Showing 36001 words to 39000 words out of 60927 words
Chapter 13 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt
wasa
"Yaa Gadanga zaka cinyeni ne wai" murmushi yayi shima yace
"Dole in kalle ki Manga wata d'aya fa zakiyi a wata qasar, gashi baki barni da wata ajiyar bama dazanna tunawa dake" wara ido tayi tana murmushi tace
"Zan baka ajiyar zobe mana kalan yanda kayi sanda zakaje soba daga kaduna" Dariya ya gano gayya take masa ya matso daf da ita ya had'e hannayensu wuri daya ya matse nata seda ta qwalla qara "Yaa Gadanga da zafi Allah" waist d'inta yakai hannu ya matsa seda ta sunkuya tana dariya
"Gobema ka qara tsokana na, yanzu muje d'akina in baki wani saqo" maqe kafad'a tayi "Bazan bikaba kamun mugunta Allah kuwan, nidai kaga su Inno ni suke jira kurin ka tafi" kallonta yayi "Aunty Manga dan Allah zan biki" murmushi tayi tasan yanda ya mat sanda ze gudu ya barta, rungumeshi tayi tana bubbuga bayanshi a hankali kalar dai yanda ya mata sanda ze gudu ya barta, sannan ta sanya hannu ta tallafo habarshi tace bayan ta sumbaceshi a kumatu
"Kayi hakuri yaa gadanga, nima badasan raina zan tafi in barka ba, ka kwantar da hankalinka ba dadewa zanyi ba wata daya kurin zanyi" ya tuna sanda abun ya faru murmushi yayi yace aranshi Manga so take kota yaya seta rama komai daya mata kenan, yace "Allah ya kiyaye hanya" murmushi ta kuma yi
"Jeka dakko kayanka zan jiraka a mota mu tafi tare" sannan ta juya bayan ta barshi a tsaye, jikinsa ne yayi sanyi yana tunanin mesa ta masa haka, Kaddai ta masa nisa na har abada, da kuwa ya shiga ukunsa ba kad'an ba......
*Yamai Niger republic*
Sosai akaji dadin dawowar Ibrahimou har wannan lokacin mahaifinshi duk yawan auren dayayi be haifi wani yaron ba, shishi kadaine agun me martab. Se bayan dasuka yi sati biyu agarin sannan Iro ya sanarwa mahaifinshi tarihin rayuwar dayayi a Nigeria da kuma wahalhalun da Manga tasha, tofa anan akeyinta domin kuwa tsohon nan gabaki d'aya yajawa Iro Allah ya isa inhar muddin be raba auren manga da Ali Abbas ba, acewar sa baya qaunar qasar Nigeria bare yabar jikarshi ta rayu acan da sunan aure, bayaga haka qasar Nigeria itace ta rabashi da yaronshi tsawon shekaru da dama, kazalika kuma jikarshi tasha wahala a gunsu, bama wannan ba shi Ali Abbas din daya bata wahala shekaru hudu yayi kadan ya moreta yanzu,iro yayi roqon duniya abu yaci tura, anmace baze koma Nigeria ba, sannan kuma ba wannan auren yaro ya aiko da takardar sakin Manga kawai, gashi bazeso ya qara sab'awa mahaifinshi ba akaro na barkatai....
Ko yaya zata kaya kuma a wannan taqaddamar,Allah masani,kudai ci gaba da bibiyar alqalamin yar galadanchi, en wattpadd u vote pllss,love ya all
Mom nu'aiym ce.
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Sadaukarwa gareki qawa ta gari Fulany saddy*
17
Manga kwance ta qurawa wayarta ido dake ta faman ringing,tanaso ta d'auka amma tanaso Ali Abbas ya gano tsananin kuskurenshi a gareta,tunda sukai waya dashi farkon zuwanta kusan sati biyu kenan bata d'aukar wayanshi, bata masan me ake cikiba har yau mahaifinta ya gagara sanar da ita hukuncin da me martaba ya yanke akan aurenta, lumshe idanta tayi zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri duk ringin d'aya da wayar zatayi yana tafiya ne tare da harbawar zuciyarta, lallai tana qaunar Yaa Ali ba kadan ba amma yazatayi ya gano d'inbin laifukan daya aikata a gareta batare data nuna masa hakan ba, dolene ta nuna masa kuskurensa.
