Showing 60001 words to 60927 words out of 60927 words
Chapter 21 - Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel By Billy Galadanci.txt
baiwa kowa dariya har Ameen yace laaa Ummi shagwaba kike kema, amma kullum sekina dungurin madeena wai kukan banza ne da ita da shagwaban tsiya" dariya suka qara sakawa ummu tace
"Gwara da ake dungurin kishiyata, dama anzo kwacen miji kuma kurwarshi kur" kwanciya akan cinyar ummu Manga tayi tace
"Uwa me dadi kaga ni bazan koma saudia ba idan kun tashi ku tafi abinku" bece komai ba se Ameer ne yace
"Idan mukace Amusement park bazaki hau lilo da dragon ba kuwa" kowa se ya kwashe da dariya Ameer an qara samun baki shekara shida se wayon tsiya, shafa bayanta ummu tayi tace
"Auta kinsan yanzu kin qara girma ko, kalli yanda kike neman b'allamun qafa dan Allah, lukuta niki d'agani dan Allah" murmushi tayi ta qara lumewa ajikinta tana cewa
"Kai ummu yanzu nice lukuta,tun yaushe rabon daki sakani a idanki,gwara ki barni in biya bashin danaci" rankwashin ta tayi ta dafe wurin tana shura kafa yayinda Abin ya matuqar burge Ali Abbas yakuma baiwa Ameer harma da Ameerah matuqar dariya suka kuwa dara ummin su tana shagwaba irin na yara...sun wuni suna raha abinsu se la'asar sakaliya suka bar gidan zuwa gidansu innon Iroh Baban Manga....Bayan gaishe gaishe aka kuma shiga hirar rabo, anan ne Baban Manga ke sanar musu mahaifinshi yazo ban haquri kuma komai ya wuce dan Haka su shirya zuwa Niger kai Madeena aganta tare dashi zasuje kuma bazasu dawo ba shida innoh kasancewar an saka rana mahaifinshi zeyi murabus shiya hau karagar mulkin.....sunyi murna matuqa daga haka aka tsaida ranar tafiyar....
*Niger republic*
Kowa seda ya hallara aka daura mahaifin Manga kan mulkin qasarsu ta yamai, inda abin Mamaki Mahaifiyar Manga ciki ne da ita harna watanni hudu amma bata gayawa kowa ba se manga acewarta kunya ma takeji wlhy, haka dai akai shagulgula irin na al'ada masu ban sha'awa aka watse, mahaifin Baban Manga ya baiwa me martaba sarkin musulmi da ahalinshi haquri kuma komai ya wuce......
Tafiya takeyi a sukwane,tayi baqi qirin zaka rantse da Allah ba Ammyn su huddy bace yanda ta lalace, a wani gindin ice ta zauna, a garin na Akrah dake cikin birnin Ghana se kallon motocin dake shawagi takeyi, sam bata iya tunano rayuwarta ta baya ko sunan ta, gabaki daya ta fita hayyacinta kowa kallon mahau kaciya tuburan yake mata, Mahaifinsu huddy daya taho gana siyan wasu qarafa acan ya hangota zaune tana zare idanu, kallo daya ya mata qirjinsa ya doka, me taxi din ya tsayar ya fito daga cikin motar yaje gareta,kallonshi tayi amma sam bata gano shiba, gashi dai a kasan zuciyarta tanaji tasan wani abu gameda wannan mutumin amma sam ta kasa gane komai, shine yayi qarfin halin kiran Allah
"Asabe kece anan, haukace wa kuma kikayi?" yana fadar sunanta komai ya soma dawo mata ta soma zare ido tana mai magana tsawa ya mata yace
"Tunda naji mugun abinda kika aikata ne ya dawo miki na denw nemanki, ki sani tun na sakeki bakida igiyar aurena akanki,sannan kuma yarki hudaisa Allah ya mata rasuwa tun watanni takwas da suka wuce, tace kuma kimata gafara, ni kinga tafiya ta....." hannu ta daura akai ta zunduma ihu yana sauri ya shige taxi din yabar agun kokadan baze iya taimakon wamda be taimaki kanshi ba shikam....mdaya dawo ya sanar wa kowa yanda sukayi iyayenta ne sukaje nemanta suka dawo da ita amma maganin duniya sunyi bata magana se idan ta haukace...mm
*Bayan shekaru biyu*
Kallon d'uwawun Manga Ali Abbas keyi har inda ta bacewa ganinshi, tashi yayi yabi bayanta a dakin data shiga yace bayan ya zauna yana shafa duwawun dayake matuqar daukar hankalin sa
"Manga wai kinsan kin qara budewa, ni arayuwa inasan jikinkin nan wlhy, kina burgeni sosai, bana iya dauke idona daga gareki duk sanda na ganki" murmushi ta sakar masa tace tana shafe kwantaccen sumar qirjinsa
"Yaa Ali aini takace, kayi yanda kakeso da jikina" sirirn hancinta yaja yace
"Kinga ni naga nawar inmiki ciki ma wlhy, yau dai sena miki ciki, ai madeena ta zama budurwa kusan shekaru uku fa,sisin ya isa haka" zillewa tasomayi ya soma mata cakulkuli tana qyalqyala dariya, samun sa'ashi tayi ta haye ruwan cikinsa tace
"Nice da kaina zan ma ciki yau, ka kwanta abinka kawai" dariya suka kwashe dashi dukkansu.....
Tammat bi hamdillah.......
Wanda suka aiko saqonni da wanda sukamun waya akan aqarawa Ali Abbas tsawo don Allah suyi hakuri wlhy abubuwan ne sukazo da haka basan raina bane,bakuma naki daukar shawaranku bane kuna raina
Suby ladan kece ta farko
Pheey tawa ina matqar yinki
Hafsatul Elham ina qaunarki besty na
Halima Umar keta dabance my fulani bata biyunki
Phertyma zahra babbar qauna ta Allah ya nunamun aurenki
Maman khadyy ubangiji ya kawo mana zuri'a rayayyu kuma muminai
Kdeey ke kikebin pherty inayinki sosai sosai
Doughter Allah ya kawo miji na gari kuma yabaki hakurin rashin mijinki na baya
Duk wanda ban anbaci sunanshi ba yana raina......naso inja lokaci me tsawo banyi rubutu ba,amma akwai wani saqo akwai saqo me dauke da tarin ma'anoni me ma'ana wanda sam zumudi baze barni naja lokaci me tsawo batare dana isar da wannan saqon me matuqar muhimmanci ba....Amma fa saqon dole se maganganu masu nauyi sun shigo aciki kazancewar yanayin saqon dole batsar itace agaba, Allah ya gani salo da tafiyar rubutunce zatazo da haka bani ba, so duk wanda yasan ze zageni karma ya soma bi,dan gaskia zan iya shari'a dashi ko waye.......Na sake maimaitawa saqon zezo ne da maganganu masu nauyi kuma wanda ze amfani kowa so bazan hana kowa bi ba......
Zaku iya ganin shi yau ko gobe ko anjima koma yaushe idan Allah yayi......
Mom Nu'aiym ke muku fatan alkhairi.