar kulawa dani kuma yana sona ba iyaka, kimun adu'a akan rashin lafiyata domin ni ina ganin haske sosai a lamarin ina kyautata zaton cewan akaina za'a samu masu cutar cancer wacce zata warke" tsaki taja
"Nafi kowa sanin inshaa Allahu mutuwa ba yanzu ba, kuma indai cancer ne zaki warke sumul, abu daya nakeso ki gane shine wlhy indai ina raye sena raba auren manga da yarima, ke bakya ganin ma tamkar duk zaman da tayi a gidan ha'intar ki sukeyi?? Lallai ki kama kanki wlhy banza sokuwa wacce batasan ciwon kanta ba"
"Nidai Ammi bazan dena miki nasiha ba wlhy, kuma duk abinda zaki aiwatar indai danni ne kidena banso, sannan idan har bakijiba kika aikata wlhy nidai ba ruwana ko a wurin Allah" tsaki uwar tayi ta kashe wayar abinta...
A yola kuwa Manga ta soma shiga damuwa sabida kusan watanninta uku kenan, batasan ma'anar kawota yolan da akayi ba, gata dai cikin gata na musamman amma sam bata jin dadin gatan, wani yammaci tana zaune a d'akin matar data fahimci itace kakarsu Ali sabida yanayin kamannin dasuke da ita se kawai taji sallamar fulany, rungumeta tayi hadda shagwab'a ita adole se bayan sun huta sun natsa sannan fulany tayi kiranta da ban
"Auta nasan bakisan dalilin daya sanya nasa aka kawoki yola ba, nakuma sani bakisa dalilina na sanya ake ta miki gyare gyare ba,ki sani abu mafi farin ciki arayuwata shine samun labarin cewar ke matar yaro ce, bantaba samun farin ciki ba makamanci sanda naji wanda labarin, nasan zakiyi tunanin naso kaina da yawa ace duk abinda ya miki inaso ki koma masa amma ki sani na fahimci kece kadai zaki zamto abokiyar shawarar yaro, kece nake sakaran zaki daurashi akan turban danakeso duba da yanayin tarbiyarki da halayyarki ta kirki, ko tashin Ameer ina sane da yawan adu'o in da kike koyar dashi komai ya iya,daidai da toilet wannan bayajin dadin shigarsa se yayi adu'a bacci ma seyayi adu'a,ina sane da komai....ki sani Auta na dade ina burin inga an raba aurenki da mijinki daya bata in sanya Ali ya aureki koda bayaso, yanzu danasan ke mallakinsa ce bazan yi wasa ya rasa uwar 'ya'ya ta gari ba, hikima ta kawoki tanan shine domin dalili biyu, na farko inaso ya d'and'ani azabar da kika d'and'ana daya barki wannan