Ana haka suka shirya tafiya Agadez garin su mahaifiyarta wanda Innoh se d'auki takeyi akan zuwanta ta gaisa da mahaifanta bayan shekaru aru aru rabon data gansu,a bakin su Ammu (Mahaifiyar Baban Manga) taji labarin dukkaninsu suna nan a raye,ba qaramin farin cikin hakan tayi ba, har zuwa wannan lokacin sam Manga bata d'aukar wayar Ali Abbas.
Ranar wata alhamis suka d'auki hanyar agadez wanda ranar ma Ali Abbas ya kasa hakuri ya d'akko hanyar Niger shida abokinsa Zuhair sunyi sab'ani da su baban Manga ba wani nuna rashin mutunci suka karb'eshi seda ya huta yaci abinci me kyau ya kuma sha, sannan sarki ya aika aka kira masa su ya kalleshi kallon nutsuwa yace
"yaro kaine mijin Manga kace ko?" gyada kai Ali Abbas yayi cikeda girmamawa gayaran zama yayi shi sarkin sannan yace
"Labarin dukkanin abinda ya faru tsakanin ka da Manga yazo kunnena kuma sam banji dad'i ba bisa wannan na yanke hukuncin dana yanke game da zamanku ina fatan dai ka shirya rabuwa da itan kaman yanda na shard'anta muku sabida a yanda na d'auka lallai ko kotu sena kaika a raba auren nan tunda basonta kakeba, baya ga haka ni sam bana qaunar qasar ku sabida itace ta shiga tsakanina da d'ana d'aya tilo dana kedashi a duniya sannan kuma ta janyowa jikata jinina musibu iri iri,ina mai baka shawara kabi umarnina batare da gaddama ba domin kuwa duba da yanayin matsayinka sam baze hanani d'aukar qwaqwaran hukunci akanka ba" cikeda rud'u ya d'ago ya kalleshi idanshi harya kawo ruwa yace murya na rawa
"Ban gane wane hukunci ba Ranka ya dad'e,bansan wannan zancen ba" kallonsa sarki yae yayi dariya irinta manya
"Aliyu ka sani babbar matsalata bana sauya hukunci na, hakance ta sanya kaga Ibrahim yabar gida kuma shi na sanar dashi kaida Manga aurenku bame yiyuwa bane sam, se an raba auren tunkan su tafi Agadez sunsan da wannan har ita Mangar sabida haka ka kwana da shirin rabuwar ku daga nan ma bawai binka zatai ba,sakarmun jika zakayi ka qara gaba" kuka Ali Abbas ya sanya masa ya soma ban baki da neman taimako amma qememe sarkin nan ya kafe, haka ba yanda zeyi suka baro fadar zuciyar sa na masa zogi, mota suka shiga suka bar masarautar sannan seda suka hau titin sosai Zuhair yayi parking ya daura hannunshi daya a saman kafadar Ali Abbas daya dukar da kanshi yana sauke numfashi a hankali lokaci d'aya kuma hawayen baqin ciki suna zarya a kuncin sa
"Kayi hakuri sarkin musulmi, bakada wani abu a duniya daze maka shamaki da manga se bironka da takardarka dazaka rubuta mata saki idan har baka rubuta sakinba to kuwa babu wani alqali daze raba aurenka da Manga, abu d'aya ne kuwa ze taimakeka shine samo yardar da soyayyar Manga, bance kabi kowaba ya taimaka maka kaine da kanka zaka taimaki kanka, ka zama jajir taccen namiji meji da kanshi wanda ya iya sarrafa kowace irin mace, ka baiwa matarka kulawa, ka rarrasheta ka kuma janyota ajikinka, ka bata gata na musamman wanda t rasashi a baya ka shayar da ita zumar dabatasan ma akwai kafuwarta a duniya ba,ka bata soyayyaarka kakuma sota ka miqa mata ragamar rayuwarka" D'ago kanshi yayi ya dire rinannun jajayen idanunshi akan Zuhair ya had'iyi wani yawu me d'acin gaske wanda yake a daskare sannan yace
"Tayaya zan nemo soyayyarta bayan tana hannunsu, yaya zanyi in ganta harna nuna mata zallar qaunar danake mata?" murmushin yake zuhair yayi
"*AGADAZ* agadaz zamuje gunta Abbas bazamu saurarawa neman yardarta ba harse ta aminta damu" sauke qwayar idanshi yayi akan agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunshi yace
"Xamu iya zuwa yanzu?" jan kotar zuhair yayi seda suka hau titi da kyau sannan yace "Canma zamu da yardar Allah yanxunnan kuwa" batare da wani ya qara yin magana ba suka kama hanyar agadez....
