Showing 27001 words to 30000 words out of 72189 words

Chapter 10 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt

17 Mar 2026

53

ke da wuya Jinah ta fada jikin Dauda tare da fashewa da kuka.

-Kayi hakuri dan Allah Dauda, na haifar da abubuwa da dama cikin danginku. Naji dadin ganinka ka warke. Ka yafe mani dan Allah, da cutar da kai da danginka da nayi. Mutanen nan suna da gaskiya, ni may...

-Shiit, yi shuru ya isa haka...

Shiru dakin yayi, babu abinda ke tashi sai sheshekar kukan Jinah. Dakatar da shurun Dauda yayi bayan wani dan lokaci.

-Ko kin san lokacin ne nafi bukatarki, abinda yafi min ciwo, lokacin na dawo hayyacina ban ganki ba, da na tambaya aka ce mani kinyi tafiyarki, naji ciwon haka marar misaltuwa. Bai dace kiyi tafiyarki ba Jinah, haka nayi ta nemanki domin yayan Sarah bai so fada min inda kike ba. Yi tunani idan da ban ganki ba, halin da zan shiga.

-Kayi hakuri, ka yafe mani.

Jinah ta fada tana kara shigewa jikinsa.

-Ban yi fushi dake ba, amma kiyi min alkwari ba zaki kara tafiya ki barni ba.

Murmushi tayi, taji dadin ganinsa da tayi cikin koshin lafiya, ya warke sumul.

-Ina sonki!

Dauda ya fada yana kallon fuskar abar kaunarsa da ta kasa cewa komai, kallonsa kawai take itama. Kukan jariran Jinah da suka tashi bacci ne ya katse masu yanayin da suke ciki.

-Ya Allah! Wai sune haka?

Cewar Dauda cike da mamaki ya nufi inda jariran suke.

-Wow masha Allah, kyawawa dasu!

Kallon yaran yake yana murmushi, yana ji tamkar nashi. Wasa ya fara yi da yaran da har ya fara manta damuwar da ke tare dashi. Jinah ce ta katse masa nishadin da tambayar da tayi silar kawo damuwa a fuskarsa.

-Dauda, me yasa ka nuna min kamar akwai aure a tsakaninmu?

-Ban gane ba?

-Akwai wata rana da muka je ni da Sarah wajen wani waza'i, nan naji malamin yana fadar, ba'a yin aure idan macen na da ciki, idan kuwa aka yi to auren bai halatta ba. Nasan ka sani, dan ina lura da yanda baka son tabani. Me yasa kaki fada min?

Wani yawu Dauda ya hade kafin yace

-Eh hakane, ina ganin wannan ita ce damar da zan samu ta kasancewa a kusa da ke. Kiyi hakuri da karyar da nayi maki.

-Taimakona ne kayi, nagode sosai.

Shiru ya dan biyo baya kafin Dauda yace

-Jinah!

-Na'am?

-Zaki aureni, auren gaske a wannan karon?

-Eh sosai ma!

Wani kayataccen murmushi tayi tare da gyada masa kai. Ta amince zata aureshi, dan ya cancanci komai, kuma tana fata itama wata rana ta soshi. Sungumeta Dauda yayi yana ta juyin farin ciki da ita a cikin dakin.

-Ba zaki san wane irin farin ciki yau nake ciki ba, ina cikin matukar farin cikin da yafi kalmar farin ciki. Nayi maki alkawarin ba zaki taba nadama ba. Gobe kenan za'a daura auren?

-Gobe?

Ta fada tana fiddo ido.

-Eh mana gobe, ko yayi nisa?

Fashewa da dariya Jinah tayi.

-Dauda, ba fa guduwa zan yi ba, dan haka ka kwantar da hankalinka! Gobe yayi kusa!

-To naji nan da kwana uku?

Nan suka fara jayayya har dai ya yarda akan nan da sati biyu.

Daukar Ayu Jinah tayi, shi kuma Dauda ya dauki Aya, suka fita dan sanar da Sarah labarin auren.

-Sarah, aure zamu yi nan da sati biyu ni da Jinah!

Dariya Dauda yaba Jinah ganin yanda yake maganar kamar yaro.

-Ah madallah, nayi murna kwarai!

Cewar Sarah tana tafa hannu.

-Na tayaku murna!

Cewar Abdul.

-Nagode nawa (abokina)

-Zan iya daukar yaron?

-Eh, me zai hana?

Cewar Dauda yana mai mika masa Aya dake hannunsa.

-Woww! Mace ce ashe, kyakyawa masha Allah! Zo ki gani Nafi!

