Showing 42001 words to 45000 words out of 60927 words
Chapter 15 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt
tayi tace
"Mama kin taba zama da kishiya wai?" kallonta maman tayi tana murmushi tace
"Acikin kishiyoyi ma ba daya ba,mesa kika tambaya?" sunne kanta tayi tana murmushi tace
"Mama banaso mijina yafi san kishiyata akaina, kokuma yafi kulawa da ita sama dani ni sam ji nake ma bana san kishiyar gaba d'aya kuma kwana kinnan na soma jin hakan" murmushi tayi tace
"Hafsat babu wata mace da namiji ze ajiye agidanshi batare dayana sonta ba,shi namiji baya zama da mace don yaranta macece take zaman gidan miji komai wuya sabida yaranta.....Duk yayinda amatsayinki na mace kika tsinci kanki acikin kishiyoyi ko kishiya toki sani bawai anfi sanki dasu bane sedai ki siwa kanki soyayya fiye data kowace mace ta hanyoyi kamar haka
*Yin Biyyayya tamkar ba gobe*
*Gujewa b'acin ranshi akomai*
*san mijinki fiyeda yanda zaki so kanki*
*Kiso yaranshi tamkar ke kika haifesu tsakani da Allah koda kuwa bakece kika haifesu ba*
*Jajircewa wurin tarbiyantar da yaranshi*
*Kare masa dukiyarshi koda baya nan*
*Nuna qwazo a saman shinfidarsa*
*Karki zamto me yawan kai qarar kishiya,yaranta ko kuma karar shi mijinki agidanku ko konasu*
*yawan adana sirrin mijinki awurin mutane*
*Iya tattali wa komai*
*Tsaftar jikinki,shinfidarki da gidanki baki daya*
*Danne kishinki akan kishiya koyaya kike jinsa*
*Karki kuskura ki d'aga muryanki sama da tashi*
*Alkunya...,yakasance saka idanki a nashi ze zamtone iya lokacin da kike tsananin buqatarshi yanda hakan ze zamto kullum sabo a wurinshi*
*Dagewa sanwar ki,ma'ana komai qanqantar cefane ki iya sarrafa shi yayi taste me ma'ana..*
"Inshaa Allah wannan kad'ai ya isheki makami,se uwa uba yawai ta adu'a da kuma ibada ako wane lokaci, zakiga soyayyar mijinki ta har abada,wanda ko mutuwa kikayi bazai fadi koman ki ba se alkhairi.....Hafsat se kirsa,karki kuskura ki nemi taimako awurin boka ko malami kedai kissar ki ta isheki da iya zama da danginshi cikeda girmamawa da qaunar juna,kuma lallai karki kuskura ki bari mijinki yaji warin baki ko na hammata kona Hq ajikin ki ba, babu abinda yake zubarwa mace qima awurin miji irin wari kowane iri ne kuwa, lallai ne a dire babin kunya alokacin kwanciya a dirje juna, ki kasance bazakiyi wankaba indai a d'akinki yake se tare dashi,banda raba kwarya da miji lallai aci abinci a tare, ki rinqa masa hira me dadi,kuma ki riqa masa labarai masu ban dariya, ki zamto me tsananin kuruciya agabanshi bazaki taba tsufa ba awurin miji 'yata, shagwaba kam kina zabga masa seya kasance idan kika soma seya zama soko agabanki,ina fatan kin gama haddace wannan ?" murmushi hafsa tayi tace
"To yanzu Mama ni idan ina wannan itama tanayi fa, Aunty huddy fa akwai tattalin namiji" murmushi tayi tace "Hafsat kije kiyi yanda babu wata mace dazata fiki awurin miji, idan dai baki fita ba tokuwa saidai kuje wuri d'aya" murmushi tawa Mama tace
"Mama na gode inshaa Allah zan kiyaye da komai ma" harta miqe maman ta riqo hannunta tace
"Manga A riqa turare kaya,kazalika ana turare jiki, wannan turarukan na wuta lallai sunfi qamshi da riqe jiki basa barin jiki sam,yanzunma zonan ba inda zaki se na gama had'aki da qamshi me dadi"....
Ali Abbas kuwa zuwa yayi waje suka gaisa da zuhair sannan yaje sukaci abinci bayan sun kammala suka fita gabaki daya,zuciyarshi a cure yana mamakin dalilin kuka Manga, wani time din kuwa idan ya tuna wawtar data rafka seyayi murmushi....