*Niger republic agadaz*
Misalin k'arfe 8 na dare suka iso garin dayake da yalwar ni'ima da sanyi, me kyaun tsari d'aya daga cikin manyan garuruwan dake cikin birnin Niger...kai tsaye fada suka nema, tunda suka tinkari fadar qirjin Ali Abbas ke dokawa, haka kawai yake gani tamkar ya tab'a tako duga duganshi wannan fadar, sam ya kasa nutsuwa tabbas yasan wannan wurin kuma ya sani ya ziyarci wurin so kusan biyu ziyartar ma tare dame martaba da Ummu suka yita in hakane me kenan hakan ke nufi Manga er uwarsace? To amma ta ina?,bashida amsar wa ennan tambayoyin a haka akai musu iso wurin sarki babu shakka wannan sarkin yafi wancen karamci da komai domin kuwa bema buqaci sanin su waye ba haka ya sanya aka dinga hidima dasu, haka seda suka huta sannan ya kallesu yace
"Kai wannan dakace sunanka Ali Abbas kana kamanni da wacce na sani a qasarku da kuka baro, kodagacan kuke yola?" kallonshi Ali Abbas yayi yace
"Ea to daga sokoto muke gidan sarkin musulmi Muhammad Auwal ni d'ane a wurinsa kuma kiji a wurin Manga jikarka,sedai kam lallai iya indai ta gidan sarkin yola kake magana ba shakka ni dinnan jikan tane,itace ta haifi mahaifiyata ta cikina" murmushi ya sub'uce masa yace yana jinjina qudira ta ubangiji
"Lallai wannan auren naka da Manga had'i ne na Allah, naji labarin komai daga bakin mahaifiyarta, kuma naji hukuncin sarki akan aurenku, ni bazan hanashi iko da jikarshiba amma zan je da kaina na bashi shawara karya kuma aikata kuskuren daya aikata a baya ya bari har idan yarinyarce tace bataso, ita haryau ma batasan me ake ciki ba sabida ba wanda ya sanar mata, Iya dakake gani ai da ita da uwar mahaifiyar Maman wato uwar Inno uwarsu daya ubansu daya, na tabbatar kasan cewar er Niger ce a garin k'wanni to kaji hadin Allah ka auri er uwarka da jini batare dakun sani ba,yanzu kai dama d'ane awurin Adama?lallai wani ikon se mahalicci kaga yanzu wannan ma wani qarin danqon zumuncinne tunda yake basa zuwa muma haka sekace zumuncin nesa sedai idan akwai lalura su hadu da iya a k'wanni,amma rabon iya ko Adama danan garin inaga tunkan ka kai shekaru goma aduniya" wani sanyin d'adi yaji ya ziyarcesa ya saki wani lallausan murmushi koba komai ya sani se inda qarfin iya ya qare wurin ganin anbarshi da Manga Allah ya saka mata san auren zumunci bare kuma uwa uba shine d'an tsakiyar tsoron kanta afagen lele
"Allah ya qara d'aukaka hakane, zuwan mu nan nakeji ajikina tamkar na tab'a zuwa nan wurin ashe banyi kuskureba gida nazo, ko zan iya ganin Manga?" murmushi sarkin yayi ya gano Ali babu komai da kowa a ranshi se Manga yace bayan ya miqe fadawa sun kareshi da manya manyan rigunansu
"Ku masa iso a masaukin baqi, kuma jekadiya ta kai Manga gareshi cikin awa d'aya" Godiya ya dinga yi har sarkin ya b'acewa ganinsa sanan ya qamqame Zuhair yana ihun murna yace
"Anzo gurin abokina wlhy gida nazo, wancen dattijon be isa ya hanani matana ba wlhy" murmushi zuhair yayi yace "Kai gadanga bafa kada kirki wlhy ni tashi muje kaji kar wani ya ganka" ba musu ya tashi suka fita.....