Ko kallo bai samu ba daga yar uwar tashi, ya cigaba.

-Wayyo dubi idanunta kamar Barbie, dubi lebenta duka kalan pink, har da ma dimples idan tayi dariya, masha Al...

Duk yana yin hakan ne dan jawo hankalin yar uwar tashi dan ya santa da masifar son yara kanana. Ai kuwa yayi nasara, tashi tayi ta nufi wajen Jinah ta karbi Ayu dake hannunta.

-Ai daman nasan ba zaki iya jurewa ba.

Cewar Abdul yana mata dariyar keta.

-Ni kyaleni!

Nafi ta fada tana turo baki, dariya sauran sukayi.

-Oh ni bari na tashi na hada mana abinda zamu ci, dan nasan kun fara jin yunwa.

-Wallahi kuwa, dan cikina har ya fara yaren Chinese.

Cewar Dauda.

-Ai bai kai nawa ba.

Cewar Abdul.

-Ai kai dama cin tsiya ne da kai.

Cewar Nafi, dariya dukansu suka yi.

-Ba sai kin wahalar da kanki ba Sarah, zamu je ni da Jinah mu siyo abincin a waje.

Cewar Dauda.

-Eh bari sai muje mu siyo dan na rogo. Fatan dai kunsan meye haka?

-Sosai ma, a cen akwai wata yar Nijar dake soyashi kusa damu.

Cewar Abdul.

-Ai na fada maku ba abinda ya sani sai ci.

Nafisa ta fada. Kowa ya kwashe da dariya. Bayan wani dan lokaci Jinah da Dauda suka nufi kasuwa.


(.....)


Dare yayi sosai, Jinah ce daga ita sai yan tagwayenta kwance akan gado. Juyi take ta yi idanunta rufe amma ba bacci take ba. Tana jin kamar mutum a kusa da ita amma bata ganinsa.

-Jinah, abar kaunata, kalleni nine Fally!

Eh Fally ne, mutumin nan dake kusa da ita wanda ta kasa ganinsa. Fally ne a gabanta, farin ciki ne fal a ransa gashi ga rabin ransa, cike da zumudi ya kai hannunsa kan gashinta yana shafawa, ganin idonta a rufe hannun nasa yakai kan fuskarta yana shafawa, ita kuma Jinah ji take yi tamkar ana shafa mata wani narkakken karfen da aka sanya a wuta. Abun bai ishi Fally ba, duko kansa yayi yana sumbatar wuyanta, a hankali ta bude ido. Baki Fally ya wage kai kace gonar auduga.

-Jinah abar kaunata!

Ya fada, ita kuma dube dube ta fara kamar wadda hanya ta bacewa. Anan ya fahimci ba ganinsa take ba. Wani haushi ne yaji ya turnukeshi, sai dai bai ida gasgata abinda zuciyarsa ke fada masa ba, yanke sharawar ya bayyana mata kansa yayi. Tsalle daga kan gado Jinah tayi, tare da kwala wata gigitacciyar kara... Tsoro duk ya kamata, jikinta sai rawan mazari yake.

-Jinah nine fa! Fally naki!

-Dan Allah kar kayi min komai, kar ka cutar dani dan Allah! Dauda! Dauda!

Ta shiga kwalawa Dauda kira.

-Kinyi alkawarin fa ba zaki manta dani ba!

-Dan Allah ka tafi, bana son ganinka!

Jinah ta fada, da alama bata jin ma abinda yake fada. Kofar dakin ce ta bude da karfi, ba kowa bane face Dauda. Sai dai Fally tuni har ya bace, ko Jinah bata ganinsa.
Ran Fally yayi matukar baci, ta yanda yake ji tamkar ya ciro zuciyarsa yayi jifa da ita nesa. Cikin awowin da basu wuce 48 ba, ya rasa uwa da uba, gashi kuma wadda dan ita komai ya faru wai ta kasa ganeshi.

"Kawai zan kyaleta da sauran aljanun su cutar da ita ma, me yasa zan kare wadda tayi sanadin wargajewar rayuwata? A'a ba zan iya ba, taci amanata!!!!"


---------------------------


Salam, miss u many, realy lol.

Bon, ina fata zaku ji dadin wannan chapter. Kar kuyi tantamar fadin kowanne ra'ayi naku game da wannan chapter, haka idan ma kalamai sunyi maku karanci zaku iya bina da stickers marar iyaka. ๐Ÿ˜‚

Merci de toujours vous retrouver mรชme si je tarde a publier, je vous adore ๐Ÿ’˜ vous รชtes les meilleurs.