A bangaren Manga kuwa yau taga gata da gatnatawa,gabki dayi seda mama ta mayar mata da jiki tamkar turaren wutar siyarwa sabida qamshi ita kanta tasani tana qamshin dadi, ta kuma qudurta aranta seta yashe ruwan da Ali ke iqirarin kaiwa huddy,kuma seta gama wanashi kazalika seta tabbatar yayi sati biyu koma fiye a garin agadaz......
Wani wankan tayi ta sake turare jikinta da turarukan da mama ta bata tayi zaman tsuguno da wani turaren,sannan ta shirya ajikin wata rigar jallabiya kalar ja me santsi tayi matuqar mata kyau kuma ta kame ta asaman a qasanta a bude, dama ta kammala girkin rana itada hadimanta se wani murmushi takeyi lokaci zuwa lokaci, tana zaune parlor ta kishin gida suka shigo shida zuhair, qura mata ido zuhair yayi aranshi yace lallai Ali Abbas soko ne,wannan tsalaleliyar haka,wani kallo Ali Abbas ya wurga mata sabida ya kula da kallon da zuhair ke mata, ita kanta ta kula seta tsargu zuwa tayi daki ta sako hijab ta had'a musu abinci sannan ta bar wurin har lokacin da zuhair yabar gidan Ali Abbas se wani kumburi yakeyi, waishi ala dole kishi ita kuma ta kasa gane dalilin fushin, qwayar idanshi na daburtar da lissafin ta, kallanshi tayi bayan ta sameshi daki tace
"Yaa Ali lafiya kuwa na kula tun dazu kake cikin bacin rai" wani kallo ya wurga mata sannan yace tamkar ze daketa
"Ya kamata kisan ke matar aurece, ki qara zuwa wurin zuhair ba hijab koma waye ke hijab zakina fita dashi inba hakaba zakiga yanda zamui dake" ita sema yanzu ta gano inda ya dosa murmushi tayi tace cikin rashin damuwa
"Seka sanyawa abokin ka iyakar inda ze shigo acikin gidanka sabida ni sam bazan fasa walawa acikin gidana ba, kune kuka same ni banice na fita a haka ba, sannan zancem hijab gaskia bazan iyaba sabida ko Auntu huddy ba a sanya mata wannan dokar ba, zandai yi lullubi iyakar iyawata,kuma yanzu zan koma part din mama tunda anan abokinka baze dena shigo waba ni kuma bazan dena zama ina shan iska acikin gida naba" kallon ta yayi yanda takeso ta kawo masa raini yakasa cewa komai tsabar b'acin rai, tana mita ta miqe tsaye "Zan turo hadima maryama ta kwashe mun tarkacena, bazan iya rayuwar takuraba zanna zuwa maka lokaci zuwa lokaci" tana kaiwa nan ta juya da sauri yasha gabanta ya riqeta sannan ya tura idanshi a nata daurewa kanta tayi aranta tace lokaci yayi dazan soma koyawa Ali Abbas hankali, d'age kafafuwanta tayi tai sallah bazata yaji bakinta a nashi, sun kusa 5 mnts suna tsotsar juna dan kanta ta janye bakinta daga nasa,dukkaninsu launin idanuwa su ya sauya zuwa ja azabar sha'awar junansu na addabar su, juyawa ta kumayi da zummar barin dakin tunkan ta bada kanta, hannunta ya riqe yace
"Ban yarda da tafiyar ki ba konan dacan, sannan me hakan yake nufi ne wai? Inafa da haqqi a kanki" kallonshi tayi sosai ta qara qanqance idanuwanta
"Banaso na zamto silar karya alqawarinka yaa Ali, ruwannan me daraja na jikinka ka kaishi ka saka a inda kayi alqawarin zaka kai, ka kaiwa wacce takeda haqqi a kanka, ka kaiwa wacce kake rantsuwar cewar bazaka zubar mata da ruwa me daraja a inda ba'a da haqqi dasuba, ka sanar mata dama wacce takewa bata buqata shekaru biyar tayi tana bata kyautar su,ko yanzu tae tayi indan ita, kaje kaci gaba da tattalin makwancin wata kaji, nisam nasan muhimmancin alqawari so bazamu taru mu karya ba, zancen haqqi kuwa ida kina maganar har kunya nakeji dan wlhy aki baka sanshi ba ma sam,ni ka sakemun hannu malam parlor zanje,ka kuma sanarwa zuhair idan be iya sallama agidan matan aure ba nizan koyar dashi, bazan takura kaina akan wani gardi ba wlhy,bakada hurumin qulleni a yanzu,shekaruna biyar ina gara ramba da igiyar aurenka bakasan ka sanyani a hijab ba se yanzu, bazan iyaba kamaji na gaya maka, dama kuma ni kowa yasan I'm hijabated so no need ka tursasani iyakokin Allah nake kiyayewa bana kaba me ruwan zinari....." sakin hannun nata yayi yana jin d'akin yana juya masa,kenan wannan ne dalilin kukan manga dazu,toshi yazeyi da wannan abin kunyar ashe taji komai.......
