Showing 42001 words to 45000 words out of 72189 words
Chapter 15 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt
taso in tafi.
-Gidan mahaifina ne ai.
-Ko ma yane ba zan iya ba!
-To nima kuwa ba zaki barni ba, domin na gaji da halin dan uwana, kuma wai kinyi tunani a kan 'ya'yanki?
-Eh, su, zasu zauna a nan, zan roketa dan Allah ta rike min su, idan naje na samu wurin da zamu zauna sai in zo in daukesu. Yanzu dai ni kadai zan je.
-Na fada maka mama tana cikin damuwa.
Cewar Aya da ta bayyana a tsakar gidan.
-Ina zaki je mama? Tafiya zaki yi ki bar mu?
Cewar Ayu cikin sigar son yin kuka.
-Wa ya fada maku haka? Ba zan taba rabuwa da ku ba. Kawai na dan lokaci ne.
-Mama, ba zan taba yafe maki ba idan kika tafi kika barmu, har abada.
Cewar Ayu. Hawaye ne suka fara ambaliya kan fuskar Jinah na tausayin kanta da kuma 'ya'yanta.
-A'a dana ka manta da akwai mutuwa?
-A'a!
-To ka dauka mutuwa nayi, amma kuma zan dawo.
-To ai baki mutu ba, kuma ma ba zaki mutu ba yanzu. Kuma ki daina maganar mutuwa.
-Ka sani dana, mutuwa tamkar kana tafiya ne tsuntsu yayi maka kashi a kai, ka shirya zuwansa ne? A'a, yana zuwa ne ba tare da sanarwa ba. Haka tana iya kasancewa a yau. Wannan tafiyar zan yita ne ba da son raina ba.
-Ko ma dai meye, mu dai damu zaki tafi.
Cewar yan tagwayen lokaci daya. Toshe baki Jinah tayi tana kokarin hana kanta kuka, ita sam bata son taje ta saka rayuwar 'ya'yanta cikin hatsari, haka kuma bata son su tsaneta kan tafiyar da zata yi. Mikewa tayi ta tattara kayansu. Suka nufi kofa da niyyar barin gidan ba tare da ta saurari magiyar da Nafisa ke mata ba.
-Ina zamu je mama?
Cewar Aya, amma maimakon taji amsar mahaifiyarta, wani dake shigowa gidan ne ya amsa.
-Ku biyoni muje!
Da ganin mai maganar, Nafisa ta fadi sumammiya.
-D.D.D...Dau.da!
Cewar Jinah kafin itama ta sume. TOOOOH
-------------------------------------
Welcome back 2 duniyarmu Dauda lol. ๐
Bon week-end ร vous tous ๐บ
See you next chapter ๐
ยฉEl_Ashtar
๐ JINAH (Matar Aljani)๐
by Malik al-Ashtar โ๏ธ
On wattpad ๐ https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New โค๏ธ Story
CHAPTER 17
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).๐ฆwe are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest๐ฆ
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
Idan mutum ya ciri tikitin mutuwa, to fa tikitin na tafiya ne kawai, ko alama babu tikitin zuwa da dawowa wannan wuri wato mutuwa.
Mutuwa wata kaddara ce da babu daya daga cikin mu da zai iya kubuce mata, kuma idan hakan ta kasance, shikenan an gama da babin mu. Ba'a dawowa idan an mutu, ana mutuwa ne sau daya a rayuwa. Mutuwa kamar lokaci ne da ya wuce, ba za'a taba iya komawa ba.
Wannan shine tunanin da Jinah da Nafisa ke yi kafin su ga Dauda a tsaye a gabansu. Firgicin da suka shiga yayi sanadiin tsunduma su cikin wani yanayi. Nafisa ce ta fara dawowa hayyacinta, da sauran yan gidan, Dauda ya basu labarin abinda ya faru dashi. Sun tausaya masa tare da girgiza da jin labarin, sai dai banda Jinah da har yanzu take a sume.
Fara dawowa hayyacinta tayi, a hankali ta fara bude idanunta. Ganinta tayi kwance kan gadonta, koda ta karasa bude idanuwanta taga Dauda kusa da ita, anan komai ya dawo mata.
-A'a! Kwantar da hankalinki, kar ki tsorata, da gaske nine Dauda..ban..ban mutu ba.
Ganin jinah alamar har yanzu bata gamsu ba, ya kara da cewa:
-Jinah da gaske nine, Daudanki, gani na dawo kuma ba zan kara barinki ba, kina tunanin zan iya tafiya na barki? Har abada kyakyawata Jinah!
