Showing 54001 words to 57000 words out of 60927 words
Chapter 19 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt
tarar da wannan cup da irin qatuwar tsutsar nan me gashi aciki, masu sanya gabaki daya quraje su fito ajikinn mutum, shine fa nacewa buwa a jefar da cup din shine wannan matar ta hauni da zagi wai ba ubana bane ya siya mata kayan dazance a wurgar, nabata labarin illan tsutsar shine fa zagi ta uwa ta uba tace a jefar da tsutsan a wanke mata cuo din ta,yanzu sabida taga qarshena shine ta zuboma ruwa aciki,nikuwa bazan bari kasha ba wlhy" Kallon sa ya mayar ga huddy daketa mayarda numfarfashi cikin kasala, taji dadin rufin asirin da manga ta mata cox wannan dukme sauqi ne ai
"Mesa zaki kawon ruwa acup din to? Sabida kishi ne kokuma kasheni kawai kikeso kiyi?" matsawa tai kusa dashi ta kamo hannunshi
"Haba Abbi yazakace inaso in kashe ka? Nice fa hudaisan ka Abbi, wlhy mantawa nayi dabadan haka ba dana kawo ma a wani dan Allah kayi hakuri" murmushi ya sub'uce masa ganin dukta damu lokaci d'aya ya gaskata cewar kuskure ne da mantuwa
"Shi kenan a kiyaye gaba plss,irin wannan qwarin sunada had'ari kinga be kyautu ace ana mantawa da inda sukaje ba,gashi damunane be tsaya ba suketa yawo,zansaka ayi maganin feshi seku koma dayan bangaren na kwana daya" yana gamar fadan hakan ya koma cikin parlor din ya zauna abinshi......Juyawa huddy tayi dakinta manga tabi bayanta...
"Aunty huddy inasan sanin ruwan meye kika zubawa yaa Ali tare da swan kikeso ki bashi yasha?" kallonta huddy tai
"Manga wai ina wasa dakene?" murmushi manga tai
"Bakya wasa dani amma kina qoqarin cutar da mijina, na duba darajar su Ameer ne ya sanya kikaga na rufe tukunyar asirinki, wlhy kiyi a hankali da bin bokaye da malaman tsibbu inba haka ba wlhy nida kene a gidannan, sabida bazaki zauna kina cutar dashi ba a banza, daga kin gano matar ceni duk kin sauya halaye ina kallon ruwan da kika zuba a cup din baqi ne qirin kina sanya swan suka hade suka dawo fari, wlhy tsafine kurin zeyi wannan kuma kiji tsoron Allah kina aikata shirka a banza a wofi sabida san duniya" kasa magana Huddy tai tagano manga taga komai asirin ta kurun take rufe wa,juyawa manga tayi Ali ma dake bakin qofar ya koma ya zauna da sauri jin shiru alamune na juyowa za'a fito yana mamakin sauyawar halin huddy gakuma mamakin wai baqin ruwa ya sauya launi zuwa fari a cup, manga na fitowa tagama fusata shi d'inma bata kalleshi ba ta nufi d'akinta, tana zuwa dining ta manta zancen kwalbar cup data fashe ta taka daya qara ta k'walla ta sunkuya a wurin riqe da qafar, da sauri ya taso yazo ya riqeta yana tambayar ta lafiya, qafar data riqe ya kall,glass din ya kafe a ciki yana ta zubar jini, ya sake kallon ruwan a saman farin tile din sunyi baqin qirin dayan barin kuma fararen ruwa na gangara wanda sukai baqin kuma sun cure wuri d'aya, mamaki sosai yake huddy kasheshi zatayi kenan?? Akan tagano tanada kishiya anya ba manga ya dace tai wannan haukan ba kuwa? D'agata yayi zuwa kan kujera ya cire mata glass d'in a qafanta sannan yace yana share mata jinin da hanky dake hannunshi
"Baki kula da glasa d'in bane Hilwa?" qwallan datake tarewa ne ya silalo mata ta sanya hannu ta share su sannan tace
"Shap na manta wlhy banma kulaba" cikin tausayi yace
"Sannu Hilwa inaga se munje chemist ko hospital ma deep ne abin" kwab'e fuskan ta tae
"Yaa Ali me zasumun acan,dan Allah karka kaini,ka sanya mun kananzir jinin ze tsaya" harara ya wurga mata
"ke kina haukane kananzir kinsan chemical nawa ne aciki,maza ni ki tashi mu tafi" tabare fuskan tayi lokaci d'aya sega hawaye sharr be kulata ba ya d'agata suka bar gidan zuwa hospital har lokacin yana tsananin mamakin mugun abinda huddy ta aikata masa ko meye ribar ta oho......