Mom Nu'aiym ce
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
*Pheey wannan shafin nakine ke kad'ai kiyi yanda kikeso dashi, ke kadai ce kika kirami a waya tun bayan da sanarwan rashin lafiya a ya sameki, ina roqon Allah ya sanya Alkhairi da Albarka arayuwarki, Allah ya shiryar miki da zuri'a ya baiwa 'yata Amira lafiya ya kuma bar zumunci....Ina yinki sosai pheeeyyyy.....*
                 20
Zama a bakin gadon yayi ya dafe kanshi, duk yanda yake tunanin kunyar nan data bashi abin ya wuce hakan agareshi, yaya zanyi da Manga? Ya tambayi kanshi miqewa yae jiki ba qwari ya sameta a parlor kallon shi tayi bayanda ya zauna a kusa da ita, qamshin datake fitarwa be saba jin irinshi a jikinta ba yanayin shigar da tayi yanzu ta tafi da imaninshi, riga ce acikinta iya cinya ta d'ame ta asama yayinda qasan yake a bud'e rigar kalar pink ce ta taje sumar kanta tayi parking dinta a tsakiyar kanta jelar ta sauka har gadon bayanta, qafarta d'aya akan d'aya tana riqe da cup da milkshake data hada da kanta tana kurba a hankali, yatsun qafarta ya kalla yaji wani yar yanda suke zara zara farare qal nails dinta sunsha ado da lalli baqi....tayi masa kyau ainun, yanda yake bin ko ina nata da kallo haka takebin qwayar idanshi dake juyawa da kallo, sa'ilin da ya mayarda dubanshi zuwa gareta suka had'a ido seda yaji wani jiri ya dauke shi, yauce rana ta farko da yaga idanuwanta manga da kwalli sam bata shafa kwalli, kuma seya masifar fito da dara daran manyan eye balls dinta dake black shar ga wani blue dayake kewaye dasu me daukar hankali,gefen farinnan ya qara haske sosai se lumshe masa su takeyi tana murmushi ganin ya kasa dauke idanshi acikin nata ya sanya ta kawar da nata maganar mama ta tuna
"Manga mesa bakya sakawa idanki kwalli?" murmushi ta mata
"Mama kwalli ai qauyancine yanzu ba'a yayinshi ni tun ina secondry school rabon dana shafa" tsaki maman tayi..
"Kufe garin neman a sanku ake mantawa daku, bari kiji wlhy hafsat kwalli shine mace duk wata kwalliya dazakiyi bazata fito ba seda kwalli, shi kwallin nan da kuke rainawa ba kamar wai sauran kwalliya bane da zakiga kinyi iyakar ta fuska, bari kiji abubuwan da kwalli keyi
*Kwalli yakan taimaka wurin kare cututttuka daga shigar wa mace ido*
*kwalli yana isar da saqon zinariyar mace acikin zuciyar mijinta, duk sanda kika saba ida idanuwanki suka sarqe dana mijinki zakiga ya masa dauke nasa a naki,akwai abubuwan dashi yake ganinsu amma ke baki san dasu ba*
*Kwalli kwalliyace dake tsayawa a zuciya da idon namiji ko bayan kin wanke, saqon dayake isarwa har cikin b'argon sa yake shiga ko bakwa tare zeke tunawa da wannan qayataccen ruwan zaibar dake zagaye da baqin idanki yana jin wata kasala*
*Duk yayinda kika sanya kwalli kafin kuyi kwanciyar aure da nijinki ki tabbatar idanuwaku sun gauraya da nashi na tsawon sakan goma ko fiye zakiji banbanci*
*Kwalli shine yake raba gaddama tsakanin wanene namiji wanene kuma mace......ki kula duk sanda bakida kwalli koya kika kai qarshe wurin iya kashe ido bazeyi tasirin idan kika saka kwallin ba*
Murmushi Manga tayi sabida taga sauyi sosai a wurin Ali Abbas yau, ya kasa dauke idanshi a nata, ajiye cup dake hannunta tayi sannan ta sanya hannayenta duka biyu ta zagaye bayanymshi ta d'aura kanta saman qirjin sa tace a hankali
"Na manta ban sanar maka ba" dan d'agota yayi yace "Menene?" murmushi ta sake sakar masa sannan tace
"Dama zan sanar maka ne kayi kyau matuqa" murmushi ne ya sub'uce masa,lokaci d'aya yana mamakin sauyawarta yanzunnan fa ta gama masifa,hannu ya sanya ya shafi sumar kanta dake matuqar burgeshi sannan ya sumbace ta a goshi yace
"Na kaiki kyau ne Hilwa aike sunanki ma kenan" qayataccen murmushi ta sake masa tace "Banga alama na maka kyauba my very own, sam baka nuna mun hakan ba" lokaci daya sunana ya sauya zuwa very own anya kuwa ba wani abin Manga ke shirya munba? Ya ayyana a ranshi kafin ya ce da ita
"Kinmin kyau fiye da kullum Hilwa nayi nauyin bakine kawai" kallon wani gaula take masa yanda yayi saurin yadda da hucewarta, shi a ganinsa zata haqura da abinda ya mata ne kai tsaye haka, murmushi tae
"Me zakaci yanzu na girka maka ne?"