Sai mun hadu a wata chapter. ๐Ÿค—

Kusha ruwa lafiya ๐ŸŽˆ

@El_Ashtar

๐Ÿ’ž JINAH (Matar Aljani)๐Ÿ’ž
by Malik al-Ashtar โœ’๏ธ

On wattpad ๐Ÿ‘‰ https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New โค๏ธ Story

CHAPTER 12

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).๐Ÿ’ฆwe are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest๐Ÿ’ฆ

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

A wajen aljanu idan daya daga cikinsu ya fada soyayya da dan adam. To fa mawuyacin abu ne dan adam din nan ya manta da soyayyar dake tsakaninsa da aljanin, sai idan dai wankin kwalwa aka masa kuma hakan na faruwa ne ko daga cikin iyayen aljanin ko kuma shi kanshi aljanin wani yayi wa dan adam din wankin kwalwa ta yanda ba zai kara tuna wata soyayya da yayi da aljanin ba. Wani lokacin kuma soyayyar da dan adam din yake wa aljani idan ya samu wani masoyin da suke jinsi daya wato dan adam kuma har yaji yana kaunar wannan dan adam din to zai gama har da shaukin soyayyar da yake wa aljanin duk ya juyeta akan dan adam din, to hakan na faruwa a hankali zai fara manta soyayyar dake tsakaninsa da aljanin. Shi yasa Fally yayi tunanin babu yanda za'ayi iyayensa su yiwa Jinah wankin kwalwa, dan suna son Jinah kuma ba zasu so ta mantasu ba. Sai dai kuma hakan ce ta kasance, mahaifiyarsa tana son Jinah, saboda haka, bata son wani abu ya samu Jinah, bata son Jinah ta tuna dasu har tayi kokarin nemansu, idan da bata manta komai ba da tuni ta shiga nemansu kuma kafin ta nemosu tana iya fadawa hannun muyagun aljanun dake son cutar da ita, bare kuma yanzu da har tanada tagwayen da kowanne aljani yake da burin mallakarsu ba. Dan haka wankin kwalwa da mahaifiyar Fally tayi mata ba don komai bane face dan ta tseratar da ita.

Ganin yanda Jinah take tadi da Dauda, suna yi suna kyalkyata dariya da irin kallon da suke yiwa junansu yasa Fally yake tunanin soyayyar da Jinah ke masa a yanzu ta koma kan Dauda, wato kenan Dauda ya maye gurbinsa. Tunani ya fara, yanzu duk wannan sadaukarwa da nayi a kanta! Sau da dama har sai yayi yunkurin tafiya ya barta in yaso aljanun su cutar da ita, amma sai ya kasa. Ga kuma 'ya'yansa dake hannunta, yana son yaran sosai domin da ya kalli yaran wani farin ciki ne ke ziyartar zuciyarsa. Suma kuma tagwayen suna ganin Fally amma sun kasa fahimtar waye shi, ba zasu gane matsayinsa ba har sai sunyi shekara daya da haihuwa kuma a kullum wannan ranar yake daukin jira.

Kwanaki da yawa sun shude, Fally bai bar gidansu Sarah ba kuma bai bar ganin abin takaicin dake faruwa ba tsakanin matarsa Jinah da kuma wannan mutumin wato Dauda. Sai dai farin cikinsa a kullum babu yanda za'ayi wani abu ya shiga tsakanin Dauda da Jinah domin har yanzu matarsa ce. Jira kawai yake lokacin da tsautsayi zai dauki Dauda yace zai kusanci Jinah ya gane kurensa. Shima haka take bangaren Dauda, yana ji tamkar ya matso sauran ranakun da suke rage na aurensu, yau ace ga Jinah a dakinsa a matsayin matarsa.

Kamar kowanne Marece tun ranar da yazo, Dauda ne da Jinah a zaune tsakiyar gida suna tadi.

-Kwana biyu kawai ya rage ki zama matata...

Dauda ya fada cikin yanayin farin ciki. Murmushi Jinah tayi. Shi kuma ya cigaba:

-Matata! Oh har na tuna da wata waka, Sunanki mai dadin fadi, kin ratsa zuciya! Kowa yazo za ayi nadi kece Sarauniya....

Dakatawa yayi da wakar ganin Jinah ta kyalkyace da dariya.

-Kushe miji fah ba kyau...

Dauda ya fada yana tamke fuska, irin dagasken nan yake.

-Eh koda yana waka da murya kamar gwangwani!

Ta fada tana dariya.

-Eh din!