Har akai kwana biyu baya kulata tayi ba ban vaki har ta gaji ya gagara sanar mata me kunnen sa ya jiye masa, ko Manga be sanar wa komai ba game da yaji zancen su, haka ya shirya ya wuce batare daya koda kulata ba ko mata sallama, abin duk yabi ya dameta, Manga ma bayan kwana d'aya ta sameshi a lagos da jirgi ta tafi....
Ammyn huddy ce tsugune a gaban boka tana sanar masa komai yanda ya faru, bayan ya gama saurarenta ya soma bugun qasa da kuma bincike binciken sa, a haka ya gano tare sukai tafiya ma suna dubai, ya gayawa Ammyn huddy ya qara da cewa
"Aljani zan tura ya shiga jikin ta ya sanya tae wata qasar daban daba tamuba bakuma inda ya dosa ba dan daganan Madina zashi, to tsayawa saka masa qiyayyar ta b'ata lokaci ne sabida haka zamu sauya akalar rayuwarta zuwa wata duniyar tare da sanya mantuwa a cikin kanta na duk wani abu data sani har abada" murmushi Ammyn huddy tae
"Madallah mun gode, yanzu meye ladan aikin?" wani zabura yae yace cikin ihu
"Mahaifar erki shine ladan aikin, idan kinso ki amince nizan tura a cirota idan kuma kinso ki gayamata, sedai zata iya yi mana gaddama"
"Nima 'ya'ya na nawa a duniya, ta samu mace da namiji, sun isheta rayuwar duniya aciro mahaifar aiba dole" wata mahaukaciyar dariya ya kwashe da ita yace
"Kije angama karki damu!!!" haka tabar wurin tanata murna ta sanya a ranta seta sanya anma kasheta gaba d'aya kowa ya huta kawai..
Kwance manga take asaman doguwar kujerar dake cikin parlor d'in, sanye take da yaloluwar rigar bacci iya gwiwa,tayi kyau matuqa sosai acikin rigar sumar kanta baje saman throw pillow na kujerar datake kai, wayanta take danna wa sanda ya shigo ya je ya janye sumar kanta data baje a kanta ya sumbace ta a goshi sannan yace
"Hilwa er dubai, kinga yanda cikin kwana ki biyu kikai fresh kuwa,lallai ke ba kalar Nigeria bace bazamu koma ba" Murmushi tae ta sanya ta shafi sajen fuskarsa,sunyi kusan dasuke jiyo bugun zuciyar junansu tace
"Kasan dai kafini jin dadin qasar nan, kalli yanda yanda kai kumatu,kuma Allah na iya kula da miji,a jikina fa kake bacci har safe,gashi kuma abinci ma sekace se a baki" dariya yayi yace
"Dakike ta tatsa na kamar me,kinga ni wanka zanyi zo muje ki tayani" murmushi tae
"Sanyi nakeji Yaa Ali, kaje kayi kayanka,idan ka gama zan tayaka shiryawa" hancinta yaja
"Zaki shafamun mai da turare da komai da komai" murmushi tae
"Rigima dai kakeji, yau ba wani wanka dazan sakaka,sedai kai ka sakani "
"Dama kin huta abinki, Auwal friend d'ina yana waje yana jirana, zamui wani lissafi" dariya tayi
"Ba komai kazomun da ice cream" wucewa yanayi yana murmushi da tsananin jin dad'in rayuwar dayake da Manga ya jima sosai yana tafkawa kanshi kuskure da qwarar kanshi" Kamar an tsikari Manga haka taji, haka kawai ta dire wayarta tayi hanyar waje, kofar d'akin ta bud'e ta fito ta soma tafiya gashi batada maraba da tsirara ita kanta bazatace ga inda ta nufaba, tadai san cewar babu nutsuwa akanta bata tunano komai daya shafi rayuwa......