"Ba abinda nakeso se wannan milkshake d'in da kika ajiye anan" Murmushi tae tace na ajiye wani a fridge ma barin dakko maka" harta miqe ya riqo hannunta ta dawo ta zauna ta sanya idanuwanta dake rikitashi a nashi,rausayar da kanshi yae gefe d'aya yace
"Manga plss abinda kikaji d'azu kark.....tsoma bakinta tae anasa y
Ta rufe rufff, ta soma kissing nashi pationately sunfi 10 mnts suna tsotsar bakin juna dan kanta ta janye bakinta daga nashi, ko ba'a fad'aba kallo daya zakawa idanta ka gano itama taba buqatar mijinta, amma haka ta kanne taje ta d'akko masa milkshake ta kawo mai, shi kuwa gogan kanzil bece da ita ba sabida yanda ta kashe masa jikinshi, tana ajiye masa taje ta zuro qaton hijab tabar gidan zuwa cikin gidan jikinta ba qwari tanaso ta koyar da Yaa Ali hankali amma ta kula idan batai da gaske ba ita da kanta zata bada kanta da kanta, qamshin jikinsa ma ya isa idan taji ya jiqar da ita harse tayi tsarki lolxx.... Shi kuwa gogan kasa koda motsin kirki yayi yarinyar nan ta gama sure imaninsa tayi habuja dashi,gabaki daya wani uban sha'awarta yakeji ga qamshin jikinta ya gama zame wa abin shaqarshi ta tafi ta barshi da qamshin na jikinta, gashi ya soma yi masa qaramci sabida nisan data masa....jikinshi a mace ya koma daki ya kwanta a rigingine ya rufe idanshi.......
D'akin kakarsu taje ta tarar bacci take, wayanta ta zaro ta kira Maman khadyy, suka gaisa sannan tace
"Maman kaddy tips zaki bani na ya da zanyi kwanciyar aure me rikitar wa, i mean wasanni da zanwa mijina, wanda babu wani kunya aciki" dariya maman khadyy tai me sauti sannan tace
"To lallai yau munji Manyan amare, muda muketa fushi anyi aure ba sanarwa, dukda haka bazan fasa baki iya abinda na sani ba,da farko dai kankije wa shinfid'ar mijinki ki tabbatar kin wanke bakinki, hammat, qasanki kuma yana qamshin ruwan miski da gabaruwa da minannas da kanun fara, ki tabbatar qamshin ki bame tashin hankali bane ya kasance me sanyi wanda baya hawan kai, ki tabbatar bakinki yanada wadatar qamshi kuma ki tabbatar kinyi shigarki ta karuwar gida ma'a me rikitarwa, akwai wani kuskure da mata keyi musamman lokacin zafi zakiga sumar kansu yana tashin wani uban wari, karki kuskura ki bari mijinki yaji kanki yana wari, idan ma bakida hand drayer ki siya koda da kitso a kanki duk sanda ruwa ya hau ki riqa busar da kan, ki tabbatar kinada hair spray shima kafin ki kwanta ke koma yaushe kina sakawa da mayukan gyaran gashi masu qamshi sosai.....bayan wannan ki iya kissinga nashi passionately, ki tabbatar kin tsotse ko ina ajikinsa ana yawan hura masa iska me d'umi a kunne, ki dire kunya hajiyata ki sha nonon sa, ki lashe ko ina ajikinsa da harshenki, harshe babban makamine, ki kiyayi yawan shan ruwa me zafi yana sanya harshe yae tauri,kazalika ki guji shan ruwa me mugun sanyi shima yana sanya harshe yae masifar tausri, ko wane kalan ruwa zakisha kiyi sese sese, laushin harshe da lips abune me muhimmanci awurin both mace da namiji, ki tabbatar kafin ku soma sex kunsha wasa,karki koyawa mijinki dira a kanki kamar doki ko wata saniya kindai gane aiko?" murmushi tayi tamkar suna ganin juna tace