*Bayan awa daya*
Zaune suke a babban parlor dake bangaren masaukin na baqi, a yanda suka kula anan zasu kwana hira sukeyi jefi jefi na al'a dun qasar Niger, suna mamakin yanayin al'adun nasu acewarsu kowane tsuntsu kukan gidansu yakeyi, ko kalar cimarsu da Niger iri daban daban suko maggie be wani dame suba a girki, da sallamarta ta shigo d'akin jakadiyar da wata mata sun rakota se zuba qamshi takeyi cikin shiga irinta 'ya'yan sarakuna,se kirarari suke mata
"Takawarki lafiya Rangida Manga,er sarki jikar sarki, matar sarki kuma....takawar ki lafiya me farin jini, anyi farar haihuwa kuma kema farar zakiyi inshaa Allah" ya mutsa fuska manga tayi ta tsani wannan ihun dasuke mata aka wanda ita sam bata gane komai ta kallesu a wahalce
"Ku tafi kawai zan gana da baqona" kallonta zuhair yayi yanda ta sauya mulki da sarauta sukayi matukar karb'ar yanayinta yace aranshi "Shisa ba'ason wulaqanta mutum, yanzu duk iya wulaqancin da huddy tagama yiwa manga takereta a matsayi gaba da baya ko wane dangi datake dashi jinine na sarauta me qarfin gaske uwa uba ko taqi kota so Manga ce uwar gidan ta.... Kallon ta Ali Abbas ya miqe yanayi ita d'inma shi take kallo ganin kallon kallo din nasu bame qarewa bane ya sanya ta mayarda dubanta zuwaga zuhair sosai ta sake masa fuska,dama ta sanshi kuma yanda ta saba haka ta masa har qasa ta duqa ta gayar dashi mamakin rashin girman kanta yake dukda ta gano asalinta,cikin sakin fuska sosai ya ansata suka gaisa sannan ya basu wuri, miqewa tayi daga tsugunon da tayi dama shi a tsaye yake be zauna ba, matsowa tayi daf dashi sanye da murmushi a fuskar ta tace
"Ina maka barka da zuwa,yaya hanya ya kuma gajiya?" murmushin shima ya sake ya damqo hannayenta duka biyu ya sumbaceta a hannun sannan yace
"Hafsat kin bani wuya,tun yaushe rabon danaji muryanki,mesa kika zab'i azabtar dani ne hafsat?" ya fad'a tare da langwab'ar dakai tamkar qaramin yaro,hakan dayayi seya bata sha'awa har wani qayataccen murmushi ya sub'uce mata tace tana qoqarin zame hannayenta daga nashi
"Bansan da zuwanka sorry na barku kuna jira" kallonta yayi yanda take qoqarin kawar da zancen dayake mata,zama yayi shid'inma kusa da ita yace
"Amma dai kin shirya komama Nigeria ko, sabida gaskia na gaji da rashinki a kusa dani" murmushi tayi
"Nina dawo Niger kenan yaa Ali,dan Allah kama dena zancen komawa na garinku" kallonta yayi batare dayayi magana ba, sabida yanda yaga bilhaq da gasken takeyi, kodai tasan sharad'in da kakanta ya gindaya ne akan aurensu, ba kamar yanda akace bata sani ba
"Kana kallo na yaa Ali, bana so ka b'atawa kanka lokaci sabida zancen gaskia yaa Ali nina rigada nazo gidan gata, bazan koma inda ba'asan daraja taba" juyawa yayi ya fuskanceta ya riqe hannayenta duka biyu
"Baby dan Allah karkice haka, ki yarda da qaddara komai ya wuce wlhy hafsat ina sonki some yawa me kuma tsananin gaske,ki bani dama in saka miki da alkhairin ki fiyeda wanda kikamun, ki bani dama in nuna miki kalar qaunar danake miki,ki bani dama in nuna miki kalar sonki danake,ki bani dama mu rayu dajuna" fincike hannayenta tayi miqe tsaye, qwallan datake tarewa ya silalo mata tace cikin d'aga murya
"Dama!!! Dama kake cewa in baka fa yaa Ali,kasan meye ma'anar dama kuwa? Kasan amfaninta? Kasan muhimmancin dama awurin d'an adam? Kasan gudummawar da dama ke baiwa rayuwar d'an adam? To idan baka sani ba bari kaji in gaya maka... Dama itace wacce takeda sauqin samu awurin d'an adama kuma take cikin abubuwa masu sauqin sub'ucewa d'an adam,yayinda sub'ucewar ke matuqar tarwatsawa d'an adam lissafi sabida sam ba'a samun dama ta biyu idan akayi sakaci da ita.....ka sani yaa Ali ka samu dama fiye da d'aya sab'anin wasu da sam idan ta farkon ta wuce shikenan ta sub'uce musu har abada....karkayi tsammanin bana sanka,sam ko d'aya kaine namiji na farko danaso tun farkon sanina dakai, kuma ka sani bakada na biyu a wurina, na soka fiyeda komai da kowa,na soka da fuskar ka ta qarya sannan na sanka da fuskarka ta gaskiya, na yarda zuciyata da taka ne a had'e amma inaso kayi hakuri ka sani cewar nayi iya qoqarin in manta wulaqancin dakamun amma sam na kasa manta komai, dan Allah ka hakura dani kamar yanda zan hakura dakai, ka manta dani kamar yanda zan mantaka a rayuwa, ka fita arayuwata kamar zan fita a taka daga yanzu har abada....." tana gama fadar haka ta juya da gudu, yayinda tabar shi cikin tsananin tashin hankali da qunan rai me tsananin gaske,ya dasqare a wurin se wasu zafafan hawaye dayake saukewa....