Auwal daya ga manga mamakine ya kamashi amma ganin ko horn aka mata ta tsayawa se tsallaaken titi takeyi ya sanya ya fara tunanin da wata matsala binta yakeyi da qafa lokaci daya yana dannawa Ali Abbas kira ba qaqqautawa shi kuwa se faman shiri yake a gurguje yaqi daga wayar gani yake tamkar dan yana jiranshi a waje ne ......
Wata motace tasha gabanshi, kafin ta d'aga ya duba qasa da sama bega Manga ba, har tsorata yae ya soma ambaton Allah, yasan yanda me gidanshi kuma abokinshi ke tsananin qaunar Manga ya kuma kula sosai batama san inda kanta yake ba, adaidai lokacin ne wayanshi ya qara da sauri ya d'aga ganin Ali Abbas
"Auwal baka reception?" murya na rawa yace
"Yallab'ai, Manga ne ta fito da wannan rigan bana tunanin tasan inda kanta yake, gani nan kan hanyar dera market kuma ta b'acewa gani na sam, mota yakai biyar daya kusa kad'ata" tunowa yae dabe ganta a parlor ba kuma bata daki,wato sabida yana sauri be kula bata dakin ba da sauri ya ce
"kaman ya wai kana nufin da wannan rigan ta fice,yanzun nan muka gama magana, yanzu tsaya ma kai kana ina?" misalta mai komai yayi ya soma tiqar gudu zuwa hanyar...... Yayinda Auwal neman duniya yayi be ga koda me kamar Manga ba!!!!!!!!!
*Fan' s ina godiya da qauna, se kuma bayan sallah idan Allah yaso* Allah sa manga ta bata,haba haka kawai tazo ta raba masoya
#Team Huddy sak# Ana tare.
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
27
Koda Ali Abbas yazo adu'a d'auke a bakinshi sabida iya tashin hankali ya shiga ciki,
"Ina kaga tabi ne?" ya tambaya a razane kanya bashi amsa ma ya hangota wata mota na shirin kad'e ta wani balarabe ya sanya hannu ya janyota da qargi ta fad'o j8kinsa, wani sanyin ganinta yaji lokaci d'aya wani azababben kashinta ya tasowa Ali Abbas da gudunshi ya nufeta har tsere suke shida yaron nashi karban ta yayi yana isa yace yana kallon ta "Hafsa lapiya kuwa? Mesa kika fito kuma a haka" kallon rashin sani ta masa tace
"Mlm lapia dai" mamakin jin furucinta yae ya d'agata kurun se Auwal yawa wannan godiya ya rufa masa baya, kokarin sauka takeyi yayinda yaci karfin ta da adu'an dayaketa tofe ta dashi yana sassarfa ba qaqqautawa.....ahaka ya dira d'akin Ali Abbas ba qaramin me ilimi bane ta fannin addini, wannan ya sanya ko sanda ya aikatawa manga wannan shirmen mahaifinshi yaji zafinsa sosai sabida yafi kowa sanin haqqin aure, Zama yayi ya ebo ruwa a kofi yadinga adu'a yana tofawa aciki yana ebo ruwan yana shafe ilahirin jikinta dashi se wani kuka ta somayi dabesan ta da wannan amon muryan ba, Aljanin ne yayi magana akan shi adena qonashi turoshi akayi akan in ba'a dena qonashiba ze koma wurin wanda suka turoshi ya batar dasu a duniyar su, magana sosai ALI ABBAS yayi dashi yasha fama har kusan Asuba akan aljanin ya fita amma pir yaqi akan lallai seya aiwatar da abinda aka umarceshi dashi, seda yaga duk an qonashi sannan kuma yayi hanzarin fita tare da alqawarin baze qara waiwayarta ba, Ali abbas ajiyar zuciya ya sauke idashi duk yayi ja ya kalli yanda wani hayaqi ke fita daga bakin Manga ta bashi tsananin tausayi,harse yaushe ne Manga zata samu kwanciyar hankali dajin dad'i? Ya tambayi kanshi,me manga tayiwa su Ammyn huddy? Meta tsare musu? Menene laifin ta? Beji dadi ba sam sabida an gaya masa da sanya hannun Ammy aciki da huddy,yana san huddy mesa zata sauya? Da wannan kurun ta gama b'atawa kanta wayo a wurinsa ace musulmi da shirka irin wannan,sallah yaje yayi ya dawo ya daga manga dake baccin gajiya zuwa gado shida Auwal suka zauna tattauna matsalar haka kawai yaji Auwal ya kwanta masa yasan sirrin sa be boye masa komai ba ya gaya masa labarin rayuwar manga da tashi gaba daya Auwal yace