Dariya dukansu suka yi. Shuru na dan wani lokaci ya biyo baya, Jinah ta lura Dauda hankalinsa yayi wani gu, ya fada duniyar tunani. Hannunsa Jinah ta kama tareda kallonsa a natse cikin ido.

-Har yanzu baka son fada min dalilin dake sanyaka cikin wannan dogon tunanin. Dan Allah ka fada min me yake damunka?

Wani dogon numfashi Dauda yaja, wanda Jinah bata fahimci komai ba, domin shiga yanayin bakin ciki ba dabi'ar Dauda bace, mutumin da kullum cikin raha yake.

-Me yasa dan Adam butulu ne? Me yasa soyayyarshi da dukiya ta wuce kima? Me yasa in dai akan kudi ne, soyayya, dangi, zumunci ba komai ba ne? Jinah da kinsan abinda ya faru bayan tafiyarki. Ya...

Sauran kalaman tsaya masa suka yi a baki. Hannu yasa yana goge kwallan dake shirin zubo masa.

-Kayi hakuri Dauda...

Jinah ta fada cikin Sanyanyar murya.

-Kinsan me yasa nake sonki, zuciyarki tsarkaka ce! Babu digon hassada ko keta a cikin idonki, fuskarki tana bayyana tsantsar gaskiya da mutuntawa. Imanina yana karuwa ta dalilinki, na kan ce koda munafukai da maciya amana ba zasu dakata da gurbata duniya ba, za'a samu mutanen kirki kamarki.

Ya fada cikin murya mai nuna yakini a maganarsa, wanda kuma yasa Jinah ta yarda lallai akwai wani babban al'amari da ya faru dashi bayan tafiyarta.

-Ka fada min abinda ya faru.

Ta fada cikin raunanniyar murya.

-Lok..loka..lokacin da na farka daga dogon suma, na samu labarin mahaifina ya rasu, anan, na tabbata bakin ciki yayi mana sallama. Yayinda dangi ke cikin jimami, Kawuna Mati, yayan mahaifina yazo, ba mutumin da na tsana kamarshi, tashi da mahaifina bata taba zuwa daya ba, shine kadai dan uwan mahaifina da ba a cikin dangi yake da zama ba. Kwana hudu da faruwar wannan masifa, kawu Mati yazo gida cike da zumudi da murmushi har kunne, ya nemi da dangi su hadu yana son magana damu. Duka muka hadu a tsakar gida, wasu takardu ya fiddo, wasu banzayen takardu wai na masana'antar mahaifinmu da kuma na gidanmu duka nashi ne. Bamu yarda da hakan ba, domin wannan ba zai taba yiyuwa ba, dattijawan garin aka kirawo da yake duk ya siyesu, har da kuma Kawunaina sai daya kawai da yace shi bai yarda ba haka yayi masa korar wulakanci shi da iyalinsa. Gashi manyan yayyena Idrisa da Isa basu duniyar, sauran kuma biyun yayyena sun tafi kasar waje gashi babu takardun dawowa a lokacin. Dayan yayan nawa kuma yi yayi kamar abun bai dameshi ba, ni kuma, nayi iya kokarina daga karshe ma korarmu yayi ni da Mahaifiyarmu da kuma kannena, inda Allah ya taimakemu dangin mahaifiyata sun karbemu hannu biyu. Na samu kuma labarin yace zai auri sauran mata biyun babana, idan basu yarda ba, zasu iya bar masa gida. Kuma kinsan mu anan, mata ba aiki suke ba, kenan ta yaya zasu iya ciyar da ya'yansu idan kuka bar gidan, kuma komawa wajen iyayensu a wannan lokacin abun kunya ne. Haka yasa biyun matan babana suka dawo matan kawuna, saboda ya kori mahaifiyata kuma Tanti Habi ta haukace. Sannan kuma ya sallami wasu kawunaina daga aikin masana'anta domin ya saka yan'yansa da kuma wadansu da suka taimaka masa wajen samun komai. Uwa daya uba daya yake da babana, amma bai ji ko digon imani ba wajen tarwatsa masa ahali. Na kudura a raina sai na yaki wannan zalunci da yayi mana, duk da mahaifiyata tace na manta komai, ba zan iya ba.. Jinah naga tsantsar rashin imani na dan adam...

Shuru yayi, ita kanta bata san me zata ce ba jin kalamansa, ta razana da jin labarin kuma taji ba dadi. Rungumesa tayi dan tunanin shi daya abinda taji zata iya, amma basu dau lokaci ba. Shuru dukansu suka yi, kafin wata murya daga bayansu ta katse shurun.