Mom Nu'aiym....
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
18
Da baya da baya ta koma ganin yanda kawu bala ya qura mata ido (yayan innoh) yanayin kallon dayake mata kadai ya sanya ta fahimci cewar yaji komai kuma ta gano ya shaqa sosai ba kadan ba, dama tun zuwansu gidan ta kula yanada zafi sosai da hannu ya mata alama akan ta koma ciki ba musu ta juya qirjinta na tsananin dokawa, a qasa ta zube yayinda Ali Abbas ya qura mata idon shi da suma rine sukayi ja tamkar gaushin wuta, be iya cewa da ita qalaba har kawu bala ya shigo parlor d'in da sallamar shi,miqewa Ali Abbas yayi ya miqa masa hannu sabida sun had'u a fad'a, sosai yake qoqarin saisaita nutsuwarsa karya fahimce matsalar dukda yake ya soma fahimtar wani abin....zama yaga kawun yayi shima ya zauna kawun ya mayarda dubanshi zuwaga Manga yace cikin nutsuwa
"Hafsat ki sani bazan miki fad'a ba, sabida na sani kinsan ciwon kanki, zan dai yi qoqarin tunasar dake abubuwan danake da tabbacin kin sansu mantawa kikayi,da farki dai kinsan kalmar zawarci ko a fad'i ba tada dadi sam bare kuma shiga acikin layin zawarawa masu jiran tsammanin dababu tabbas, ki sani yanzu zawarawa neman miji suke ido rufe, kin girma kin isa kisan me duniya take ciki sabida haka yanzu na miki tuni akan siyawa kai zawarci, abu mafi muni shine tsinuwar Allah dakike janyowa kanki kina hanawa mijinki haqqinsa, kana kina neman saki da kanki, ke a wa da zaki keta haddin Allah? Kinsan abinda kike fad'a kuwa?, ki sani dama kakanki na wurin uba ya rantse seya raba aurenki da mijinki koda kotu ne se sunje sekije ki biye masa ku shiga hurumin Allah,dandai iyakar sanina aure raine dashi kuma se ranar ajalinsa ze qare lallai ki nutsu ki rungumi mijinki sau da qafa kuma ki tabbatar kin bashi kulawa ta musamman, me martaba be turoki wannan sashen danki ci zarafin sa ki wuce ba anan zaki zauna ki kwana atare da mijinki harse ranar daya shirya barin garin nan, dama aikoni kurun akayi na kai abokinsa masaukinsa na daya baren ke kuma ku zauna anan gidan" sadda kanta kurun tayi qasa batai magana se hawaye, yaya zatayi ta aiwatar da shirinta bayan idan ta kalli qwayar idanshi yana saukar mata kasala da wani qaunarshi, duk sanda ya matso daf da ita hakan yakan saukar mata da wani shauqi na musamman gaurayuwar numfashinsu na saukar mata da tsananin nutsuwa da farin ciki,duk yayinda ya had'a hannayenta da nashi ji take tamkar bazata iya haqura dashiba harse ta manna jikinta da nashi.....taso yasan muhimmancin ta a rayuwarsa amma bazata taba iya aiwatar da hakan ba sabida ganinsa kurun yana hanata aiwatar da dukkanin ayyukanta,kallonshi tayi bayan kawun yabar wurin shida zuhair sunbar part d'in gaba d'aya tace
"Zanje na shiryo kayana ka bani awa