A wannan karon Jinah, ta fara sakin jikinta sannan ta samu damar bude baki:
-Ta yaya hakan zai yiwu? na ganka fa ba rai Dauda, nayi kukan...
-Ba mutuwa ba nayi Jinah, ina tunanin zuciyata ta tsaya da buguwa na wani dan lokaci. Amma yanzu gani, kuma babu inda zan kuma zuwa, nayi maki alkawari.
A yanzu kam Jinah ta gama yarda da zancen Dauda, tsalle tayi jikinsa ta rungumeshi tare da fashewa da kukan farin ciki, farin ciki sosai take ciki, ba kamar mintuna ashirin baya ba da suka wuce. Yan tagwaye, Nafisa da Sarah ne suka shigo dakin, sakin Dauda Jinah tayi, tare da bin Sarah da kallo amma da mamakinta sai ta ga alamar farin ciki a fuskar Sarah.
-Fada mani, ina zaku je da kayanku dazu?
Dauda ya tambaya. Sarah ce tayi saurin cabewa da cewa:
-Ba inda zasu je, ba wanda zai je ko'ina, yau ranar farin ciki ce. Yan tagwaye ku dauki kayan ku mayar dasu inda suke.
Mamaki, Jinah ta kasa cewa komai. Sarah tana cikin farin ciki da dawowar Dauda, wannan ne dalilin da yasa ta fasa korar Jinah. Tunda mijinta ya dawo, yanzu zata shafawa Abdul dinta lafiya, sarah ta raya a zuciyarta. Tana son zaman Jinah a kusa da ita, amma kuma tana jin wani abu da yake ingizata a kan sai ta kori Jinah.
Shi kuwa Abdul yana daki, ransa a bace, sakamakon duk plan nashi yabi ruwa, kuma Sarah tazo ta tabbatar masa da Jinah da tagwaye babu inda zasu je. Me ya kamata yayi, abinda yake ta maimaitawa kenan. Idan ya cigaba da bata lokaci, to fa tagwaye zasu harbo jirginsa domin dama cen ba wani yarda suka yi dashi ba.
-Ko barka da zuwa ba zan samu ba?
Cewar Dauda da ya shigo dakin Abdul ba tare da Abdul din yasan shigowarsa ba. Wani murmushin karfin hali Abdul din ya kirkira tare da nufar Dauda suka rungume juna.
-Nayi farin cikin dawowarka abokina!
Cewar Abdul.
-To ai ban ga alamar farin cikin ba a fuskarka.
Dauda ya fada cikin sigar zolaya.
-Kawai bana jin dadi ne kwana biyu, amma da gaske naji dadin ganin fatalwarka.
Abdul ya bashi amsa shi ma cikin sigar zolaya.
Dariya suka yi, kafin Dauda yace:
-Zaka bani labarin duk abinda ya faru bayan tafiyata.
-Karka damu, zaka ji komai.
A wannan ranar kowa cike yake da farin ciki banda Abdul, Nafisa ce ta hada masu lafiyayyen girki.
Dauda kuwa sai fira yake da yan tagwaye, koda yazo kan labarin aljanu, tattara hankalinsu suka yi, suka zuba mashi na mujiya.
-Ina da wani kawu da yake mu'amula da aljanu, yasan sirrukansu da dama kamar misali idan aljani yayi tarayya da mutum sannan suka haifi 'ya'ya to yana wahala yaran su rayu, idan kuwa suka rayu, yace yaran ana ce masu yan baiwa kuma ruwa biyu ne, suna da tsananin karfin da babu wanda yasan adadinsa, kuma zasu iya yin abinda aljanu ba zasu iya ba, misali zasu iya karanta tunanin kowane irin aljani.
Hmmm kunji sai shirme nake ta zuba maku ko, ni kaina bansan dalilin da yasa nake baku labarin nan ba, wasu har cewa suke yi kawuna haka haka ne (mahaukaci ne).
Shuru tagwayen suka yi suna juya maganganun Dauda kafin su fara magana tsakaninsu ba tare da bakunansu sun bude ba. Idan abinda Dauda ya fada masu gaskiya ne, kenan Zumana yana boye masu wani abu, domin yace masu basu kai girman da zasu iya karanta tunanin aljani ba.
-Taso muje Aya na nuna maki wani abu, yanzu mun dawo Tonton Dauda (Kawu Dauda).
-Ku dauki iya lokocin da ku so yarori. Dauda ya fada yana murmushi.