"Ni yallab'ai a ganina matarka dake gida zigata akeyi irin wannan tunda aikin datake ma na neman lada ne bawai sabida ta rasa abin bane datseshi zakayi ka dauketa itama daga Nigeria din ka kaita Madina inda kake shirin kai Mangan koda na wata shida ne ko kuma shekara d'aya,ina ganin sam be dace ka bari a wargaza mata rayuwaba harda Aikata shirka alhali kasan bawai haka bane halinta dacen" nisawa yayi yace
"Zanwa Ummu waya in sanar mata komai tayi shawara da me martaba yanda suka yanke hakan za'ayi ni ina tausayawa rayuwar Huddy ina tsoron ingantaccen hadisin nan ya tabbata akanta, dake sanar mana mutum ze kasance yana aikata Aiki irin na aljanna harse ya kasance tsakaninsa da ita be wuce kamu d'aya ba sekuma ya dawo ya aikata aiki irin na 'yan wuta kuma ya shige tsundum a wutar, kazalika masu aikata irin na wutan seya kasance tsakaninsu da wutar be wuce kamu d'aya ba sesu aikata aiki irin na en aljanna be wuce kamu d'aya ba seya aikata aiki irinna en aljanna kuma ya shigeta, dukda yake rayuwar kowa a hannun Allah take amma tun zuwanmu india an sanar dani dayan Maman ta ma ya kamu kuma idan hakan ta kasance sedai ajira lokaci sam huddy batada lafiya qarfin hali kurin takeyi kuma na sani amma kishi yana hanata ango rayuwarta na cikin garari se shirme takeyi me Manga ta musu? Yarinyar nan da Badan Allah ya taqaita mata wahala ba da baka gantaba wlhy daban masan ta fita ba Da Allah ma yasa kun hadu jiya kayi saurin ganeta, kaima gudun dakasha Allah ya saka maka alkhairi ya ceto rayuwarka sanda tsananin buqatar hakan Ameen" murmushi yayi yayinda shi kuma ya tashi zuwa dakin nasu, koda yaje ta farka amma ta kasa tashi, murmushi ya sakar mata ita dinma haka ta mayar masa da martanin murmushin sa, yace yana qoqarin boye mata meya faru
"Ki tashi kiyi sallah har tara ta gota se tashinki nakeyi kiyi sallah kinqi" zumburo baki tayi tace
"Nidai nayi mugun mafarki wai inata gudu bansan inda zani ba, ynzu kuma na farka gashi inata faman tsamun jiki na kasa tashi" zuwa yayi ya d'agata ya daura kan cinyarsa, sumba ya manna mata a goshi sannan ya cire mata yaloluwar rigar ya wurgar a gefe sannan ya d'aga ta cak zuwa ban daki,da kanshi ya had'a ruwan zafi ya mata wanka ya gaggasa mata jiki se shagwab'a take narka masa, yayinda takejin jik8nta tamkar ba nata ba dukda yake yayi mata matuqar nauyi, a haka ta dauro alwala ta dawo tae sallah breakfast kurun taci ta zari wayanta kallon sosai ya mata yace
"Manga inaso ki ajiye wayar nan zamuyi magana dake" nutsuwarta ta tattare gu d'aya shi kuma ya soma magana
"A d'an zaman nan damukayi dake na kula da abubuwa dayawa gamedake,da farko dai idan kikayi sallah Allah Allah kikeyi ki sallame ki dauki waya ko kallon tv ko karatun novels kodai wani abu mara muhimmanci a rayuwarki wanda ko a duniya baze qareki da komai ba bare kuma lahirarki, ki sani bakya san yawaita adu'o in tsari ko Azkhar dan Allah Manga ki taimaki rayuwarki ki dena wannan abun, yanada kyau matuqa ki ragewa baiwa waya muhimman lokutanki ki sani ba abu bane me kyau ace wai bakada lokacin mahaliccinka sena kanka, ki sani Allah baya buqatar komai daga wurinki kece