-Ba laifin kawunka bane, shi ne! _Yana nuna yatsa zuwa sama._ Ba shine ke da ikon komai ba? Me yasa ya bar wannan mutumin ya cika burinsa, kamar kuma yanda ya dauke min mahaifiya?

Abdul ne ke fadar haka lokacin da yaji labarin Dauda. Zaunawa kusa dasu yayi.

-Muna sallah, muna azumi, muna yin duk abinda ya wajaba a kanmu, muna kuma barin duk abinda aka hanemu! Toh me yasa kullum mune cikin masifa? Irin kawunka ya kamata su shiga irin wannan halin ba mu ba!

-Abdul. _Cewar Jinah kafin ta cigaba cikin tausashiyar murya._ Daga Allah muke kuma gareshi zamu koma.

-Amma ya kamata ya barmin ita, naso ace har na kai matsayin da zan sanyata cikin farin ciki, na bata duk wani jin dadi na duniya, na mayar da ita tamkar sarauniya, kar ta rasa komai na rayuwa kuma ta dinga alfahari dani.

-Akwai lokacin da ina cikin damuwa sosai, wani ya taba fadamin, idan bakin ciki ya bubbuga mana kofa, ko ya adadinsa yake, mu kasance masu godiya ga Allah, wannan ba wani abu bane face jarabawa domin jarraba imaninmu. Kuma a lokacin da muka koma gareshi zaka ga ya saka mana da mafificin alkhairi. Komai ya samemu na dadi ko akasinsa dole mu kasance masu godiya ga Allah. Kuma mutumin da ya fada min haka ba kowa bane kai ne Dauda, to kenan kai ba zaka yi amfani da nasihar da kayi min ba? Kai kuma Abdul, uwa bata bukatar zinare, kudi ko lu'ulu'u domin tayi alfahari da danta, yanzu da bata duniya bata bukatar komai illa addu'a.

Dukansu biyun jikinsu yayi sanyi da jin kalaman Jinah. Haka suka cigaba da hira da tayi sanadin gusar da duk wata damuwa tasu, har sai da dare ya tsala sannan kowa ya nufi makwancinsa.

Jinah kasa bacci tayi, tunanin abinda ya faru jiya take, ganin wannan mutumin ba karamin tsoratata yayi ba, ta kasa fahimtar komai game da lamarin, yanke sharawar daukar maganar Dauda tayi kawai ba komai bane face mafarki. Haka tayi ta tunani har bacci barawo yazo yayi gaba da ita.

-Babu abinda za'a yi, kawai ina son a daura auren, to wai ma wa zan gayyata, ba wanda na sani kuma la'akari da abinda ya faru kasan babu wani danginka da zai tako kafa wai da sunan zuwa wajen biki.

Jinah ke fadawa Dauda ana gobe daurin aure.

-Eh, na samu labari duk abinda suka yi maki, kuma har yanzu Mahaifiyata tayi imani da wannan karairayin amma idan muka yi aure, zamu je mu ganta kuma zan canza mata wannan tunanin. Kuma dan Allah kiyi hakuri akan abinda suka yi maki, ki yafe min na rashin kasancewata a wajen domin kareki.

-Me zaka yi kenan? Ai ni naji dadin rashin kasancewarka a gurin, domin ba zan so a dalilina ka samu matsala da mahaifiyarka ba.

-Toh yanzu manta da wannan, ya riga ya wuce, yanzu ne da kuma gobe a gabanmu.

Ya karashe maganar da murmushi a fuskarsa. Ita kuma Jinah fargaba ce duk tabi ta dameta, domin tana ji a jikinta wannan auren ba karamin kuskure bane yinshi. Da sauri ta dawo daga tunanin da take jin daya daga cikin tagwaye ya tsala wani uban kuka, wani lugude zuciyarta tayi kamar zata fito daga kirjinta, tsoro duk ya mamayeta. Domin babu daya daga cikin yaran da ya taba yin irin wannan kukan. Da gudunta ta nufi gurin yaran da ta bari cikin daki tareda Nafisa, Dauda na biye da ita a baya. Tarar da Nafisa suka yi itama na kuka.

-Me ya faru?

Murya na rawa Jinah ta fada tare da karasawa ta dauki danta da yaki daina kuka.

-Na..na..na fita ne yanzu.. naje..debo ruwan sha shine da naji kuka na rugo... shine na tarar da Ayu na kuka...ita..ita kuma Aya ban ganta ba.

Jinah kalmar karshe kawai ta iya rikewa, sai yanzu ta lura da babu Aya.

-Me? _Ta fada da karaji._ Ina 'yata?

-Ku kwantar da hankalinku duka, bazata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login