-Ya kamata muje mu kure wannan aljanin domin ina tunanin ya mayar damu shawaragai, ya mana karya akan abinda muka iya.
-To idan fa da gaske kawun tonton Dauda haka haka ne?
-Ni bana tunanin haka, amma mu je mu bincika.
-Toh muje yana cikin daki a yanzu.
Tarar da Abdul suka yi kishingide da alamun tunani yake, tun da plan dinsa ya wargaje babu abinda yake yanzu face tunani.
-Yaushe babanmu zai dawo?
Aya ta tambayeshi domin ta dauke masa da hankali, shi kuma Ayu yana kokarin karanta tunaninsa.
Ganin Ayu shuru, yasa Abdul saurin harbo jirginsu saidai kafin yayi wani yunkuri yaji kamar an saka hannu an shake masa wuya, yana kokowar kwatar numfashi, magana yake son yi amma babu dama.
-Zaka fada mamu ne a yanzu inda babanmu yake, ko sai na...
-Me kake kokorin yi, kashe shi zaka yi?
Cewar Aya, da alamar kwalla a idanunta. Abdul ya fahimci Ayu ya gane makirin plan dinshi, tsoro ne ya dabaibayeshi domin yana tsoron abinda tagwayen zasu yi masa.
-Kana son sanin me zamu yi maka? Da farko zaka fita daga jikin Abdul, sannan ba zamu yi maka komai ba idan ka bamu babanmu ba tare da komai ya sameshi ba.
Cewar Ayu kafin ya saki wuyan Zumana da ya lura yana son yin magana. Rokonsu yayi da kar su kasheshi kuma yayi masu alkawarin zai kaisu inda mahaifinsu yake. Ba tare da fata lokaci ba ya daukesu zuwa inda babansu yake, domin Zumana yasan irin karfin dake ga yaran shi yasa ba zai gangancin yi masu abun da zai sa su halakashi. Kai su yayi wurin da kamar sahara, mahaifinsu kawai suka gani a daure, abokin Zumana wata kila ya buya ko kuma ya tafi wani wajen. Koda tagwayen suka yi tsalle suka rungume babansu, Zumana yayi anfani da wannan damar ya gudu. Ko ta kansa basu bi ba, domin ta mahaifinsu suke da yake cikin wani yanayi.
-Bari ka gani!
Cewar Aya kafin ta dora karamin hannunta kan goshin mahaifin nasu, cikin kankanin lokaci Fally ya dawo hayyacinsa, murmushi yayi na ganinsu a kusa dashi.
-Ban taba tunanin zai ci amanata ba.
-Eh mana, ai indai mutum taurin kai ne dashi zai gani...
Kallon da yar uwar tashi tayi masa yasa ya kame bakinshi. Shi baban nasu ma bai damu ba, hasalima dariya yayi.
-Shikenan baba, ba zamu kara yarda da kowa ba idan ba wanda suke kewaye da mu ba, nayi farin cikin ganinka a raye, na tsorata sosai da na gano, yana wasa da tunanin mu ne.
Cewar Aya kafin ta kara rungume baban nasu.
Suna komawa gida, Fally yayi matukar mamaki da takaicin ganin Dauda, a ranar haka ya wuni sukuku. A ranshi ya raya, dole yayi wani abu ganin ya raba Jinah da wannan mutumin, zai bi ko ta halin yaya ganin Jinah ta tuna dashi da kuma soyayyarsu. Bayan yan tagwaye sun bashi labarin ta yanda suka gane makircin Zumana, turasu yayi su tambayi Dauda ko ya taba jin irin makamancin labarinsa a wurin kawunshi; dan Adam da ya kasa tuna soyayyarshi da aljani.
Dauda amsa masu yayi da eh, kuma har da ma tagomashin sanin yanda ake dawo da tunanin. Ya basu labarin komai da yayi masu karyar kawunsa ya fada mashi. Ba tare da wani tunani ba, Fally ya yarda da maganganun Dauda, har ya yanke shawarar da marecen nan zai aikata abinda ya fada masa.
A bangaren Sarah, sauyi sosai ta gani ga Abdul, sai dai tayi tunanin wata kila saboda Jinah bata bar gidan bane ya dan dameshi. Yanke shawarar zuwa ta fahimtar dashi tayi, daman kuma sosai tayi kewarshi, da dadewa kenan rabon da ta jita manne a jikinsa, da wannan tunanin mai cike da tsantsar kunya ta karasa dakinsa.
Tarar dashi tayi zaune, ya kurawa bango ido, hankalinsa na wani gu, a hankali ta rugumoshi ta baya, yayi firgigit ya mike.