kikeda tarin buqatu awurinsa wanda duniya kaf dama lahira shi kadai ya isa ya biya miki su, so ki nutsu ki riqe Allah mintuna biyar dai bayan ko wace sallah ya isheki kiyi adu'a bawai da zaran kin gama ki gaggauta miqewa shagalta da lamuran duniya ba,sannan kuma ki sani ina kulawa dake bakya adu'a yanzu idan zaki shiga ban daki, saka tufafi ma wannan yanzu mutane sun wurgarda yin bismillah kafin su saka kema kuma kina ciki, abubuwa masu muhimmanci an watsar sabida haka ki kiyaye, yanzu kina kewaye ko mahasada so kina azumin litinin da Alhamis da yawaita adu'o i da kuma istighfari, dan Allah ki kiyaye,kuma adena gayu na tsiraici ga kwalkiya nan da gayu masu aji, base ka wofintar da tsiraicinka ba dan Allah a kiyaye da yanayin shiga ina fatan kin gane?" jinjina kanta tayi
"Inshaa Allah yaa Ali zan kiyaye duk zanna yi" murmushi yayi ya yai alamu da hannunshi akan tazo
"Thats ma baby love,common lemme hug u" rungumeta yae sosai a jikinsa ya cura bakinsa a nata passionately yake kissing nata mutuniyar harta soma shid'ewa, cafko masa nashi bakin tayi ita ba qaqqautawa take kissing nashi batamasan sanda hannunta yayi tattaki zuwa cikin rigarshiba, gashin qirjinsa ta soma wasa dashi har zuwa saman nipples d'inshi wani dad'i takeji idan suna cikin irin wannan yanayin harda ke sanya take manta me takeyi, nonuwanta ya soma sosa mata a hankali seda ta kusan aomewa sannan ya kai harshensa ya soma wasa da nipples din....nidai ganin tamkar za'a samu matsala ayi sirri a gabana ya sanya na sulale na kauce wa masoyan.....
Tun bayan da akayi sallan asuba Ammyn huddy ta zari key ta fita tabar gidan, sanin halinta na ficewa aduk sanda taga dama ya sanya babu wanda ya nemeta har aka kwana aka wuni, seda yayanta qanana suka ga shirun yae yawa sannan suka fara nemanta inda ko labarin motarta babu bare ita gaba daya........ Ummu kuwa Ali abbas ya sanar mata komai sedai ya gaya mata be gayawa manga komai ba yadai bata adu'an dazata riqayi na tsari....baqaramun godiya ummu tawa Allah ba akan kubutar da manga dayayi, sannan ta shaida masa akan huddy kam se yanda mahaifin sa ya tsara....
Yaudai manga an dira a Madina, tun bayan kwana biyu data gabata suka samu labarin b'atar Ammyn huddy yayinda Ali Abbas ya kasa gayawa kowa meya sameta tunda a duk fadin duniya shine kurin ya sani se kuwa Auwal....Tunda suka isa Manga keta tsulala amai, acewarta sam batasan warin dakin dasuka sauka, ko ruwa tasha se amai dukta gama galabaita, ya sauya musu masauki kusan sau biyar amman haka taketa yin aman har washe garin ranar da suka isa wannan ya sanya yakaita asibiti badan yasoba, gwajin farko kuwa akace manga ciki ne da ita da wata daya kacal, an samu an tsayarda aman Ali abbas se rawan qafa akeyi aranshi yace wannan cikin a madina za'a haife masa abinshi kuma bama ze sanarwa kowa ba har Ummu se an haihu tukunna, se murna ake anata jijji da manga yayinda ita kuwa se narkewa takeyi tana shagwaba, dukta gama feqe qa ciwon kwana daya tayi fayau da ita.....
Mom Nu'aiym
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
28
Ammy bayan barinta gida duniya kawai ta shiga, haka ta dinga shiga daji batare datasan inda ta dosa ba, tayi tafiya mara adadi sabida da full tank ta fita a motar ta amma seda manta ya qare qat sannan taja burki ta tsaya sannan ta waiga ta kalli wurin, bata kawo komai akanta ba sabida sam tama manta wacece ita a wace duniyar take