"Kai Maman khaddy ni yanzu yanasan zanyi? Kunya nakeji wlhy" tsaki maman khadyy taja
"ke wlhy kije ki tambayi yaa Hajja ma haka abin yake, ai ba'a wasa da shinfid'ar miji,duk wani abu ajiyewa akeyi a sha shagali qawata, ko pherty zahra dabata da aure ta gama haddacewa ta rubuta ta ajiye tace ita sam bazata bari mijinta ya nemi komai awaje ba idan sunyi aure, ni pherty tana burgeni wlhy dagani zatayi tattalin mijinta, ke gakinan komai baki sani ba sabida bakya shiga cikin mutane yanzu zaki wani ce kunya, kinga ko uwani kishiyar jidda data tattare shirme ta ajiye ai Elmustapha da girmanshi da komai ya hau ya d'ana, bare ke kuma" nisawa tayi tace
"To maman khadyy zanyi yanda kikace inshaa Allah, amma yazanyi na hada wannan ruwan miskin?"
"Yauwa ki samu ganyen magarya, ganyen bagaruwa da ita kanta bagaruwar, minanas da kanun fari, se ki saka a butar qarfe ki zuba ruwa da garin lalle da kuma sansaminsa ki zuba ruwan miski da miskil abyal, ki tafasa sekina tsarki da ruwan,wannan had'ine na alfarma koba komai ze saukar da qamshi me dadin gaske ajikinki, kazalika kuma ze hana infection zama ko shiga ajikinki" godiya tawa maman khadyy sannan ta ajiye wayan.
Da qyar ta gama harhada kayan da ka lissafa mata tun tana tafasa ruwan qamshin ya mata yanda takeso, koda tazo tsarkin ma abin ya mata daidai,qamshin ya shige mata kai....ta caba gayu cikin gajeruwar riga iya cibiyarta da dan skirt qarami mara nauyi me pant aciki mahad'in wannan rigar, tayi kyau ta baje sumar kanta daketa tashi qamshi har gadon bayan ta, kallonta Ali Abbas yayi ya had'yi wani yawu,sannan ya dauke kanshi daga dubanta, batare data kalleshi ba ta zauna saman cinyarsa ta fuskanceshi sosai sannan tace
"Baka kwanta ba kenan? Murmushi yae yace "Hilwa baki shigo ba zan kwanta, yazan iya bacci batare dake ba kuma?k murmushi ta masa "Kumafa hakane na tuna ai" kan waninsu yae magana wayan Ali ya soma ringing Manga ta kula ringtone din Huddy ma na dabanne dauke kanta tae ganin ya daga kiran bataso ya kula da dokawar da qirjinta yae har a fuskarta.....
"Baby ina kika shigane inata kiranki a waya baki dagab'a?" a d'ayan b'angaren Manga najiyo ta sabida kusan datake dashi sosai
"Kai hakuri Abbin Ameer naje wankane kuma sanda na dawo ban dauki wayan ba se yanzu" jinjina kanshi yae tamkar tana gabanshi
"To ya jikinki na damu sosai da kikace bakida lafiya, kaddai nonon ne?"
"Na sanar maka koda nake zuwa checkup an sanarmun dayan lafiyanshi lau, bana fatan dan abinda kake moruwa dashi shima ya samu matsala,khair inshaa Allah"
"Allah ya kareki da kariyarsa,yanzu me akeyi ne?j ya buqata
"Kwantawa zanyi bacci nakeji kaifa me kake har yanzu baka kwanta ba? Kallon Manga yayi yace
"Ba komai nima yanzu zan kwanta"
"To muyi labari mana har bacci ya daukemu,ni kamun labari plss" murmushi yayi
"Zanyi wankane yanzu zan kiraki idan na gama da wuri"
"Senaji kamar bakasan mun magana sam" kallon