-Subhanallahi, ah ke ce? Wallahi har kin tsorata ni.
Abdul ya fada cike da tsoro, ba tare da ya fahimci abinda Sarah take nufi ba. Sai dai lokacin da ta matso kusa dashi ta dora labbanta akan nashi, fiddo ido yayi waje kamar zasu bar cikin kurminsu.
-Meye...haka...saboda..
Tsabar firgici ya kasa hada kalaman da zai fada.
-Na san ka damu ne saboda ta tsaya, amma kar ka damu ba zata kara takuraka ba, zamu iya yin soyayyarmu babu shamaki.
-Baki da hankali ne? Fita daga dakina yanzu yanzu, kin manta ke matar babana ce?
-Daman nasan wata rana zaka ce min haka domin ba sona kake ba, yanzu na tabbatar da wawancina da na yarda da kai.
-Ki fita dan Allah!
Kallonsa take cike da damuwa da da na sani, ba tare da ta hana hawaye wanke fuskarta ba ta fice daga dakin. Da na sani fal a ranta, tana jinta tamkar hankicin da aka yi anfani da shi aka jefar. Abinda bata sani ba, Abdul ba zai iya tuna komai ba da ya faru tsakanin ita da shi, ko kuma in ce tsakanin ita da gangar jikinsa. Shi kanshi ya kasa fahimtar komai, yana jinsa kamar wanda ya samu tabin kwakwalwa na wani dan lokaci ko kuma wanda ya dauki kwanaki masu tsawo yana bacci. Tashi yayi da niyyar zuwa wajen kanwarsa, domin yana son suyi magana. Tarar da ita yayi tare da Jinah, ya nemi guri kusa dasu ya zauna. Kallon da yaga suna binshi dashi yake jin kamar ya aikata wani abu da shi ma bai san meye ba.
-Me yake faruwa? Irin wannan kallo kamar na aikata wani mummunan abu?
-Tambaya ma kake? Mtssww.
Cewar kanwarshi.
-Me nayi?
Ganin basuda niyyar bashi amsa, ya cigaba da cewa:
-Ko ma dai meye na aikata, ina neman afuwarku har cikin zuciyata, ina sonku kuma kun sani, idan na cutar daku to ba da sanina bane.
Ba tare da ya jira jin ta bakin daya daga cikinsu ba, ya bar wurin, tunaninsa a wannan lokacin kawai ya koma Nigeria zai fi, ya kasa fahimtar komai a cikin wannan rayuwar, tunani yake ma idan ya zauna da wanne irin ido zai kalli matar babanshi, bordel rungumarsa fa tayi.
Da marece, ya fara tattara kayansa, ya kuma ce da yar uwarshi ita ma ta hada nata.
-Dan Allah Abdul, mu kara ko sati ne. Kar muyi irin wannan tafiyar ta farat daya.
-A'a. Ya kamata mu tafi, kuma kinga an kusa komawa school.
-Babu baba babu Mama a cen, ko ba komai nan munada yan uwa, dan haka nidai zan zauna anan.
Ta fada da yar hayaniya.
-Dan Allah Abdul, ku kara wasu kwanaki mana.
Cewar Jinah da ta shigo.
-To naji naji, kar ki wage mana wannan bakin naki.
Cewar Abdul ga kanwarsa da yaga tana shirin fara kuka, tsalle tayi ta kankameshi tana murna.
-Yauwa yayana na kaina, irin wanda ba kowacce kanwa ke da irinshi ba.
-Eh ai na jima da sanin haka.
-Banda dai girman kai.
-Ai ba sai nayi ba, tuni kambun sauratana ya riga da ya mayar min shi katoto.
Dariya su duka suka yi, dukansu ukun suna cikin farin ciki, matan a yanzu suka tabbatar da Abdul din da suka sani a baya ya dawo, mai raha da barkwanci.
Zuwan Yan tagwaye yasa Jinah ta bar Abdul da Nafi, taja yaranta da niyyar zuwa su kwanta. Bayan ta kwantar da yaran, ta nufi hanyar zuwa wajen mijinta dake daki, sai dai akan hanyar taci karo da Sarah zaune ita kadai, ta buga uban tagumi, da yanayin damuwa a fuskarta, taso yi mata magana amma ta fasa.
-Me yasa kazo ka tsabbace anan? Jinah ta tambayi mijinta.
-Ba komai kawai yar gajiya ce.
Dauda ya bata amsa, da murmushin tabbatarwa akan labbansa. Canja kaya Jinah tayi sannan ta kwanta kusa da mijinta, taga sauyi sosai a tattare dashi, amma hakan bai dameta ba ko ba komai yana kusa da ita. Bata jima ba tana tunani bacci yayi awon gaba da ita, wani mafarki ta fara yi mai firgitarwa.
-A'a, a'a! Kar ka tabani a'aaa! Wayyooh, ka sakeni, dan Allah ka daina.
Ihu da take yi kenan, a tsorace take, na ganin wannan mutumin da yake yawan tsoratata yayi mata fyade a cikin mafarkin, kuka take yi iya karfinta amma babu mai iya jinta. Ta kai har ta jika zanin gadon da zufar da take yi. Firgigit tayi ta farka, ganin duk halin da take ciki da murkususun da tayi ta yi bai iya tada Dauda daga nauyayyen baccin da yake ba, yasa ta gama kai da gwiwa, haka ta kasance har wayewar gari.
Wannan tsoron kin sakinta yayi tsawon ranar. Wani lokacin ma sai ta dinga jin ana mata rada a kunne ba tare da ganin mai yi ba, wani lokacin kuma mutum take gani yana bayyanar mata yana bacewa akan idonta. Ayyanawa tayi a ranta idan haka ta cigaba da kasancewa to zata haukace.
(....)
-Fada min yaya plan namu yake tafiya?
-Komai yana tafiya daidai! Zumana ya dade da fita daga filin tseren, shi kuwa wannan sakaran Fally tuni ya fada tarkona. Hahahah, bai san cewa yana haka kabarinsa bane.
-Hahahahahaha!, ina alfahari da kaina! Zaka iya komawa, ka cigaba da aikinka.
-Kar ki damu shugaba, wadannan tagwayen da ma duk wani karfinsu nan da ba da jimawa ba zasu zama mallakinmu.
-A'a! Mallakina! Mallakina dai! Na kagu naga cikar burina!!!!!!!!
*****************************""****
After un long moment! J'suis enfin de retour mes vrais ๐ค
Ya hakurin jira? Fatan dai ba'a yi fushi da yawa dani ba?
ยฉEl_Ashtar
๐ JINAH (Matar Aljani)๐
by Malik al-Ashtar โ๏ธ
On wattpad ๐ https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New โค๏ธ Story
CHAPTER 18
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).๐ฆwe are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest๐ฆ
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
Cikin kankanin lokaci, Jinah duk tabi ta lalace, ko ina a jikinta kasusuwa ake gani, rama ta ban tausayi tayi ba tare da tasan wace irin cuta ke damunta ba, eh cuta mana me zuwa ba tare da sanarwa ba ko dalili, abar da kullum muke takatsantsan wajen ganin mun kare kan mu daga kamuwa da ita. Cuta bata bamu zabi. Muna iya wayar gari lafiya amma mu kwanta da ciwo, mu dinga jin wani yanayi da zafi da ba zamu iya misultashi ba wanda hakan zai sa muje asibiti domin a fada mana abinda ke damunmu. Sai dai ita tata cutar Jinah, har likitocin sun kasa ganota, sakamakon ganin abu yaki ci yaki cinyewa Sarah ta dauketa zuwa asibiti sedai an kasa gane sahihin abinda ke damunta. Gashi dai a jikinta da ka gani kasan batada lafiya, amma kuma sanin ciwon nata ya gagara. Ganin haka likitocin suka bata shawarar kawai taje birni domin a kara dubata amma taki a cewarta idan har likitoci sun kasa gane abinda ke damunta wata kila ciwo ne mai wucewa, ba babba ba.
Sedai kuma kullum ciwon nata kara ta'azzara yake, wannan ma ne yayi sanadin jinkirin tafiyar su Abdul.
Halin da take ciki ya tayarwa da kowa hankali ba kamar ma yan tagwaye da suka kasa yin komai har da karfin tsafinsu, a tsorace suke sosai.
-Me kake tunanin shine sanadin rashin lafiyar mama?
Aya ta tambayi dan uwanta.
-Ina tunanin baba ne!
-Me? Hakan ba zai yiwu ba, baka ga shima ya damu sosai ba, kuma shima yana iya kokarinshi ganin Mama ta warke.
-Eh, amma idan fa shine sila ba tare da ya sani ba, baki lura ba hakan ta fara faruwa tun lokacin da ya fara abinda tonton Dauda ya fada mashi zai yi domin mama ta tuna dashi.
Shuru yar uwar tashi tayi alamar